Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 41


Sakon So 41
Viral

EPISODE 4️⃣1️⃣
Falo suka shiga a tsaye sukaga su Hajiya da Ibro da Hamza da Abdallah da Maman Aneesarh sai Kausar dan Lujain na sama tun safe data fito ta gaida Hajiya takoma waje Abee yasamu yazauna anatse yasauke wani kalan babban ijiyan zuciya dayasa har Musty saida ya kalleshi, Hajiya tace “Musty an wankesu? Yanzun nan Hamza da Ibraheem kebani labari” cikeda farin ciki Musty yace “Alhamdulillah Hajiya komi yazo karshe Abdul suntafi da yaron police station ma nasan anjima kadan zamuga broadcast” Hajiya takalli Abee dan murmushi kadan yasaki yakalli Maman Aneesarh da Kausar yace “I need my breakfast” wani kalan dadi Kausar taji rabon dataga Abee haka harta manta, zama Musty yayi kusadashi suna breakfast din tare sai kallon Abee yake idan akwai wanda yasan Abee sama dashi aduniyan nan yana ganin saidai Hajiya datake mahaifiyarshi dan tun suna yara tareda Abee suka taso kuma yasan menene azuciyan Abee yanzu haka alkawari daya zaiyi shine bazai taba bari Abee yarabu da Lujain ba Allah yamai kyautan taba sai inda karfinshi yakare yana cikin breakfast wayanshi yay kara hakan yasa yadauki wayan yakalli screen din ya amsa wayan chan yace “alright gani nan zuwa” ijiye wayan yayi Musty yace “ina zaka”? Ahankali yace “akwai some UK agent dazasu so daman yau, wai sunzo zanje nagansu zaka” girgizamai kai Musty yayi yace “bazani ba, mikewa tsaye Abee yayi yakalli Kausar yace “kawomin key motana adaki” gyadamai kai tayi tawuce sama tadauko key tasauko tabashi karba yayi yajuya Musty yabishi yace “ahaka zaka kaman wani black arab”? Gyadamai kai yayi yace “yes” haryakai mota zai shiga Musty yace “best friend” tsayawa Abee yayi yakalleshi, Musty yace “tell me what’s on ur mind” wani kalan kallo Abee yamai yace “kafi kowa sanin what’s on my mind” dasauri Musty yace “Imran menene aibun yarinyar nan? Why do you wanna leave her? Batada any matsala rabon danaga mutum this innocent kaman Lujain harna manta, Gatanan gradually she’s fitting into your family, batada matsala da su Kausar yaranka ko mahaifiyar ka, maisa zaka rabu da ita please accept Lujain as your wife” tunda yake maganan Abee ke kallonshi yace “ka isa kasani dolene”? Shiru Musty yamai yana kallonshi Abee yace “do you expect me nai accepting wanchan jaririyan yarinyar amatsayin mata for God sake Mustafa my last born ta girmeta what is that child abuse or mene”? Baki Musty yabude zaiyi magana Abee yadagamai hannu yace “ko yanzu ma dan fitan nan daya kamani ne Allah yakaimu anjima after isha’i dakaina zan kaita gidansu komi yakare” yana maganan yabita gefen Musty yabude motanshi yashiga yaja motan yabar gidan Musty yadade tsaye yana kallon gate din anatse yace “Imrana I am your best friend, kamin komi aduniyan nan, I’ve watched you suffered for good 13yrs, bazan taba bari ka koma rayuwan nan ba, bazan taba bari karabu da Lujain danasan she’s the best thing right now in your life ba dan bazaka taba samin matan dazaka samu peace kaman da ita ba” yana tsaye wajen aka bude gate Anty Binta ne tashigo da jeep dinta ganin mijinta tsaye yasa takarasa parking tafito tace “Baby ya akayi” fuskanta yakalla yace “Wifey inaso kibani honest answer not because of me tell me the truth kinason Auren Yayanki Imran da Lujain”? Wani kallon kallonshi tayi ganin how serious he is yasa anatse tace “Husby inason Auren su sabida banjin Ya Imran zai iya samin mata kaman Lujain ba, she’s fragile sweet and easy to handle gata yarinya kuma Lujain batada matsala, her whole life is just she and her grandma, I love them together, maisa kamin tambayan nan yace zai saketa ne sabida ankama yaron”? Gyadamata kai yayi anatse yace “Wifey I have a plan, but kafin nai plan kune yan uwan Imrana zan biku gabaki dayan ku one by one na tambayeku idan kuna sonshi da Lujain inhar dukanku kunaso I will do something today and I will need your support” dasauri Anty Binta tace “count me in” daidai nan Ibraheem da Hamza suka fito alamu yamusu dasuzo hakan yasa suka taho, Musty yakallesu yace “kunason zaman Imran da Lujain”? Dasauri Hamza yace “sosai ma Uncle Musty, wlh I love Lujain she’s so calm batada magana, ni kawai ina sonta sosai” Ibrahim yace “konima haka I wish Ya Imran zai sota sosai danafi kowa jin dadi but har yanzu he’s not ready to accept any woman”, murmushi Musty yamusu yace “kuwuce kutafi” wucewa sukayi shida Anty Binta ciki, a dinning yaga Kausar na kokarin kwashe plate karasawa yayi yana tayata yace “muje nakai miki kitchen Auta na” murmushi tayi tace “to second Dad” saida sukakai kitchen yana ijiye plates din batare daya kalleta ba yace “kinason zaman Abee dinki da Lujain” dasauri tadago kanta takallai folding hannunshi yayi akirji yana kallonta ahankali yace “Kausar kinason yanda Babanki baida peace of mind, you are not a small girl Kausar kema yau ko gobe zaki iya aure at any given time, why don’t you wanna understand your father that gives you everything? Inhar yaga kunason Lujain he will accept her too bakisan cewa idanma kina tunanin sabida kin girmi Lujain ne yasa baki sonta yarinya irinsu sune babanki zai iya ya tsawataar mawa kuma taji, yace tayi tayi tabari tabari but babba bazai taba iya controlling nata ba, give me ur answer Last Born kinason rayuwan Babanki da Lujain ko a’a”? Ahankali tace “da banaso Second Dad but yanzu inaso banso Abee ya auri wacce zata wahalar dashi gwara Lujain kaga tsoronshima takeji” murmushi yamata yace “Allah miki albarka” Abdallah da Maman Aneesarh duk ya tambaya ta siyasa suma sukace sunaso dakin Hajiya yashiga yasameta zaune bakin gado tana waya zama yayi akas saida takarasa wayan yakalleta yana murmushi yace “Hajiya kinason zaman Lujain da Imrana”? Murmushi Hajiya tayi tace “inaso sosai Musty, sonake ma yadawo muyi magana nasan nace I want to support him amman harga Allah banso yace zai rabu da yarinyar nan” murmushi Musty yayi yace “in sha Allah bazai rabu da ita ba Hajiya bari naje anjima kadan zan dawo” to adawo lpy, bude kofa yayi yafita afalo yaga Anty Binta zaune fita yayi hakan yasa tabiyoshi dasauri tace “ina zaka?” Dan jim yayi yace “I have a plan but it involves Docton Imran bari naje nasameshi baran dade ba” gyadamai kai tayi tareda murmushi motanshi yashige itakuma takoma cikin gida sama tawuce direct dakin Lujain tayi kwance taganta akan gado daure da towel tana rikeda hook nata na school alamun karantawa take ganinta yasa Lujain taji wani dadi ta tashi zaune tace “ina kwana Anty” murmushi Anty Binta tamata tace “wai wannan kan naki da santsi dukya warware Lujain tashi kisa kaya muje na kaiki saloon a tsefe awanke baraki kitso ba sai a gyara miki kumba” dasauri ta sauka dagakan gado tana murmushi tace “dama nagaji Anty” shiryawa tayi sharp sharp tasa dogon hijabinta sukama Hajiya sallama suka tafi saloon.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply