Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 37


Sakon So 37
Viral

EPISODE 3️⃣7️⃣
Bayan salla isha’i ta tashi daga kan gado tanajin dariyan Gwaggo dan turobaki tayi tarasa ganekan wajenta Gwaggo tazo ko wajen yan gidan nan tana gama bata tea yanzun nan takara fita, wanka tawuce tashiga tadade abayin tafito shiryawa tayi tsaf bayan ta shafa mai ta feffesa body spray tasaka wani rigan bacci orange yana nan kaman t-shirt a iya knees dinta kanta babu dankwali saitayi kaman wata Cinderella, sake tsugunnawa tayi taleka karkashin gadon tana kara duba wayan Mandawari but still bata ganiba, wuraren 10:30 Gwaggo tabude kofa tashigo dakin ganin yanda Lujain take daddaga filoli da bargo tana neme neme yasa Gwaggo tace “nashige su mehaka kika juyamin daki wai mekike nema haka kinbar mijinki shi kadai adakinshi ke kina nan tun dazu yatafi ya kwanta” turo baki tayi tazauna ganin bakin gadon tai tagumi ganin bataga wayan ba, karasowa dasauri Gwaggo tayi gabanta takama hannunta tareda mikarda ita tsaye tace “yo wai ke wace kalan yarinya ne Lulu iyye? Oya wuce kitafi dakin mijinki” turobaki tayi tace “ni anan nake kwana” baki Gwaggo tasaki saikuma tamata dakuwa kaman zata tsokale mata idanu da sauri ta kulle idanunta Gwaggo tace “aida kin barshi bude kiga yanda zan tsiyaye miki wayan nan idanuwan magen naki tunda bakida hankali, wuce kitafi dakin mijinki” akufule Lujain tace “ni bansan dakinshi ba Gwaggo kumani ki kyaleni” hararanta Gwaggo tayi kawai ta finciki hannunta tayi waje da ita tana masifa tace “da girmana billahillazi barakisa nayi abun kunya ba nazo gidanku inaji ina gani kizonan ki kwana dani barakije ki kwana da mijinki ba” duk yanda Lujain ke turjewa kin sakinta Gwaggo tayi har gaban dakin Abee kai tsaye Gwaggo tabude dakin tareda wurgata ciki itama tana shigowa Abee dake zaune gaban study yadago kanshi yakallesu yanda Lujain ke makema Gwaggo kafada alamun barata zauna anan ba Gwaggo ta washe baki tana kallon Abee tace “Imrana zan lallasa matar nan naka akanme sabida taganni barata kwana dakin mijinta ba sai wajena, kibiyoni kiga abinda zan miki” Gwaggo tawuce tafita tareda rufomusu kofan tsayawa wajen tayi chak kanta akasa hawaye ya gangaro daga idanunta takai hannayenta tanajan riganta kasa she’s so uncomfortable, Abee cigaba da abinda yakeyi yayi batare daya kara bata second look ba, gajiya tayi da tsayuwa ganin kafafunta na neman rikewa ta tsugunna ahankali akasa saikuma tazauna awajen kaman marainiya tarasa abinda kemata dadi, wuraren 11 tafara gyangyadi awajen.

12 daidai Abee yagama aikin dayakeyi tass yakashe computer sannan yajuyo ahankali yadaura idanunshi akanta gabaki daya atakure take tana gyangyadi kanta na lilo awahale. “Kee!” Wani kalan mugun firgita tayi tabude idanunta dasauri tareda mikewa tsaye tana kallon Abee awani kalan tsorace, mikewa tsaye yayi ahankali tareda zuba hannayenshi acikin aljihun wandon dake jikinshi yafara tafiya yana tahowa inda take, batasan mesaba wani kalan faduwa gabanta yashigayi yawani kalan cika mata idanu yamata mugun kwarjini kasa jure kallon dayake mata tayi dawani kalan sauri tasauke kanta kasa, karasowa yayi gabanta ya tsaya chak hannunshi zube a aljihu yana wani kalan kallonta, tunda take bata tabaganin mutumin dayamata rumfa kaman yanda Abee yamata ba ganin yanda ya tsaya daf da ita ko Baba baya mata rumfa haka, hakanan jikawai tayi kafafunta sun kasa daukanta, dukewa tayi awajen dasauri tana wasa da yatsunta, kallonta yayi cikin kakkausar murya yace “stand up!” Babu musu ta mike tsaye kirjinta nawani kalan bugawa babu kakkautawa bata tabajin kalan faduwan gaba datakeji ayanzu ba wani kalan zati da kwarjini Abee yakedashi da ita kanta bazata iya bayani ba, ganin yanda takasa dago idanunta takalleshi yasa strictly yace “look into my eyes!” Dago idanunta tayi tadaura akan nashi kasa cikakkun 3secs tayi ganin kalan kallon dayake mata zata sauke idanubta kasa azafafe yace “don’t you dare!” kafeta yayi da idanu yana tura hannunshi cikin aljihu yaciro wayan Mandawari tareda nunamata wani kalan ijiyan zuciya tasauke saida yaji saukan numfashin akan fuskanshi gashi ya tsareta da idanu bayako kyaftawa daburcewa tayi daburcewan dabata tabayiba tunda tazo duniya kawai fashewa tayi da kuka, yatsanshi yakai kan lips nashi hakan yasa tawani kalan hadiye kukan tass, anatse yace “kuka nace kimini”? Girgixamai kai tayi tanawani kalan sauke ijiyan zuciya gwanin ban tausayi, ganin yanda take numfashi kaman zata shide yasa ya sassauta murya ahankali Yace “what did I say?” Adaburce tace “kace wayan waye wannan?” Tsareta da idanu yayi alamun yana jiran amsa, lips dinta har rawa suke kaman an jonamata electric shock tace “Maa…….Man…….d…..wari yab……b……bani” tafada dukta burkice, wani irin kallo dayamata yasa taji cikinta ya murda batasan lokacin datace “a school din nan yakawomini” wani irin kallo Abee yamata yace “ina jinki” kuka ne a muryanta sosai amman yahanata yi in that crying tone tace “ina aji security guy yazo yace Yayana nakirana I thought kaine naje naga shine, he asked me yanda akai auren mu, saiya bani wayan yace zai kirani and he’s inviting me to his welcoming party, da……daz….zu ma yaaaaa…..kir……rani” Abee jiyayi kaman ta watsamai garwashin wuta azuciyanshi, nunata yayi da yatsa yace “listen here girl babu abinda zanyi dake, I don’t consider you my wife one bit, ko anjima aka kama yaron nan I will be sending you back to your father’s house batare dana bari kin kara koda kwana daya agidan nan ba, but listen here dagayau don’t ever bring wani abu that belongs to wani namiji into my house kinajina” gyadamai kai tayi dasauri tana tagwayen ijiyan zuciya idanunta na mugun kyalli sabida yanda suka cikada hawaye, cikin zazzafan murya Abee yace “nine nace you can live anyhow and talk to duk wanda kikaga dama and that same me yau na janye! Inhar kina gidan nan kina zama karkashina karki kara kula wani, idan kika kara koda kallon that small boy saina baki mamaki kinajina” gyadamaikai tayi dasauri tace “eh naji” cikin fushi sosai Abee yace “just sit and be praying akamo mutumin nan so that you will get out of my life forever nagaji dake! I am tired of you! Pray akamoshi sabida narabu dake only then you can do duk abinda kikaga dama and talk to duk wanda kikaga dama Imran doesn’t care! Understood” gyadamai kai tayi dasauri, hakan yasa yawuce fuuuuu yafada bathroom nashi, wanka yayi yafito sanye da kayan dayashiga dasu bayin yana fitowa yabude kofa yashiga dakin closet nashi yadan jima aciki sannan yafito dawasu pj dark blue ajikinshi yana wani kalan kamshi hannunshi rikeda wani babban bargo batare daya kalleta ba yace “jeki kwanta akan gado” dan dago kanta tayi takalleshi ganin yay kan dogon couch din wajen yana shirin kwanciya yasa ta tashi ahankali tai kan gadon har wani tsoron hawa gadon take, gadon fes fes bedsheet din fari kal amike kaman ba’a kwana akai, kaman wacce bata bata ganin gado ba tahaukai ta kwanta gadon nawani kalan kamshin turarenshi, bargo taja ta lullube sabida yanda dakin keda sanyi, kashe wutan dakin akayi hakan yasa ahankali tasauke ijiyan zuciya tareda lumshe ido.
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply