Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 33


Sakon So 33
Viral

EPISODE 3️⃣3️⃣
Afalo yasami Musty yana zaune kusada Hajiya rikeda radio nata da screw yana gyara wata Yar waya data katse ciki, dago kanshi yayi jin kamshi dakuma sallaman Abee yace “shine zaka koramin mata to ai gani nan nazo daukanta ko angaya maka nima so nake tana zama agidan dakake zaune bayan kowa yasan you are bad energy” wani kalan mugun kallo Abee yamai batare dayace komi ba, Musty yace “Hajiya kinga irin kallon dayakemini kuwa kimai magana” juyowa Hajiya tayi takalli Abee hakan yasa ya gyara fuskanshi da sauri tareda dan sosa kai yayi yasami waje ya zauna Musty yagama gyara radio tareda kunnawa radio yafara magana yace “gashi Hajiya angama” cikeda jin dadi Hajiya tace “nagode Mustafa Allah ya shimaka albarka” dariya yayi yatashi bayin falo yashiga tareda wanko hannunshi yafito kusada Abee yazauna yana kallon fuskanshi yace “how far”? Kallonshi Abee yayi shima yace “what”? Dan kallon Hajiya yayi ganin hankalinta nakan radio ta yace “about that small boy”? Dan yatsine fuska Abee yayi yace “ohh I can’t even recall his name” dan murmushi Musty yayi yafi kowa sanin halin Imran aduniyan nan this answer kadai na nufin baikarabi takan yaron ba yaron kuma bai karamai magana ba, abinci Kausar takawo musu bayan ta gaida Second Dad dan haka suke kiran Musty tawuce sama.

Wuraren 11 shida Anty Binta sukabar gidan Hajiya tuni ta shige dakinta, tashi Abee yayi yarufe kofa tareda kashe wutan falon yawuce sama abincin dake gaban dakin Lujain yabida kallo dahar lokacin ba’a tababa yawuce dakinshi wanka yasakeyi ya chanza kayanshi zuwa pajamas dark blue, coffee da aka ijiyemai adaki yabude flask din yazuba a mug yadauka ya jingina da gado tareda kaiwa baki yay sipping, drawer shi yabude yaciro novel din dayake karantawa yacigaba da karantawa yanashan coffee.

Wuraren 1 tabude idanunta daga wahalallen baccin datayi dudda wutan dakin a kunne amma wani kalan jiri jiri take gani cikinta namata wani kalan ciwo dabazata iya misiltawa ba sabida yunwa, rabonta da abinci tun chips da Anty Binta tasa taci dan kadan dasafen nan sai ruwa kawai data dingasha, kokarin tashi tayi zaune amman jitayi takasa cikinta yamata kaman gyambo takasa mikewa wani kalan fashewa tayi da kuka ahaka, kofan dakin take kallo da idanunta da key kofan data ijiye gaban madubi tana tunani yanda zata tashi taje tadauki key tabude kofa tadauko abincin bakin kofan taci, da duka dan energy daya rage mata tayi yunkurin tashi wani kalan ciwo da cikinta yamata batasan lokacin data saki wani karaba tafado kasa akife tafashe da kuka sosai…..

Gently Abee yamaida novel din hannun nashi yarufe yay dan jim yana sauraron yanda take kuka wanda kaman akunnenshi takeyi, ijiye novel din yayi akan side drawer ahankali ya yaye bargon daya rufe kafanshi dashi yasauko da kafafun kasa yasaka bedroom slippers sannan yamike tsaye yana kulle boturan gaban riganshi da kyau ahankali yayi wajen kofa, bude kofanshi yayi yafita yana tafiya a natse yafito daga corridor ya tsaya gaban dakinta taredakai hannunshi ya murza handle na kofan jin har lokacin a kulle yasa yay dan jim saikuma yajuya yakoma dakinshi wani drawer yaja da keys daban daban keciki yadauki wani key yatashi yafito gaban dakin yazo yasaka key aciki ya murza sannan yabude kofan ya tsaya chak inda yake batare daya shiga cikin dakin ba, daga ita sai wani dan pink towel data daura kanta babu dan kwali tana kwance akasa ta kife cikinta da hannunta kekai tana kuka sosai dabaima fita da kyau tsabagen yanda ta galabaita idanunta akulle, sai hawayen dake fitowa daga cikinsu kana ganinta kaga wanda yunwa ya mugun galabaitar, juyawa yayi yakoma dakinshi karamin fridge dake cikin dakinshi yabude wani goran almond milk yadauko yamaida fridge din yarufe yafito dan tsayawa yayi agaban dakinta kaman wanda ke tunanin shiga ciki saikuma yashiga ciki ahankali tareda maida kofan dakin yarufe yakarasa zuwa gabanta, gently ya tsugunna tareda ijiye goran Almond milk din agefe, hannunshi yakai ahankali zai daura akan shoulder dinta saikuma ya tsaya tareda maida hannunshi yarufe ahankali yana kallon fuskanta yace “Ke” ahankali take bude idanunta kafin tagama budesu tass tadaurasu kan Abee, jiri take gani sosai amman dudda haka tagane fuskanshi, kwayan idanunta kadai yakalla da yanda sukeyi yagane jiri take gani, with a very calm and light tone yace “sit up” girgizama mai kai tayi dawani kalan sigan shagwaba tana turo pink lips nata, cikin wata kalan murya yar karama tace “carry me” dan kallonta Abee yayi dasauri kaman wanda baisan abinda taceba, ahankali take kuka tana kara kama cikinta dake yakushinta sosai tana kallonshi da idanunta dasuka kankance sosai suke juyawa, gently yazaro hannunshi yamika mata hannun guda daya batare daya tabata ba alamun tarikeshi ta tashi zaune, hannunshi takalla that is so clean ahankali kaman wata yar karaman yarinya tadaga dayan free hannunta dabata kama cikinta dashi ba, gently takai hannun saitin hannunshi dayake bata idanunta na ganin jiri takai hannun awani kalan hankali tasaka hannunta cikin hannunshi hakan yasa soft tafin hannunta yasauka akan tafin hannunshi har cikin brain dinshi Abee yaji wani iri hakan yasa ya lumshe idanunshi kafin yabudesu ahankali yadaura kan cute chubby hand nata dake cikin nashi farcenta farare fat dogaye kaman tana wankesu da farin fenti, ahankali yadan kama hannun da kyau sannan yajawota tashi zaune tayi tawani kalan fashe da matsanancin kuka tayi tace “wayyoo cikina ciwo, Uncle zan mutu” wani kalan mugun kallo yamata baice komiba hannunshi dayan that’s free yamika yabude goran almond milk din sannan yadauka yajuyo tareda mikamata yace “karba kis……” wani kalan kawo fuskanta tayi da sauri takama hannunshi hade da goran takai bakinta tanasha dawani kalan sauri kaman irin yaran dasuka dade basuci abinci ba sunajin extreme yunwa, ahankali yabi hannunshi data rike gam da kallo tanashan milk din zuwa fuskanta gently yadaura idanunshi kan goshinta da gashin kanta suka kwanta lub lub wasu kuma sunyi coiling ga kitson da akamata kanana dasukai bala’in kyau bakin jelan gashin sun soma warwarewa da kansu sosai sabida santsi, idanunta duka biyun a lumshe sai dogayen gashin idanunta dasuka jike sharkar da ruwan hawaye, dauke idanunshi yayi daga kallonta saida ta shanye milk din tass sannan ahankali tasaki hannunshi tana komawa baya ta jinginar da bayanta da gado tana kama cikinta dataji yawani kalan daure mata fiyedana da tana lashe lips dinta dan almond milk din yamata dadi bata tabashan irin madaran ba, hannunshi Abee yakalla sannan ya ijiye goran akasa yakalleta kana ganin yanda take kasan ciwon yakaru ne yace “gobe ma you should starve yourself” hannayenta duka biyun takai kan fuskanta tafashe da kuka sosai dayasa Abee kawai ya tsaya yana kallonta yarinyar nan badai shagwaban banza ba, yunkurawa yayi zai mike tsaye dawani kalan sauri tazo gabanshi kaman zata shige cikin jikinshi dan komawa baya yayi dasauri kaman wani matsoraci yace “Ke what”? Cikin wani kalan kuka tone tace “har yanzu yunwaaaaa” dan hararanta yayi yatashi yajuya yafita daga dakin yamaida kofa yarufe tsugunnawa yayi abakin kofan ya kwashe kulan abincin da flask yawuce yasauka kasa yana tafiya ahankali, bude kulolin dinning yayi babu wani abinci daya rage hakan yasa gently yajuya yakalli kofan kitchen dinsu ahankali yabude kitchen din, rabon daya shiga kitchen dinan harya manta ko ranan a microwave na dinning yadumama abincin yakai mata, dan tsaki kadan yayi yashiga kitchen din ruwa yasa a kettle sannan yay shiru yana tunanin meya iya dafawa mezai kaimata? Idanunshi ne suka sauka akan egg, guda two yadauka yafasa saikuma kaman wanda yay tunanin wani abu yakara two again yafasa yasa pan a wuta da oil juye kwan yayi dayadan soyu yajuya sannan yakwashe a plate yakashe gas din yataho yahada mata tea mai kauri yasa a tray yadau bread yafito yawuce sama yana tafiya ahankali, bude kofan dakinta yayi ahankali tana kwance inda yabarta ganin yashigo da tray da sauri tamike tana zaro idanunta dasuka kankance tana kallon tray daya shigo dashi, karasowa gabanta yayi ya ijiye tray akasa dawani kalan sauri tadauki tea zatakai baki dasauri yace “Ke is hot” fashewa tayi da kuka sosai da abin yaso yama bashi dariya dan girgizakai kawai yayi danbaimasan mezaice ba yace “give it to me” karban mug din yayi yajuya tea tareda daukan bottle water mai sanyi dayasa akan tray yakara ruwa kadan aciki sanan yasake juyawa yadauka yabata dasauri takarba takai bakinta tafarasha, bread yabude yaciro one slice yabata sauke tea tayi daga bakinta da sauri ta ijiye akasa takarbi bread din, da spoon yadebo fried egg din yadaura mata akan bread din dasauri tai folding nasu takai bakinta ta gutsura gadai kwan da zafi amman ko gishiri babu a kwan bare Maggi, dan dago idanunta ahankali tayi takalleshi hada idanu sukayi dasauri ta maida kanta kasa tacigaba dacin bread din da kwan ahaka sannan tadau tea tasha, bread yakara daukowa yabata zai samata kwan ta girgixamai kai alamun a’a bari yayi ta karbi bread din taci, kusan 9 slice of bread ta cin ta shanye tea tass sai alokacin taji ciwon cikin yadaina sosai, half fried egg dake plate din takalla saikuma tadan kalleshi hada idanu sukayi karaf kai tsaye yace “what” dan zaro idanu tayi tareda dan turo baki kadan kaman mai tsoron fadin abinda zata fadi murya chan kasan makoshi tace “you can’t…..cook Uncle” takarashe maganan wani short smile na kubuce mata abaki dayasa dimples dinta suka wani kalan lotsa duka biyun dawani kalan sauri Abee yadauke kanshi yashiga hade komi a tray sanan yamike tsaye batare daya kalleta ba yace “is that your thank you”? Wani kalan sunnar da kanta kasa tayi akunyace tace “thank you” dan dago kanta tayi jin bataji any motsi ba hada ido sukayi wani mugun kallo yamata dayasa ta sauke kanta kasa dasauri yajuya yafice daga dakin, sauka yayi yana maimaita abinda tacemai wai you can’t cook uncle, children of now adays ba basu da at all, kitchen yashiga ya ijiye tray din harya juya saikuma yajuyo hannunshi yakai ahankali ya gutsuri fried egg din kadan yakai bakinshi dawani kalan sauri ya tofar sai yanzu yatuna baisa komi a kwanba kawai ya fasa ne ya soya, wani kalan kunya yaji girgiza kai kawai yayi yawuce yafita daga kitchen din yahayo sama kallon kofar dakin nata yayi yawuce yashiga dakinshi bayi yashiga dan dauro alwala dan yanzu lokacin sallan daren shine.

https://chat.whatsapp.com/DinmgBAo43r4mDZSIUvrBb
Exquisite world collections

Muna sai da jakakkuna da takalma masu kyau wanda idan kuka siya ba lallai ku sake ganinsu wani wuri ba . I assured you. Ku siya ku godemin daga baya domin ingancin kayana. Ina turawa ko ina kike ni kuma Ina Abuja.

Wannan shine instagram handle dina.

I’m on Instagram as shukhria. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ithkqozo1zuq&utm_content=oeu4f73

08108517010 wannan shine number wayana kuma dashi zaku sameni a whatsapp.

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply