Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 22


Sakon So 22
Viral

Wajen motanshi yayi yabude yashiga ciki yana jefa jakan daya dauko baya yatada motan Musty na kallonshi baicemai komiba saidan murmushi dayayi tareda gyara zamanshi, ganin ba hanyar pharmacy sukayi ba sai barrack dasukayi zuwa filin kwallo yasa Musty kawai murmushi yace “maganin Hajiya fa” changing room Abee yawuce batare daya amsashiba Musty yabishi abaya suka shiga shidayake Musty nada kayan chanzawa a locker shi na changing room shiryawa sukayi suka fito suka shiga field sosai suke buga kwallo team na Abee daban nasu Musty daban Abee saicin kwallon yake kana gani kasan ya iya kwallo sosai ya kware, saida aka fara kiran sallan magrib sannan suka tashi wanka sukayi suka maida kayansu sannan suka wuce mosque.

 

Saida akayi isha’i sannan yadawo gidan kashe mota yayi yafito yana magana da waya akan kunnenshi, yashiga falo anan ma yake gani suma basu dade da shigowa ba, samin waje yayi yazauna yakarashe wayan dayakeyi sannan ya amsa gaisuwan kannenshi daidai nan Hajiya tafito daga dakinta da charbi a hannunta tace “waini tunda nashigo banga Lujain ba, ke Kausar tashi kije ki kiramini ita nasata a idanu” tashi Kausar tayi ahankali tawuce sama, Hajiya takalli Abee tace “dazu fa kaman nace itama ta shirya tabimu sunan saikuma dai na bari dan bangaya maka ba” shiru Abee yayi baice komiba dan baimaso anamai magananta daidai nan Kausar na saukowa tace “tana wanka Hajiya” amman nafada mata daidainan Anty Binta takawoma Abee shayi zubamai tayi a mug tabashi karba yayi ahankali tace “Yaya nakawo maka dinner”? Girgixa mata kai yayi yace “no” saida ya shanye shayin tass sannan yatashi yace “Hajiya bari naje daki” “to Imrana Allah bamu alkhairi” wucewa yayi yahau stairs yayi sama yana gab da karasawa gaban dakin Lujain Lujain tabude kofan tadakinta tafito tana sanye dawani doguwan riga black tana rawa rawan sanyi dan bala’in sanyi takeji gashin kanta ya dan hargitse ga lema leman ruwa tagaban gashin, juyowa tayi bayan ta maida kofan tarufe karaf suka hada idanu da Abee dake tahowa yana tafiya one one kaman wani sarkin kasa, wani kalan mugun faduwa gabanta yayi dawani kalan sauri har hannunta na rawa tabude kofan dakin takoma cikin dakin dasauri tareda maida kofan tarufe daidai wani atishawa na zuwan mata tayishi, bin kofar dakin nata Abee yayi da kallo yawuce yashiga corridor yabude dakinshi yashiga.

Ahankali tazauna kan gado tai shiru tadade zaune ahaka saikuma ta tashi tacire rigan tadauko towel tadaura tasake dawowa ta zauna bakin gado tasakeyin shiru tanajin wani kalan yunwa, wani kalan kwanciya tayi kaman marainiya tana kallon kofa bude kofan nata akayi aka shigo saida tadan firgita ganin Anty Binta ne yasa dasauri ta tashi Anty Binta tace “kince ma Baba baki kara zama da towel amman kinata zaman ko” sauke kanta tayi ahankali kasa tana wasa da yatsanta batare datace komi ba, Anty Binta takaraso gaban gadon tace “Hajiya na kiranki mesa bakizo”? Dago kanta tayi ahankali takalli Anty Binta saikuma takalli kofan dakin takasa cewa komi, kallon kofan Anty Binta tayi itama ganin kofan take kallo saikuma ta kalleta tace “Ya Imran yahanaki fitowa”? Gyadamata kai tayi ahankali hawaye na gangarowa daga idanunta wani kalan mugun tausayi Anty Binta taji tabata hakan yasa gently tazauna bakin gadon bama tasan mezata ce ba tace “ki yakuri kinji Lujain” kaman jira Lujain take fadawa jikin Anty Binta tayi ta kankameta sai kuka, dan lunshe idanu Anty Binta tayi tabudesu zatama Hajiya magana tagayama Ya Imran yanemi makaranta yasata tun wuri kan wani abu yasami yarinyar mutane gashi babu mai kulata daga ita sai Hajiya ke kulata yanzu idan ta tafi next week yazatayi, tadade tana kuka sannan Anty Binta tace “Ya isa to” Anty Binta takai hannunta kan fuskanta tana sharemata hawayen tana mamakin taushin fuskanta da kumatunta kaman fuskan Yar jaririya, ahankali Anty Binta tace “kinajin yunwa ko”? Gyadamata kai tayi cikin kuka, murmushi Anty Binta tayi tace “to bari naje nakawo miki abinci da shayi, stop crying now konai fushi” hadiye kukan tayi tana kallon Anty Binta, murmushi Anty Binta tayi tajuya tafita daga dakin bata wani jimawa suka dawo itada Kausar daketa kumbure kumbure tadauki tray na kayan shayi itakuma Anty Binta tadauki flask guda biyu Kausar na ijiyewa ko kallonta batayiba tajuya tafita itakuma Anty Binta ta ijiye tace “to sauko kici” ahankali tasauko tana dake goge hawaye.

 

Zaune yake gaban desktop nashi yana wani aiki dagashi sai singlet dawani dan gajeren wando wayanshi ne yay kara hakan yasa yadauka ganin Hajiya ne yasa yakai wayan kunnenshi yana mamakin meyafaru take kiranshi.
“Ka sameni adakina Imrana” ta katse wayan, ijiye wayan yayi yatashi tareda daukan jallabiya yasaka sannan yasa slippers yafito batare daya kalli kofan dakin Lujain dayake iyajin maganan Anty Binta aciki ba tana mata fira wucewa yayi yasauka kasa Hamza da Abdallah yagani a falo suna buga video game suna ganinshi duk suka natsu dakin Hajiya yawuce da sallama yabude kofan yashiga Hajiya na zaune bakin gadonta tana kallonshi hakan yasa yakarasa ciki yazauna kan lallausan carpet na tsakar dakin ahankali yace “gani Hajiya” karasa jan charbi datakeyi tayi ta ijiye sannan takalleshi tace “Imrana” dan dago kanshi yayi yakalleta yace “na’am Hajiya” ahankali tace “I promise not to meddle with affairs naka dana matarka but I think akwai somethings that I can overlook a matsayina na babba” Hajiya tadanyi shiru saikuma tace “banson damuwa yama Yar karaman yarinyar nan yawa Imran, kaiba kulata kake ba kannenka ma haka, Binta ne kawai ke kula da yarinyan nan agidan nan nikuma baran iyaba dan kafafuna ba barina zasuyi ina hawa saman nan ina saukowa kullum ba” Hajiya takarayin shiru sannan tace “inaso gobe kafin katafi aiki ka dauki yarinyar nan ka kaita makaranta mai kyau kasata, islamiyya kuma zaka sata wanda su Kausar ke zuwa asabar da lahadi, amman dai gobe yarinyar nan tafara makaranta kaga karatu nata wuce ta, tunda bawai wani abu take agidan ba banda zaman kadaici da kuka dan haka ka kaita kasata a makaranta mai kyau kaji ko Imrana” gyadama Hajiya kai yayi yace “to” Hajiya tabishi da kallo tace “tashi katafi to Allah bamu alkhairi” ahankali yace “Ameen” yatashi yafita daga dakin tareda maida mata da kofan yarufe, sama yakoma daidai lokacin Anty Binta tafito tareda Lujain din da hijab ke jikinta black dayawani kalan haskata, ganinshi yasa tasauke kanta akasa tashige bayan Anty Binta ahankali tana wasa da yatsunta, Anty Binta ma sauke kanta kasa tayi ganin yanda yake kallonsu da wannan idanun nashi dabaka jurewa, kallonsu yayi ba yabo ba fallasa yace “where to”? Ahankali Binta tace “dakina zamu ta kwana awajen Ya Imran wai bata iya kwana ita kada…….” wani mugun kallo yama Anty Binta yace “bacemin daga nan” dawani kalan sauri Anty Binta tawuce tayi hanyar dakinta, wani kalan kuka Lujain taji yazomata batare data kalleshi ba tajuya ahankali takoma cikin dakinta ko tsayawa kulle kofan ma batayiba da gudu tafada gado sai kuka, yadade awajen tsaye sannan yakarasa gaban dakin nata batare daya kallo ciki ba yasa hannu yajawo kofan yarufe yawuce dakinshi.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply