Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 34


Sakon So 34
Viral

EPISODE 3️⃣4️⃣

 

Wuraren 6 tabude idanunta ahankali sosai tayi mamakin yanda babu wanda yatasheta yau tashi zaune tayi ahankali tana taba cikinta dataji baya mata ciwo kuma tamike tsaye ahankali tawuce bathroom dan dauro alwala ganin small blood yasa tai brush tareda wanka tafito daure dawani towel daban zama tayi abakin gado tai shiru tana tunani tunawa datayi da wayan Mandawari yasa tasauka kasa dagudu tana leka karkashin gadon jawo wayan tayi tana dannawa ganin 6 miss calls dinshi dakuma 2 messages from him dasauri tabude messages din.

“Ke kinsan waye ni? Dan kinma samu ina kiranki shine baraki dagamin wayaba dan kina tareda wannan Baban mijin naki don’t ever call me again”
Wani kalan faduwa gabanta yayi gently tashiga second messege din.

“Wlh idan kika bari yamiki wani abu kokuma kika yaudareni Lujain saina wulakanta miki rayuwa! You belong to me Muhammad me only!”
Wani kalan faduwa gabanta yayi duk zuciyanta yamata badadi dialing number shi tashigayi daidai lokacin taji ana shirin bude kofanta dawani kalan sauri ta tura wayan karkashin cinyanta ta gyara zama tana kallon kofan daidai lokacin Kausar tashigo takalleta tace “Hajiya tace ki sauko muyi breakfast ki shirya daganan zamuje hadda” juyawa Kausar tayi zata fice dasauri Lujain tace “Kausar” juyowa Kausar tayi takalleta batare datace komiba, ahankali Lujain tace “please kibani pad bandashi da maganin ciwon ciki anjima kadan cikina zai fara ciwo” dan hararanta Kausar tayi saikuma tace “ni banda maganin ciwon ciki dan banayi” tana maganan tawuce tafita bata wani jimaba tadawo dakin dauke da pad guda biyu masu kyau dan ita kanta Lujain bata taba ganin irinsu ba bata tayi hannu tasa takarba tana murmushi tace “thank you” juyawa Kausar tayi zata fice tace “kuma kiyi sauri” tana fita tamike tsaye tareda daukan wayan taduba gani tayi yama dauki call din but ya katse sake kiranshi tayi tawuce tana shiga bayi tareda maida kofan tarufe, saida wayan yayi kaman zai katse yadauka kafin tamace wani abu yace “who do you think you are Lujain sabida kin samu mutum kaman ni na kulaki bakisan I am doing you a favor bane? Tell me what is good about you? Kene yarinya a sex tape that went viral online, kene gaki nan kaman zaki fashe, yarinya babu shape babu kyau, anhadaki da tsoho yanzu still na tsaya akanki nace zan aureki amman harkin kai matsayin ni Mandawari the biggest footballer in Nigeria na kiranki baki dagamini ba, where were you danake kiranki”? Wasu kalan hawaye ne sukazo mata sabida yanda yake mata ihu yana masifa sosai kaman zai daketa daga wayan, jin yanda tai shiru yasa abin yakara tunzurashi yace “Lujain nike miki magana ni Mandawari kikama shiru kika share? Fine dagayau bani bak……” cikin wani kalan sauri bakinta har rawa yake tace “da……..dan Allah kayakuri” wani kalan lumshe idanu yayi yanajin yanda harshenta ke rawa alamun kuka take yarasa what’s so special about this local girl da Allah yajarabeshi da sonta, idan yatuna yakirata last night bata daukaba saiyaji wani mugun kishi ya turnikeshi, dan calming muryanshi yayi kadan dan baiso yamata ihu jin tana kuka yace “kina ina jiya da daddare bayan nagayamiki zan kiraki wajen mijinki kikaje? Meya miki did he hold your hand? Touch you did he kiss you koko yanzu finally kunyi sex din da akayi accusing naku dashi ne” dasauri tashiga girgizamai kai kaman yana gabanta tace “a’a” cikin ihu k aman yasamu yarshi yace “to me yamiki! Tell me” Yanda ya daka mata tsawa saida ta janye wayan daga kunnenta dan kaman zai fasa mata kunne, maida wayan kunnenta tayi ahankali tace “wlh babu abinda yamini jiya banida lafiya ne” ahankali yace “are you sure”? Gyadamai kai tayi tace “eh” dan sassauta muryanshi yayi yace “meya sami baby na what’s wrong with you”? Dan murmushi tayi jin yanda yakirata da baby ahankali tace “cikina ke ciwo I was so hungry” dan shiru yayi saikuma chan yace “waike akwai abinda kika sani sama da abinci kuwa aduniyan nan? Sabida nahana ki kada kici abinci shine zaki bingile da ciwon ciki, hope bakici abincin ba haka kika kwana”? Gyadamai kai tayi ahankali tace “eh” dan murmushi yayi yace “good baby, that’s why I love you” wani kalan murmushi tayi mai dan sauti yace “tom yanzu kije ki nika fruits kisha idan akwai salad zaki iya ci, daga yanzu salad su yayan ganye da yayan bishiya ne abincin ki kinji” gyadamai kai tayi tace “tom” ahankali yace “I want to see you today, 4 ne za’a fara event dina a city conference center zan turamiki address din, makesure you look peng okay” gyadamai kai tayi saikuma kaman mai tsoron magana tace “mutane zasu ganni suganene nice ta video” murmushi yamata yace “babu wanda zai ganki you are coming to see me akwai wanda zaizo yadaukeki yakawoki har private room danake ciki okay” gyadamai kai tayi tace “to” murmushi yayi yace “now go and have breakfast Mandawari’s baby, I love you Lujain” wani kalan sanyi taji azuciyanta tadade tana mafarkin rannan da Mandawari zaice mata he loves jitayi kaman zata zauce, wani kalan murmushi tayi zatai magana taji ya katse wayan fitowa tayi daga bayin tawuce tadauki wani handbag cikin wayanda Anty Binta tasaya mata tasa wayan aciki sannan ta shirya tsaf cikin wani Riga da skirt na kanti milk skirt din yawani kalan fito da katon hips nata, inba kasan Lujain ba kaganta zaka dauka all this yaran nan dasuka kai 24/25 ne sabida yanda takeda girman jiki da gabobi saidai idan tayi magana kokuma ka kalli kwayan idanunta dan akwaita da zakin murya ga muryan Yar siriruwa, wani milk hijab sabo fil dake wardobe din tadauko tasaka takoma gaban madubi tana kallon fuskanta wayan hijabin yadan mata yawa kadan hakan yasa yadan zame baya kana ganin gaban gishinta da farko farkon kitsonta da hakan yasa tai bala’in kyau, babu abinda tashafa a fuskanta amman tai wani kalan kyau tai haske sai naman idanunta dasuka danyi ja sabida kukan datayi jiya da daddare dakuma yanzun nan, turarukanta ta dauka ta feffesa tana murmushi bakaramin dadi sukedashi ba, wani black flat takalmi ta zura kafafunta aciki dan yatsun kafanta sukai wani kalan kyau aciki sosai sannan tadauki jakan tafito tana kallon dakin dabata gyaraba dudda bawani datti sauka tayi kasa Hajiya ne kawai a falo sai Kausar dasu Aneesarh da yaran Ibro da Baban su yakawosu yanzun nan yafice, ganin Lujain yasa Hajiya tace “zonan Lujain karna karajin kince barakici abincin agidan nan ba kina jina, ke bakisan kiba rahama bace jibeki kaman asace agudu kina nema ki lalata kanki dawani rama, Allah shiya hallito sirara shikuma ya hallito masu kiba to akanme kikeso kice ke ga wanda kikeso? Kada nakarajin kinyi irin abinda kikayi jiya kinji” gyadama Hajiya kai tayi ahankali kanta akasa tace “baran karaba Hajiya kiyakuri” wani kalan murmushi Hajiya tayi tace “nayi yanzu jeki debo abincin ki kizo nan kici Hamza zai kaiku hadda mijin naki yafita ni banmasan inda yaje yau asabar da sassafen nan ba Imran dabai cika fita weekends ana kiranshi awaya yafice, tafi hado breakfast naki kizo” tashi tayi ahankali tawuce kitchen babu kowa a kitchen din, blending fruits tayi kaman jiya ta shanye a kitchen din tana bata fuska sannan tahada tea batasa madara ba ta debi kwai tafito kin zuwa falon tayi tazauna a dinning ta cinye tass sannan ta tashi takai komi kitchen saida ta wanke sannan tafito Hajiya tace “tashi Kausar kutafi Hamza na tsakar gida” tashi Kausar da itama ke sanye da hijabi tayi tadauki jakanta tai gaba Lujain tabita abaya tace “muntafi Hajiya” murmushi Hajiya tayi tace “adawo lpy” bude kofan tayi ahankali tafita daidai lokacin wani jeep na benz na shigowa cikin gidan motan tabi da kallo daga ita har Kausar suna sauka daga dakali, parking motan yayi bude gaba akayi aka fito Abee ne yana sanye da jean da wani t-shirt fari mai v neck daya kamashi sosai chest dinshi yafito broadly, kafanshi sanye da crocs black, kofan baya yabude ahankali Gwaggo tasauko daga motan tana wani kalan washe baki tana gyara dankwalin kanta dake neman zamiyewa hannunta rike dawata Yar purse da akayita da yadin atampan jikinta takalli Lujain dake kallonta saikuma ta taba Abee tace “jibin mini sha sha shan yarinyar chan taganni kuma ta tsaya sangangan kaman gunki tana kallona uwa bata sanni ba” wani kalan murmushi Lujain tayi jin muryan Gwaggo batasan lokacin data wani kalan kwasa da gudu ba tana zuwa wajen wani kalan mugun tsalle tayi ta rungume Gwaggo tana wani kalan dariya da bala’in murna. “Oyoyoooo Gwaggooo na”.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply