Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 7


Sakon So 7
Viral

Tana shiga school ana cewa sufito afara shigan bus dan 9:30 zasu bar school yan class nasu yan SS2 akace sufara tafiya bus nasu ita hartama saba batada friend shiga tayi itane sit 1 dan ita tafara biyan kudi tana zama tabude jakanta tadauko ledan biscuit tafaraci yan ajin saikaga wannan yataba wanchan anunata sai akwashe da dariya ko kallonsu batayiba dake bude jakan tayi ta leka wayan Ya Samira tareda dannawa taduba time dan 11 Mandawari zaizo live a IG, murmushi tayi maida jakan tarufe tana cigaba da cin katon biscuit dinta wata Yar class dinsu tamike tsaye a bus din bayan an gama shiryasu an koma wani bus ana shirya wasu yan ajin base on payment tace “Hey Class mate I have a story to tell u tantadaaaaa” duk kallonta akayi wasu yan mata da samari click dinsu sukace “we are listening princess” dariya tayi tace “I want to call some part of the body kugayamin uses dinsu” duk akace okay, tace “the eyes is for whattt?” Yan ajin sukai ihun “seeing” tace “the ears is for what”? Suka kara ihun “hearing” cikeda zolaya from her tone tace “and the mouth is for whatttttttt?” Yan ajin sukai ihu atare “eating” tace “for what” sukace “eatingggggg” Haba sai dariya duk Lujain najinsu hakan bai hanata cigaba da cin abinta ba, komawa princess tayi tazauna tana dariya saiga wata ta tashi da ake cema Lily tace “aga aga” dayake dudda akwai Christian a ajin but duk sunajin hausa universal language sukace “aga” tace “aga chop chop din aji” atare duka suka nuna Lujain sukace “aaaagannntaaaaaa” sai dariya tace “aga mara kawa” suka nunata sukace “aaaaagannnntaaaa” tace “aga mara aboki” sukace “aaaaagannnntaaaa” sanan tai wani ihu irin na final one din nan tace “aga mara boyfrienddddddd” duk aka nuna Lujain akace “aagannnnnnntaaaaa” kwarema Lujain tayi ba kakkautawa dasauri tashiga bude jakanta taduko ruwa da sauri tashiga sha saida tasha sosai sannan click din su princess din sukazo inda take tsabagen son ta kulasu Princess tace “ke miss chubby bakijimu bane Fatty bom bom” wani mugun kallo Lujain tamata batai wata wataba tamike tsaye tareda ajiye jakanta kan sir din dasauri Princess suka koma baya dan sun zaci dukansu zatayi ko zaunesu cikin kunanrai Lujain tace “Ohhkayyy you want me to say something ko” boldly takalli yan cikin bus din tace “aga aga” Yan makaranta fa akwai son bala’i da fitina, they live for it shine the joy and the fun that comes with being in school da sauri sukace “aga” Lujain tace “aga masu satan amsa during test and exam masuyin chokes olodon aji amman sunfi kowa iya makeup” habawa sai dariya kyakyalya bakaramin kunya princess da Lily sukaji ba, Lujain tanunata da hannu tace “idan kika kara kirana Chubby kowani stupid name saina fasa miki ciki, my name is Lujain but I prefer idan ankirani da LJ, and I am pretty, prettier than this bullies, and I am brilliant cus banayin choke, and I am beautiful I don’t need makeup kuma I have boyfriend a celebrity for that matter” tanunasu habawa sai ihu ajin ana bubbuga kujeru da kasan motan da kafa ana dariya yan class din suka fara matching ana tafi “LJ! LJ!! LJ!!! LJ!!!!” juyawa tayi takoma sit dinta dasauri ta bala’in danne kukan datakeji Gwaggo tasha gayamata kada tasake tayima yan ajinsu kuka idan sun kirata da sunaye dan zasu cigaba saisa bata sake tai kuka and bata taba nunawa wani dan ajinsu she needed them ba tana homework dinta tai karatunta da kanta dan Allah yamata brain.

Teacher dake incharge na class nasu ne tashigo tareda zama akan kujera tace “let’s settle down student remember not to touch without being permitted and not to go anyway da abace muje ba understood” duk suka amsa, juyawa tayi ta kalli Lujain da already ta tara ledojin biscuit uku agabanta tanacin na hudu zatamata magana saikuma kawai tai shiru ta gyara zamanta bus dinsu yafara tafiya.
Bini bini Lujain ke bude jakanta tana duba time awayan Ya Samira ganin har lokacin eleven baiyiba yasa tai murmushi ta juyarda kanta tana kallon hanya, sunyi tafiyan kusan 30min sannan sukakai wani dankareren babban building ita duk zamanta a Abuja bata taba zuwa wajenma bama tasan wajenba to inama take zuwa daga boko sai islamiyya da yamma sai hadda weekend, building na company yayi kyau an rubuta “IMRAN CERAMICS” security gate ne sukai directing nasu to inda zasuyi parking dan musamman aka basu special parking space dan student dole adauki caution saukowa akayi sannan one by one aka fara basu wani sticker dake dauke da rubutun visitor ajiki agaban riguna nan school nasu dake matsayin access card nasu, tanaji wasu yan ajinsu na “wow babban company na wannan, just look at how beautiful visitor’s access card namu” sai alokacin tama kalla dan ana bata mannawa kawai tayi saida teachers dinsu aka kara maimaitamusu yanda zasu behaving da banda tabe tabe sanan akace zasu iya shiga wani ajiyan zuciya tasauke dan surutun yasa bata iya duba wayanta ba kafin teacher sugani a kwace ahankali take tafiya kafin ahankali tasaka kafanta tashiga cikin katon hall don dayake nan reception wani kalan sanyi taji dayasa ta yatsine fuska ahankali tace “AC yay yawa” ihu principal nasu tayi da shigowanta kenan cikin personal car tazo tace “Assemble yourself student” assembly duk sukayi gwanin ban sha’awa murmushi principal din tayi daidai lokacin Hamza yakaraso yana sanye da suit cikeda girmamawa ya gaisa da ita sannan yace “sudan jira kadan CMD na attending ma wasu baki ne” murmushi tamai sannan takalli daliban tace “I am sure all my students here wants to meet the owner, the brain behind this company, this art, this ceramic work dakenan number one a Nigeria keji dashi, the only ceramic company dake exporting kayayyakin su su plate, verse, mugs, tiles dasauransu zuwa kasan waje, let’s know little about him and his success story right, what’s the best way to know inda daga bakinshi ba” student akace yes Ma tace “tom gashinan zuwa” sauke jakanta Lujain tayi tana yatsine fuska kawai anzo an ajiyesu waje daya su haryanzu baa nuna musu komiba ko mene zasuyi damai company oho, danna wayan tayi tacikin jaka ganin 11:05 yasa ahankali tace “Innalillahi na shiga uku” tashi tayi tashiga waige waige ganin teacher su anan baya tsaye yasa tai wajenta dasauri teacher tamata alamu da hannu menene? kaman zatai kuka tace “I want to pee zai zubo” binta da kallo teacher tayi kaman tamaketa tace “Ya za’ayi bazakiji fitsari ba babu kalan abinda bakici ba amota kaman danke kadai akai abubuwan ci aduniya” tai maganan tana cewa follow me binta tayi dasauri zuwa wajen wani security guard tace “excuse me rest room please my student wants to excuse herself” wani waje yanuna musu hakan yasa tace “Oya go” Gyadamata kai tayi ita bama tagane ina ake nunawa ba kawai tawuce abinta da sauri daga malaman har daliban aka bita da kallo wasu na danne dariya ganin yanda hankalin kowa yayi kanta yasa principal tace “attention” duk juyowa sukayi suna kallonta tacigaba da jawabi, ko kadan ita bataga bayin da akacemata ba amman ba wannan ne matsalanta ba waje take nema inda zata labe ta zauna takalli live na Mandawari wani babban corridor data gani yasa tai wajen da saurinta tashiga tafiya harta fita daga corridor taga wani bene da gudu gudu tana haki tashiga hawa benen at the same time tana cire jakanta daga baya duk tana gudu, kaga yanda take tafiya zaka dauka all this kafin agric ne da ake shirin yankawa sunason su gudu, wayan taciro da sauri tana kunna data tana makala earpiece akunne ta sannan tasa hannun tadauko ledan chocolate guda biyu atare tabare ledan ta yarda ledan akasa, jakan batare data rufeba ta sagale a hannunta tana finciko goran fanta da Gwaggo tasamata agefen dan ragaragan aljihun nan na wajen jaka, daidai tana shiga instagram tai logging into her account tana kokarin takai duka chocholate biyu dake hannunta baki ta balla tana kalle kalle ko kadan batasan inda takeba bama tasan tayaya tazo wajenba tadaisan dazu tahau staircase cigaba da sauri tayi ganin duka offices ne awajen kuma duka akulle yasa tacigaba da tafiya zuwa wani corridor data hango daidai tana shiga live din daidai tana yankan kwanan corridor din kawai karo taci da mutum fantan data bude dake hannunta ya kware ajikin mutumin zuwa kasa chocolate din hannunta yawani karye ajikin mutumin yafadi akasa tasan tafadi tasan taci karo da mutum amman still gabaki daya da fuskanta da hankalinta nakan wayan da shi kadaine abinda bai fadi daga hannunta ba sabida yanda tarike gamgam dan shiyafi mata komi mahimmaci ayanzu, ko kallan wanda tabuge batayiba kawai tabi ta gefenshi da bala’in gudu tacigaba da tafiya takara shan wani kwana data gani kawai taga wani kofa abude batai wata wataba tafada ciki ganin bayine ga bayuka kusan biyar kowanne da kofanshi inda take tsaye kuma wajajen wash hand basin ne da mirror yasa da gudunta tayi bayin farkon wajen tana budewa ta sauke marfin masan dakennan karkal ta zauna akai tareda yarda jakanta akasa tawani sauke ijiyan zuciya ta tura kofan dabaigama rufuwa har karshe ba balle tamasaka sakata tana kara tura earpiece din kunnenta da kyau tana kallon wani bakin gaye mai irin askin yan kwalo dinnan da aka kitsa yana sanye da rigan kwallo na magana yana murmushi wani farin hakorin makka na shunning abakinshi wani kalan murmushi tasaki takai wayan ta rungume kirjinta tareda lumshe ido zuciyanta na bugawa tace “I love you Mandawari” na kusan 30sec sannan tacire wayan daga kirjinta tafara replying to live dinshi I love you Mandawari from LJ, My heart beat for you, please check your DM kullum saina maka magana, emojis babu na kalan soyaya dabata dinga turawa ba tana. Cewa please if you see my comments ko sunana ne ka kira a live din nan kana ganin yanda takeyi kasan gabaki dayan brain nata na live din nan.
***
Waiwaye baya kadan….
Daidai taci karo dashi aka bude kofan wani office wani zai fito but ganin Oga tareda wata katuwan yarinya dake sanye da uniform ajikinshi dukansu a tsaye yarinyar na kallon waya kaman abu take nunamai shikuma Oga na kallon fuskanta yasa yakoma cikin office da sauri batare daya gama rufewa ba yana leke, wucewa tayi batare data dauki goran fanta daya fadi da gutsurorin chocolate nataba ta fanfala da uban gudu.

Chak Abee ya tsaya yanabin jikinshi da kallo gabaki dayan suit din dayasa yabaci har zuwa farin rigan ciki dan bai kulle boturin jacket dinba afarin rigan fanta ya zube ga chocolate din some sun manmanne a rigan kaman kashi, sai alokacin ma ya iya juyawa amman hartai kwana sai farin safan kafanta da sandals daya hango azuciyanshi dudda baisan kalan uniform na makarantan dazasu excursion ba but yasan babu any of his employee dazasu dressing like that dan haka that must be a student what on earth student keyi in this floor, kwata kwata nothing yahadasu da this floor dan dazaran yay welcoming nasu factory za’a wuce dasu dake ciki cikin building din suga yanda ake production, jikinshi yakara kallo tayaya zai sauka kasa ahaka yay addressing student, juyawa yayi ahankali cikeda takaici yabude kofan wani office daban ma’aikatan wajen duk suka mike batare daya shigaba yace “call cleaners agoge nan” atare sukace yes sir sannan yawuce yana tafiya anatse zuwa wani special corridor dakenan dawani hadadden office da aka rubuta CMD ajiki murda kofan yayi yaji akulle sai yanzu yama tuna yabar Ibro a office yacemai idan yagama yarufe kofa yakai mishi wasu files mota dan yana gama magana da student fita zaiyi yanada wani meeting dawasu Chinese dasuke son yamusu toiletries, wani mugun tsaki yayi yanzu dole saiyaje General rest room na this floor fitowa yayi yajuya yashiga wani corridor yafara tafiya daidai nan shima wannan employee dayaga lokacin dasukai karo yafito daga office ahankali ganin Oga yay hanyar da yarinyan tayi yasa ahankali yace “Oga yasanta ne”? Saikuma yahau tafiya da sauri yace “interesting I thought ustazun mutumin nan baison mata so apparently he’s deceiving kowa” ahankali Abee yabude kofan bayin yashiga ya tsaya gaban wash hands basin yana kallon kanshi ta madubi dan gajeren tsaki yayi ganin yanda kayanshi suka baci sosai bude tap yayi yatara ruwa a hannunshi ya yarfe hannunshi yakai yana goge chocolate din wani kalan mugun tsaki yayi ganin chocolate din kara spreading ma yake kawai kayan bazasuyi ba dole ya chanza su yasa yaciro wayanshi yakira number Ibro kai tsaye yace “where are you now”? Yadanyi shiru yace “leave the factory ka koma mota ka kawomin office key” yana maganan ya katse waya ji yayi ma he’s a bit press hakan yasa yajuya ahankali direct first bayin dake wajen dayaga kofan adan bude yanufa kai tsaye yana tafiyan yana kokarin bude belt din wandonshi daidai lokacin mutumin nan yaturo kofan bayin batare daya shigo ba yakawo wayanshi taciki yana video don baison aji mutum awajen afasa abinda za’ayi saisa yaturo waya yana video ganin Abee na kokarin cire belt yasa yaware idanu yakai hannunshi kan bakinshi aranshi yace “badai yarinyar ke jiranshi anan ba, ai Oga baya using this restroom saina office nashi” kai tsaye Abee yabude bayin tareda shiga ciki atare wani irin ware idanu yayi ganin yarinya zaune akan masan data rufe ga jakanta akasa waya a hannunta tana kallo earpiece akan kunnenta ga chocolate a hannunta tanaci tana murmushi sosai tana kallon waya, alamun kaman da mutum akanta dataji yasa tadago manyan cat eyes dinta ahankali dan ko kadan bataji shigowanshi ba dan ta taushe kunnenta da earpiece maganganun Mandawari kawai takeji, wani kalan mugun ihu ta kurma tareda zabura ta mike tsaye tana maida kofan tarufe su, takai hannayenta tadaura kan idanunta tace “wayyooo uhmmmmm” tashiga bubbuga kofan da bayanta tana kokarin bude kofan tana kuma kokarin kama bakinta ganin mutum babba kaman aljani akanta.

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply