Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 12


Saran Boye 12
Viral

No. 12

________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*

*_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi🤣, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana😉😘😘😍😋._*

___________________

…………….Sai da ya kammala ƙalular shirinsa cikin kayan barci wando 3quarter da riga Armless sannan ya zura slippers masu taushi ya fita. Kusan su shidda ya iske a falon kowa da hidimar da yakeyi. Wasu kallo wasu danna waya wasu surutu.
Da sauri Miracle ta ɗauki remote ta rage ƙarar television ɗin dan tasan ya tsani hakan. Shikam baimabi takan kowaba ya nufi d/table. Kafin ya ƙarasa Miracle ta rigashi isa, yana ɗaura hannunsa saman kujera zai jata baya ta ɗora nata akan nashi. A take fuskarsa ta sake tsukewa, ya ɗago fararen idanunsa ya zuba mata wani banzan kallo. Maimakon ta janye hannun saita kashe masa ido ɗaya tana murzawa a hankali. Kallon hannun yayi cike da tsantsar fushi. Duk da tsoronsa dana yanayinsa a yanzu ke ratsata bata fasaba, saima karta zaƙo-zaƙon faratan ta ta farayi tana matsawa da hannunta gaba akan nashin cike da salon iskanci.
Ita da kujerar ya haɗa ya wancakalar gefe, kafin takai ƙasa ya bita da halbi, sai gata ƙasa wanwar. Ƙarar data firgita kowa a gidan ta ƙwalla tana faman ihu kamar wadda aka yanka. Dukansu kanta sukayo, yayinda Yoohan ya sake ɗaga hannu zai ƙwaɗa mata mari Gebrail ƙaninsa yay saurin riƙesa, fisgewa yay yayi ƙwallo da kujerar kusa da shi ta dining ɗin ya juya fuuu kamar wani kumurci ya nufi sama. Da sauri Mom data fito daga wani ƙofa yanzu saboda jiyo ihun Mira ta shiga ƙwala masa kira da turanci. “Yoohan! Yoohan!! Yi hakuri zo kaci abinci”.
Baiko waiwayeba balle tai tunanin samun amsa. Da gudu ta bisa tana haɗa steps ɗin da bibbiyu. Kafin ta ƙarasa har ya tura ƙofar ya maida ya rufe. Bugawa Mom ta shigayi tana kiransa cike da lallashi “Yoohan! yi haƙuri kaji, kar kayi fushi zo kaci abinci Please”. Duk da yaransu take maganar, amma yaƙi buɗe mata. Shi tunima yabar jikin ƙofar harya shige bedroom ɗinsa.
Zuciyarsa cike da matsanancin ƙunci ya faɗa saman gadonsa ya kwanta a rufda ciki. Ji yake gaba ɗaya duniyar ta masa masifar ɗaci, yaja filo ya danne kansa da shi da ƙarfi.

A falo kam Mom data sakko a ranta a ƙuntace ta ƙarasa inda Mira ke faman kuka har yanzu, cikin faɗa tace, “Miracle bance ki fita hanyar Yoohan bane? Kin riga da kinsan halinsa baya son wannan banzan halayar amma ke kam bazaki kama kankiba. Ki cigaba, wataran idan ya karyaki ko ya miki mugun dukan da za’a gaza ganeki zaki kiyayesa ai”. Batare da ta saurari amsa daga Mira ba ta wuce ɗakinta cikin fushi itama, dan a rayuwarta ta mugun tsanar ganin an ɓatama Yoohan rai a gidan. Tana masifar son yaronta fiye da sauran ƴaƴanta.
Kuka Mira ta sake ɓarkewa da shi iya ƙarfinta su Joy na lallashinta, da ƙyar suka iya ɗagata dan tanada jiki sosai bawai siririya bace, sannan a shekaru sai dai suyi sa’anni ma da Gebrail ƙanin Yoohan ɗin.
Da taimakon su Joy Miracle taje ɗakinta, sai da suka kwantar da ita a gado Gebrail ya kalleta shima cike da takaicinta. “Mira idan baki fita hanyar Brother ba na tabbatar shine zai maidaki gurguwa kafin ki koma gidanku, nasha faɗa miki shifa a rayuwarsa yanda ya tsani shan giya haka ya tsani harka da mata. Wanda yay kashi biyu cikin ukun rayuwarsa a turai matan can basu sakashi ya iskance ba ta yaya kike tunanin ke ƙaramar ƙwaruwar Najeriya zata iya sakashi aikatawa? Ƙilama dakin kama kankine zai soki kamar yanda kikai fata, amma a haka ina tabbatar miki tsanarki yake ƙarayi dan baya ɗaukar lamarin ta fuskar soyayya, idan kinji shawarata sai ki kiyaye”. Yana gama faɗa ya juya yay ficewarsa, kafin duk suma sauran su fito a barta daga ita sai Joy da take kusan sa’arta itama. Dan twins ne ita da Gebrail ɗin. Hawayenta ta share tana danna ƙafarta data buge, da yarensu tace, “Joy wai miyasa Brother ɗinku bashi da kirki?, gashi duk iskancin da wulaƙancin da yakema mutane su Mom sai sudinga goya masa baya basa son ɓacin ransa, kamar sunajin tsoronsa ma……” da sauri Joy ta rufema Miracle baki da hannu tana girgiza mata kai, sai da ta tabbatar tayi shiru kafin ta saketa, ƙofa ta nufa da sauri ta leƙa, ganin babu kowa saita maida ta rufe sannan ta dawo wajen Miracle ɗin. Daf da ita ta zauna cikin magana raɗa-raɗa tace, “Ni kaina na daɗe inason yin maganarnan da Wani Mira, kinga dai su Mom duk su suka haifemu, amma idan kika lura sunfi son Brother Yoohan, ko yaya suka gansa a damuwa sai kiga sun rikice, sannan duk abinda yakeso shi ake masa. Kiga dai yanda kike sonsa yana wulaƙantaki a gidan nan amma basu taɓa nuna masa rashin dai-dai akan hakan ba. Kowafa tsoronsa yakeji anan gidan har Mom ɗin”. Mira dake sauraren Joy kamar mai ɗaukar karatu tace, “Yayi kuɗi ne shiyyasa ai”. Kai Joy ta girgiza mata da faɗin, “Sam ba haka bane Mira, ki tuna tuntuni suke masa wannan gatan na fitar hankali, makaranta saida ya zaɓa ya darje mai mugun tsada a ƙasar waje, har sai da ya cika burinsa na zama babban likitan da yakema duniya aiki bama Najeriya kaɗaiba, amma kina gani ni da Gebrail a 9ja muka fara karatunmu, sai yanzune da shi yace zai fita damu sannanfa suka yarda”. “Hakane Joy. to ammafa kinsan Yoohan yanada bala’in ƙwaƙwalwa, dan sister Divine tace min sanda suna primary yafi kowa hazaƙa da ƙoƙari a ajinsu, yanzu za’a karanta masa yanzu zai ɗaukesa a kai. Ni yanda ya tsaya yay karatun ya birgeni, dan masu irin shegen kaifin ƙwaƙwalwar nan tasa basu da yawa a cikin mutane, zakiga kuma mafi yawansu sunfi yarda su zama mugaye fiye da mutanen kirki, balleshi daya tashi ɗan gata ma. Amma kigafa shi a ma tsarinsa baya shan komai har giya da ba komaiba, baya neman mata, abinda kawai ya sani a rayuwarsa shine aikinsa da Family ɗinsa. Gaskiya ina masifar son gayen nan Joy, komai nashi yana birgeni”.
Dariya Joy tayi sosai, ta wani juya idanunta cike da yanga, “Ai bake kaɗaiba Mira, koni da yake Brother ɗina sonsa nakeyi, haka ƴammata da yawa suke haukacewa a kansa, shiko babu wacca ta ishesa koda kallo ma, Mom tace tunda suke da shi bai taɓa ce musu ga budurwarsa ba. Ke nifa da ƙanwa zata iya auren yayanta da Brother Yoohan zan aura fa”. Baki Mira ta taɓe cike da kishi ta ɗauke kanta batare data bama Joy amsaba.
Joy data fahimci kishi Mira keyi saita kwashe da dariya ta miƙe, amma ita tasan har cikin ranta son Brother ɗinta take da gaske. Kuma harga ALLAH tana kishin ganinsa da wata mace har Mira ɗin, dan yau sosai taji daɗin mazgar da yayma Miracle.

🤣Joy kedai muguwace to.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

_______________________

A tsarin gidan dolene duk safiyar duniya ka fito babban falo inda suke taruwa su duka har ma’aikatan gidan suyi addu’oinsu. Yoohan ne dama sai ya gadama randa ta raya masa yake fitowa idan har ya kwana a gida, dan yafi ganema yayi tasa a ɗaki shi kaɗai baisan hayaniya, garama idan Papa ya takura masa.
Yauma kamar kullum duk sun hallara, har ƙananan yaran duk an tasosu, Papa da yay tafiya ne kawai babu sai Yoohan da kowa yasan yau bazai fitoba tunda jiya da haushin Miracle ya kwanta. Amma duk da haka sai da Mom taje ta buga masa ƙofa.
Yana jinta sarai, dan tashinsa kenan yana zaune a kan gadonsa ido a rufe yana addu’ar shima. amma yay mata banza, sai da ta gaji dan kanta ta haƙura. Sauka yay a gadon fuskar nan kamar kullum a cinkushe, amma hakan bai hana ƙyawunsa da ALLAH ya azurtasa dashi bayyana ba (damma babu hasken bautar UBANGIJI a cikinsa Yoohan daya zarce hakan ga mai kallo😭).
Slippers ya zura ya nufi toilet, ya kusa mintuna goma a ciki sannan ya fito, da alama dai ba wanka yayi ba, dan kayansane a jikinsa bai canja ba. Ficewa yay daga ɗakin gaba ɗaya ya fito falonsa, a mamakina sai naga ya ɗaga labulen bangon gabas, sai ga ƙofa a wajen ƙatuwa ta glass. Danna wani abu yay a bangon ta zuge da kanta ya shiga. Ƙaton ɗakine da aka cika da kayan motsa jiki kala-kala. Gaba ɗayansa kuma da glass aka yisa, ta ciki kana iya hango harabar gidan dama cikin anguwar gaba ɗayanta. Zama yay ya ɗaura takalma a ƙafarsa batare daya canja kaya ba ya fara motsa jiki a style kala-kala. Yana a kusan mintuna hamsin da farawa amintaccen yaronsa da Nu’aymah ta fasama kai jiya ya shigo ta wata ƙofa ba wadda shi ya shigoba. Madaidaicin tiren hannunsa ya ajiye kan wani table dake can gefe gaban kurera doguwa guda ɗaya kacal dake a ɗakin, sannan ya dawo inda Yoohan ke cigaba da ɗaga ƙarfe yace, “Good Morning sir”. Sai da ya furzar da zufan dake sakko masa har kan laɓɓa sannan yace, “Morning” a taƙaice.
Ajiye ƙarfen yay ya miƙe ya sake komawa kan wani machine ɗin, sai da ya fara batare daya kallesa ba yace, “Solo! Aikin dana saka ka fa?”. Kan Solo a ƙasa yace, “Sir komai ya kammala, yanzu haka ma nasan sun kama hanyar tafiya dan tunda daddaren na sanar masa, ya kuma tabbatar min za’a haɗa komai tun a daren, a yau su tafi kaiwa”.
“Good” ya faɗa a taƙaice yana kallon agogon dake manne a bango ƙato. Lumshe idanunsa yay ya buɗe yanata faman fidda numfashi da sauri-sauri. Sajensa kansa ɗigar da zufa yakeyi balle murɗaɗɗen jikinsa dake sharkaf tamkar wanda yayi wanka. Sauka yay daga saman machine ɗin ya amshi ƙaramin towel dake a hannun Solomon ya fara goge fuskarsa zuwa wuya.
Da sauri Solo ya ɗakko tiren daya shigo dashi shima. Iska Yoohan ya furzar kafin ya ɗauka babban kofin glass dake cike da tatattun kayan marmari da babu koda suga a ciki akan tiren dake hannun Solomon. Barin wajen yay da kai kofin bakinsa yana sha, ya ƙarasa kujerar nan ƙwara ɗaya ya zauna da ɗaura ƙafa ɗaya a kan ɗaya ya ɗauka remote ya kunna television dan akwai program ɗin da yake kallo a NTA kullum safiya a irin wannan lokacin a duk inda yake, inhar kaga bai kalli wannan shirinba to sai dai inda yake babu wutar nefa kuwa.
Dawowa Solo yay gefensa ya tsaya suna kallo a tare, yana shan lemonsa suna magana jefi-jefi akan tafiyar da zasuyi yau har aka kammala shirin, dan minti ashirin ne dama. Ajiye kofin yayi ya miƙe bayan ya cire takalman yabar Solomon na gyara ɗakin da maida kowane abu inda yake.

Kusan 9am ya fito daga ɗakinsa cikin gayunsa dake rikita ƴammata, sai baza ƙamshi yake kamar wani gonar turare. Sai dai tamkar kullum fuskar dai babu fara’a. Sajen nan da gashin sunsha uban gyara na ɗaukar hankali kamar dansu kawai aka yosa duniyar.
Tunda ƙarar takunsa ta fara bayyana garesu falon yayi tsitt, kowa ya zubama hanyar benen idanu duk da sunsa wanene ɗin mai tahowar kuwa.
Kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa yana sake tamke fuska musamman da yaga Miracle zaune. Mom ce cike da farin cikin ganinsa ta miƙe tsaye tana buɗe masa hannayenta alamar yazo. Fuskarsa ya ɗan saki amma ba murmushi ba, ya nufeta ya ɗan rungumeta a gefe saɓanin ita da ba haka take buƙatar yi masaba, ta fison ta jisa sosai a jikinta, sai shi kuma sam baiso. yace, “Good morning Mom”. “Good Morning my boy, ka tashi lafiya?”. Kansa kawai ya gyaɗa mata. Tai murmushin jin daɗi tana kama hannunsa cikin nata.
“Good morning Brother”. Suka haɗa baki wajen faɗa yaran suma, amma banda Mira data haɗe rai wai ita a dole fushi take da shi. Kallonsu yay sosai da fararen idanunsa ɗaya bayan ɗaya kafin ya amsa musu da muryarsa mai amo. Ya ɗaura da tambayar lafiyarsu kamar yanda ya saba cike da kulawa da sonsu. Dukansu fuska a washe suke amsa masa, dan sunsan yana ƙaunarsu. Idan dai baƙin halinne ya motsa ba sani ba sabo yakema kowa a gidan.
A tare suka ƙarasa d/table shi da Madan Chioma, ta zaunar dashi da kanta ta shiga zuba masa abincin da tasa akai masa na musamman. “Thanks” ya faɗa a saman laɓɓa ya ɗauka cokali ya fara ci. dai-dai misali yaci, dan badan ma tafiya da zaiyiba bazai karyaba a irin wannan lokacin. Dan shi mutum ne mai ƙa’ida da tsari. Komai nasa a tsare yake tamkar wani bature😜 (mudai munsan ALLAH shike tsara rayuwa ba mutum ba😁).
Cikin damuwa Mom daketa kallonsa tace, “Badai ka ƙoshi ba?”. Idanunsa ya ɗan lumshe mata alamar amsawa. Tai saurin kamo hannunsa tana girgiza masa kanta. “Jiyafa bakaci abinciba ka kwanta, shine yanzu kuma……” “Shiiii!!” ya faɗa yana ɗora ɗan yatsansa akan bakinta, “Mom ya isheni haka”. Badan tasoba ta barsa. Yasa tissue ya goge bakinsa sannan ya miƙe, “Mom zan wuce Lagos, zata iya yuwuwa daga can bazan dawo nanba zanje ƙasar Kenya. Cike da damuwa take kallonsa, har yanzu ta kasa sabawa da waɗannan tafiye-tafiyen nasa, dan ko kaɗan batason yay nesa da ita, a koda yaushe tafison taita ganinsa tare da su.
Kansa yaɗan girgiza dan yasan miyasa jikinta yay sanyi. Ya kama hannunta da yasha farce zaƙo-zaƙo, murya a tausashe yace, “Mom kimin addu’a mana, baƙyaso na cigaba da taimakon mutane ina samun lada?”. Da sauri tai murmushi, “Inaso sosai Yoohan, sai dai aikin nan ya maka yawa, gaba ɗaya baka da wani lokacin kanka kai saina wasu. ALLAH yasa kaje lafiya ka dawo lafiya”.
“Amin” ya faɗa da yin kissing hannun nata.

Gaba ɗayansa suka fito domin masa rakkiya har wajen da motar da zai shiga take, cikin girmamawa guards ɗinsa da securitys gidan suka iso ɗaya bayan ɗaya suna gaishesa. Kamar yanda ya saba musu alkairi idan zai yi tafiyar kwanaki haka yauma duk ya bisu da shi ta hanyar Solomon dake da kusan ci dashi fiye da kowa, dan duk inda zaije tare suke tafiya, sannan komai nasa shi yake sakawa. Dan haka yasan sirrinsa sosai da halayensa fiyema dasu iyayensa. A tare suka shiga masa addu’ar fatan alkairi, ƙannensa kowa na masa shagwaɓar zaiyi missing ɗinsa. Babu dai dariya a fuskarsa, amma duk yana binsu da kallon kulawa. Kafin ya bisu ɗai-ɗai yay kissing nasu a kumatu, banda Miracle dako kallon inda take bayayi. Gebrail ya buɗe masa mota ya shiga, shima ya zagaya ta ɗayan gefensa ya shiga dan zai masa rakkiya airport ne.
Ɗaga fararen idanunsa yay ya kalli Mom da duk fuskarsa tai kalan damuwa. Yatsunsa biyu yasa a gefen bakinsa yay mata alamar *_Smile_*. Murmushin kuwa ta saki har haƙoranta na bayyana kafin ta ɗaga masa hannu. Shima yatsunsa biyu ya ɗaga mata daɗan motsa laɓɓansa kaɗan yay maganar da shi kaɗai yaji kayarsa. (Dan nidai banjiba🙄😏).

Ganin motocin sun fice Madam Chioma ta sauke ajiyar zuya, yayinda Miracle ta share hawaye masu zafi da suka gangaro mata batare data shirya hakanba.
Juyawa sukai suka koma ciki, dama yaran sun wuce school su tun ɗazun.

__________________
*_NU’AYMAH_*
_________________

Tunda garin ALLAH ya waye kaikawonsu suketayi na hidimar walima a cikin gidan marayun. Da safe kusan goma Hajjo ta iso tare dasu Hajarah. Su Umm kuma sai zuwa anjima.
A babban harabar farkon shigowa cikin gidan marayun aka kafa manyan rumfuna tare da kujeru masu yawan gaske. Sai babban munbari da malamai zasu gabatar da lectures insha ALLAH.

Nu’aymah harkokin gabanta take kawai, tama manta da wani faɗa da tayi da wasu jiya. Haka take, akwai saurin fushi da tsiwa akwai kuma saurin sauka da mantuwa. Itadai wuyarta ace ta rama kota maida murtani, daga haka kuma ta manta sai wata ta taso.
Wajen misalin sha biyu saura ta kammala shirinta cikin baƙar jallabiya datasha adon manyan jajayen duwatsu masu ɗaukar ido. Itace shigar da gaba ɗaya ƙawayen amare zasuyi a wajen walimar. Tayi ƙyau sosai, ta sake gyara gashinta da saida akasha dagama kafin ta yarda aka tsefe aka wanke mata shi. Tanada gashi gwargwado dan yana sauka mata har kan kafaɗa, amma ta tsani kitso, gashi ta zama budurwa amma batabar kukan kitso ba har yanzu. Tsifar kai ma kuka take masa da wankewa balle kuma kitso.
Jan veil ɗinta madaidaici ta naɗa, kalar saita sake bayyana ainahin hasken fatarta da kwarjininta da ƙuruciya. Ga jambakin data saka kaɗan a laɓɓa ya sake ƙawata madaidaiciyar kwalliyar tata. Sauri take taje kiran da baba malam ya aiko ai musu yanzun nan tana wanka. Tasa turare kaɗan ta fito da ɗan hanzarinta.
Tare suka tafi ita da Amal da Yusrah, dan su ukun ya aiko kira. Suma sunsha ƙyau cikin kalar rigar da Nu’aymah tasa iri ɗaya komai da komai. Akwai tazara tsakanin office ɗin baba malam zuwa sashen gidajen yaran, amma haka suka taka cikin nutsuwarsu suna ƴar hira har suka isa. Sai da aka nemar musu iso sannan suka shiga.
Baba malam ya ɗan kallesu ya ɗauke kansa, a ransa yanajin daɗi da godema UBANGIJI daya azurtasu da kamilan yara da yayi. Basu izinin zama yay kafin su gaidashi. Ya amsa musu kamar yanda ya saba. Sannan ya lissafa musu aikin da zasuyi a wajen walimar. Sai dai ba komai ya saka Yusrah a cikiba kasancewar tanada aure ita.
Suna shirin miƙewa zasu fita security yay knocking ƙofar office ɗin dayin sallama. Amsa masa sukayi, baba malam ya bashi iznin shigowa. Cike da girmamawa yace, “ALLAH gafarta malam saƙone wani bawan ALLAH ya aiko dashi”. Baba malam dake saurarensa yace, “To aike kuma Rufa’i. Nami kenan?”.
“Kayan abincine dai mota guda gasu can a waje”. Baba malam bai sake cewa komaiba ya miƙe. Shi ya fara fitowa sannan su Nu’aymah a bayansa.
Mota ce ta kamfani, dan haka baba malam ya ƙarasa suka gaisa da drivern cikin mutuntawa. “Malam ko zan iya sanin saƙo daga ina haka?”. Baba malam ya faɗa cikin fara’a da mutuntawa. Murmushi drivern yayi, shima cike da girmamawar yace, “Ranka ya daɗe wlhy nima bansan daga wa kayan sukeba, amma dai wani bawan ALLAH ne ya saya a kamfaninmu ya kuma bada wannan address ɗin a kawo tare da wannan”. Ya ƙare maganar da miƙa masa leda madaidaiciyar ruwan ƙasa.
Sai da baba malam yay ɗan jimm kafin ya amsa, dan su gidan marayunsu nada tsari, ba komai suke amsa kai tsayeba babu bincike saboda gudun abinda zaije ya dawo. “Idan bazaka damuba ko zaka bani Number ɗin Manager ɗinku?”. “A babu damuwa ranka ya daɗe, dan dama shima yace na baka idan nazo”. “To Alhmdllh”.
Wucewa sukai tare office ɗin baba malam ɗin, inda suka bar su Nu’aymah nan tsaye suna kallon kayan cike da jin daɗi da jan addu’ar alkairi ga wanda ya aiko ɗin. Suna a wajen tsaye baba malam da drivern nan suka sake figowa, a yanda sukaga fuskar baba malam ɗin yanzun sunsan ya amshi kayan shima. Umarni ya bama security ɗin nan akan a raka drivern har jikin store ɗin Orphanage ɗin a sauke kayan…………….✍

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
_ANNUR PERFUMES: GIDAN KAMSHI KENAN.! WANI KAYA SAI AMALE! HAKAN TAKE, INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGATATTUN KAYAN TURARE NA GIDA DANA JIKI DANA KAYA NA MAIDUGURI? KU MATSO KUJI! NESA TAZO KUSA, ANNUR PERFUMES. KAMFANIN TURAREN MAIDUGURI NE DA RESHEN SA KENAN JIHAR KANO. MUNA DA KOWANE IRIN SAMFURIN KAYAN KAMSHI KAMAR SU; TURAREN WUTA NA KAYA DANA JIKI DANA TSUGUNNO, MUNA DA KHUMRAH, KULACCAM GANGARIYA DA ALMISKI(THAHARA/AYSHA/BAKI DA JA) MUNA DA DECORATIONS NA TSINTSIYA DA SAURAN SU, AKWAI KAYAN MATA INGATATTU MAI SA KISHIYA KWAFA, BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNADA KAYAN MATSI YAN GASKE, NAMU BA IRIN NASU BANE. _

_DUKA WADANNAN JERIN TURARUKA MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYI ‘DAI DAI. ADIRESHEN MU; MUNA KANO, UNGUWAR GAIDA, LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK. LAMBOBIN TARHON MU: 07086341096/07069036534. MUNA AIKA KAYAN MU KO’INA A FADIN NAJERIYA, KAMSHI RAHAMA NE YAN’UWA, MUSANMAN KAMSHIN ANNUR PERFUMES DAKE SANYA NUTSUWA DA KWANCIYAR HANKALI. GA ARHA GA LAGWADAR KAMSHI SAI ANNUR PERFUMES_

____________________________

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply