Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 15


Sakon So 15
Viral

💃EPISODE 1️⃣5️⃣

Ahankali Hajiya tabude kofan dakin tashiga ciki tareda maida kofan dakin tarufe dakin duhu kaman tsakiyan dare bata ganin komi amman haka ta lallaba takarasa da tattaba bango harzuwa wajen gadon tazauna abakin gadon ahakali, dan ijiyan zuciya tasauke tana gyara numfashinta ahankali tana saita kanta, murya chan tace “Imrana Hajiya ce, your Mom” dan murmushi tayi, tace “natuna ranan da aka faracewa ina dauke dakai acikin cikina I was so so soo happy, tun aciki ka kasance yaro mai hakuri wanda baida damuwa ko kadan, cikin duka yaran dana haifa aduniya dudda kaine dan fari kai kadaine banma mugun laulayi ba sannan nakudan kama haka kasan me mahaifinka ke yawan kiranka dashi”? Tadanyi murmushi tace “dan baiwa” dan dariya tace “kuma bantaba karyata sunan ba sabida hakika kai dan baiwa ne, you are a God gift, muna tsananin talauci amman muna haihuwanka Allah yafara budama Babanka kofofin samu, tun kana dan yaro kankani 10yrs ka sauke Al Qur’ani mai girma, kana zana JSSCE kaci, WAEC da Jamb duka sau daya kayi kaci, kana applying zama soja sau daya kasamu, bayan kai quitting kanasa hannunka a sana’a Allah yadafa maka kalli company daka gina ayau in just how many years, kampanin ka shine number one a Nigeria dana Africa gabaki daya, kuma kampanin yay suna aduka duniya gabaki daya, imagine kampanin ka nacikin top ceramic company da Forbes sukai publishing, idan kai ba dan baiwa bane kai menene Imran? You are my son Imrana, abin alfaharina, sanyin idaniyata, yarona mai kyakkyawan zuciya, yarona mai taimako, yarona mai jama’a, yaron na yaron Hajiya Sadiy…….” Ahankali taji saukan kanshi akan kafafunta yakama duka hannayenta biyu hannunshi narawa sosai yakaisu zuwa fuskanshi ya kankame muryachanchan kasakasa dan itama Hajiya dabadan ta natsu ba da barataji ba yace “Hajiya” ahankali itama kaman yanda yay magana tace “Imrana” bakinshi da lips dinshi da duka jikinshi bari suke duka cikin wani kalan murya yace “Hajiya I am scared hold me” wani kalan kankameshi tayi yakifa fuskanshi akan cikinta kaman dan yaro jikinshi nawani kalan bari, ahankali tace “shi shiiii I am here now don’t be scared yarona, Mamanka na nan” wani kalan jiniya taji yafara daya tahoda kuka sosai tunda Hajiya take tana ganin tun bayan da Inrana yay girma yaune nabiyu datake ganin kukanshi da rasuwan Muna shima hawaye ne kawai sai yau yaukuma kukane jitayi zuciyanta na breaking babban mutum ke kuka haka Innalillahi wa innailaihi raji’un, cikin kuka yace “Hajiya they killed her sannan suka dauketa sukai hanging nata da igiya a fanka kirjinta na fitarda jini from harbin bindiga, kalli hannuwa Hajiya gabaki daya duk jini Muna da nasu Abdul ne kingani” cikin kukan yadaga hannayenshi yana nuna mata acikin duhun dakin, gyadamai kai tayi ahankali tace “nagani Imrana Allah zai saka maka kaji, daina kuka kada su rainamin kai, kanuna musu kai jarumine jarumina kaji” wani kalan ajiyan zuciya yake saukewa yana shesheka, ilimi education ma yayi ne arayuwa dan idan wasu sukaga irin abin nan da Abee yake cewa zasuyi kodai Ya haukace kokuma aljanu ne nanko is a medical condition call PTSD, zaro hannunta Hajiya tayi tasaka cikin suman kanshi tana shafa kanshi ahankali tace “ya isa hakan nan duk wanda ke neman ganin bayanka Allah bazai barsu ba kuma kasan mene duk wanda aka kashe dan aljanna ne so be happy, I love you so much Imran, nasan cewa bansha gayamaka hakaba sabida bakada magana sosai bakada hira dani, kuma I use to feel ka girma kai babba ne ga manyan yara what’s the point of telling you ina sonka, but I love you deeply Imrana, ina bala’in kaunar ka dako sauro banson yatabamini kai, kome zai sameka gwara yasameni burina kullum inganka lafiyanka kalau, I want you to fight Imran, fight this thing for me ni mahaifiyar ka, for kannenka, for yaranka Abdallah da Kausar, fight for your family, fight for your friends and love ones, tell yourself I am fine! I am okay lafiyata kalau, you are a fighter! Yarona jarumi ne that can fight anything, inasonka sosai Imran” Mama tai maganan duka ahankali takai bakinta saman sumanshi ta sumbaci kanshi jin kukan dayakeyi na raguwa ahankali, murya chan kasa tace “zakasha ruwa”? Girgixamata kai yayi alamun a’a, murya chan kasa tace “shayi fa Kausar ta dafamaka shi zakasha”? Shiru yayi kaman bazaice komiba saikuma ya gyadamata kai ahankali wani kalan hamdala tayi azuciyanta tace “kwanta anan in daukomaka” baiyi ko motsi ba daga jikinta hakan yasa gently ta kwantar dashi akan gado da saurinta tai wajen kofa tana budewa taga tray shayin da kof an ijiye musu da magani balli daya rak akai hakan yasa tadauko tashigo dagashi tazo tadinga bashi shayin tass ya shanye yasha maganin sannan yakara maida kanshi kan cinyanta ahankali take shafa bayanshi ahaka bacci yayi awon gaba da shi.
Kusan 2hrs Hajiya tayi adakin saida ta tabbatar da bacci yashigeshi sosai dan ayanda yake baccin zaka gane yadade baiyi bacci ba yasa ta tashi tareda jan bargo tarufamai, tsugunnawa tayi ta tofamai addu’o’i sannan tabude kofa ahankali tafita daga dakin tasauka kasa, duka yaran tagani afalo Musty shima yana nan Kausar da Abdallah takalla dake kallonta ba kakkautawa tace “In sha Allah komi yazo karshe now kowa yaje yacigaba da aikin dayake” tana maganan kowa yamike yana hamdala Maman Aneesa da Kausar dasu Sajida da Zainab suna kitchen Hajiya tawuce daki tama Musty da Anty Binta alamun su biyota daki, zama duk sukayi Anty Binta tace “Hajiya menene”? Ahankali Hajiya tace “anya auren nan dana yarda akama Imrana namai adalci kuwa? Nasan wannan matsalan na Imrana tun bayan rasuwan Maimuna amman bantaba ganin yanda yake ciwon da idanuna ba sai yau kunsan har yayi yagama babu wanda zai sashi a ido sai likitanshi yauda naganshi jikina yay sanyi” shiru duk sukayi saikuma chan Musty yace “Hajiya aure rahama ne kuma mata garkuwan mijinta ne, saiki iyaganin sanadin auren nan sanadin warakanshi kenan” shiru Hajiya tayi tana kara tuna condition dinshi tace “anya kuwa Musty zancen auren ne yatada ciwon nan fa, nidai barance komiba dan lamarin nan is complicated, abu daya dana nasani shine idan yaji bai iya zama da yarinyar nan zai sauwaka mata bazan hanashi ba idan kuma ya zauna da ita still duk daya all abinda nake cewa shine I will support Imrana dan Imrana is suffering fiyeda tunaninku, My son is suffering” cikeda kulewa dakuma damuwa Anty Binta tace “koma wanene wannan mutumin dayama Ya Imran abin nan wlh wlh bazamu yafemai ba zaisan yataba bawan Allah, tayaya ma Ya zai zauna da wacce ko Kausar dinshi ta girmeta ni kawai sabida tashin hankalin nan yasa nai shiru amman idansu Ya Abdul police suka kamo yaron dazaran yayi confessing agaban duniya ya wankesu Ya Imran kawai ya saketa tunda baison Auren abarshi meyake nema? Yanada yara yanada sanaa yanada family Hajiya, Muna kadai yakeso and he will love her har karshen rayuwanshi, mubar Ya Imran yay kome yakeso Auren nan is nothing but a trash…….” wani kallon da Musty yamata yasa tai shiru da maganan yakalli Hajiya yace “Hajiya kuyi taking komi easy nasan kun damu da Imran, yanzu an gama saka furnitures adakin da yarinyar zata zauna?” Kallon Anty Binta Hajiya tayi tace “angama aikin?” Tabe baki tayi tace “oho ni banduba ba kaima Husby saikace auren soyayay ne dakawani bada kwangilan saka sabbin furnitures adakin kaman wanda suke dakin basuyiba” hararanta yayi yatashi yace “bari naduba dakaina” sama yawuce wani daki wanda dagashi sai kwanan lungun dakin Abee yaje bude dakin yayi dakin yay kyau anmishi wani babypink fenti sannan ansaka wani farin gado mai bala’in kyau, ga carpet akasa ga komi da komi, kusanshine yay komi da kudinshi dan Imran deserve more kome yamai bai biyashi ba aduniyan nan maida kofan yayi yarufe sannan yakalli lungun dakin Abee saikawai yajuya, fita yayi waje yadauki wayanshi yakira Anty Binta sannan yashiga bayan mota yazauna fitowa tayi sanye da mayafi tazo wajen motan bude baya tayi tashiga tana kallon fuskanshi ganin bacinrai karara akai, kai tsaye yace “are you trying kisa Hajiya ta tsani yarinyar da she’s not to be blame for anything daya faru ko itama kinzaci tanason auren ne? Kinsan hakkokinta nawa aka tauye Fatima? Explain your behavior to me?” Shiru tayi tana kallonshi saikuma ahankali hawaye yazubo daga idanunta da sauri ta sharesu tace “kayakuri Husby nasan ban kyauta ba, wlh ko nasan yarinyar is not to be blame for anything kawai I can’t help it ne some part of me nacemin duk ita taja inda at the first place bataje bayin maza ba itada Ya Imran bazasuyi wannan clash dinba, sannan inda badan aurenta ba PTSD Ya Imran bazai tashi yau 4days kenan ko 5 nema dukanmu bamu sashi a ido ba baci basha ba fita,duk ciwon dazai hana Ya Imran fita masallaci ai kasan babba ne, jibi yaranshi yanda sukai zuru zuru Abdallah yayi missing test a school yaron dake medicine sabida all this things, look at Hajiya, look at us kanninshi kowa ya susuce kaman bamuba kowa lost his happiness, I can’t help it but to blame her for everything dudda nasan non of it is her fault I am sorry Husby” bakaramin tausayi tabashi ba ganin yanda take kuka jawota jikinshi yayi ta kankameshi yana bubbuga mata abaya murya chan kasa yace “I know non of this makes sense nasani, but I want you kizama kaman ni duk wani hard situation dakika sami kanki arayuwa think of the positive things that could come out of it, yanzu idan aka wayi gari Auren nan resulted to something meaningful fa mezamuce? Imran yazo yana sonta morethan the way yaso Muna ma” dagokanta Anty Binta tayi daga jikinshi takalleshi kallon irin anya, murmushi yamata yace “yes baby is very very possible, I am a man loneliness is not good for anyman, kinzaci yanda Muna ta mutu feelings din Ya Imran sunbita sun mutu sun tafi ne? No wife basu tafiba, Ya Imran is suffering nasan bai kamata ina gayamiki this ba danke kanwarshi ce but I think you need to know dan kece elder idan su Sajida sukaga bakison yarinyar kina kyaranta suma haka zasu dingayi, abinda yakamata muyi nidake is muzama team and help Imran batare da yasani ba let’s make them come closer, let’s unite them batare dasu kansu sunsan they’re getting closer ba, bakisan kirki da Imani dakuma kyautatawan Yayanki bane yasa Allah yamishi kyautan fresh yarinya rana tsaka ba, is it easy mutum mai shekarunshi yasami danyan yarinya jagab haka shekara 19 bakisan irinsu ne sukafi shiga zuciyan babba tashi dayaba? Yanzu idan ya auri bazawara ko wata mai shekaru haka is not like I am saying bazai sotaba no zai sota but time phase dazai dauka to fall in love with yarinya karama will be faster than time phase dazai dauka to fall in love with Babba mai shekaru, budurwa of 19 are sweet charming an shiga rai” turobaki tayi tace “wannan daka dage kanamin wannan bayanin hope ba shiri kake kamin kishiya da yarinya Yar 19yrs ba” wani dariya maganan ta yabashi baisan lokacin da yay Yar dariya ba yace “mata da kishi Allah dai ya yayemuku yanzu dai kingane what I am saying, I want us to be team both not team your brother kadai” murmushi tamai ta rungumeshi tace “thank you Husby for enlightening me, na amince and I am ready to support you and make things work daga yanzu nadawo team both” murmushi yamata yace “da this weekend zamu koma gidanmu an gama fentin but for this our mission nakara miki one week” dariya tayi sosai tana murna yace “muje kiga gidan daganan ma nadanyi kin gane ai” Ya kashe mata ido daya” dariya tayi tafito suka koma gaba suka bar gidan.

Asabar!
Karfe 4:30 yabude kofanshi yafito yana sanye dawata white jallabiya dayasha karin guga yasaka hula fara sai wani kalan kamshi yake mai kwantarda hankali, bakaramin kyau yayi ba saida kana kallon kwayar idanunshi zakaga yadan fada sosai yarame, direct dakin Hamza yashiga bubbuga bakin gadonshi yayi Hamza yabude idanu ahankali ganin Ya Imran har sake goge idanu yayi zaiyi ihu yatuna maganan Dr, “bazaka tashi bane” Abee yay maganan ahankali murmushi yayi ranshi fess yatashi da sauri yace “natashi Yaya Imran” ficewa Abee yayi daga dakin yashiga dakin Abdallah dake bacci Abdallah daya bude ido yaga mahaifinshi saura kadan yafada jikinshi yadaure baiyiba yatashi yawuce bayi yana murmushi kaman anmai kyautan dream car nashi c300, dakin Kausar yawuce ya kunna wuta yana kallon yanda ta kudundune abargo dakinta kaman fridge AC yafara kashewa sannan yabubbuga gadon yana karbe bargon hakan yasa tabude idanunta ganin Abee dawani kalan sauri ta mike tsaye daga gadon kawai tafada jikinshi dan lumshe ido Abee yayi yabubbuga bayanta, sakinshi tayi tana murmushi tace “Abee sorry na rungumeka banyi wanka ba mafarki nayi na rungumeka saisa ina ganinka nayi” hancinta yaja yace “talkative” washe mai baki tayi yajuya yafice daga dakin kap yatada sister nashi duk wanda yaganshi saikaga smile of happiness akanshi sauka kasa yayi zuwa dakin Hajiya dayaga wutan a kunne ganinshi batasan lokacin data shafe addu’an datake ba tace “zaku wuce masallacin”? Gyadamata kai yayi yace “eh Hajiya” murmushi tayi tace “incedai wannan mayen baccin Hamza yatashi” dan murmushi yayi yace “yatashi” daidai nan daga waje Hanza yace “to natashi Hajiya kuma naji abinda kikace” murmushi yayi yafito daga dakin Hajiyan suka fice Hajiya tadaga hannu tareda godema Allah daya fito yau dakanshi.

Hi GGM, did you know just because you act different baya nufin kai mahaukaci ne, sometimes is just PTSD! Now check on your family members and share ❤️

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply