Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 26


Sakon So 26
Viral

 

Shuku Anty Binta tasa akamata mai bala’in kyau, mai style yan kanana nan da nan tayi kaman ba itaba, tasa aka wanke mata kumbunan kafa da hannu Anty Binta sai kallon yatsunta take both nakafa da hannu sunada bala’in kyau gasu so chubby sannan yatsun farare dogaye, mace mai ni’ima kana iya ganewa daga yatsunta both na kafa da hannu, bakaramin addu’a take kan Ya Imran yafara son yarinyar nan ba dan Lujain is a gift from Allah, kyautanta Allah yamai bayan wahalan rayuwan dayayi, 13yrs ba mata sai zaman kadaici da bautan Allah saisa Allah yabashi Lujain cus babu abinda Lujain batadashi gatada shiga rai, bala’in shiga rai, daga zuwanta saloon din nan harsun fara sonta, mai saloon din harda cema Anty Binta tanason sister nan nata tamata influencing saloon din nan adauki pictures nata zata biyata da kyau, saida tanuna musu matan aure ne mijinta bazai yarda ba sukabar zancen.

Biyan kudi sukayi sannan suka fito wani babban super market sukaje jakunkuna Anty Binta tasaya mata da takalma masu kyau da yankune da agogo, bracelets irin na yanmata dinnan, da kayan sawa english wears masu kyau sosai su sexy gowns, shorts, shirts, jeans dan sotake tadinga sawa Ya Imran yasoma dawowa hayyacinshi, takara mata abayoyi, da turaruka, harzasu fito tace “Anty su Chocolate” wajen chocholate sukaje sai alokacin Lujain tafara deban chocholates dasu biscuits dabama tasan dasu aduniya ba ita Anty abin dariya ma yabata tace “ai saisa kike kiba sweet tooth ni mutafi” biyan kudi sukayi aka kaimusu kayan mota sannan suka tafi bayan magrib suka shigo anguwan Anty Binta ke tuki gidan dake kusada nasu sukaga an bude ana shiga da sababbin furnitures Anty Binta tace “kowaye yasai gidansu Maman Adam oho” kallon gidan Lujain tayi dayake abude sai gyare gyare ake har fenti anyi, Anty Binta dake tuki tana kallon gidan tace “Maman Adam makotan mune sunada kirki gidansu ne amman sun saida sabida mijin zai koma US yasami aiki a chan” daidai anbude musu gate suka shiga cikin gidan, parking tayi suka fito zare hijab din school Lujain tayi tadauki ledan chocholate dinta tayi gaba mai gadi natayasu daukan sauran kayan sallama tayi tashigo falon ahankali daga Hajiya sai Musty da Abee afalo Musty ne ma yadago shi daga masallaci dabai shigo gidan ba sai bayan isha’i, kallo daya Abee yamata yadauke kai Hajiya tace “yan makaranta an dawo” Gyadamata kai tayi batare data karasa wajen ba tace “ina wuni” sannan takalli Musty ahankali tace “ina wuni” murmushi yamata yace “lpy lau” Hajiya tace “aiko kitson yay kyau mekika riko mana a leda” ledan takalla for the first time dan murmushi tayi tace “chocholate dina ne” dan dariya Hajiya tayi tace “sabida bakiso kibani ne kike cewa chocholate dinki ne ai shikenan jekisha Lujain” akunyace tadan sunnar da kanta kasa kaman mai koyon magana tace “Allah ni zan baki Hajiya” shi kanshi Musty dan murmushi yayi jin yanda tai maganan Hajiya tace “to nagode Allah amfana jeki cire kayan makarantan saikizo kici abinci” Gyadamata kai tayi tawuce sama, tana shiga dakinta taga jakan school nata an ajiyemata waje daya, bayi tawuce tacire kayan school nata tareda jefawa a washing machine sanan tai wanka da ruwan zafi tafito daidai Anty Binta na shigowa dakin rikeda manyan ledojin kayanta Maman Aneesarh ma natayata dan kallon Lujain din Maman Aneesarh tayi yanda kitson yamata kyau tace “Ya school”? Ahankali Lujain tace “lafiya lau ina wannan baby”? Murmushi Maman Aneesarh tayi tace “tayi bacci” sannan tawuce tafita daga dakin, Anty Binta saida tajera mata kayan tass dan ita bata salla sannan tawuce tafita itakuma tana idarwa zama tayi kan gado tabude ledan chocholate nata tashiga sha saida tasha daban daban kusan guda 7 sannan ta tashi tasakeyo alwala tafito tahau kan dadduma tana salla shigowa Anty Binta tayi ta ijiye mata abinci a kula tana idarwa taci batawani ci dayawa ba sabida yanda tasha chocholate din nan hawa gado tayi ko 3min batayiba sai bacci danta gaji.

Wuraren 2:30 tabude idanunta ahankali sabida shegen yunwan datakeji, dakin da hasken wuta hakan yasa ahankali ta tashi zaune sauka tayi daga kan gado tabude kulan abincinta dabata ci jiya da daddare ba, yatsine fuska tayi danji tayi batasoncin abincin tamaida tarufe ledan chocholate nata ta dauka tabude ciro chocholate guda uku tayi sannan tabude jakan school nata tafito da books dinta tana duba abinda aka musu tanaci saida tacinye tass sannan ta tashi ahankali tasake hawa gadon nan da nan bacci yay awon gaba da ita.

4:30 Abee yafito saida yatada kowa sannan yakoma dakinta knocking yayi tareda bude kofan ahankali ledojin chocholate daban daban kusan 10 dayagani akasa yasa yakalleta tana kwance kan gado tadan rufa tana bacci ta peacefully, katon ledan chocholate din yakalla dahar ya rage yawa sannan daganan inda ya tsaya yace “Ke! Kee!” Firgigit tabude idanunta ahankali tareda dan turo baki saikuma chan kaman wacce ta tuna abu bude idanubta tayi tass ganin Abee ne ba Gwaggo ba yasa dasauri tamike tsaye tawuce bayi Abee yajuya yafice.

Wuraren 7:00 tabude kofan dakinta ahankali tafito ta shirya tsaf cikin kayan makarantan dasuka mata mugun kyau tagoya jakanta abaya hannunta rikeda farin hijab din dabata sakaba tanabin saman da kallo daidai Abee ya hayo sama kallo daya yamata yadauke kai itakuma ta tsaya chak inda take takasa koda motsi saida yakaraso daidai inda take yace “today should be the last time dazan ganki a falo babu hula ko lullubi” yana maganan yawuce dan turobaki tayi tasaka hijabin sannan tawuce tasauka kasa saida tafara gaida Hajiya sannan tai breakfast sosai taci abincinta baruwanta tashi tayi Hajiya tace “ina zaki Imrana dazai saukeki baima fitoba” ahankali tace “zan zauna awaje ne inga rana” murmushi Hajiya tayi tace “tom jeki” wucewa tayi tabude kofa tafita waje Kausar tabita da harara ahankali take kallon ko’ina na tsakar gidan tana kallon yanda gardener dinsu ke zubama flowes ruwa, juyawa tayi tayi wajen gate nasu tabude karamin gate din kadan tana leken waje batasan mesaba hakanan taji kaman wani abu na janta zuwa wajene ahankali tasa kafanta tafita waje wani sanyi taji yashigeta ahankali tadaga kanta tana kalle kalle titin estate din shiru babu motoci dan duka duka yanzu is 7:15, jitayi kaman ana kallonta ahankali yasa ahankali tajuyo da kanta takalli gidan dake kusada nasu chak taji numfashinta ya tsaya.

Mandawari tagani yana tsaye gaban gate nasu sanye dawani rigan jersey na Liverpool dark blue dawani farin short bathroom slippers ne a kafanshi hannunshi rikeda iPhone 14 dayakai kunnenshi da alamu waya yake amman idanunshi kyar akan na Lujain dabai taba tunani zai gani ba dan duka duka ko 20min baiyi da zuwa duba aikin da akeyi agidan ba.

Wani kalan sauke numfashinta Lujain tayi takai hannayenta dasauri ta goge idanunta dan tanaso takara gasgata ba gizo idanunta kemata ba Mandawari take gani yanzu haka agabanta jingine dawata mota black yana waya, ganin still shine yasa taji gabanta nawani irin mugun gudu takasa koda motsi, kusan 2minutes sukayi tana kallonshi yana kallonta yana waya sannan yazare wayan daga kunne awulakance yamata alamu da hannu datazo nan, nuna kanta tayi tace “ni?” Gyadamata kai yayi batare dayace eh ba, gabanta nafaduwa sosai tafara tafiya ahankali takarasa gabanshi ta tsaya tana kallonshi, cikin sigan yanga yace “why are you looking at me like that kinsanni ne”? Wani kalan lumshe idanu tayi tabude ga muryanshi nan sak wanda takeji idan yana live video batare daya kyafta ko idanu ba tana kallonshi tace “nasanka” tsareta yayi da idanu hakan yasa tace “you are Mandawari, kana buga kwallo, kai player Liverpool ne, sannan kana bugama Nigeria, ina following naka a IG, my name is Lujain and I am your biggest fan” takarashe maganan tana gasping breath tana wani kalan kallonshi kaman zata hadiye shi da idanu, dan yatsine fuska yayi yadau wayanshi yadan daddana batare daya kalleta ba yace “my biggest fan can’t be this ugly” dasauri takalleshi looking confuse, janye wayan dayake dannawa yayi daga fuskanshi sannan yakalleta awulakance yanunata da wayan dake hannunshi daga sama har kasa yace “I mean look at you, you are so soo fat, I don’t think ko mai cikin 5 months takaiki katon teba, so please excuse me go and loose weight saiki dawo kimin magana” yay maganan tareda juyawa yabude kofan motanshi ya shige tareda jan motan da gudu yawuce yabar anguwan daidai hawaye na zubomata sharrrr, “ana kiranki” taji muryan Kausar hakan yasa tajuya da sauri hada idanu sukayi da Kausar, Kausar zata juya takoma ciki dasauri Lujain tace “Kausar” hakan yasa Kausar ta tsaya tana kallonta karasawa wajenta Lujain tayida sauri, bakin Lujain har rawa yake cikeda wani kalan damuwa tace “Kausar dan Allah kifadamin gaskiya, please inada kiba”? Tsayawa Kusar tayi tana kallon fuskanta ganin yanda idanunta sun cicciko da hawaye ga damuwa karara afuskanta yasa tace “ke baki sani bane kike tambayana” juyawa Kausar tayi zata wuce dasauri Lujain tarike mata hannu tace “dan Allah kifadamini gaskiya nasan you don’t like me so you will tell me the truth” dan shiru Kausar tayi yanda taga she really wants to know yasa tace “eh kinada kiba Lujain” kaman jira Lujain take hawayen idanunta ne suka zubo dan zaro idanu Kausar tayi tana kallonta tace “Waike lafiyanki kalau kodai kinada aljanu ne” sakin hannun Kausar tayi daidai lokacin Abee yabude kofa yafito Kausar tayi wajenshi tace “Abee waje taje tana kuka” dan kallonta yayi yanda take tsaye awajen gate takai hannunta kan fuskanta tana sharewa kawai yawuce wajen motanshi hakan yasa Lujain ta taho tashiga motan Abee yaja motan suka tafi harsuka kai school baice mata komiba sauka tayi tashiga ciki yabita da kallo kafin yatada motan yawuce shima.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply