Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 27


Sakon So 27
Viral

EPISODE 2️⃣7️⃣
Ranan har aka tashi daga school tarasa abinda kemata dadi koda taje lunch takasa cin abinci sosai, 4 suka tashi tadauki jakanta tafito daga ajinsu tundaga nesa tahango Abee tsaye jikin motanshi yana sanye da suit nashi black yasaka wasu bakin glass a idanunshi wayanshi akan kunne yana magana ahankali take tafiya harta karaso inda yake tasauke kanta kasa tana wasa da yatsunta murya chan kasa tace “ina yini” wani kalan kallo yamata sannan yashiga cikin motan itama zagawa tayi tashiga yatada motan suka tafi, tunda suka shiga estates nasu take kallon gidan Mandawari dataga gate din arufe horn Abee yayi aka bude musu gate suka shiga cikin gidan parking yayi tareda kashe motan dan juyowa tayi ta kalleshi daidai shima yadan kalleta ganin bata bude kofa tafita ba, sauke kanta tayi kasa tashiga wasa da yatsunta kaman yabude kofa yafice abinshi saikuma yace “me kike bukata”? Dan dago kanta tayi takalleshi ganin ita yake kallo yasa ahankali tasauke kanta kasa tana wasa da cute white chubby fingers dinta dakenan gyare tsaf murya chan kasa kaman batason abinda zata fadi tace “dama….dama…..” saikuma tai shiru batasan tayaya zata tambayeshi kudiba, dan dago kanta tayi ganin kallonta yake yasa tadauke kanta dasauri tace “I…..don’t have any money Uncle……” taidan shiru realizing this is the first time take kiranshi kumama wai Uncle abin yamata wani banbaran abaki, dan kallonshi tayi kadan suka hada idanu dan lankwashe kai tayi kaman wata macijiya murya chan kasa tace “kuma…..kuma magani nakeson in saya” kallonta yake kyar batare dayace komiba, dan dago kanta tayi suka hada ido murya chan kasa tace “uhmmm….maganin rage ki…kiba” dan lumshe idanu yayi yakalleta sannan yace “a ina ake saida maganin”? Dan kallonshi tayi kana ganin kwayan idanunta kasan batasani ba, ahankali tace “nima bansani ba amman ai za’a samu a kasuwa” wani kalan kallo dayamata yasa tamaida nata idanun kasa yace “kintaba ganin yaran gidanmu sunje kasuwa?” Girgixamai kai tayi, ahankali yace “kin taba zuwa kasuwa?” Sake girgixamai kai tayi tace “amman Gwaggo na na zuwa tana sayo magunguna da yawa nasan zan samu nima innaje” tunda take maganan yake kallonta yace “did anybody told you kinada kiba a school ne”? Sake girgixamai kai tayi tace “a’a” ahankali yace “maisa kikeson kisha maganin rage kiba”? Batasan mesaba hakanan taji takasa fadamai karya ahankali tace “Mandawari bayason mace mai kiba” yadade yana kallonta harsaida tadago kanta takalleshi dan gajeren tsaki yayi yace “yabaki maganin rage kiban to” yay maganan yana yunkurin tashi dasauri tace “namishi magana”? Dan tsayawa yayi saikuma yajuyo yakalleta yace “I told you zaki iya kome kikaga dama I don’t consider you my wife and you are not my wife, dazaran this whole thing yalafa aka kamo yaron zan rabu dake” wani kalan murmushi tayi daya lobar mata da dimples nata tace “thank you Uncle” tai maganan tana bude kofa tafito tawuce ciki tana tafiya ahankali yadan bitada kallo.

Hajiya kadaine a falo da Maman Aneesarh ahankali tace “ina yinin ku” murmushi Hajiya tayi tace “sannu da zuwa” Aneesarh data gani taduka tadauka tana murmushi tace “zomuje dakina” murmushi Mamanta tayi tace “wanan saita batamiki daki wlh da barna” murmushi tayi tace “dan Allah kibarni natafi da ita Allah ina sonta” Maman Aneesarh tace “shikenan kuje” wucewa sukayi sama Abee yashigo shima gaida Hajiya yayi, Hajiya tace “sannu da zuwa Imrana” ahankali Maman Aneesarh tace “sannu da zuwa Yaya” Gyadamata kai yayi yawuce sama, Maman Aneesarh takalli Hajiya tace “Hajiya Ya Imrana is so nice towards this girl” Hajiya tace “Imrana has always being nice to kowa, banbancin Babba mai hankali kenan da kananun yara samari, Lujain is just like Kausar kozai wulakantata bazai iyaba dan kaman diyar cikinshi ne bazai iya imagining wani ya wulakanta mai Kausar ba, nasan Imran dina dudda bayason Auren nan bazai taba cutar da ita kokuma yaga abin cutarwa yabari ya cutarda ita ba” Maman Aneesa tace “saisa yasata a makaranta mai tsada ko su Kausar ba makarantan turawan nan sukayi ba” Hajiya tace “inba irin makarantan nan ba awanne za’a sata yarinyar da fuskanta ya zagaye yanar gizo so kike kullum adinga dukanta ta tsani makaranta gabaki daya taki fita” ahankali Maman Aneesarh tace “Hajiya ni tausayi yarinyar ke bani koda zamuso zamansu da Ya Imran tayaya zata fara kula da Ya Imran? Babu abinda ta iya wannan saidai shi yakula da ita ai” Hajiya tace “daga next week duk idan tadawo daga makaranta zan dinga sata tana shigowa kitchen kuna koyamata abu daya biyu haka harta kware” kallonta Maman Aneesarh tayi tace “Mama kinason auren su ne?” Hararanta Hajiya tayi tace “kin isheni da tambaya amman abu daya zan fadamiki babu Babba dazai cemiki yanason mutuwan aure duk Auren da aka daura fatanmu shine yadaure har abada, idan zamansu tare Alkhairi ne Allah yahada kansu kullum shine addu’a na”.
***

 

Olusay ke tuki suka shigo estate din, horn yayi gaban gidan gateman yabude musu suka shiga ciki Olusay yace “wow gidan yay kyau wlh Man” yadan kalleshi ganin yana cikin IG, karasa parking yayi ganin Mandawari baima saniba yasa gently yakai hannunshi yadaura akan shoulder nashi hakan yasa dasauri Mandawari yakalleshi yace “ohh harmun shigo”? Olusay yace “kanachan kana kallon hoton stalker naka yaza’ayi kasani” kallonshi Mandawari yayi, ahankali Olusay yace “can I talk to you Man I am serious”? Dan yatsine fuska yayi yana cire sitbelt yace “what”? Dan jim Olusay yayi dan baisan how he’s going to take the magana ba ahankali yace “first of all Muhammad I don’t know your reason na sayan gida right next to gidan da stalker dinka ke aure, nabiyu you saw everything mezakayi da matan aure yarinyar data Riga tayi aure? Thirdly kasan your Mom bazata taba bari ka auri yarinyar that went viral online hakaba, and nahudu kariga kayi loosing chance dinka da bakin wulakanci for the past how many years yarinyar nan namaka magana wulakancinka yahanaka kulata sai yanzu bayan an mata aure ne zaka fara sonta what’s all this Man? Mezakayi da wannan yarinyan kanada thousands of mata har yan film dake sonka sai wannan da aka mata unfortunate Marraige din nan zaka wani fara so” shiru Mandawari yayi saikuma chan yace “you want an honest answer?” Gyadamai kai Olusay yayi ahankali yace “I buy this house triple amount na gidan nan because of the girl dan wasu harsun sayi gidan nakara kudade, sannan kai kanka you just call the marriage unfortunate one kawai anyishine dan ayi blocking mutane from saying shit akan honest mistake datayi well koma Iskancin tayi da mutumin I know he must be the one to force her dan that girl love only me, and again what made you think Mom harta isa tagayamin ga wanda zan aura ga wanda bazan aura ba bayan ita taje tayi aurenta da Dad dina yarasu? She have no right over me, lastly kowa yarinyan nan ta aura I don’t bloody care she belongs to me! Just me, watch and see how I win my girl and shape her to abinda nakeso that fat everything she will loose it, idanma takasa dakaina zan kaita amata tummy tuck” dan murmushi yayi yace “how is my welcoming party going”? Tabe baki Olusay yayi yace “I know how stubborn you are just be careful, mijin yarinyan nan is not our mate that’s number one tsoho ne, nabiyu kuma he’s a soldier, a retired old soja” dan dariya Mandawari yayi yace “that’s more of the reason why I want to save her, mezatayi da tsoho dakeda yaran dasuka girmeta? She’s to young and fresh for him, bata sonshi ni kadai takeso, just sit back and watch how I open her eyes and show her the world” “hmmmm” Olusay yace da mamaki yabude mota yafito shima Mandawari yafito Olusay yace “ni bantaba ganin mutum irinka ba yarinyar dabaka nuna mata so bamaka kulata” dan tsaki yayi yace “leave me alone please, kaji da kanka” taba yaciro yakunna yanasha Olusay yawuce ciki abinshi, saida yagama sha ya yarda karan ya shiga ciki.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply