Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 21


Sakon So 21
Viral

 

Abee na zaune a office nashi wuraren 2:30 aka tura kofan office dinshi batare da anyi knocking ba aka shigo dago kanshi yayi kallo daya yama Musty dake sanye da manyan kaya yana kalllonshi yana wani makirin murmushi yadauke kai yacigaba da abinda yakeyi, maida kofan Musty yayi yarufe yakaraso gaban table yace “Ango Ango kai kaga wani glowing dakakeyi ne irin na amarcin nan” dan dariya yayi ganin ko kallonshi Abee baiyiba Musty yace “no bama wannan ba tell me everything about the first night” wani mugun kallo da Abee yamai yasa yawani kalan kyalkyace da dariya yace “inda kallo na kisa da yanzu idanunka sun kasheni yafi sau dari” dauke kanshi Abee yayi yacigaba da duba papers din dake hannunshi yace “idan abinda yakawoka wajena kayi kenan kabarmin office please” hadiye dariyan Musty yayi yakalli Abee yace “to ka ijiye takardun ka kallen mana muyi magana” dan ijiyan zuciya Abee ya sauke ya ijiye takardun ahankali yakalleshi tareda folding hannunshi a kirji cikeda tsokana Musty yace “yaushe zaka komarda Amarya gidanka? Kasan gidan Hajiya bazai barka kai amarci da kyau bako”? Akufule Abee yatashi pappers din yashiga tattarewa yabar wajen yakoma kan lumtsetsen couch na office din yazauna ahankali yacigaba da abinda yakeyi anatse shikuma Musty yana zaune inda yake yana kallonshi yakai kusan 10min sannan yatashi shima yazo yazauna kusadashi batare da Abee yakalleshi ba yace “zan barmaka office din gabaki daya fa Mustafa” murmushi Abee yayi yace “nasan zaka iya, all jokes apart magana nazo muyi Imran look at me” yanda yay sounding serious yasa Abee yadago idanuwanshi ahankali yakalleshi alamun ina jinka. Ahankali Musty yace “Nasanka to be someone da kana taimako kana tsayama wayanda bama kasansu ba kabi musu hakkinsu ka kwace yancinsu, yaran dakai sponsoring education nasu bansan iya adadinsu ba saisa yauma is still on that matter nakeso nida kai muyi maganan fahimta best friend” shiru Abee yayi still yana kallonshi anatse Musty yace “I know bakason auren nan and you don’t consider this girl your wife” daukekai Abee yayi hakan yasa dasauri Musty yace “hear me out mana Imran bawai inaso nace you should consider her matarka bane wlh ko daya I accept that take as long as u want kafin kai accepting nata kokarkayi accepting nata ni duk dayane awurina but as your friend reminder na musulunci nazo namaka” shiru Musty yakarayi sannan yakalli Abee yace “I know you better than anyone nasan yanda kake idan bakason abu yanda kake wulakanta abin, banso kama dat small innocent girl that kind of treatment Imran, bance kai accepting nataba as your wife but inaso ya zamto ka kiyaye hakkokinta na musulunci, lafiya, ci, sha, sutura and respect, duk kabata kaga idan ka wulakanta yarinyar nan and neglect her mutanen gidanku kap haka zasu mata suma, remember bata tareda dan uwanta ko daya, remember kaman yanda su Kausar basuda mama itama batadashi su Kausar sunma fita gata in the sense sunsan mahaifiyarsu banda haka kaga ga all your sisters and family sun taso cikinsu itako has only her grandma! Just grandma, inaso kajata ajiki be nice to her please Imran, saikuma second abu dazan fadamaka is school idan all this issue yakara sanyi saika nemi wani good school kasata since school datake sun koreta saita fara wani sabo mai kyau kaji Imran that’s the only abu da dama zan maka magana akai kaji”? Dan dauke kai Abee yayi kaman bazaiyi magana ba saikuma chan yace “naji” murmushi Musty yayi yace “to hurry ka karasa abin nan gashichan ana kiran salla muje muyi saimu wuce gida”.
**

Koda takoma daki kayan tacire tashiga bayi tana wanke kafanta wajen dan ja yayi dan bawani konewan kirki bane towel ta daura tafito tana kallon kulan abinci da tray shayi dataga an kawo mata dabatasan waya kawoba, zama tayi tahada shayin dakanta ta shanye tass sanan tacinye duka chips da egg dake kulan ta shanye farfesun shima tass rabonta da abinci tun jiya hawa gado tayi ahankali sai bacci koda Anty Binta tashigo ganinta kwance kan gado da towel yasa ta murmushi ta kwashe kayan abincin tafita, wajajen azahar ta tashi tashiga bayi da ruwan sanyin still takara wanka tafito tana atishawa hijabi tasa tai salla sannan tazauna kawai tai shiruu tana kallon dakin, duniyan kawai yamata ba dadi, komi ya tsayamata chak, gidan yamata wani kala kawai sai hawaye sosai tayi kuka jin ana taba kofanta ana magana yasa tashare hawayenta da gudu, Anty Binta ne tashigo tareda wata mata kallo daya Anty Binta tamata tagane tai kuka amman tai kaman bata saniba tace “anzo aunaki tashi to” tashi tayi ba musu matan ta aunata tsaf sannan suka fice itada Anty Binta chan saiga abinci wata Yar aiki takawo mata dauke kai tayi wasu hawayen sun sake zubomata that means bara’akaita gidansu ba kenan, tsanan abincin taji tayi jin ana kiran la’asar yasa tawuce bayi tadauro alwala tazo tai salla, jin dakin yamata wani kala sotake tama danga hasken rana babu yasa ahankali ta tashi tai wajen window ta yaye labulen tareda bude window wani kalan iska ne yabuge fuskanta ahankali tasauke ijiyan zuciya tadade tsaye wajen sannan tajuyo akwatin da aka kawo mata tai wajensu tabude duka, robobin daddakkun magungunan ne daban daban da sauri ta maida tarufe dan barata shaba magungunan nan da badadi dayan tabude ganin su chocholate minti biscuits da yogurt daya cika akwatin yasa batasan lokacin datai murmushi ba tawani fashe da kukaba takifa kanta kan kafa ahankali tace “Gwagooooooo” sosai take kuka da sunan Gwaggo, chocholate guda uku ta dauka sannan tarufe akwatin tasaka wani white slippers pink dake dakin masu kyau daidai kafanta tabude kofa ahankali tafito tana mamaki dataji gidan tsit babu ko muryan yara bin ko’ina take da kallo hartakai stairs tafara sauka tana bude chocholate dinta wata Yar mata tagani afalo tana shara matan jin tafiya yasa tadago kanta dan murmushi tayi ganin Lujain tace “ina yini amarya”? Dan turobaki Lujain tayi jin ankirata da amarya takarasa saukowa ahankali tace “ina masu gidan”? Murmushi matan tayi tace “duk sun fice nan makota yau ana sunan matan Kamal” shiru Lujain tayi sokawai take tafita waje juyawa tayi tafara tafiya zuwa kofa itadai Yar aikin tacigaba da sharanta tana mamaki ina Amaryan gidan nan zata daga ita sai towel akirji babu ko hula, bude kofa ahankali Lujain tayi tana kallon babban tsakar gidansu dayaji flowers ahankali tashiga sauka dagakan dakalin tana kallon gate dababu kowa awajen wani zuciyan nacemata tawuce tabude tafice abinda ta tafi gida wani zuciyan kuma nacemata karta fita kotaje gida daga Gwaggo har Baba zasu kara dawo da itane, tafita ma mutane su ganta ayita kallonta ana kiranta Yar iska tunda yanzu duniya gabaki daya sun santa, hawaye taji sunzo mata tunawa datayi abinda yasa tamazo gidan nan in first place, karasawa tayi wani wani plastic chair dake wajen flowers na compound din ta zauna takai chocholate nata baki ta balla tana taunawa still tana kallon gate din, kaganta kaman wata aljana fatarta fari kal kaman jini zai fito idan katabata ga pink towel da slippers ajikinta she looks so adorable and very cute.

 

Tana nan tanacin chocholate din tana kallon gate aka bude karamin gate dasauri aka shigo mai gadi ne baima lurada itaba key gate yacire da saurinshi sannan yashiga bude gate din sai zare idanu take innocently tana kallo tanakai chocholate bakinta tana balla.
Ana bude gate din daga Abee har Musty dukansu hangota sukayi zaune kan plastic chair daga ita sai towel babu dan kwali akanta hannunta rike da 3 different chocolate data bare tana ballansu all at the same time, da sauri Musty yadauke kanshi yaciro wayanshi yana dannawa kaman baiga komiba shikuma Abee kuri yayi yana kallonta yanda tadage tana kallon wajen gate din har mikarda wuya take kaman wata jimina tanacin chocolate kaman akwai abinda ta ijiye waje, jan motan yayi ciki tabi motan da kallo batare data gane waye aciki ba dan bata iya gani mai gadi yashiga kulle gate din.
Ta glass Abee ke kallonta batare daya fito ba kozata tashi tashige ciki amman ko gezau sai kallon gate din dama tacigaba da yi tanacin chocholate dinta, dan kallo Musty yayi ganin yana danna wayanshi yasa batare daya kashe motanba yace “I need to get something for Hajiya bari na karbo prescription din mutafi” “okay” Musty ya amsashi atakaice hakan yasa Abee yabude kofa yafito tanacikin kallon gate taji karan bude kofan mota hakan yasa takalli wajen da sauri hada idanu sukayi itada Abee dake mata wani kalan kallo wani kalan faduwa gabanta yayi takasa cigaba da tauna chocholate din datakeyi takasa tashi takasa zaune takasa komi, sai kirjinta dake bugawa dum! Dum! Dum! Daidai Abee yakai gabanta batare daya kalleta ba babu alamun wasa a voice nashi yace “follow me” yay gaba tashi tayi hakanan kawai taji jikinta yafara rawa falon itama tashiga amman taga haryay stairs hakan yasa tabishi abaya agaban dakinta taga ya tsaya yay folding hannunshi akirji yajuyo yana kallonta, jitayi legs nata are shaking amman haka tadaure kanta akasa takaraso ahankali gaban dakin ta tsaya tana watsa da yatsunta cikin sanyin murya da yet zaka jishi a zafafe yace “bakida kayan sawa ne”? Girgizamai kai tayi batare data dago kanta sama ta kalleshi ba, cikeda dan zafi Abee yace “then why are you sitting outside da towel”? Dan tabe baki tayi irin na masu shirin yin kuka jin yanda yake mata magana kaman zai daketa ahankali tace “ai kaya tsungulina sukeyi, haka nake zama awajen Gwaggo naa” wani mugun kallo yamata yace “look up” ahankali gabanta na racing tadago idanunta dahar sun cika da kwalla sosai takallai, babu wasa kan kwayar idanunshi yace “this house yamiki kama da gidanku?” Girgixamai kai tayi daidai hawayen na zubowa sharrr yace “then this should be the last time dazaki daura this thing kifito waje understood”? Gyadamai kai tayi ahankali saikuma tajuya da sauri tabude kofan dakinta tashige tareda fashewa da kuka sosai tafada kan gado, yakai kusan 1min tsaye wajen yanajin karan kukanta yadanja tsaki yawuce dakinshi yarasa mesa yakemata magana with anger he’s so pissed of ne wlh.
Wanka yayi ya shirya tsaf cikin jeans da Riga yadauki wasu jersey yahada awani karamin workout bag dan yanaso yabuga kwallo bayan magrib yafito batare daya kalli kofan ba yawuce yasauka kasa.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply