Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 38


Sakon So 38
Viral

EPISODE 3️⃣8️⃣
Hakanan jitayi baccin yaki zuwan mata tarasa sukuni bakaramin damuwa ne aranta ba, yace zai saketa dazaran gaskiya ya bayyana amman kuma yahanata magana da saurayinta mai sonta wanda zai aureta dazaran sun rabu, duka maganganunshi dawomata suke, wani kalan kukane yazo mata taushe bakinta tayi da bargon data lulluba dashi tadinga kuka, tarasa farincikin ta rana daya kawai sabida wani mugun shairi dawani mutum yahada mata, dudda Babanta baida kudi Babanta atampopi yake saidawa akasuwa gidansu babu Ac kaman wannan, gidansu is not mansion kaman wannan, babu motoci agidansu kaman irin manyan motocin gidan nan but she has always been a happy person, kometakeso takeci, Baba nadadewa kafin ya yanka musu kaji but Gwaggo koda yaushe tana cikin yanka mata kaji tana soyamata, dudda lokacin Mandawari baitaba kulata ba ko amsa messages nata still she’s always happy, she’s always at each she sleeps peacefully clinging to Gwaggo so tight, but rana daya she lost everything she lost her sweet life, kunya da tsoron fita take, zaman aure take dabama tagane kan Auren ba, zama take a inda batasan kowaba, Mandawari da sunan shine kullum acikin sallolinta biyar finally Allah yahadata dashi he loves her so much har yana bata iPhone IPhone dabata taba rikewa a hannu ba, but Mandawari yabata yay yay inviting nata but she couldn’t show up duk sabida wannan kaddararren auren duk dan sabida wannan shairin da aka mata, Allah kadai yasan yanda Mandawarinta yake fushi da ita yanzu ina zatasa kanta taji dadi, babu abinda kemata dadi aduniya, cikinta ne taji yadaurenata kanta na sarawa, lallashin kanta tasomayi juye juye tadingayi akan gadon tarasa abinda kemata dadi aduniya, daga baya tashi zaune tayi gashi wutan dakin akashe abinda yakara kara mata damuwa kenan, yaye bargon tayi ahankali tasauke kafafunta sama dudda dakin ba duhu mikewa tayi ahankali tana shafa bango kaman mayya tana kokarin locating bayin dataga yashiga dazu, jin ta taba kofa yasa ahankali ta murda kofan tabude wani kalan farin bayine tsaftaccen gaske ita har tsoron shigama tafara dan karta mai datti da bayin ganin yanda hasken bayin ke shigowa cikin dakin yasa tadan juya atsorace takalli kujeran dayake kai ya lullube fuskanshi kadaine ke waje dasauri tashige cikin bayin tareda maida kofan ahankali tarufe, tana kalle kalle, wanke fuskanta tayi da ruwan sanyi takalli fuskan nata a madubi idanubta sunyi jajir sun kumbura sabida kuka, bayin tabida kallo ganin bataga towel ba wani drawer mai bala’in kyau datagani takai hannunta har rawa yake tabude towels tagani kusan guda 10 farare tass anmusu wani kalan rolling ninki sotake tadauka tadaura amman yanda taga an gyarasu awajen yasa tsoro ma yahanata tabawa, bayin tashiga kallo tana kallon sabulan wankanshi kadai kusan 13, different shower gel na maza, da scrubs dakuma set na bubble bath, abubuwan dayake dashi ko ita batadasu bayin sai kanshi yake bude kofan tayi ahankali tafito ta maida tarufe tana daddafa bango tawuce takoma gadon ta kwanta ahankali tacigaba da rolling still takasa bacci sai wajajen 2:30 bacci yay awon gaba da ita.

Tashi Abee yayi ahankali ya zauna dan all this while ba bacci yakeba yan addu’a yayi 3 dot as usual yatashi yawuce bayi alwala yayi yafito yahau kan dadduma yafara salla har zuwa 4:00 yanakan dadduma sannan yatashi bayi yashiga wanka yayi yafito da pj dinajikinshi yawuce closet nashi shiryawa yayi cikin wani jallabiya fara kal da hula sai kamshi yake zubawa yafito ko kallon gadon baiyiba dan yasan ba salla takeba yabude kofa yafito tada mutanen gidan yayi suka wuce masallaci.

 

Wuraren 6 tabude idanunta ahankali tanabin dakin da kallo daya kunna wutan ciki, gently ta tashi zaune kaman wacce ta tuna wani abu saikuma ta yaye bargo tasauka daga gadon dasauri tana kallon zanin gadon ganin bata batamishi ba yasa harwani ijiyan zuciya ta sauke, agurguje tashiga gyara gadon dan amike taga bedsgeet din kaman ba’a kwana akai, maida bargon shima tayi ta shimfida yanda tasameshi sannan tajuya tana bin dakin da kallo dakin komi white kar kar sai kamshi kaman kada kafita shi karan kanshi dakin nauyin kallo yake mata kaman mai dakin naciki, kaman yana kallonta daga wani waje wucewa tayi tafita daga dakin dasauri tawuce dakinta tabude kofa tashiga babu Gwaggo adakin ko ba’a fadamata ba tasan tasauka kasa ne bayi direct tawuce brush tayi tai wanka tafito tasake shiryawa tsaf wani gown tasaka very simple mai ruwan ganye daya tsayamata a guiwa sannan ta feffeshe jikinta da turare tasake kwanciya agado tanajin wani sabon ciwon ciki dan rabonta da magani tun wanda tasha jiya, bude kofan dakin akayi Anty Binta ne murmushi tayi ganinta sanye da gown idan tasaka kaya saitayi daban saita kara kyau, karasa shigowa dakin tayi da katon tray tace “sauko kiyi breakfast kisha magani bari nakawo miki atampopinki da aka gama dinkawa jiya daman sabida bakida lafiya ne nan baki ba” tana ijiye tray akasa tawuce tafita, saukowa tayi ahankali tazuba shayin a cup tana kallo, bude kofa Anty Binta tayi tashigo dawani katon ghanamasgo dan anan telan ta lodo kayan bin Anty Binta tayida kallo data wuce gaban wardrobe nata tashiga jera kayan itakuma ahankali tadauki tea ta shanye tasss, takasa cin daidai da kwai kawai babu abinda kemata dadi ko kadan dawowa wajen Anty Binta tayi tadauki magungunan ta tashiga ballo mata tace “ga maganin kisha tundadai yauma baraku hadda ba sai kuma next week ke ba lafiya Kausar kuma wai bazata ita kadaiba saikace da chan ba ita kadai ke zuwa ba” tabe fuska tayi ganin maganin da Anty Binta ke bata, Anty Binta tace “wlh ko kisha kona fita nakira miki Yaya Imran daman yadawo” hannu tamika mata dasauri kaman zatai kuka tace “ai zansha” runtse idanu tayi tasha kaman zatai amai da sauri Anty Binta tabata tea tasha sannan ta tashi zatahau gado Anty Binta tace “sauka kizauna bakisan babu kyau dazaran mutum yaci abinci Ya kwanta ba, baida kyau sannan yanasa kiba, yanasaka katon ciki, medically kuma yanasa abinci yadawo maka har hanci tashi muje falo ki gaida su Hajiya saiki dawo ki kwanta tunda bakida lafiya” Gyadamata kai Lujain tayi tamike tsaye ahankali tareda saka slippers zata fita Anty Binta tabita da kallo yanda manyan hips nata ke shaking a rigan are way too sexy, wani kalan crazy sexy shape ne da Lujain babu abinda batadashi all this chubby orobo fine yaran nan she’s just one, gashi su Harun da Musty duka abokanen Ya Imran na falo idan akwai one thing datasani kan Ya Imran lokacin tun Mamansu Kausar na raye shine yanada bakin kishi dudda dai Lujain bawai sonta yake ba kokuma yadauketa matsayin mata bane still bazaiji dadi tafito falo haka gaban abokanenshi ba babu ko dan kwali gatada gashi duk wanda zai kalli kitson shukun kanta saiya kara sabida yanda yay kyau bakin kiston duksun warware ma tsabagen santsi sunyi coils, “Lujain” Anty Binta takirata dasauri ganin harta bude kofa, juyowa tayi Anty Binta takalleta tace “zoje dauki hijabi kisaka” Gyadamata kai Lujain tayi takoma tashiga cikin dakin tana tafiya ahankali Anty Binta na kallonta dan bata saka bra ba yau ko singlet dinma bata saba rigan kawai tadaura ajikinta Anty Binta tace “maisa baki son saka bra Lujain batun yau na lura ba bakison nonon ki zasu zube ba” karasa saka hijabin tayi tareda lankwaye kanta murya chan kasa dan yau ko magana ma bason yinshi takeba tace “ni damuna yake” yanda tai maganan Anty Binta takalla saikuma tai murmushi tace “muje” mamaki kawai take da har yanzu Abee bai farason Lujain ba she’s damn adorable, yanda yake abubuwa ashagwabe, her expression, dan karamin pink lips nata, kumatunta are just so sweet and too cute to watch, she just wish inama Allah zai bata diya Yar chubby haka kaman Lujain daba karamin dadi zataji ba.

Tunkan takarasa saukowa Gwaggo dake falo suna hira dukansu Maman Aneesa, Ibro da matanshi, Hamza, Musty, Harun da matarshi Amina dakuma Hajiya, Gwaggo ta dama musu fura mai dan karan dadi har Hajiya saida tasa aka zubamata tanasha shima Abee na rikeda cup a hannunshi yanasha yanadan danna wayan dake hannunshi baya amsa hiran dasuke, ganin Lujain da Anty Binta yasa Gwaggo takafe Lujain da idanu saikuma tajuya takalli Abee da hankalinshi kekan waya tace “Imrana wai wani mai kasiyama Lujain ne haka kaga yanda takara uban haske kuwa wannan ai zabiya take neman zama Innalillahi” Anty Binta dahar sun karaso cikin falon da Lujain da kanta ke kasa sabida yanda Gwaggo tasa duk ake kallonta tace “Gwaggo man datake shafawa bayasa haske ko daya nima shinake shafawa kawai gyara jikine dashi yasa asalin kalan fatarka tafito bagashi ni ina shafawa ba amman ni baka ce” baki Gwaggo takama tace “ba shakka ai haka mahaifiyarta take nan fara tal usulin bafulatana, Maman mahaifiyarta takoya mini yanda ake fura da nono, toke rashin lafiyan har bakinki yakama ne Lulu kinzo kinga tulin jama’a baraki gaisuwa ba” sauke kanta kasa tayi ahankali tana wasa da fararen yatsunta tace “ina Kwanan ku”.
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;

Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply