Hausa Novels Sakon So Hausa Novel

Sakon So 9


Sakon So 9
Viral

EPISODE 9️⃣

Bayan one week!
Yau Saturday kasancewa jiya Zainab ta tafi dan mijinta yadawo yasa jama’an gidan suka ragu, kowa na gidan nanan Abdallah ne kawai bayanan danshi both asabar da lahadi duka yanada lectures.
Zaune yake a falo yana sanye da jallabiya fara mai kyau hannunshi rikeda wani cup na shayi mai kyau yana kallon Hajiya da Mustapa dawani abokinshi Haruna shima soja ne yau kuma yashigo Abuja sai hira suke da Hajiya suna dariya shi iyakanshi yay murmushi aka tambayeshi eh ko a’a idan dasabo harsun saba da halin nan nashi, idan baka sansu bama zaka dauka shine bako su Musty sune yaran Hajiya, shayin yakai bakinshi ya kurma daidai wayanshi kiran IPhone 14 pro max dake aljihun gaban farin jallabiyan shi na kara ahankali ya ijiye mug din kan coffee table dake gabanshi yaciro wayan ganin messege ne from an unknown number yasa gently yabude.
“You have 24hrs to pay sum of 100 million in cash dakuma papers na company na Imran ceramic inba hakaba we will release your sex tape ma duniya, in 24hrs time zamuyi contacting naka ta hanyar fadamaka inda zakakai komi ka ijiye”.
Abee kyar ya tsaida idanunshi kan messege din daya karanta kusan sau hudu. “Hey hey Imran!” Firgigit dayago kanshi ganin Mustafa akanshi da Haruna sai Hajiya duk suna kallonshi, ganin idanunshi yasa Mustapa yace “lafiya dai ko me kake dubawa haka”? Mustapa yay maganan yana kokarin karanta abinda ke screen nashi da sauri yay locking wayan yana mikewa tsaye yace “time for asir ko let’s go” atare dukansu suka fice suna hira Haruna yakalli wani babban gym dayaga ana fito da tsofaffin kayan workout din ciki ana saka sabo yace “anya kuwa Musty komu sojoji zamu nunama Imran training kuwa”? Dasauri Mustafa yace “inafa bakaga saisa baya tsufa ba look at him please kaman Yayan Abdallah” wani mugun kallo Abee yamai yace “kadaina maidani yaro I don’t appreciate that” Musty shima mugun kallo yamai yace “kayi zuciya kai tsufa to” daidai sun kawo masallaci.
Har suka idar da salla sex tape na ranshi to kodai bashi za’a turama sakon ba sukai mistake amman kuma sun kira sunan company shi, gida suka koma daidai an gama lafiyayyen tuwon shinkafa da miyan kubewa da kifi yana zaune akan kujera wayanshi yakara kara ahankali yabude wayan video yaga an turamai babu wani rubutu tareda video, 5 secs video ne hakan yasa yabude tareda maida karan to mute shiya gani a video abayi yana tafiya yana kokarin kwance belt zaije bayin nan just 5secs yakare shiru yayi bayan video yakare he don’t really know what to think wannan ranan dahar yay using that general restroom was ranan da yan makarantan nan sukazo to where is the sex yan second dayayi abayin nan ne sex? waye a company shi yamai wannan video? Blocking number yayi sannan yay deleting message din gabadaya dan baiga amfanin abin ba though abin ya tsayamai arai dan shi yasan baiyi wani abu mara kyau ba.
“Are you eating ko mu cinye mubarka”? Musty yay maganan yana kallon Abee, Hajiya tace “ahap wannan aishi da abinci makiya ne baci zaiba kuci abunku ku manta dashi” mikewa yayi dagakan kujera yace “kuci I will eat later ina zuwa” yana maganan yay stairs duk suka bishi da kallo, dakinshi yawuce zama yayi akan gado yay shiru sai chan yay dialing number chief head of security na company shi ringing daya yadauka yace “Sir” anatse yace “Mr James I need you to email me the CCTV footage of on 23rd right away” cikeda girmamawa yace “yes sir” tashi yayi yawuce wajen desktop nashi ya zauna tareda kunna desktop din ya bude email nashi daidai video yashigo budewa yayi sunada yawa danna kowani department daban department da office nashi yake yabude yay fast forwarding zuwa daidai lokacin dayaje bayi saikuma yadawo baya daga lokacin daya fito daga office nashi yana waya har zuwa yazo corridor nan saiga yarinyar tazo da gudu ta bangaje shi alokacin yaga wani ma’aikacin shi da bazai ma iya tuna sunanshi ba but yasan yana cikin Human Resources team nashi, zama yayi yana kallon komi harzuwa sanda mutumin yaje wajen bayi a corridor bayi akwai cctv but babu acikin bayi daidai inda mutumin yafito da wayanshi yasa acikin bayi yay lumshe idanunshi yayi yay shiru meyama yaron nan da yakeso yabatamai suna daidai nan aka turo kofan dakinshi aka shigo dasauri ya kashe desktop din ganin Mustapha da Haruna, Musty dake kallonshi trying to read something from his face yace “are you okay kuwa Imran” key dinshi na mota dake kan desk din yadauka yace “I need to go to office now something came up” ta gefensu yabi yafice yabarsu nan tsaye Haruna yace “what is this saying ma?….Hali zanen dutse ko” tabe baki Musty yayi yace “ai murdadden halin Imran bazai taba chanzawaba tun yana yaro” zama sukayi, Haruna yace “Musty yafijin maganan ka wai har yanzu bazai aureba Kodai yanada matsala ne irin I mean medical one din nan” dan dariya Musty yayi yace “lafiyanshi kalau wlh” Haruna yace “to tayaya yay surviving 13yrs ba mata ni gashi yanzu inada mata biyu na uku ma nake neman yi yanzu dan sunmin kadan, nakasa gane yaya yake surviving” tabe baki Musty yayi yace “ohon mishi idan yazo katambaye shi, ni tashi muje mu buga ball jikina yamin nauyi sabida yan kwana biyun nan damukai ban motsa jiki ba” Haruna yace “yaushe za’a gama aikin gidan naku ne kadau matanka kutafi” murmushi yayi yace “cikin this week yau suke fenti ma dazu nida Imran munje gidan” suna hira suka fice daga gidan bayan sun gayama Hajiya zasu dawo suyi dinner tace to su kawo mata inibi.

Zama yayi acikin office nashi bayan yaciro file din Human Recourse team nashi kowanne ga sunanshi da passport da information nashi awajen akan yaron ya tsaya sunanshi Abdulganiyu Olaniyi Asiwaju Razak bayerabe ne from Osun state aikin nan ne yadawo dashi Abuja this is his second year a company shi, shiru yayi yana kallon hoton yaron, saikuma ahankali yashiga daukan number shi yay dialing yaji akashe ajiyan zuciya yasauke ya maida paper ya ijiye yay shiru kana ganinshi kasan tunani yake yana nan cikin office shi kadai har magrib jin ana kiran salla yasa yatashi yakulle office yafito tareda masu gadinshi sukai salla yajasu jam’i suna idarwa kyautan kudi yamusu har mota suka rakashi suna godiya yawuce yatafi tsayawa yayi wajen masu saida fruits siyan dayawa yayi aka samai a boot harzai wuce saiga mai saida ribbon Muna yatuna batada wani gashi but yanason ribbon most time yakan tsokaneta da aukin siyan ribbon amman babu gashin dazata kama dashi kiran mai ribbon din yayi yace “kawo” dasauri mutumin yazo kafinma mutumin yay magana Abee yace “nawane duka”? Washe baki yayi yace “duka nan kayan 4,500 ne” 5k yaciro ya kirga yabashi godiya mutumin yashiga yi yaciro komi yahada yabashi karba yayi yaja motanshi yawuce.

Saida yafara tsayawa yay isha’i a masallacin anguwansu sannan yafito yawuce gida bayan ya dauki su Hamza da Abdallah daya gani amadallacin yana parking ribbon din kadai yadauka yaba Hamza key yace “ku kwashe fruits kukai ciki” yawuce babu kowa a falo hakan yasa yawuce sama ahankali yay sallama tareda bude kofan dakin Kausar tana zaune sanye da dogon rigan atampan ta mai kyau rubutu takeyi tadage ganin Abee yasa ta yarda biron ta tashi da sauri tace “Abee dana dawo daga kitso bakanan” tai maganan tana tafiya wajenshi dan yana tsaye gaban dakin, ganin yana kallon kitson da aka mata yasa tawashe baki tace “kitson yay kyau Abee” gyadamata kai yayi yace “sosai” ledan hannunshi yabata dasauri ta karba tace “meka siyamin Abee” ganin ribbons dayawa daban daban wani kalan ihu tayi ta rungumeshi tana tsalle tace “Abee thank you” dan murmushi yayi yace “saken kije kicigaba da assignment dinki, kinci abinci”? Gyadamai kai tayi tana kallon ribbons dinta hankalinta yay nisa awajen, fita yayi daga dakin zuwa nashi.

Wanka yayi shayi kawai Hajiya ta aikamai dan tasan yanda dare tayi bazaici abinci ba, zama yayi yanashan shayin yana tunani na farko babu anything like sex dayayi so wanan ma is off list, nabiyu this so called guy dake blackmailing nashi employee nashi ne and when something happen that has to do with employee naka you need to handle it with lots of precaution, he will try his number again tommorow yaga how things goes.

Washegari yay dialing number still akashe ganin har yamma still babu komi yasa ya tattara komi ya watsar dan in the first place yasan babu wani sex video ballema har ayi leaking nashi a online.

Yau monday as usual bayan breakfast kowa yakama gabanshi Abdallah tareda Kausar suka tafi school dan lecturer su nasafe yace baida lpy bazai zoba, Hamza ya sauke yara yawuce shima Abee yashirya cikin wani Italian suit black dayamai kyau bana wasaba hannunshi daure da rolex, yana kaiwa company abinda yafarayi was yashiga office na HR amman seat na guy din empty bai zuwa wucewa office nashi yayi dan yanada ayyuka dayawa dazaiyi.

 

Wuraren 10 aka fita break kowa na ajinsu SS2A yafita banda ita dake zaune tafito da duka abubuwan da Gwaggo tazuba mata a jaka tanaci one by one, tana cikin cin egg and chips princess tashigo class din da ita da Lily dawasu maza guda biyu rike da goran drinks a hannunsu kallo daya tamusu tadauke kai ganin sun dumfarota tacigaba da cin abincinta gabanta na faduwa ganinsu su kusan shidda amman bata nunaba Princess na karasowa gabanta batai wata wata ba duka kayayyakin abincinta tawani barar dasu dayasa Lujain tamike tsaye dasauri tana kallon Princess da some much anger tace “mehaka princess”? Wani mugun kallo princess tamata tanuna kanta tace “kinganni Miss Chubby, kinga Lily we can proudly say eh munji muna chokes dasauran su but I can assure you this muba yan iska bane, our vaginity is intact unlike you dakin saba har kin iya moan” wani kallan kallo Lujain tamusu tace “me akace miki nayi I don’t understand ni kike kira da yar iska”? Wani murmushi princess tayi Lily ta tofar da miyau agefe tace “you disgust me Lujain you look so innocent babu wanda zai miki kallon karuwa sabida yanda kika kware a pretending” Lujain zatai magana Princess tace “kola play the video for her” dasauri Lujain takalli Kola dake danna wayanshi yana chewing cingum abaki kaman dan daudu saiga muryan Lujain tace “wayyooooo, Hmmm, Hmmm, hmmmm” hmmm hmmm din was repeating babu kakkautawa da karan buga kofa babu wani baligi mai hankali da zaiji da bazaice Iskanci akeba, Kola da abokinshi sukahau dariya Kola yace “Ashedai Fatty bombom tasan dadi kizo muyi dake I promise zan saya miki 5 shawarma da chocolates goma expensive ones ba irin na yan 500 din nan da kike zuwa dashi school ba” dukansu sukahau dariya princess tace “karuwa kawai mai gindin roba” baki Lujain tabude zatai magana kawai taji saukan drinks masu sanyi ana tsiyaya mata akai har zuwa jikinta princess tace “bari mu miki wankan tsarki da drinks” daidai nan Principal tashigo class din dakusan all the school teachers biyeda ita abaya.

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply