Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 3


Sakon So 3
Viral

EPISODE 3️⃣

 

Koda aka idar da Magrib gyara zama yayi dan yaji ta’aleem wanda dama shi haka yake sai bayan yay isha’i yake komawa gida, yana zaune inda yake wani yaro dan matashi haka dabazai wuce 22yrs ba yay kamadashi kaman yay kaki yatofar yazo kusadashi ahankali ya zauna tareda daura hannunshi kan nashi warmly yace “Abee” dagoda fuskanshi yayi yadaura akan fuskan yaron asanyaye yace “Ya school”? Murmushi yaron yamai yace “fine Abee yanzun nan nadawo nashigo masallaci dannai salla bari naje gida nai wanka naci abinci Abee I am hungry” gyadamai kai Abee yayi hakan yasa yatashi tareda wucewa yafita daga masallaci mahaifin nashi nabinshi da kallo ganin yanda gajiya ya nuna afuskanshi karara.

 

Sai bayan sallan isha’i sannan suka fito daga masallacin dashi da kannenshi biyun maza Hamza da Ibro sai Abdallah, magana yayi da Ibro dazai wuce gidanshi dan yanada mata gidanshi babu nisa da nasu shima a estate din yake zaune da matanshi da yaranshi Mata guda biyu hakan yasa shida Hamza da Abdallah dakemai hira sukai cikin gida ko kadan baida magana amsanshi baya wuce uhnnn u’u, suna shigowa falo akan lumtsetsen one sitter kujera yazauna dake facing wanda Hajiyanasu ke zaune akai 2 sitter, idanunta kyam akanshi tace “an dawo daga masallacin”? Gyadamata kai yayi yace “eh Hajiya” murmushi tayi tace “to Madallah kowa yaci abinci jeka dinning kaci naka kaima” dan yatsine fuska yayi tareda girgiza mata kai kaman wanda akace yay wani mugun abu ahankali yace “coffee kawai zansha Hajiya ankaimin daki”? Tabe baki tayi tace “ai tuni diyar nan taka mai rawan kai takaimaka daki” tashi yayi yace “to saida safen ku” tashi shima Abdallah yayi yace “Inna nima nagaji bacci zan gobe inada 6 nasafe, good night” binsu Hajiya tayi da kallo saikuma tai shiru murmushi Hamza dake kallon Hajiya yayi yazo kusada ita zama yayi yatasata agaba kuri yana kallo hararanshi tace “me kake kallona kaikuma”? Murmushi yamata yace “Hajiya kinga kiragema kanki wannan damuwan ko dazu saida Anty Binta tamiki fadan nan, kirage damuwan nan kan Yayanmu ba yaro bane he can take care of himself, kowa yasan Yaya baida yawan cin abinci idan yaji yunwa dakanshi zaisa akaimishi” baki tabude zatai magana daidai akai sallama tareda shigowa falon wani magidancin mutum ne wanda akalla zaiyi sa’an Abee washe baki tayi tace “surukina oyoyo Mustafa” murmushi yayi yataho da sauri har gabanta yaje ya tsugunna yace “ina yini Hajiya mun sameku lpy” murmushi tayi tace “Alhamdulillah dan nan yakuma zaman jidda? Ya fama da abincin larabawa mara magi sai uban kanunfari su masoro da sauransu”? Murmushi yayi yace “Alhamdulillah Hajiya” gaidashi Hamza yayi daidai nan su Anty Binta da kanneta duk suka fito gaidashi sukayi Ya amsa tashi Anty Binta tayi zata kawomai kayan kwalama yace “ina Imran Wife”? juyowa tayi takalleshi tace “yana dakinshi” tashi yayi dasauri harzai wuce Hajiya tace “Mustafa” dawowa yayi dasauri gabanta yace “na’am gani Hajiya” dan ijiyan zuciya tasauke baki tabude zatai magana saiga hawaye Hamza dake kusada ita yace “kinfara ko Hajiya”? Dan murmushi Mustafa yayi taredakai hannunshi yakama na Hajiya anatse yace “zan mishi magana Hajiya Dan Allah kidena kuka” bakin zaninta takama dasauri takai kan idanunta ta share tass sanan takalli Mustafa tace “Mustafa dole na koka Imrana shine yarona na farko wannan wani kalan kaddaran rayuwane, shine uban duka yaran nan nawa, ganida yara mata, yanzu nan nan Rahama uwar Aneesarh tadawo gida da yara biyu mata mijinta yarasu, idan wani abu yafaru shi za’a nema shine me tsaya musu, bama wanan ba at least wayannan su kannenshi uwa daya ta haifesu yaranshi daya haifa fa iyye? Yaran cikinshi fa Kausar da Abdallah? Yazaci su basu damu kullum suna ganin ubansu haka bane? Nasan yawahala arayuwan nan na………” “Hajiya!” Mustafa yakira Hajiya ahankali dayasa ta kalleshi murmushi yamata yace “in sha Allah zanyi magana dashi yau bari naje” tashi yayi ahankali yay sama sukuma duka yaran har Anty Binta sukazo suka zagaye mahaifiyar tasu kowa yay zugummm kunsan ance yara mata dabanne akwaisu da tausayi da jinkan mahaifiyarsu duk lallashinta suka cigaba da yi kowa na bata baki.

 

Yana zaune agaban study desk dinshi har lokacin yana sanye da jallabiya ya kunna desktop dinshi ga coffee a mug yana kurba yana aiki akai knocking kofar dakinshi tareda bude kofan gabadaya aka shigo hakan yasa yadaga kanshi dasauri yakalli kofar danko Hajiya bata shigomai daki kai tsaye batare daya bata izinin shigowa ba balle kuma wani na gidan, ganin Mustafa yasa yasaki wani kalan coool smile taredajan kujeran dayake kai baya yamike tsaye yakaraso inda Mustafa ke tsaye gaban kofan yana murmushi yabashi hannu tareda cewa. “Wata sabon gani” murmushi Mustafa yayi yakarbi hannunshi yace “I missed my best best besssst friend my one and only childhood friend, Imrana waikai baka tsufa ne for God sake look at me look at you, jibeni kaman wani yayanka”?Dan murmushi yayi akunyace yace “common don’t start with this your blabbing mushiga ciki wants some coffeee”? Ciki babban dakin suka shiga Mustafa yazauna kan lallausan carpet din dakin dakeda wani kalan shegen taushi kaman gado shikuma Abee yawuce dauko flask na coffee da mug Mystafa nabinshi da kallo yace “jibeka kaman yayan Abdallah ba Babanshi ba” tsiyayamai coffee yayi yabashi batare dayace komiba hakan yasa ya amsa yana kallonshi yakai baki yadan kurba sannan ya ijiye, ahankali Abee yace “Ya Jiddarh how is the course going”? Dan yatsine fuska yayi yace “nima wlh retire zanzo nayi kwanan nan kaman kai, aikin soja barinma na Nigeria is exhausting and energy draining, you know what they say problem no dey finish for naija” murmushi dukansu sukayi atare Abee yakai mug na coffee bakinshi yanasha ahankali shima Mustafa yanasha yana kallonshi 1yr kenan da tafiyanshi Jiddah one year kenan rabon dayasashi a idanu gani yayi Abee yawani kara kyau wlh kaganshi zaka dauka matashi ne dake tsakiyan lokacinshi kawai maturity da yanda yake daukan kanshi ne zaisa kagane Babba ne mutumin nan ya kwan biyu aduniya but other than that yamafi wani lafiyayyen matashin kyan gani da kyawun jiki kaman daga sama yaji saukan tambayan Mustafa akunne shi. “When are you getting married again Imran”? Chak ya tsayar da mug din dayakai bakinshi zai kurbi coffee yakai kusan 2min ahaka ko motsi baiyiba sannan gently yazare mug din ya ijiye ahankali kan tray din kafin yamike tsaye Mustafa nabinshi da kallo yawuce gaban desk dinshi yaja kujera yazauna yacigaba da aikin dayakeyi acikin desktop din batare dayace uppan ba, dan murmushi Mustafa yayi ajiyan zuciya yasauke yakarasa shanye coffee cikin mug dinshi sannan ya ijiye cup din yamike tsaye shima ahankali yakaraso tsakiyan dakin ya tsaya anatse yace “kayi avoiding this question for good 13yrs but this time Imran ko bakaso you must answer me” yay dan shiru yatako zuwa bayan kujeran dayake zaune ahankali ya tsaya taredakai hannayenshi yadafa kafadanshi yace “duk wanda yashigo cikin gidanku abu nafarko dazai gani shine one bigggg happy family, ga Hajiya da yaranta dakuma jikokinta sun cika gidan leaving happily kansu ahade but trust me that still person dayayi tunani u people are happy family will take him just a day to realize you guys are not happy, dan behind that happiness is one huge big sorrow dayay surrounding zuciyan kowa all because of you Imran, kowa is not happy, your family supported you throughout the difficult time dakai going through arayuwanka, everything, kullum suna cikin battling da PTSD dinka, burinsu yanzu daya ne kasami mata kai aure ka natsu yaranka su sami uwa eh Imran” dan lumshe idanu Abee yayi sannan ahankali yabudesu tareda juyowa hada idanu yayi da Mustafa dake kallonshi kaman yaune yafar ganinshi, wani abune yaji ya tsayamai azuciya hakan yasa yasake lumshe idanu kawai yay shiru ahankali Mustafa ya tsugunna agabanshi tareda kamo hannayenshi yarike hakan yasa yabude idanunshi ahankali, ahankali Mustafa yace “talk to me I am your friend, I am here for you, talk Imran” kadawa idanunshi sukayi sukai jaaaa kaman bashiba ahankali muryanshi harta dishashe yace “I don’t wanna get married again! I don’t want tooo” yay shiru tareda sake lumshe idanunshi dan murmushi kadan Mustafa yayi ahankali yace “bakason kasake wani aure because you feel you are betraying Muna (Maimuna)”? Murya chan kasa yace “kowa knows how deeply you love Muna Imran, soyayya kukai kaida muna soyayyan da tun kuna yara tun bakusan ciwon kanku ba, soyayya ce dakuka farata tun baby class, primary school har secondary school, kaida Muna are just like Zara da wata, duk inda aka ganka anga Muna akaga Muna anganka, I remember lokacin nan kuna kare secondary school aka muku aure sabida kun ishi mutane da soyaya” Mustafa yayi murmushi ahankali murya chan kasa yace “is not easy to loose the love of one’s life along with 2 of your beautiful children Abdulhamid da Asiya, I know you are suffering I know your heart is shattered but trust me Imran this is not what Muna wants for you kana wannan miserable life din rayuwan kadaici kullum daga office sai masallaci sai gidan Hajiya for the past 13yrs kana tunanin Muna and your two marigayun yara wants that?” Wani kalan gaggauran ijiyan zuciya yasauke har lokacin idanunshi a lumshe dazaka iya dauka ko bacci yakeyi, ahankali Mustafa ya matse hannunshi yace “13yrs kenan da aka kashe maka mata da yaranka biyu tun kana shekaru 36yrs yanzu you are 49 Imran me kake nufi you will not move on ahaka zaka karasa rayuwanka kana zaman kadaici kullum mahaifiyar ka your old mother cikin kuka take kullum kanninka su Binta cikin kunci suke yaranka ma haka all because of you shin kamusu adalci kama dattijuyar 70yrs old Mom naka adalci da at this stage babu abinda take bukata banda farin ciki, kama Muna adalci datake sonka sama da rayuwanta eh Imran”? Wani kalan ijiyan zuciya mai zafi ya fuzar sannan yabude idanunshi ahankali yakalli Mustafa murya chan kasa yace “kowa zan aura Musty kasan cutar da ita kawai zanyi, my heart my soul my whole body and everything belongs to only one woman which is Muna, bazan taba iyason kowace mace ba kuma arayuwana, I cannot love again, kota Auren gangan jikina kawai aka aura, I can’t love again, bazan taba samun wata kaman My Muna ba” murya chan kasa Mustafa yace “kai Allah ne? Kasan gaibu ne? Did you know what tommorow holds for you don’t say that Allahn daya baka Muna can give you wacce tafi Muna” ajiyan zuciya yasake saukewa murya chan kasa still Mustafa na kallonshi yace “how are you even surviving Imran all this years? Tayaya kakai har war hakama bakai aure ba? Imranan dana sani dakenan duk shakara Muna ke haihuwa, I remember lokacin damuke trainning na sojoji a chan jaji kusan duk bayan 2days kake sabewa tabayan katanga kadawo gida just to come and ease yourself da iyalanka eh? I know you best friend naji bazaka tabaso wata ba but you are punishing kanka, grieving Mamaci daban sannan halittun da Allah yamana ajikinmu daban, yudaya baya hana daya grief Muna as much as you want but you are suffering, for the past 13yrs rabonka da wata mace idanba kanason kai loosing sanity naka loose focus bane kanemi mata kai aure” fuzar da iska yayi ahankali yace “I am sorry Musty but bazan taba iya neman wataba, and the suffering I am suffering lemme suffer it I deserve it, bayan aurenmu danake cema Muna I want to become a soja bataso she stop me but nakiji sabida it has been my childhood dream nazama soja, Muna was always scared idan aka turamu for assignment kada akashe mata ni not knowing bani Zaa kashemata ba itane za’a kashemin, had it been I listen to her I went for another course instead of becoming a soja da yanzu My Muna na raye, so lemme suffer I deserve it I have been selfish and stubborn and a bad husband to her” baki Mustafa yabude zaiyi magana Abee ya nunamai kofa da hannu kai tsaye yace “leave me alone Musty leave my room” kallonshi Musty yayi idanunshi sunyi jajir yasan idan ya tsaya zai iya sawa yanzun nan ya birkice kuma yau ya birkice babu wanda zai runtse agidan nan ga Dr shi baya Nigeria yayi dan tafiya hakan yasa ahankali yadaga hannunshi yace “okay I rest my case best friend saida safe” yajuya yay kofa yabude Anty Binta yagani gaban dakin idanunta sunyi jaaa maida kofan yayi yarufe kaman jira take kawai tafada jikinshi ta kankameshi tana kuka ahankali janta yayi saida sukai wajen bene sannan ta tsayarda kukan tareda dago fuskanta tashare idanunta ahankali tace “please kada kagayama Hajiya yanda kukayi wlh zuciyanta zai iya bugawa” Gyadamata kai yayi tareda murmushi yace “I know wife muje” sauka sukayi zuwa dakin Hakiya dake nan akasa a falo dan bata iyawa da benen nan tana ganin Musty cikeda murna tace “yakukayi dashi Mustafa ya aminci zaiyi Auren”? Dan murmushi Musty yayi yace “eh Hajiya amman yace adan bashi lokaci ya kammala project dindayakeyi a company shi” dan murmushi Hajiya tayi one thing is dudda tsufanta babu wanda yakaita sanin halayen yaranta kawai tasan bahaka sukai dashiba ne amma she knows what to do.
SAKON SO

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply