Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 17


Sakon So 17
Viral

 

Wani kalan faduwa da gabanta yayi saida taji kanta yasara dum, hannunta Baba yakama yace “namiki laifi da dama Lujain tun kina Yar kankanuwan ki, lokacin banda courage na kallonki ne sabida banda abinda zan kuladake, wannan auren ma bawai dan Gwaggo tadage akai yasa na yarda ba is because that’s the only right thing I can do for u, dakina karama I couldn’t do anything but yanzu I can do anything to protect you, your image, I can do anything dan inga society ya girmamaki, yakuma darajaki, nasan bakisan mutumin nan ba shima baisanki ba but abu daya dana sani shine bazai cutarmini dake ba dan shima yanada kamarki kokuma nace wacce tafiki agida, he’s a father so he can handle you, munyi bincike akanshi shaida daya bamu samu akanshi na cewa mutumin banza bane dan haka inaso ki zama mai tsoron Allah ki manta da komi kicigaba da rayuwanki amatsayin matarshi kinji” wani kalan kukane taji yana tasomata amman kotari takasa tana tsoron Baba dako gardama batayi agabanshi Baba nada dukan yara yasha dukanta dasu Samira ita kuma babu abinda take tsoro kaman duka yanzu wayau Gwaggo dama tamata dasu Ya Samira, sai alokacin hawaye yazubo mata dasauri takai hannunta ta share, amman ina bini bini saisu zubo ta share sunyi tafiya mai nisa sosan gaske sannan sukakai wani mahaukacin estate dinsu bude musu gate akayi dan ansan da zuwansu har gidansu Abee gateman yabude musu gate suka shiga yamaida gate yarufe yatafi ciki da gudu duk suna zaune cikin motan Musty yafito shida Harun duk suna sanye da manyan kaya sai Anty Binta da Matar Harun mai suna Amina sunci atampopi masu kyau sunsha aiki kana ganinsu kama hadaddun mata masu kudi, bude mota su Baba sukayi sannan Baba yasa hannu yafito da Lujain daga cikin mota, gently tasauke kafarta akan interlock na compund din wani kalan sanyi taji yashigeta kaman zata sandare dan har hanjinta taji sanyin, ahankali Baba yaja hannunta tsayawa tayi kikam dayasa Baba yajuyo yakalleta wani kalan fashewa tayi da kuka tana girgizama Baba kai dan sai yanzu ta yarda wani wuri fa yakawota tace “dan Allah Baba karka kaini wlh bansan su ba, Baba baran kara rashinji ba, ban kara zama ba dan kwali, ban kara zama da towel, ban kara aran wayan Ya Samira wlh Baba zanmabar wajen Gwaggo nadawo kwana adaki dasu Ya Samira amman dan Allah kada ka kaini ko’ina mukoma gidanmu” Shi kanshi Baba sanyi jikinshi yayi baitaba kawowa cewa Lujain ce zata fara aure acikin duka yaranshi ba, amman yadaure yay ta maza wani mugun kallo yamata yace “let’s go my friend banson shirme” kafafuwanta har girgidi suke kaman maijin fitsari tabishi kanta akasa tana kuka sosai duksu Anty Binta dasuke dan nesa dasu na kallonsu afuskansu kadai zaka gane suma jikinsu yay sanyi jin maganganun Lujain, karasawa gabansu su Baba sukayi da fara’a aka gaisa sannan sukace bismillan ku, Baba na rikeda ita suka shiga falon sake tirjewa tayi ajikin kofa ganin mutane afalon cike kowa kuma su ake kallo, Hajiya da duka yaranta, sai Abdallah Kausar da matan Ibro sai Abee dake zaune kan 3 sitter da Hajiya ke zaune kai dan anan ta umurce shi da zama yana sanye da shadda anmai dinkin jumper da hula akanshi yay wani kalan kyau kaman kasace shi kanshi na kasa dan shi kadaine adakin wanda ba kofan yake kallo ba, ganin mutane na kallonsu gashi ta turjemai yasa Baba yajata da karfi but karfin dat is not obvious shigowa Anty Binta da Amina sukayi suna ayiriririiiii kujerun dakenan empty su Baba suka zauna da Lujain na kusadashi kanta akasa tana kuka sosai, cikeda dattaku Hajiya tai murmushi tace “barkan ku da zuwa ah’ah amaryan tamu mai kuka ce kodai Alhaji kun tsunguleta a hanyan zuwa ne” dan murmushi Baba yayi yace “munsameku lafiya Hajiya” murmushi tayi tace “lafiya lau” cikeda dabara ta taba kafan Abee hakan yasa anatse yadago kanshi yakalli Baba ahankali yace “ina yini” murmushi Baba yayi shima yace “Alhamdulillah Imrana” kayan ciye ciye aka shiga cika gabansu dashi murmushi Baba yayi yace “Alhamdulillah sassannunku da aiki an gode Allah amfana” mikewa tsaye yayi ahankali sannan yakama hannun Lujain da kanta ke kasa tana kuka har lokacin yadagata yaja hannunta tana biyeda shi Dan murmushi Hajiya tayi tamike tsaye ahankali tareda komawa gefe, gently Baba yazaunar da Lujain kusada Abee kuka take ita bama gani takeba balle tasan meke faruwa hannunta da Baba kerike dashi yadauka yakama na Abee da kanshi ke kasa yasa aciki dudda kukan da Lujain take but she was able to understand hannunta baya cikin na Baba kuma, wani kalan warm serene cold taji akan hannun Abee dake shiga cikin fatar hannunta, matse hannun Abee Baba yayi kan nata hakan yasa Abee yarike hannunta gam addu’a Baba yatofa a hannayen nasu biyu da duka Ya rirrike yahada sannan yakalli fuskan Imran dake kasa ahankali yace “Imrana” gently Abee yadago idanunshi yadaura akan na Baba, ajiyan zuciya Baba yasauke dan Abee nada wani kalan kwarjini da charisma da idan yakalleka dole kagani yace “ga diyata nan Lujain nabaka ita amana, bansanka ba amman na yarda dakai zuciyata ta aminta dakai sama da yanda kake tunani, karikemini ita amana daga yanzu rayuwanta komi nata na hannunta ne banda iko akanta saikai karike amana kaji Imran” Abee jiyayi kanshi yamai nauyi ganin yanda Abee ke kallonshi amsa yake jira yasa ya gyadamai kai batare dayay magana ba dan baijin zai iya magana ba, sakesu Baba yayi yatashi yajuya yakalli Hajiya hannunshi yahade yace “Hajiya ke mahaifiyar muce nan gabaki daya ga diyata nan nakawo muku marainiya ce tun kafin a haifeta mahaifiyarta tarasu, a hannun mahaifiyata ta girma takuma tashi, Lujain goyon kakace, nasan zakuga abubuwa da dama na shirme da rashin wayau dakuma rawan kai ina rokonki da idan batai daidai ba ki tsawata mata dan kin isa ne, sannan ku dorata akan hanya mai kyau, Alhamdulillah nazo na ganku duka naji dadi hankalina ya kwanta dan Lujain tabar family tane tazo tasami even a bigger family dan haka kurikemini amana nan ta, tunda take aduniya yaune rana na farko da barata kwana tareda kakarta ba kokuma agidansu ba ko tafiya bata tabayiba, dan Allah kuyi hakuri da ita sannan ku dorata kan hanya madaidaiciya” wani kalan kuka Lujain take tafara kokarin cire hannunta daga nacikin Abee kallon hannun nata dake cikin nashi Abee yayi saikuma yadauke kai batare daya saketa ba dayaji takeson yayiba, ahankali Hajiya tace “na dauki amana in sha Allah bazamu cutar da Lujain ba namaka wannan alkawarin” murmushi Baba yayi yace “to mungode mungode bari mukoma gida saida safen ku” cikeda girmamawa Hajiya tace “Muma mungode saida safe agaida kowa da kowa” tashi su Baffa sukayi Baba yajuya shima zai tafi jin da gaske Baba tafiya zaiyi yabarta agidan nan wani kalan fizge hannunta Lujain tayi daga cikin na Abee ta tashi da gudu ta kankame Baba tabaya tana kuka sosai har gyalenta na zamewa kasa lafiyayen gashinta da aka kama da ribbon mai kyau ya bayyana cikin kuka sosai tace “Baba dan Allah dan Allah kada katafi ka barni wlh ban sansu ba, wlh kuwa” bata damu da da karfi take maganan ba tarike Baba gam cikin kuka tace “Baba wlh baran kara maka barna ba, Baba nace baran kara aran wayan Ya Samira ba saika siyamini tawa Baba dan Allah kada kabarni anan” tahowa su Baffa sukayi ganin yanda ta rirrike Baba tabaya yakasa motsi kaman zata karyashi Baffa Hadi yace “ke cikashi” cikin kuka ta makemai kafada tace “dani zaku tafi Baffa” Musty daduk suke kallon drama yay murmushi yakalli Anty Binta da Amina hakan yasa suka taho wajen Anty Amina tace “yakuri Lujain ki barsu sutafi” wani kalan ihu tabuga da saida yasa for the first time Abee yadago kanshi yadaura akanta, dudda he’s not seeing her face directly but yaga yanda goshinta har zufa yake ketowa kuka harda majina ga gashinta da aka gyara tsabagen yanda take jujjuyar da fuska abayan Baba harya hargitse babu lallashin duniya da Anty Binta da Amina basuyiba har Hajiya tasa baki ina taki sakin Baba da Baba ta kular dashi wani kalan tsawa yadaka mata Lujain! Yanda taji saukan tsawan saida ta sakeshi tai tangal tangal tama fadi akasan tiles na wajen jikinta narawa sosai tana girgizama Baba kai, kowa na falon su yake kallo jin yanda Baba yadaka mata tsawa, kaman Baba zai daketa yace “stand up go back to your sit ki zauna” juyawa tayi da sauri tana rarrafe ta tashi yanda ta tashi takoma tazauna zaka dauka mala’ikan mutuwa tagani, tahowa Baba yayi azuciye batasan lokacin datai pulling hannun Abee ta kama hannun Abee gamgam ba ta boye fuskanta akafadanshi kaman zata shide tace “Baba dan Allah kayakuri karka dokeni” yanda jikinta ke bari da yanda take numfashi kaman zata shide Abee could hear it, yanda tarike hannun Abee gam tana boye fuskanta abayanshi Musty yakalla daidai itama Anty Binta takalleshi kashe mata idanu yayi tayi murmushi Baba zaiyi magana Hajiya tace “aaaa ina ake haka Alhaji? Har gidana zakazo ka firgitamin diya sabida tayi kuka kan katafi da ita bata sanmu ba yo ai batai karyaba babu wanda tasani anan, kataba ganin inda aka rabu da amarya lafiya dama ai sai sunyi yan koke koken nan, karma kafadi abinda kakeson fadi dan nasan fada zaka mata” dan murmushi Baba yayi akunyace yace “shikenan to Hajiya saida safen ku” anatse kowa yace “Allah bamu alkhairi” fita sukayi hakan yasa ahankali tasaki hannun Abee sannan takoma gefe takifa kanta akafa tana kuka sosai tashi Abee yayi yawuce sama Hajiya tabishi da kallo tashi Kausar itama tayi tawuce fuuuu sama ahankali Hajiya tazauna kan kujeran daidai nan mai gadi yashigo dawasu jakunkuna manya guda biyu yace “Hajiya ina za’a saka wayan nan” Hamza ta kalla tace “jeka kaimata dakinta” gyadama Mamanshi kai kawai yayi yawuce sama ahankali Hajiya takai hannunta tadaura saman bayan Lujain cikeda lallashi yace “kiyakuri kowace mace saitaji irin abin nan dakikeji idan aka kawota gidan mijinta, amman zakigani nan da sati kin warware kin daina tunanin gida ko” ta tambayi su Anty Binta dake tsaye akansu sukace “hakane” murmushi Hajiya tayi tace “ku kaita dakinta Binta” Gyadamata kai Binta tayi dagata itada Amina sukayi suka wuce da ita sama Mama takalli su Sajida da Zainab tace “ku kai abinci dakinta dan ba lallai taci abinci ba” dan tabe baki sukayi saikuma suka tashi itadai Maman Aneesa na zaune tana magana da yaran tace “Aneesarh takarasa maganin ta” gyadama Hajiya kai tayi takalli Abdallah dayay shiru tace “kaikuma fa dakai shiru haka”? Dan murmushi yayi yace “bakomi ni zuwa zanyi ma na kwanta inada lectures gobe” Maman Aneesarh tace “dole abama Abdallah award din shine mai fara zuwa ya kwanta agidan nan kafin kowa” murmushi yayi yawuce abinshi.

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply