Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 36


Sakon So 36
Viral

EPISODE 3️⃣6️⃣

JaI

Fita tayi daidai Gwaggo da Kausar data rike mata hannu na hayowa sama Gwaggo na salati tana sallallami tace “bani zaku maida kuturwa agidan nan ba, wannan bene haka haba” karasawa dakin Lujain din tayi atare dukansu ukun suka shiga dakin Gwaggo na ganin Lujain duke tace “ke kinfara ciwon cikin ne ohhh ni wannan ciwon ciki yaushe zaibar Yar nan, ina kukasa akwatinan nan nasaka miki maganin aciki, Binta da Kausar kutayani dagota ahankali kafanta yarike” da Anty Binta da Kausar ne suka dagota da kyar kwantar da ita sukai akan gado sannan Anty Binta takawo mata akwatinan Lujain din Gwaggo ta aika Kausar takawo ruwa, nan da nan Gwaggo tajika mata wasu magunguna saida sukai da gaske sannan tasha kadan Gwaggo tace “kunganta nan banga wanda yakaita laulayin ciwoba tun tana yar yarinyan ta amman tafi kowa tsanan magani” bacci ne ya kwasheta Gwaggo tamike takalli Kausar dake kallonta tace “zomuje ki kaini bayi” daga Kausar har Anty Binta dariya sukayi Kausar tanuna mata kofan bayi tace “ga bayi nan” ahankali Gwaggo takarasa tabude bayin tana kallon komi naciki saikuma tajuyo takalli Kausar tace “yoo ta ina na iya amfani da kalan wanga bayi kaman a film” kaman abinda Kausar da Anty Binta ke jira kenan dariya sukayi Kausar tashiga bayi ta gwadama Gwaggo komi sannan tafito suna duk suka fice yin salla.

Bayan anyi azahar Abee yashigo gidan sama yayi daidai Anty Binta nafitowa daga dakin Lujain dake bacci kaima Gwaggo abinci ledan magunguna yabata dasauri takarba taredayin murmushi tace “thank you Ya Imran” wucewa yayi abinshi itakuma tajuya takoma dakin Gwaggo tabama ledan tace “gashi Gwaggo mijinta yasayo mata magani” wani kalan murmushi Gwaggo tayi tasa hannu takarba tace “yayanku na kulan mini da jika da kyau Allah dai ya sakamai da alheri, idan ta tashi dakaina zan kiraki kizo kibata danni ba gane rubutun maganin asibiti nikeba” murmushi Anty Binta tayi tace “to shikenan” wucewa Anty Binta tayi tafita itakuma Gwaggo tabude kuka ta debi shinkafa da stew da soyayyun kaji dayawa tana murmushi tace “abinda ba’aci agidan ubanki kenan sai salla salla inbadai nina soyamiki” sosai taci tai kat tasha ruwa da lemu anan kasa bacci yay awon gaba da ita.

Vibration yatadata a bacci datakeji kaman a kunnenta bude idanunta tayi ahankali tana dube dube saikuma chan ta hango waya akarkashin gado nakawo haske yana vibration hannu Gwaggo tasa tace “waya manta da wayanshi adakin nan gashi sai kira ake” tashi tayi tafice rikeda wayan dake vibrating bude kofa tayi daidai Abee da dawowanshi kenan daga sallan la’asar a masallaci yahayo saman ganin Gwaggo yasa ya sunnar da kai kasa ahankali yace “ina yini Gwaggo” murmushi Gwaggo tamai itadai bakaramin kima da mutuncin shi take ganiba tace “kaga Imrana bansan ko Binta ko Kausar bane sukabar wayansu ba bacci fa nake naji giririrriii natashi shine naga waya akarkashin gado anata kira itakuma tana bacci balle nabata takawo musu gashi katayani basu bari naje nai salla tunda wayan yatadani” ahankali Abee yakarbi wayan daidai number da akai saving da Mandawari na kira Gwaggo kuma tajuya takoma daki tareda maida kofa tarufe Abee yadade yana kallon wayan harta katse daidai nan kuma yaga hoton Mandawari ajikin screensaver, yakai kusan 2min yana tsaye awajen kallon wayan yake yaji zuciyanshi nawani kalan tafarfasa dayarasa dalilli kafin ahankali yafara tafiya yawuce dakinshi, Binta IPhone 14 take amfani dashi, kannenshi da yaranahi dukan su 13 pro max garesu har Kausar Wanan ne kawai 12 agidan nan, yana shiga dakinshi ijiye wayan yayi kan desk yawuce yafada bayi.

 

Wuraren 5 tafarka ita kadaine adakin amman tana iyajin muryan Gwaggo anan falon sama tana zuba sai waka takema jikokin gidan su Aneesarh, gently ta tashi zaune tanajin ciwon cikin nadawo mata sabo fresh, sauka tayi dagakan gadon ahankali tawuce bayi wanka tayi da ruwa mai zafi sosai tafito daure da towel shiryawa tayi tsaf tadauki wani simple gown mai spaghetti hand anytime take period she don’t use to feel comfortable at all takurama rayuwanta yake ba kadan ba dan batason saka pant naturally, kuma batason zama da kaya, feffesa turaruka tayi tana kallon kulolin abincin dake dakin amman bakinta baya mata dadi daga kanta tayi tabi dakin da kallo idanunta ne suka sauka kan agogo 15min after 5, wani kalan zaro idanu tayi tamike tsaye dasauri tai wajen gado taleka zata ciro wayan da dazu tacire daga jaka ta tura karkashin gado amman bata gani ba, tashi tayi dasauri taje ta dayan side din gadon tana leka karkashin gadon amman bata ganiba jin anbudo kofa yasa dasauri ta dago Gwaggo ne, zaro idanu Gwaggo tayi tace “ke ciwon cikin keneman sakaki shigewa karkashin gado, zokisha magani mijinki yasayo miki kici abinci” shigowa Anty Binta tayi tace “sannu Lujain kinji Zokisha magani” girgixakai Lujain tayi tafashe da kuka tace “ni naji sauki basainasha magani ba” Gwaggo tace “hakafa take sainai da gaske yarinyar nan keshan magani, ballo maganin kigani Binta” ballo magungunan Anty Binta tayi guda hudu ne tana gani Lujain tawani kalan fashewa da kuka mikewa tsaye tayi dawani kalan gudu tabude kofan tafita daidai Abee dake waya yazo zai wuce wani kalan fadawa jikinshi tayi one two three Abee yay tangal tangal, baya Abee yayi kaman zai fadi saikuma yay sauri yay standing on his feet waya na kunnenshi still yabita da kallo yanda ta rirrikeshi ta kulle idanunta gam danta dauka fadi zatayi ana hello hello awayan da Abee yake yakasa cewa komi hakan yasa gently tadago kanta jin hello da akeyi hada idanu sukai da Abee dake mata wani mugun kallo dawani kalan sauri tafita daga jikinshi takoma baya, Anty Binta da Gwaggo dasuka fito dasauri Gwaggo tace “yauwa Imrana kaga magani take guduwan mawa haka hartanacin karo dakai gashi mugun ciwon ciki take” kallon Anty Binta dake rikeda maganin da ruwa a hannunta yayi babu alamun wasa a muryanshi yace “bata tasha” mikamata Anty Binta tayi tace “gashi” karba tayi ahankali tana wani kalan shagwababben kuka daga Abee har Gwaggo da Anty Binta kallonta suke, Anty Binta sai murmushi take dan gown din datasaka yamata wani kalan kyau shape nata yafito sosai, ruwa tasaka abaki sanan tadau daya zata saka Abee yace “drink all” gyadamai kai tayi ahankali takara sautin kukan datake Gwagho tace “aisai kiyi nagode ma Allah da yanzu inada maganin ki” watsa maganin tayi abakinta tana yunkurin amai Abee yace “don’t you dare” hadiyewa tayi tana batarai tawuce tashige dakin dasauri Abee yawuce yasauka kasa abinshi, abinci taci badawani yawaba dan bakinta badadi gabanta sai faduwa yake tarasa ta yanda zata tambayi Gwaggo wayan haka taja bakinta tayi shiru tun cikin namata ciwo harya daina.
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply