Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 14


Saran Boye 14
Viral

14

……………..A tare suka fito harabar gidan, inda suka iske matan gidan da sauran samarin da basu kai ga ficewa sabgoginsu ba duk sun fito suma.
Suna ƙarasawa ga ƴan sandan Nu’aymah da Amal taje ta kira itama sai gata ta fito tana ɗan ɗingisa ƙafa. Sanye take da siket da riga na atanfa, sai ƙaramin hijjab da Umm ta sabar mata da sakawa a cikin gidan saboda samarin gidan tunda ba muharramanta bane ba.
Tunda su Baba malam suka fito jikin wasu a cikin police ɗin yayi sanyi ganin dai da gaske an turosune gida mai daraja kamar wannan dan suyi abinda basu da tabbacin faruwarsa tunda ba’a gabansu akaiba. To amma yaya zasuyi, d.p.o ne da kansa ya sakasu zuwa su kama Nu’aymah, ga kuma kuɗaɗe da sukaci har kashi biyu daga Papa da kuma guards ɗin Yoohan na toshiyar baki. (Ya rabbi ka tsaremu cin rashawa da bada ita. Amin🙏🏻😭).

Sun gaisa dasu Abba cikin girmamawa, kafin su sanar musu daga station ɗin da aka turosu da kuma abinda zasuyi. Kusan a tare su Abbah duk suka juya suna kallon Nu’aymah. Baba malam ne kawai kansa a ƙasa yana ɗan murmushi. Batare da yace komaiba ya nufi inda jama’ar gidan ke tsaitsaye suma suna kallonsu hankali a tashe.
Hannun Nu’aymah ya kama batare da yacema kowa uffanba. Itama kuma babu musu ta bisa har wajen ƴan sandan. Ya miƙama macen hannun Nu’aymah yana faɗin, “Itace wannan?”.
Kallon hoton dake a waya babban nasu yayi, kafin ya kalli Nu’aymah. “Eh itace ALLAH ya gafarta malam”. Ya faɗa cike da girmamawa ga baba malam. Murmushi baba malam yay musu yana nuna masu Nu’aymah dake kallonsa kamar wata sokuwa. “Gata nan, zaku iya tafiya da ita”. Da sauri Abban su Abdallah ya yunƙuro zaiyi magana baba malam ya ɗaga masa hannu fuska a ɗaure. Cak ya tsaya hankalinsa a ƙololuwar tashe. Hakama su Abban Adawiya hankalin nasu a tashe yake da hukuncin da baba malam ya shirin yankewa. A ganinsu ai basai anje station ba, zasu iya tsayawa su tattauna anan, musamman ma shi Abban Adawiya da yana cikin Orphanage randa abin ya faru. Kuma an sanar masa komai akai.
Godiya ƴan sanda sukai tare da juyawa da Nu’aymah zasu tafi. Tirjewa tai tana kallon Baba malam daya ɗauke kansa gaba ɗaya daga garesu tamkar baisan mi akeyiba. Hannunta ta fara ƙoƙarin fisgewa idanunta na cika da ƙwalla. “Abba wlhy bansan mina musu ba”. Tai maganar muryarta na rawa.
Juyawa baba malam yayi zai bar wajen batare daya kula maganar Nu’aymah ba. Sai da yay taku biyu uku sannan ya tsaya tare da juyawa ya kalli ƴan sanda da Nu’aymah data fisge zata dawo. Cikin tsananin kaushin murya yace, “Idan bazata biku da arziƙiba ku ɗauketa!!”.
Tsayawa Nu’aymah tayi cak tana kallon baba malam ɗin. Sai kuma ta kalli inda su Umm suke. Sake dawo da idonta tayi kan ƴan sandan da suma ita suke kallo. kunyar baba malam ce kawai ta hanasu fara cin ƙaniyarta tun anan. Tsaf ta haɗiye kukanta. Ta juya cikin ɗingishi ta nufi ƴan sandan. Basuce mata komaiba suka tasa ƙeyarta gaba suka fita waje inda motarsu take.
A gaban ƴan anguwa daketa kai kawo aka sakata a motar ƴan sanda. Gaba ɗaya hawayen da Nu’aymah ta fara ɗazun sun ƙame ƙaf. Ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta tai shiru. Sai faman cije baki kawai take saboda zugi da ƙafarta ke mata. Har suka isa police station ɗin bata ɗagoba. Sai da ƴar sandar ma ta taɓata sannan ta san sun iso. Ɗago kanta tai a hankali ta kalli station ɗin, sai kuma ta juya ga ƴar sandar dake mata kallon tausayi. Dan ita yanda taga mutanen na hanƙoro akan yarinyar ta zata ma wata tsohuwar macece, ashe yarinyace ƙarama. Itace ta taimaka mata ta fito, ta kama hannunta ganin kamarma ta kasa tsaiwa. A haka suka shiga cikin station ɗin da taimakon ƴar sandar.

“Amma Yaya ka…….” hannu baba malam yay saurin ɗagama Abban su Adawiya dake son masa bayanin ainahin abinda ya faru. Ya kallesa fuskarsa babu wasa, “Banason jin komai akan hakan Mustapha. Kaje ka shirya mu wuce banason yazam mu ake jira”.
Kai kawai Abban su Adawiya ya kaɗa masa. Kafin ya kalli su Abba Musbahu ya bar wajan jiki a sanyaye. Da sauri su Abban Abdallah suka nufi mota da nufin bin bayan su Nu’aymah, sai kawai a bazata suka tsinkayi muryar Baba malam na faɗin, “Na haramtawa kowa bin bayanta a cikin gidan nan, idan kuma wani ya aikata koda ban saniba zai fuskanci fushina”.
Cak suka tsaya daga yunƙurin shiga motar, kowannensu goshinsa na tara zufa. Babu wanda ya iya sake cewa komai har Baba malam ya shiga sashensu ya fito cikin shirin fita. Ta gabansu ya wuce zuwa sashen Hajjo data sha maganin mura tun ɗazun ta kwanta. Duk wainar da ake toyawa bata saniba dan barci takeyi. Baifi mintuna biyarba sai gashi ya fito.  Yanzunma bai kalli sashen da kowa yake ba ya nufi inda motar da zasu tafi take, sauran motocin uku da ɗalibansu zasu shiga da ƴan agaji kuma duk suna a harabar massallaci.
Suna kallo motar ta fice batare da ko mutum ɗaya ya iya cemasa a dawo lafiya ba, shima kuma bai nuna ya damu da hakan ko jiran cewar tasu ba.

Umm ce ta fara sulalewa ta koma ciki, kafin sauran suma su fara zare jiki ɗai-ɗai suna shigewa sashensu. Addah dai bayan Umm tabi tana share hawayen da ke sakko mata batare data farga da fitowarsu a cikin idanunta ba.

_____________
*_ABUJA_*

Tunda labarin kama Nu’aymah ya isa kunne Papa farin ciki ya mamayesa shi da Madam Chioma, breakfast da suke shirin zamanyi ma su kasawa sukayi, sai kai kawo sukeyi zuciyoyinsu fes kamar an basu rabin duniya.
Dolene yasa a koyama yarinyar hausawan nan hankali, dan shi a rayuwarsa idan da abinda yafi tsana a rayuwarsa to ƴan yankinta ne. Ya tsani yarenta fiye da mutuwarsa, a cewarsa babu abinda suka iya sai haihuwa, ƴaƴan nasu kuma babu tarbiyya sam, daga ƴan bangar siyasa sai masu bara. Sam mutanen da yankinsu basu masaba, inda ace zai iya zama shugaba, sai ya shafe yankin ko tarihinsu baza’a sake aji ba. (hummm Papa, a ringa sara dai ana duban bakin gatari).
Abinda papa ya keta faman rayawa a ransa kenan yana murmushi. Waya ya sake ɗagawa yay magana da d.p.o ɗin akan yanzunan a bama guards ɗin Nu’aymah su taho masa da ita Abuja. Shi kuma d.p.o ya turo da accaunt Number ɗinsa yanzu zaiji alert.
Cike da farin ciki d.p.o ya amsama papa. Babu ko tunanin komai a ransa ya aika da accaunt details nashi, ya kumayi zaman shirya takardar ƙarya akan laifin da bashi Nu’aymah ta aikataba.

(Humm! Ya ALLAH ka shiryemu ka shiryi shuwagabannin mu da jami’anmu. Ka tsame bara gurbin cikinmu, idan masu shiryuwane ka shiryesu. Idan bazasu shiryuba UBANGIJI kafimu sanin miya dace dasu, mun barka dasu😭🙏🏻).

________________
*_LAGOS_*

Fitowarsa kenan daga ɗakin theatre a matuƙar gajiye. yanda yake tafiya kawai zai baka wannan amsar. Tare yake da likitoci uku da suka tayasa aikin, sai Nurses suma guda uku. Dai-dai sun ƙaraso ƙofar wani office nurse ɗin dake a gefen damarsa ta miƙa masa tasar hannunta ya jefa hand gloves ɗin daya cire daga hannunsa ya jefa a ciki, hannu ya ɗaga musu kawai alamar su dakata anan ya tura ƙofar ya shige.
Basu damu ba, dan kowa yasan Dr Yoohan haka yake, mutum ne mai ƙoƙari akan aikinsa da himma, ga tausayi sosai musamman ga marasa ƙarfi. Bashi da yawan magana, sannan baida fara’a. Wanda bai fahimcesa ba zaita ɗauka kamar kullum shi cikin ƙuncin rayuwa yake, kokuma girman kaine bisa ga ɗaukakar da ALLAH ya basa. Idan kuma ka fahimcesa zaka gane cewa haka halayyarsa take, shi kawai aikinne a gabansa ba shiririta da shashanci ba. Akance likitoci mafiya yawansu sunada son mata, sai dai ga Dr Yoohan sam ba haka baneba. Duk yanda matan ke binsa da soyayya shi bama su ishesa kalloba, shi fa a rayuwarsa damuwarsa kawai shine aikinsa, sai ko family ɗinsa da taimakon marasa ƙarfi. Idan ya shiga cikin musulmi bazaka taɓa cewa shi ba musulmin bane, musamman daya ajiye ƙasunba da yanda yake gudanar da al’amuransa sak halayyar musulman ƙwarai. Sai dai fa idan kaci karoda sarƙar Cross a wuyansa da akoda yaushe baya fashin sakawa ne zaka gane daga ina ya fito. ALLAH ya ɗaukakashi a duniya a dalilin ƙwaƙwalwar aikin likitanci daya azurtashi da ita, likitane shi da kota wane fanni zai iya gunar da aikinsa akan mara lafiya, sai dai abinda ba’a rasaba kam, dan UBANGIJI shine mai komai da kowa.

Office ne daya amsa sunansa office. Bakajin komai sai sassanyan ƙamshin turarensa dana ac. Wanda ke zaune a rikunin kujeru uku dake can gefen office ɗin yana aiki ya miƙe yana masa barka da fitowa cike da kukawa.
Kansa ya ɗaga masa fuska a yamutse na alamar gajiya. kafin ya ƙarasa ga kujerar zamansa yaja wani file dake a jiye ya fara singing.
Tasowa Richard yay da sauri garesa yana murmushi, ya ajiye files ɗin hannunsa gaban Dr Yoohan ɗin yana faɗin, “Doctor akwai mutane biyu da zaka ganifa yanzun kafin ka tafi hutun awa uku da rabi, idan lokaci ya cika zaka sake shiga theatre room, na mutane biyu da suka rage suma”. Da sauri Yoohan ya ɗago yana kallon Richard fuska a marairaice kamar zai fasa kuka. Richard yay saurin haɗiye dariyar dake neman kufce masa dan yasan shima da gaske Yoohan ɗin ya kai iyakar gajiya, amma sai ya fiske yace, “Da gaske nake Yoohan, gama files nasu na kammala dubawa”.
“Rich.. Please, wlhy na gaji, sai dai kai ka dubasu” ya faɗa yana sauke numfashi da miƙewa ya nufi wata ƙofa.
Murmushi Richard yayi yana binsa da kallo harya shige. Ya ɗan girgiza kansa da kwasar files ɗin ya fice daga office ɗin zuwa nashi shima.
ALLAH ne ya haɗashi da Yoohan tun a secondary school, a farkon haɗuwarsu sam basa shiri, dan abokan faɗan junane a aji. Ba komai yasa rashin jituwa tsakaninsu ba sai kasancewar su duka sunada matuƙar ƙoƙari, kafin Yoohan yazo school ɗin shike ɗaukar na ɗaya a ajinsu, amma Yoohan na zuwa ya amshe wannan matsayin. Kafin zuwan Yoohan ɗin kuma kowa sonsa da girmamasa yake a ajin, hasalima shine Monitor, ƴammatan ajin ji suke tamkar su haɗiyesa kuma. Amma Yoohan na zuwa nanma komai ya canja, kan ƴan ajin ya rabu biyu, wasu na ɓangaren Yoohan wasu Richard. Dan haka aka zama abokan dabin juna, duk da sam Yoohan baya kula duk haukarsu. Rashin kulawar Yoohan ɗin tasa a koda yaushe shi da tawagarsa suke ɗauka Yoohan matsoracine, dan babu wanda ya taɓa ganin faɗansa. Sai fa wataran da suka kaishi bango yayma Rich dukan mutuwa, da ƙyar aka karɓesa a hannunsa dan Yoohan akwai zuciyar tsiya. Tun daga wannan duka da Yoohan ya masa suka koma abokan juna, tun sauran ɗalibai na ƙalubalantar abotar tasu har suka fahimci ta gaskiyace suma sukabi. Shi da Yoohan duk burinsu ɗaya ne akan karatu, dan haka haɗewarsu waje guda ta ƙara musu himma da ƙwazo. Koda suka kammala secondary kuma cikin amincin ALLAH iyayensu suka amince musu tafiya karatu tare. A gaba ɗaya rayuwarsu tare ta gudana, sai daga bayane Yoohan daya cigaba da wasu kwasakwasai (Courses) ne suka ɗan rabu, danshi ya amshi aikin da aka bashine a ƙasar London bayan zamowarsu cikakkun likitoci, saɓanin Yoohan daya ƙi amincewa.
Daga baya Yoohan ya kuma samun ɗaukaka fiye da tashi, danshi ya ƙara faɗaɗa wasu karance-karancen daya bashi damar iya duba marasa lafiya ta kowane fanni, aikinsa ya zam zai iya yinsa a kowacce ƙasa kuma.
Bayan shekara ɗaya da fara wannan gwagwarmayar Yoohan ya fahimci bazai iya shi kaɗaiba sai da taimakon Richard, dan haka yaje ya dabaibayesa da daɗin baki har saida ya amince suka sake curewa waje guda suke gudanar da aikin a tare. Yanzu haka shekararsu ta biyu kenan da fara aiki, suna ɗaya daga cikin manyan matasan likitoci da duniya ke alfahari dasu bama ƙasarsu ko yankin Africa kawai ba.
A yanzu haka dai shi Richard ana shirin aurensa ma da wata baturiya, shiko Yoohan yaƙi motsawa sam, a cewarsa shi bama zaiyi aure yanzuba sai nan da wasu shekarun daya tsara.

Ɗakine madaidaici dake ɗauke da kayan ɗaki complete, shima sai ƙamshi yakeyi kamar ba’a cikin asibiti ba. Kansa tsaye toilet ya nufa yana faman lullumshe idanu dan barci yake matuƙar ji. Tunda ya iso Lagos a daren jiya bai hutaba, dan ya iske patients da yawa da sukai booking ɗin ganinsa. Tun a jiyan yay dauriyar zaman duba files ɗinsu, waɗanda yasan akwai mafita ya rubuta musu Doctors ɗin da zasuje su gani ya turama Rich. Waɗanda kuma yasan sai shine zai duba ya sanar da Richard ya sanar musu time ɗin da zasu gansa ta hanyar text messeges.
A safiyar yau tun ƙarfe huɗu na asuba ya baro gida, tunda yazo kuma aiki yake bai hutaba. Bayan ya gama duba adadin daya ƙayyade ya shiga theatre akan matsaloli daban-daban kuma, yanzunma ba ya gama baneba, yanada loacin hutawa ne na awa uku da rabi kafin ya koma ɗakin theatre ya ƙarasama mutane biyu dake a ƙasa kamar yanda Rich ya faɗa. Bayan ya kammala dasu zai ƙara hutun awanni uku jirginsa ya ɗaga zuwa ƙasar Kenya inda wasu patients ɗin ke jiransa canma.
Bayan wasu mintuna ya fito daga toilet ɗin sanye da rigar wanka Blue, sai hular wanka data kare gashinsa daga jiƙewa, da alama dai baya buƙatar jiƙawar. A bakin gadon ya zauna yana mai furzar da iskar daya cika bakinsa da ita, yajawo wayarsa dake a drowar gefen gadon a jiye ya cireta a silent. Dan ya sakata a silent ɗinne tun lokacin dazai shiga theatre room. Solomon ya kira, sai akai rashin sa’a ya samu wayarsa a busy.
Kume fuska ya sakeyi alamar baiso hakanba, ya ajiye wayar. ɗayar ya ɗauka itama ya cireta a plane mode daya sakata. Kamar jira ake ya cire ɗin sai ga kira ya shigo, kafin ya amsa kuma akai knocking ƙofar. Rasa wanne zai farayi yayi. Ɗaga wayar? Kokuwa buɗe ƙofar?.
“Yoohan!” ya tsinkayi muryar Richard na kiransa. Duk da yayi tunanin akan maganar patients ɗin da Rich ɗin yay maganar zai dubane hakan bai hanashi tashi ya buɗe masa ƙofaba, sai dai ya sake haɗe fuska alamar da gaske ya gaji baison takura.
Yana buɗe ƙofar yace, “Rich plea…..”
Saurin katsesa Richard yay da faɗin, “Yi haƙuri ba wancan maganar bane, akwai damuwa Yoohan, matar da kaima aiki a kano yanzun nan Doctor Sa’ad ke sanar min an samu matsala”.
“What?!” ya faɗa hankali tashe. Shima Richard da hankalin nasa ke a tashe ya shiga jinjina masa kai. Juyawa cikin ɗakin yay da sauri, yama manta da wata gajiyarsa. Wayarsa ya ɗauka domin neman Dr Sa’ad. Ganin ashe shinema ya kirasa ɗazun lokacin da Richard ke knocking ya sakashi kiransa. Bugu ɗaya kuwa Dr Sa’ad ɗin ya ɗaga.
Ko gaisuwa basuyi zaman yiba Dr Sa’ad ya shiga masa bayanin dukan abinda ya faru, da halin da matar ke a ciki yanzun.
Hannunsa dafe da kansa cikin tsagwaron damuwa yace,  “Dr Sa’ad ta yaya hakan ta faru? Ince duk yanda ya kamata a bata kulawa na sanar muku. Miyasa kuke da sakaci akan rayukan mutane!!?” ya ƙare maganar da ɗan kaushin murya.
Dr Sa’ad da maganar Dr Yoohan tai masa zafi ya buɗe baki zaiyi magana cikin ƙoƙarin danne fushinsa, amma sai Yoohan ɗin ya kuma dakatar dashi ta hanyar faɗin, “Bana buƙatar jin komai please, zan turo maka hanyar da zakubi wajen fara bata taimako yanzun, nima ina hanyar tahowa”.
“Okay Sir” Dr Sa’ad ya amsa masa daga can cikin wata irin murya mai cike da ɗaci da takaici. Yaro ƙarami dashi yana juyasu dan kawai ALLAH ya basa baiwar da tafi tasu, tabbas idan ba kawar da Dr Yoohan sukaiba a duniya rayukansu da hanyar cin abinsu na a cikin garari.
(Ni dai nace Humm).

Shi Yoohan baima saurari amsawar Dr Sa’ad ɗinba, dan tuni yayi wurgi da wayar saman gado cike da takaicin likitoci irin Dr Sa’ad, da a kullum basu da kishin ƙasarsu da jama’arsu, burinsu sudai kuɗi kawai da taƙama da aikinsu. Da hanzarinsa ya fito ainhin Office ɗin yana faɗin, “Rich Please ka bincika min idan akwai jirgi mai tafiya kano daga nan zuwa mintuna talatin”.
Da sauri Richard ya fita daga office ɗin zuwa nasa, dan yabar wayarsa a canne. Shi kuma Dr Yoohan yaja Laptop ɗinsa dake saman tebirin daga tsaye ya shiga dannata da sauri sauri cikin ƙwarewa. A haka Solomon ya shigo ya samesa, batare daya tsayaba yay saurin shigewa bedroom ɗin domin fidda masa kayan da zai saka dan Richard ya sanar masa halin da ake ciki, kuma shi Dr Sa’ad ya fara samu a waya kafin Richard ma.
Dr Yoohan na kammala tura abinda zai aikama Dr Sa’ad ya nufi ɗakin shima. bai wani damu da tsayawa duba kayan da Solomon ya ajiye masanba ya ɗauka ya fara ƙoƙarin sakawa, shi kuma Solomon ya fito ya bashi waje.
Shirin yake ransa duk a jagule da takaici, yana kammalawa ya fito jacket ɗin suit ɗinsa a hannu, necktie ɗinma haka. Gashinsa kansa yau sama-sama ya samu gyara. Haka yake shi, a kullum matsalar al’umma itace tashin hankalinsa da damuwarsa. Da kaga damuwa a idanunsa to patient ɗinsa na cikin matsala ne. Baiko kalli inda Solomon ke tsaye da jikkarsa a hannuba ya nufi hanyar fita fuskarnan babu alamar wasa.
Kusan cin karo sukai da Richard dake ƙoƙarin shigowa ya sanar masa an samu jirgi, kuma cikin amincin ALLAH zai tashi nan da mintuna goma sha bakwai ne, da ƙyar akama samu ticket ɗin guda biyu. A yanda Dr Yoohan yasan garin Lagos da yammaci irin haka yasan kafin su isa airport ma lokacin tashin jirgin ma ya wuce, dan haka ya yanke shawarar su tafi a Ambulance kawai zasufi samun hanya da sauri.
Rich kansa yayi na’am da wannan tunanin na Yoohan, dan haka yama yanke shawarar kaisu da kansa ko Yoohan ɗin zai kuma samun nutsuwa………….✍

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba’a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________
*_SAUDIA_*

………….Kai kawo taketa faman yi a falon nasu dake wadace da sanyin ac da ƙamshi kai kace safa da marwa take gudanarwa. Ta canja sosai, dan komai na jikinta ya ƙara girma da cika. Daman can duk tafi su Nu’aymah girman jiki kasancewar ta ɗakko jikin Addah. Yanzu kuma darajar aure saita sake bata damar buɗewa tamkar ba ƴar shekara goma sha takwas ba.
Tabbas tana samun ci da sha da sutura duk irin wadda ta buƙata, sai dai a watanni tara kenan da aurenta da Yah Abdallah babu wata rana da zata ware ta dangantata da farin cikinta. Idan har ta samu kulawarsa to na wasu awoyine da zai biya buƙatarsa. Baya son zaman gidan sam, ita kanta har mamaki take da al’ajabin ina yake zuwa bayan makaranta da harkar kasuwancinsa?.
Duk yanda taso fahimta ko gano hakan ya gagara, babu kalar dabaru da maman Aaida bata koya mataba duk kuma ta bisu daki-daki amma ta gaza samun haske. A yanzu haka wata ƙura ta fahimta baibaye da ita game da mijin nata shine dalilin kaiwa da kawowar tata.
Tun daga randa Abdallah ya fara kusantarta ba’a cikin hayyacinsa ba a washe gari ya haɗata da wasu ƙwayoyin magani guda biyu. Daga haka kuma duk sanda zai kusanceta sai ya batasu ta sha. Tun bata taɓa kawo komai a ranta game dasu ba harta fara zargar wani abu. Ba komai ya kawo mata zarginba kuma sai haihuwa da akullum maman Aaida ke kawaɗaita mata ta sanadinta zata iya samun soyayyar Abdallah, tunda sunyi dukkan wasu dabaru yaƙi hawa network. Da farko Adawiya batason ta haihu yanzu, amma da taji wannan magana daga maman Aaida sai taji ƙwaɗayin hakan itama dan tana masifar son Yah Ab. To amma sai me? Har yanzu babu ciki babu alamarsa a gareta, har zuwa asibiti tayi a ɓoye aka dubata Doctor ya tabbatar mata inhar bata daina sha maganin hana ɗaukar cikiba bazata taɓa samun ciki ba.
Wannan magana ta daki zuciyarta, dan a ɗan hasashenta ta fahimci kenan maganin da Yah Ab ke bata kullum na hana ɗaukar cikine? Duk da zuciyarta taƙi aminta da hakan sai taji tana ƙwaɗayin dubawa ta tabbatar. Wannan shine dalilin kai kawonta tana nazarin hanyar data dace tabi wajen binciken maganin a ɗakinsa batare daya saniba ko ya ganta. Saboda haka taƙi zuwa makaranta yau ta zauna gadin fitarsa. Sai dai kuma har yanzu bataji ko motsin alamar zai fitoba balle tayi tunanin fitar tasama kamar yasan mi take shirin yi….

(Humm muje zuwa baby Adawiya😉😂).

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

_______________________
________________________

Dr Yoohan ya bama matar da yazo kano dominta dukkan gudumawar data dace har ALLAH ya bashi nasarar dai-daita komai da taimakon Dr Aysha. Sai dai fa Dr Sa’ad yasha masifa dan tabbas harda sakacinsa. Ba komai ya sashi sakacinba kuma sai kasancewar matar talakace, hasalima Dr Yoohan shine ya biya mata kuɗin aikin dukda kuma shine yayi aikin. Ya kuma bama marayun ƴaƴanta wasu ƴan kuɗaɗe tare da buƙatar takardun makarantar babban yayansu dake riƙe da gidan da ƴar sana’arsa ta saida ruwa a cikin kasuwa. ALLAH ya taimakesa tun mahaifinsu nada rai ya haɗa diploma ɗinsa da ƙyar da siɗin goshi. Wannan alkairi nasa a garesu ya sakasu cigaba da jera masa addu’oin fatan alkairi da nasara a rayuwarsa. Tare da fatan ALLAH yasa yanada rabo cikin addinin islama.
Tunda Dr Sa’ad yaga Dr Yoohan ya wuce sai ya fara sakaci da kula da matar yanda ya kamata saboda takaicin ƴarta data bijire masa tun farko. Da farko shine zaima matar aiki akan matsalarta, ya buƙaci kuɗaɗe masu nauyi daga wajensu na aikin amma suka tabbatar masa basu dasu. Sunta roƙonsa ya taimakesu ko rabi su bada kafin ta warke sai su cika ya nuna bazai iyaba, sai kuma ya koma ta bayan fage ya nema yarinyar matar akan inhar zata bashi kanta shiko zaima mahaifiyarsu aiki ƙyau bama sai sun biyaba. Itako tace bazata aminceba, dan ran mahaifiyarsu a hannun ALLAH ya ke, sun kuma dogara da shi.
Wannan shine farkon matsalar. Lokacin da Dr Sa’ad ke bibiyar yarinyarnan saiko karaf a kunnen Dr Aysha, hakanne yasa ta koma a ɓoye ta kira Dr Yoohan da roƙon ya taimaki yaran inhar yanada halin yin hakan. Da yake tasan yana Abuja yana hutun kwanaki uku. Sanin ƙyaƙyƙyawan halin Dr Aysha ya saka Dr Yoohan yarda ya baro Abuja ta mota ya nufo kano. Da taimakonta sukaima matar dukkan hidima, ya tafi yabar amanar kulawarta a hannunta ita da Dr Sa’ad. dan Dr Aysha ta ɓoyema Yoohan sunansa dan kare masa mutuncinsa.
Da Dr Sa’ad ya fahimci Dr Aysha ta ɓoyema Dr Yoohan sunansa da ainahin gaskiya sai yay shirin ɓata aikin da akaima matar saboda jin zafin rashin haɗin kai da bai samuba na yarinyarta. Dr Aysha dake taimaka musu kuma data fahimci hakan ta tabbatar masa saita sanarma Dr Yoohan ɗin komai. Wannan shine yay masifar tada hankalinsa kafin ta sanarɗin shi ya kira ya sanar.

Yunwa da gajiya taima Dr Yoohan rumusu zuwa yanzun, haka ya fito a matuƙar wahale Dr Aysha biye dashi tana masa bayani akan nasarorin da suka samu game da sauran aikin da yayi a wancan zuwan kafin yima wannan matar aiki. Sosai yaji farin ciki a ransa, dan haka ya biye mata suka shiga zagaya ɓangarorin da marasa lafiyar suke yana dubasu.
Duk inda ya gitta addu’a ake binsa da shi, duk da wasu da an masa addu’ar zakaji sunce. Arne ne fa. Jin hakan kansa wasu jikinsu yay sanyi. Wasu kuma suce dan arne ne baza’a masa addu’a ba bisa ga ƙyautatawarsa?.
To shidai baimasan sunayiba, dan farincikine shimfiɗe a ransa ganin nasara na kuma ziyartar aikinsa a koda yaushe. Amma duk da wannan farin ciki sam babu fara’a kota sisin kwabo a fuskarnan tasa saboda halittarsace haka rashin fara’ar.
Suna kammala zagayawa ya kalli agogon dake a tsintsiyar hannunsa. Ganin yaci a wanni uku a cikin uku da rabi na hutunsa ya sauke ɓoyayyen ajiyar zuciya. Bashi da tabbacin samun jirgi mai komawa Lagos yanzu, dan haka ya yanke shawarar nufar Abuja a mota kawai, sauran patients ɗinsa kuma sai dai Richard ya dubasu.
Da wannan tunanin yayma su Doctor Aysha sallama ya fito batare da ko office ɗinsa yay tunanin shiga ba. Amma duk da haka sai da Doctors ɗin dake matuƙar yinsa suka firfito suka gaishesa, sannan suka yo masa rakkiya zuwa wajen guards ɗinsa da basuyi tunanin fitowar tasa ba a yanzun. Dan Solomon suke ta bama labarin abubuwan da suka faru game da kama Nu’aymah da aka turosu yi.

Cike da farin ciki Solomon ke wata shegiyar dariya, ya ƙyalƙyale da ita yana faɗin, “Inason kafin kuje abuja da ita kuci ubanta a hanya ta ƙarasa da ƙafa ɗaya. Kai bama nason taje da numfashi gaba ɗaya. ku kaita da rabin rai yanda oga zai ƙarasata da kun isa, dan bana fatan kafin mu dawo Abuja boss yaji koda ɓurɓushin labarin abinda ya farune. Kunsansa ɗan hana ruwa gudu ne. Shi a dole masoyin ƙ……….”
Da sauri Solomon ya haɗiye sauran maganarsa jin ƙamshin turaren Dr Yoohan ya cika wajen. Yay azamar juyawa kamar yanda suma sauran duk suka juya a tsorace.
Ganin yana maganane da Doctors ɗin da sukai masa rakkiya ya sakasu sauke ajiyar zuciya. Dan sun tabbata baiji komaiba.
Dr Yoohan yay sallama da abokan aikinsa kafin ya shiga motar da aka buɗe masa yana nai ɗaga musu hannu hamar yanda suke ɗaga masa. A haka motocin suka fito daga cikin asibitin.
“Sir! Zamu koma airport ne?”. Cewar Solomon fuskarsa ɗauke da murmushin jin daɗin kama Nu’aymah da har yanzu ya gaza barin fuskarsa.
Shiru Yoohan ya musu tamkar bai jiba, yama maida hankalinsa kan files ɗin daya fiddo a jikkarsa yana dubawa. Sake maimaitawa Solo yayi.
Nanma sai da yaja wasu sakanni kafin yace, “Police station”.
Ji kake ƙiyyyyy!!! Driver ya taka wani uban birki a firgice, tare da haɗa baki shi da Solomon waje. faɗin, “Police station kuma sir?!”.
(🙄🙄😏An yanka ta tashi ko masu gadi?).

Idanu ya zuba musu na wasu sakanni fuska a matuƙar ɗaure. Sai kuma ya ɗauke kansa ya cigaba da abinda ya keyi. Ganin gaba ɗaya wutar kansu ta ɗauke a fusace ya sake kallonsu “Kona canja yaren da nai maganar da shi ne bakuji wannan ba?”.
Da sauri suka shiga bashi haƙuri, driver ya ƙarama mota gudu zufa na keto masa ta ko ina a sassan jikinsa. Kai kace motar babu ac. kallo ɗaya zaka fahimci tsagwaron tashin hankali da ɓacin rai tattare da su. Driver bashi da wata hanyar daya wuce ya ɗauki hanyar police station ɗin da suka bar Nu’aymah. Acan kuma ƙasan ransu shi da Solomon tunanin mafita sukeyi.
Sunci rabin tafiya wani dabara yazoma Solo a rai, dan haka ya ɗauka wayarsa ya rubuta text ya turama Madam Chioma. Mintuna uku ba’ayi cikakkuba sai ga kiranta ya shigo wayar Yoohan.
Idanunsa ya ɗago daga abinda yakeyi ya kalli fuskar wayar. Duk da yaga sunan Mom ɓaro-ɓaro a jiki sai ya ɗauke kansa ya cigaba da abinda ya keyi. Kiran ya yanke wani ya sake shigowa. Yanzun kam maimakon kallon wanene sai ya lumshe idanunsa ma, sai da sukai kusan sakan goma a rufe sannan ya buɗesu akan su Solomon dake a gaba suna addu’a da fatan ya ɗaga wayar kafin su isa station ɗin.
Lip ɗinsa na ƙasa yaɗan lasa da harshe ya sake maida idanunsa ya lumshe bayan ya kife wayar alamar dai bazai ɗaga ɗinba..
“S…S sir ana kiran wayarka fa”. Solomon ya faɗa da rawar baki.
Tamkar yayi magana da dutse, dan Yoohan yi yay kamarma bai jisa ba, kuma sarai yaji miya faɗa ɗin.

A haka suka iso station ɗin, bai fitaba sai da yaja wasu mintuna, ta cikin motar ya gama ƙarema station ɗin kallo har su Solomon da suka fita suka buɗe masa. Solomon yay ƙasa da kansa ganin banzan kallon da Dr Yoohan ɗin ke masa. Batare da yace da shi uffanba ya zuro ƙafafunsa ƙasa ya fito. Gaba yay suka take masa baya kowanne zuciya babu daɗi.
Duk da ƴan sandan basusan wanene shi ɗinba shigarsa da waɗanda suka rufa masa baya ya sanar dasu ogan gayunne gaba ɗaya. Suda ya kamata ya fara gaidawa sai gasu suke masa tarba cikin tsantsar girmamawa kai kace wani babbane a cikinsu.
Ransa dake a ɓace da guards ɗinsa ya sakashi ɗaga musu hannu kawai batare da ya cire ko baƙin glasess ɗin idonsaba ya buƙaci a kaisa office ɗin d.p.o. Guards ɗinsa zasu magana da nuna masa sunada power ɗin shiga kai tsaye basai an nema masa isoba yay saurin ɗaga musu hannu suma cikin fushi. Tsitt sukayi kuwa kowa kai a ƙasa.
Maida dubansa yay ga ƴan sanda ya sake sanar musu su nema masa iso office ɗin d.p.o. Babu musu suka amsa masa cike da girmamawa, yayinda ɗaya a cikinsu ya nufi Office ɗin d.p.o ɗin domin sanar masa.
“Ranka ya daɗe yace ka shiga”. Ɗan sandan ya faɗa da harshen hausa yana ɗan risinawa. Ko motsi Yoohan baiyiba. bai kuma nuna yaji mi ɗan sandan ya ceba. Wani cikinsu dake acan gefe daya fahimci Yoohan baya jin hausa yay saurin sake maimaita abinda ɗan uwansu ya faɗa da turanci. Sai lokacin ne Yoohan ɗin ya motsa tare da ɗaga musu hannu.

Da sauri Solomon ya buɗe masa ƙofar office ɗin ya shiga. D.p.o yay azamar ajiye biron hannunsa yana mai miƙewa cike da tsagwaron mamakin ganin wanda baiyi zato ko tsammani ba. Shi kansa Yoohan ɗin tsaye yayi kawai yana kallonsa, a ransa yana raya ashe papa yayi amfani da wanda ya sanine shiyyasa ya nuna ƙarfin ikonsa…….
D.p.o ya katse tunaninsa da faɗin, “Oh God! Dr Yoohan!”. Hannu Yoohan ya saka ya zare glasess ɗin idonsa, batare da ya amsa d.p.o ba ya zuba masa idanu kawai kamar mai nazari. Har inda yake d.p.o ya ƙaraso shi, ya nuna masa kujera cike da girmamawa yana faɗin Please Sir ka zauna, ka taimakeni ka zauna”.
Kamar bazai zauna ɗinba, sai kuma miya tuna oho masa sai ya zauna a kujerar da d.p.o ya gyara masa tare da harɗe ƙafafu ya ɗora glasess ɗinsa saman table ɗin.
D.p.o daya koma tamkar ya mance da matsayinsa da kansa ya buɗe fridge ya ɗakko ruwa da lemo da kofi ya ajiye saman table ɗin. Abin mamaki duk ya wani rikice.

Nu’aymah na zaune a office ɗin ta cusa kanta cikin ƙafafunta dake mata wani irin ciwo taji takun shigowar mutum office ɗin. Yanda taji D.p.o na magana ba ƙaramin takaici ya bataba. A ranta rayawa take ‘Shin sai yaushene wai ƙasarnan tamu zata gyarune? Sai yaushene jami’an tsaronmu da duk wasu ma’aikatunmu zasu daina fifita masu hannu da shuni akan talaka? Ta taso gidan da Alhmdllh akwai arziƙi da wadatar zuci, akwai kuma kima da daraja na babban gidan. Dan haka duk inda suka tsinci kansu da wuya kiga ba’a girmamasu, sai dai idan ba’asan su ɗin su wanene ba. Ta tabbata wannan d.p.o ɗin inda ace bahaushene da babu yanda za’ai ya kasajin kunyar tura yaransa har gidansu ɗakkota, koda kuwa za’ace an basa kuɗin toshiyar baki. To amma yanda akema talaka na sosa mata zuciya da ruhi. A yanzu haka shigowarta station ɗin nan taga abubuwa kala-kala da suka sosa zuciyarta duk kuma an yisune akan talaka’. Batare data saniba tsaki ya kufce mata, cikin zafin zuciya da takaicin d.p.o ta ɗago dan taga wane shashasha ne yazo ake masa wannan tarbar tamkar wani IG ko gomnan kanon ma gaba ɗaya.
Akan bayansa ta sauke idanunta, dan ya juya mata bayane bata ganin fuskarsa, ta zuba ma bayan nasa harara duk da bawai ta gane wanene ba.

Yoohan da baisan Nu’aymah nayiba ya kalli d.p.o fuska babu walwala yace, “Inason ka saki yarinyar da papa yasa aka kawo nan”. “Sir amma…..” hannu Yoohan ya ɗaga ma d.p.o da sauri. “Emanuel! Haka kawai nake buƙatar ayi”.
“Za’ayi yanda kakeso sir, sai dai nima ka saurareni ko kaɗanne Please ”. Shiru Yoohan ɗin yayi alamar ya bashi dama. D.p.o daya fahimci hakan sai ya gyara zama, cikin kwantar da murya yace, “Ka taimakeni ka kira Pastor ka sanar masa kaine ka bada umarnin a saketa kar yaga kamar na saɓama umarninsa rayuwata ta shiga garari.
Lumshe idanu Yoohan yayi, wani irin takaici da ƙunci na daɗa faɗaɗa a cikin ransa. Yanajin zafi da matuƙar damuwa idan yaga yanda mutanensu ke masifar tsoron papa. Yakan rasa minene dalilin hakan? Dan kawai yana pastor ne ko me? Kodai akwai wani abu da bai saniba game da mahaifin nasa ne? K……..’
“Please sir!”. Maganar d.p.o ta katse masa tunani. Maimakon ya amsa zai kira Papa, sai yace, “Ina yarinyar take?”. Da hannu D.p.o yay masa nuni da Nu’aymah dake bayansu ta sake duƙar da kanta saboda ƙafarta. Kafin Yoohan yace wani abu d.p.o ya bata umarni akan ta taso. Ko motsi bataiba dan abinda ya dameta shine matsalarta ba tsawarsa ba. Yunƙurawa ɗaya daga cikin yaransa yay a fusace zaije gareta Yoohan ya ɗaga masa hannu. Komawa yay ya tsaya inda yake cike da takaici.
Nu’aymah da duk tana jinsu bata motsaba, sai da ƙafarta ta lafa mata. Ƴar sandan da suka ɗakkota a gidace ta shigo bisa umarnin d.p.o ɗin ta taimaka mata ta miƙe. Miƙewar tata tayi dai-dai da ranƙwafawar Yoohan da ya miƙe yana faɗima d.p.o “Police ɗin da suka ɗakkota su maidata, su kuma bama iyayenta haƙuri da wanketa, inba hakaba Emanuel kaine zaka ɗauki laifin”. Da sauri d.p.o ya ɗaga masa kai zufa na keto masa. Yoohan ya ɗauki glasess ɗinsa ya juyo zai saka a ido. karaf suka sauka akan Nu’aymah dake tsaye tana binsa da wani shegen kallo na fusata, dan ko kaɗan batai tunanin shiɗinne yasa a kawota nan wajenba, saboda sam bata wani gane guards ɗinsa ba, hasalima ta manta da shi da abinda ya faru tsakaninsun.
Nunashi tai da ɗan yatsa babu alamar koda tsoro tattare da ita, “Kai ne dama kasa a kawoni nan wajen?” tai maganar fuskarta ɗauke da murmushin takaici, sai kuma ta haɗe fuska da maida dubanta ga d.p.o. “Yallaɓai ai bani na cancanci zuwa nanba wannan mai suffar ƴan damben ne, dan haka nima yanzu na kawo ƙararsa”.
Kafin d.p.o yace wani abu ta fisge hannunta daga na ƴar sandar ta fice a office ɗin da ɗan sauri duk da tana ɗingishi. Saurin bin bayanta d.p.o da ƴan sandan da ke office ɗin sukai, yayinda Yoohan ya lumshe idanu da saka glasess ɗinsa da ganinta ya hanashi sakawa ɗazun shima yabi bayansu.
Isowar su d.p.o yayi dai-dai da furucin Nu’aymah dake tsaye gaban ƴan sandan dake wajen kanta  . “Yallaɓai na kawo ƙara”.
A tare suka kalleta, ɗaya a cikinsu yace, “ƙarar wa? A kanmi kuma?”. Juyawa tai inda su d.p.o ke tsaye cike da al’ajabi da mamakinta, dai-dai kuwa da fitowar Dr Yoohan daga lungun da office ɗin d.p.o yake ta nunasa da faɗin, “Ƙarar wannan mai siffar ƴan damben na kawo”…………✍

😂Wagga ɗiya kina da tsaurin ido aradu😚🚶🏻.

Barka da juma’a😘😍🤗.

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*

*_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi🤣, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana😉😘😘😍😋._*

_______________________________

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply