Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 31


Sakon So 31
Viral

 

Bin wayan tayi da kallo sannan ahankali ta ijiye wayan akarkashin gado tareda kife cikinta dake mata ciwo sosai sabida yunwa tunda take arayuwanta bata tabajin yunwa irin na yau ba chocholate dinta takalla dake leda lips dinta talashe tareda lumshe idanunta bacci ne ya saceta sai around 6 ta tashi kulan abinci tagani ankawo a injiyemata tashi tayi tawuce bayi alwala tayi tazo tai sallan la’asar sannan ta tashi tareda cire hijabi tana gyara towel din jikinta gaban kulan taje tabude su ahankali, biryani rice ne dayaji naman rago baja baja aciki wani kalan kugi cikinta yayi batasan lokacin data fashe da kuka ahankali ba tana kallon abincin cikinta nawani kalan murdawa dawani kalan sauri tarufe kulan tareda juyama abincin baya tadaura kanta saman gado, bude kofan dakin akayi hakan yasa ahankali tadago kanta Anty Binta ne idanunta kadai takalla tace “why did you cry Lujain menene”? Girgizamata kai tayi alamun babu komi sai kuma hawaye yazubo mata sharrr binta Anty Binta tayi da kallo ganin yanda tai zuru zuru yasa Anty Binta tace “kinyi lunch a school”? Girgixa mata kai Lujain tayi ahankali dan ita har yanzu bata iya karya hakanan ba, hakan yasa Anty Binta tabude kulan datagani adakin na abinci ganin bata tababa yasa ran Anty Binta abace tace “wai what is this behavior Lujain? Cikin gidan nan akwai wanda yamiki complain angaji da abincin dakikeci ne koko muncemiki munaso kirage kibane why will you be hurting yourself like this eh Lujain”? Wani kalan matsiyacin yunwa takeji dayasa takasa hadiye kukan, Anty Binta tadauki kulan gabaki daya takawo gabanta tareda saka mata spoon akai tace “dau abincin nan kici” girgixa mata kai tayi tana kauda kanta gefe tace “ni baran ci abinci ba” shiru Anty Binta tayi tana kallonta tace “sokike nabata dake ko Lujain” girgixa matakai Lujain tayi tana goge hawaye tace “kiyakuri Anty” tashi Anty Binta tayi tace “shikenan nima yau zan tattara nakoma gidan mijina dama sabida ke nadan zauna agidan nan sabida kisake amman tunda you are so stubborn kina neman yima kanki illa shikenan ke kadai kiyi amman zanje yanzu nafadi ma Hajiya sannan nafadama Ya Imran shima” tana maganan tamike dasauri Lujain tarike mata hannu tana kuka sosai tace “dan Allah kada kifada musu Anty” fizge hannunta Anty Binta tayi tafita daga dakin dan sosai ranta yabaci kana ganinta kasan bala’in yunwa takeji barinma ita da yawanci ita kebata abinci tasan yanda Lujain kedacin abinci all of a sudden tana neman kashe kanta, fuuuu tawuce tasauka kasa Hajiya na zaune tareda Abee da shigowanshi kenan ganinta kadai yasa Hajiya tace “lafiya ranki abace Binta” cikin fushi Anty Binta takalli Abee daya zubamata shima yana jira yaji meke faruwa tace “Ya Imran ga matanka chan na neman kashe kanta” wani kallo daya mata yasa tadan lumshe idanu tabude tace “I mean Lujain tun safe bataci abincin kirki ba, smoothie tayi na celery wai na weight loss, yanzu ma takicin abincin da aka kaimata sai kuka take, Ya Imran kamata magana please” wani kalan kallo yamata Hajiya tace “Imrana jeka mata magana haka yara yanzu suke su kawai su gansu sun dawo kaman tsinke Allah day ya kyauta jeka mata magana” wayanshi yaciro batare daya dagokanshi ba yace “kubarta taji yunwa zataci abinci da kanta” baki Hajiya tabude zatai magana yamike tsaye yace “I have to go Hajiya”.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply