Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 40


Sakon So 40
Viral

Dago manyan idanunta tayi ta kalleshi yanda ya tsareta da idanu yasa takai bayan hannunta tagoge fuskan nata tass murya chan kasa tace “sabida nace zan bita idan zata koma gidan mu” tunda take maganan lips nata da kumatu yake kallo, dauke kai yayi yace “jeki cemata nace takara miki” dasauri tadago idanunta takallai, wani mugun kallo yamata yace “tunda bakijin magana, what did I tell you about this thing” yay maganan yana pointing towel na jikinta da hannu, dasauri ta tura kofan dakin tashiga tareda maida kofan yarufe girgiza kai kawai Abee yayi yawuce yatafi dakinshi.

Tunda Gwaggo tashigo gidan gidan yakara wani kalan dadi da annashuwa Baba yay kiran dubiyan nan Gwaggo taki dauka wai ita barata komaba saitagama hutun datazoyi agidan nan koda wasa kuma babu wanda yataba muna ta isheshi koyagaji da ita saima dawowa datayi kaman itace asalin Gwaggon gidan.
Kullum dare Gwaggo saita kadata dakin Abee dakin Anty Binta take zuwa ta kwanta dan Anty Binta ta tafi gidanta babu kowa adakin, ita rabon datasa Abee a idanu tun ranan Sunday dan Hamza ne ke kaita school yanzu, hakama Mandawari abin bakaramin damunta yayi ba bata ganinshi gashi babu halin taje koda kofar gidansu ne dan ba fita takeba.

Yau juma’a Baba cire kunya yayi shida Hadi sukazo har gidan bayan magrib awaje suka tsaya dan gani sukayi Gwaggo batasan abin kunya ba tazo gidan da jikanta ke aure ta tare tun ranan asabar haryau juma’a kwananta shidda kenan haba mana ai bai daceba.

Abee na masallaci Abdallah yazo yakirashi baiwani jimaba yafito tareda Abdallah har zuwa wajen su Baba cikeda girmamawa Abee ya gaidasu, Baba shima cikin mutunci yace “Imrana dan Allah kuyakuri da halin Gwaggo wlh fitinace da ita haba tazo ta tare taki tafiya” dan murmushi Abee yayi yace “bakomi bismillan ku” dasauri Baba yace “ai muna nan munriga munsa maigadi yakirata ta fito mutafi” danjim Abee yayi dan baisan mezaice ba, ahankali yace “dan Allah ku barta duk randa takeso saita dawo” dasauri Hadi yace “Bakasan Gwaggo bane Imrana bazata taba dawowa ba”……..

Sosai Gwaggo tafashe da kuka afalo kowa na falon lallashinta yake tanuna kanta tace “ni su Hadi kema bakinciki sabida nazo gidan jikata nahuta shine harda zuwa har kofar gida amaidani gida karfi da yaji ko….” Bude kofa Abee yayi yashigo Gwaggo takallai tana sharce hawaye tace “Imrana sunki tafiya sunce saisun tafi dani ko”? Dan shiru yayi yakalli yanda Gwaggo ke kuka dakuma Lujain dake gefenta ahankali yace “eh” saikuma yawuce sama baiwani dade saman ba yafito da bandir yan 1k guda biyu a hannunshi yazo har gaban Hajiya yabata alamun tabama Gwaggo, murmushi Hajiya tayi tabama tace “Gwaggo gashi Imrana yace abaki” ganin kudade mikakku farare fes yasa duk wani kuka da Gwaggo take ya tsaya tace “wayyo Allah na dubu dari biyu, Imrana nagode nagode Allah maka albarka ubangiji Allah yakawo ciki da goyo tsakaninka da Lujain bari natafi” tamike tana tura kudin lalita duka yan dakin murmushi sukayi, tashi Lujain tayi kaman zata bita tace “Gwag……” wani kallo da Abee yamata yasa dagudu ta juya tai stairs tana kuka Gwaggo tace “aisai kiyi tunda bakida hankali ne da aurenki zan tafi dake jama’a saduwan Alheri” duk rako Gwaggo sukayi har compund ta tafi Abee kuma yakoma masallaci.

Sosai Lujain tai kuka jitayi zuciyanta yamata nauyi da zafi Kwanan nan da Gwaggo kenan gabaki daya ta manta menene bakin ciki ko fushi har damuwan Mandawari ta manta dashi amman daga tafiyan Gwaggo saitaji komi yamata duhu sosai ahaka bacci yay awon gaba da ita.

Tun wajajen 3:30 tafarka tabude idanunta hakanan kawai gabanta sai faduwa yake abin namata kaman ma zazzabi zazzabi takeji, saukowa kasa tayi ahankali tareda daura kanta akan gado hawayene yazubo mata she’s soooo sad and she’s hungry again, all abinda takeso shine taganta agidansu.
Bude kofa Abee yayi 4 dot yafito sai kanshi yake yau Jallabiya ce ajikinshi fara da hula akanshi kofan Lujain ya kalla saiya karasa wajen anatse yabude kofan dago kanta tayi takalleshi suka hada idanu kafinma yamata magana ta mikeda sauri tawuce bayi dan haushin shi takeji daya hanata bin Gwaggon ta jiya dan jim yayi ya tsaya kaman mai tunanin wani abu saikuma yajawo kofan yarufe yawuce yatada su Abdallah yasauka kasa yajirasu suka fice tare zuwa masallaci.

Dayake yau asabar yadade amasallacin sai wajajen 7:00 nasafe yafito tareda Baba Liman dawasu jama’a na masallacin duk sun tsaya gaban masallaci suna magana kan Solar da Abee yasayoma masallacin daza’a fara aikin yau kaman an jefo mutun kawai wani saurayi suka gani agabansu ya tsaya yana sanye da jean da Riga bakake yasaka bakin facing cap da nose mask da bakin glasses dudda sunada yawa amman Abee yake facing, daya daga cikinsu yace “kaikuma Malam lafiya haka”? Tsugunnawa yayi agabansu ahankali tareda saka hannu yazare facing cap din kanshi, sannan yasa hannu yazaro shades din ya ijiye sanan yacire nose mask din ahankali ya ijiye kasa kafin gently yadago jajayen idanunshi dasuka kumbura suntum yakalli Abee dake kallonshi, dasauri jama’an wajen suka nunashi sukace “bakaine mutumin dayama Alhaji Imrana shairi ba ai munga hotonka a news” gyadamusu kai yayi ahankali sannan yahade hannayenshi yana kallon Abee dake kallonshi kuri saikuma kaman wanda ya haukace ya kwala uban kara cikin harshen turenci yace “mutanen estate din nan kufito dan Allah, gani nan nine nama Alhaji Imrana shairi nakuma kawo kaina da kaina” daidai lokacin Mandawari yafito daga cikin gidanshi zai tafi gudu chak ya tsaya yana kallon gaban masallacin da jama’a suka taru harda masu gadikan anguwan dakuma mutumin hakan yasa yakarasa wajen daidai Ibro shima yana karasawa wajen dan fitowanshi daga gidanshi kenan yazo zai shiga gidansu yaji muryan mutumin hakan yasa yashiga kiran Hamza, kallon duka mutanen dake kallonshi kuri yayi mutanen kuma suka cicciro wayoyinsu ana video yakalli Abee yace “dan girman Allah kayafemini wlh wlh bantaba sani hakkin wani abune mai girma ba sai bayan namuku kazafin nan kaida wannan innocent yarinyar” yay shiru dasauri Hamza yashiga kiran Uncle Abdul Police shikuma Ibro yashiga kiran Uncle Musty, cikin wani kalan yanayi na tsantsan nadama yace “tun bayan nai editing video nasaka a yanar gizo nakasa samin kwanciyan hankali dudda nai deleting amman a banza dan yarigaada ya yada duniya, bana iya bacci, banda sukuni banda natsuwa, kirjina da kaina wani kalan nauyi sukemin kaman an dauramini tankin ruwa akansu, tundaga ranan dana watsa video nan idanun nan nawa basu kara runtsawa da sunann bacci ba wlh wlh da wannan azaban gwara nakawo kaina ankaini gidan yari, nazone nafara rokonka da yarinyar gafara kafin nakai kaina dakaina police station dan Allah dan girman Allah kuyafemini, jama’a kutayani rokon gafara” yay magananan yana kallon kowa na wajen saikuma ya shiga babbaka kuka sosai kana ganinshi kasan babu peace arayuwanshi, ko’ina najikinshi rawa yake yace “wlh wlh koda wasa ba fasikanci sukayi ba nine na maida abin yazama haka da editing na computer, wlh nine nan na shirya komi nahada wlh wlh shairin shaidan ne da ruwan ido da son abin duniya yakaini na aikata abinda nayima Ogana mutumin daya bani aiki nake samu naciyar da yan uwana tasanadiyanshi shine nama haka dan Allah kuyakuri” kallon Baba Liman Abee yayi yace “Baba bari nashiga gida” gyadamai kai Baba Liman yayi hakan yasa yajuya zai wuce karaf mutumin yakama kafarshi tareda kwanciya akasa awajen flat yana kuka sosai yace “dan girman Allah ka yafeni kona samu na rufe idanuna yau ko baccin minti biyu ne nayi dan darajan Allah, wlh wlh bazan karaba shairin shaidan ne nasan nabata maka suna nabatama yarinyar suna kuyafeni” wani kalan murmushi Mandawari yayi ya gyara tsayuwa he’s enjoying the show koba komi yanzu ai zai sakin mai babe dinshi, daidai lokacin motan polisawa har guda uku suka shigo estate din suna jiniya, Abdul da Musty ne suka fito daga wani jeep na Musty, some police abayansu Abdul yace “you are under arrest for defamation of character, for threat, i advice you to keep quiet cus anything you say or do will be use against you in the court of law, kuyi arresting nashi” kara kankame kafan Abee yayi yana ihu sosai ihun da ko’ina na anguwan na amsawa mata har lekowa suke daga gidaje suna kallon abinda kefaruwa sai video ake, bambareshi akayi daga kafan Abee aka dagoshi sama Musty baiyi wata wata ba abunku da soja yabashi two sided mari at a spot yace “dan Shegiya zakaci ubanka yau” dasauri polisawan dasuka dagoshi suka sakeshi ganin Musty soja ya mareshi, wani kalan kwashemai kafafu Musty yayi yazube awajen kanshi yay wani kalan mugun buguwa zai kara kaimai duka Abee yakama hannunshi gam hakan yasa cikin fushi Musty yace “ku barni natafi dashi gad-room a barrack gobe nakawo muku shi police station wlh ko amafarki your generation to generation to more generation bazasu taba tunanin batama wani sunaba sabida yanda zan dispilaka kai kasan sunan wane kabata kasan waye Imran kuwa? Did you know how many lives Imran ya chanza including mine how dare you” azuciye Musty ya yunkura zai kara kaimai duka amman yakasa sabida yanda Abee yamai riko mai kyau, kaman jira yan anguwan suke sukace “ai wlh mumishi duka kafin atafi dashi, jungle justice in his life bazai kara tunanin yada abun kazafi ba yana batawa mutane suna babban mutum haka dakeda manyan yara” hannu Hamza yashiga gyarawa shida Ibro zasu sa hannu a lallasashi wani kallo Abee yamusu yace “ku wuce gida” ba musu duk suka juya batare da sunji dadi ba sukai gida, Abee yakalli Abdul yace “kutafi dashi Abdul nobody should touch him again” yay maganan yana kallon mutanen dake shirin dukanshi, bada go ahead Abdul yayi aka wuce dashi mota Abdul yabisu Abee yakalli Musty da ranshi ke bace yana kallonsu yace “let’s go” sannan yasakeshi, sai alokacin Musty ya iya motsi dan Abee akwai karfi, binshi Musty yayi suka wuce Mandawari yabisu da kallo wani kalan mugun kishin Abee yake kaman ba gobe duk ta yanda ya kalli Abee Abee yafishi in any way, what did he do how did he earned this much respect daga jama’a? Shi dudda yana footballer one of the best yadawo anguwan nan babu maibi takanshi saidai masu gadi ne ma ke tambayanshi for selfie, what’s so special about this man da ake sonshi sama dashi mai about 400M followers a just IG, har neman Abee yayi a social media amman yaga he’s not on any of those social media platform, wani kalan kishin Abee yake dabazai iya misiltawa ba baitaba haduwa da mutumin dayaji existence nashi poses as a threat to him ba sai Abee, yarasa sukuni, yanda Abee yake nuna baimasan dashi ba is what is killing him more, yaso bayan yama Abee maganganun nan Abee ya nemi bala’i dashi ko yasa acireshi daga community kokuma wani abu dazai bashi liver yay bura’uba dashi amman no baimasan ko yana rayeba.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply