Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 15


Saran Boye 15
Viral

15

……………..Kaɗan ya rage su makara a hanyar zuwa airport, ALLAH dai ya taimakesu suka isa gab. Sai da Richard ya ga tashin jirgin sannan ya bar Airport ɗin yana mai kiran Dr Sa’ad ya sanar masa ga Dr Yoohan nan ya taho su kwantar da hankalinsu.
Duk da Dr Sa’ad baiso hakanba sai ya amsa masa harda addu’ar isowarsu lafiya. A ƙasan ransa kam ji yake kamar zuciyarsa zata babbake da wuta dan takaici da tsanar Dr Yoohan ɗin da bai taɓa tare masa komai a duniyaba bayan nusar dashi ya san kansa kawai.
Yana sauke wayar daga kunnensa kiran Madam Chioma na shigowa. Ɗagawa yay da hanzarinsa, dan yasan dai bai wuce ta kira Number Yoohan ɗin bata shigaba ko bai ɗagaba. Ya gaidata cikin girmamawa kamar yanda ya saba, kafin ya ɗora da faɗin, “Mom lafiya dai ko?”. Daga can tace, “Eh Richard, lafiya, amma na kira abokinka sau uku bai ɗagaba, nayi zaton ko yana akan aikine idan ya kammala zai kirani, sai dai har yanzu banga kiransaba. Na kuma nemesa yanzu da kaina wayarsa bai tafiya. Shine nace ko lafiya?”.
Murmushi yay yana ƙara jinjina ƙaunar wannan uwa da ɗa a zuciyarsa. Cike da kulawa yay mata bayani yanda zata fahimta, sai dai yanda tai azamar katsesa jin ya ambaci kano sai abin ya nema firgitashi. Kafin ya samu damar tambayarta dalili harta yanke kiran.

*_ABUJA_*

Hankalin Madam Chioma a tashe tai kiran Guards ɗin Yoohan dake shirin tahowa da Nu’aymah Abuja. Cikin azalzala ta sanar musu karsu taho su ajiye Nu’aymah a police station ɗin maza su nufi airport su tarbi Yoohan gashi nan ya taho da ga Lagos. Tai mugun basu gargaɗi akan inhar wani abu mara ƙyau suka bari ya faru da Yoohan ɗin yau to su tabbatar a bakin aikinsu kenan, bayan horo mai tsanani da zasu fuskanta kuma.
Sanin Madam Chioma zata aikata fiye da abinda ta faɗa inhar akan Yoohan ne ya saka guards ɗin Yoohan bin dukkan umarninta. Har an fito da Nu’aymah da ko harara babu wanda yay mata a station ɗin, hasalima tana a office ɗin d.p.o tunda aka kawota suka sanarma d.p.o halin da ake ciki game da umarnin mahaifiyar uban gidansu.
Babu musu ya amince da ajiye Nu’aymah har suje su dawo, su kuma suka shiga motocinsu suka bar station ɗin zuwa airport ɗakko Dr Yoohan da suka san nanda mintuna ƙalilan ne jirginsu zai sauka.

Murmushi Nu’aymah tayi tana mai buɗe tafin hannunta ta kalli ƴar takardar da baba malam ya saka mata lokacin daya kamo hannunta. Takardar ta sake buɗewa ta karanta addu’ar dake ciki tana murmushi, wata irin ƙaunar mahaifinta da tausayinsa na ratsata a zuciya da ɓargo. A yau ta ƙarajin ƙwarin gwiwa akan shirin mahaifin nata. Wanda daga ita sai shi sai ALLAH daya hallicesu sukasan da shirin. Amma ko Umm yaja mata gargaɗi mai ƙarfi akan karta bari ta sani, bakomai yasashi yin hakanba sai wani dalilinsa da itama yace ba yanzu zai sanar mataba sai nan gaba.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

______________________★

Gaba ɗaya Yoohan ji yake kamarma jirgin baya wani sauri, duk bayan mintuna sai ya kalli agogon hannunsa yayi ƙaramin tsaki da Solomon ne kawai ke jinsa, yay masifar ƙosawa yaga sun sauka. A yanda hankalinsa ke a tashe har sai da Solomon yaji tausayinsa ya kamasa. Yana mamakin yanda Dr Yoohan sam babu wani ƙyashi ko ƙabilanci a ransa, game da aikinsa bai taɓa banbanta kai ɗan wane addini bane ko kai ɗan wane yankine. Kansa tsaye yake ƙoƙarin sa, shiyyasa a kullum ALLAH ke sake ɗaukaka darajarsa, dan kullum bayin ALLAH cikin masa addu’oi suke a zahiri da baɗinin zuciya.
Duk da burinsa nason jirgin yay saurin sauka ahakan bai hanashi fita cikin nutsuwa ba lokacin da jirgin ya taɓa ƙasa. Yanda yake tafiya kawai ya isa abin kallo ga mutane. Duk da fuskarsa kullum a cinkushe take hakan bai hana ya ɗauki hankalin masu kallonsa daga maza har mata ba.
“Welcome sir”. Yaji an faɗa Lokacin da suke isowa wajen masu taxi shi da Solomon dake a bayansa. Kamar zai share sai kuma dai ya juya. A bazata idanunsa suka sauka akan guards ɗinsa waɗanda baiyi zato ko tsammanin ganiba.
Da sauri suka ƙaraso gabansa zuciyarsu na dukan ɗari-ɗari ganin kallon da yake musu na tsagwaron mamaki da tuhuma, cike da girmamawa suka shiga gaishesa ɗaya bayan ɗaya, kafin su ɗora da masa bayanin Mom ce tace suzo su tarbesa.
Duk da akwai magana a bakinsa game da ganin nasu a kano sai ya share bai yiba. Ya nufi inda ɗaya daga cikinsu ya buɗe masa mota ya shiga.
Sai da suka fito da ga airport ɗin gaba ɗaya suka hau kan titi sannan ya jefama driver da Solomon ke kusa da shi tambaya a bazata.
Cikin harshen nasara yace, “Miya kawoku kano?”. Cikin faɗuwar gaba driver ya kallesa ta madubi. Sam bama kallonsu yake ba, hankalinsa nakan waya yana dannawa. Cikin ɗan rawan baki na rashin gaskiya driver ya bashi amsa da faɗin, “Sir M… Madam ce ta aikomu”. “Yin me?”.Yoohan ya faɗa da ɗago fararen idanunsa ya zubama drivern cike da nazari. Sosai kallon ya firgitashi, dan anyi sa’a lokacin da Yoohan ɗin ya ɗago idanu yayi dai-dai da ɗagowar driver shima ya kallesa.
Saurin riƙe sitiyarin yayi jin zai ƙwace masa, dan har motar sai da tayi ɗan tangaɗi kaɗan. “I am sorry sir” driver ya faɗa da sauri ƙirjinsa na dukan tara-tara ganin yana neman zubar dasu a ƙasa. Shiru Yoohan bai tanka ba, hasalima ya ɗauke kansa tamkar baiga wani abu daya faru ba. Sai ma ya ɗauka waya yay kiran Dr Sa’ad da kai hannu saman kunnensa ya gyara Bluetooth ɗinsa na fama dake a maƙale.

Solomon da duk ya fahinci akwai wani abu dangane da zuwan ƴan uwanasa kanon ya haɗiye yawu da ƙyar shima yana satar kallon madubin, ganin hankalin Yoohan ɗin baya garesu sai yay saurin maidawa ga drivern. Ƙyaftama juna idanu sukai, alamar dai sun saba da yaran. Solomon ya ɗan gyaɗa kansa yana gyara zama.
A haka suka isa asibitin batare da kowa ya sake magana ba. Tun kafin a buɗe masa shi harma ya buɗe ya fice abinsa. Da yake yau zuwan bazatane Dr Sa’ad kawai ya san zaizo sai Dr Aysha, sauran Doctors ɗin basu fito sun tarbesa ba kamar yanda suka saba.
Sai dai tun shigowar motocinsa wasu daga ma’aikatan asibitin suka fahimci shine. Yayin da gefe guda kuma da ya zama abin kallo ga mutane. Musamman ma yanda yake tafiya Guards ɗinsa na take masa baya. Waɗanda suka sanshi nata faɗin, “Dr Yoohan yay zuwan bazata, yaukam za’asha masifa musamman akan ma’aikatan dakeda sakaci akan aikinsu.
Duk da ya fahimci yanda wasu a cikin ma’aikatan ke ta guje-gujen sanarma iyayen gidansu zuwansa basuko ishesa kalloba. dan abinda ya kawosa shine kawai a gabansa ba su da shirmensu ba.

Tunda su Solomon sukaga shigewarsa sai yaja hannun ɗaya daga cikin Guards ɗin suka fito, sauran kuwa na tsaye ƙiƙam tamkar an dasasu gadin duniya🙄😏, sai zazzare idanu suke sun hana masu kai kawo ta wajen sukuni. Ba marasa lafiya da ƴan uwansu kawaiba, hatta ma’aikatan asibitin a takure suke. Masu sanya da aikinsu duka sun dage saboda jin zuwan Dr Yoohan. (ALLAH ya ƙyauta. Bazakaji tsoron UBANGIJIN daya halicceka ya baka amanar wannan aikin a ranka ba sai wani shasha mutum irinka, ba kuma komai ke kawo tsoronsa ba sai gudun karka rasa aikinka🤦🏻, ya salam. Musulmai ina muka ajiye gaskiyar tamu? Ina muka ajiye koyarwar addinin namu? Ina muka ajiye tausayi dajin ƙan da aka san mumini da shi?. Ku dubafa Dr Yoohan ba musulmi bane, baɗan yankinku bane, ba yarenku bane? Amma yana nuna fushinsa akan sakaci da cigabanku, yana nuna damuwarsa akan ƴan uwanku, yarenku addininku, yayinda ku son zuciya da burin tara duniya ya rufe jinku da ganinku. Kaje asibiti kaga ana wulaƙanta marasa ƙarfi dan kawai sunzo neman lafiya. Babban abin takaicinma yafi yawa a ɓangaren mata masu haihuwa. Kaga ma’aikatan asibiti nacin zarafinsu dan kawai sun kasance ƙauyawa ko talakawa. Haba ƴan uwana, wannan aikinfa da kike cin zarafin wasu dashi tamkar mabuɗine na gida guda biyu. Wuta ko aljannah, ya rage naki/nak ka zaɓama kanka wanda kafi buƙata. ALLAH ya shiryar damu dai, ya rabbi kai riƙo da hannun ma’aikatanmu masu ƙyawawan zukata domin rahamarka da alfarmarka🙏🏻😭).

__________________________

Tunda Addah ta isko Umm a ɗaki basu iya cema juna uffan ba. Kowa ya zabga uban tagumi ne yana saƙa mai fishshesa. Sun kwashi tsahon mintuna sha biyar a haka kafin Addah ta katse shirun nasu da faɗin, “Ni nama rasa abin faɗa wlhy akan wannan al’amari, har nawa Nu’aymah take da ƴan sanda zasuzo su tafi da ita? Mi ma to tayi musu? Sannan miyasa yaya malam zai yanke wannan hukuncin mai tauri haka?”.
“Wannan sune tambayoyin da nake taima zuciyata Addah, amma sam na gaza samo amsar ko guda a ciki. Ina ƙyautata zaton a tafiyarsu bikin nan koma miye ya faru acan ya faru, dan……..”
“Haba Umm miyasa zakice haka? Naga dai su a cikin Orphanage suke? To mima zata aikata da har ace mu bamujisa ba?”.
“Addah yaran nan kafa haifesu ne amma baka haifa halinsu ba, minenema bazasu aikataba tunda basa ganin idon kowa. Ballema Nu’aymah da batajin magana sam, wuyarta dai ta samu sakewa ne kawai, shiyyasa sam banason ko gidanmu tace zataje ta kwana ko wani waje wlhy, danni bansan ina ta ɗakko wannan halin nata na tsiwa da rashin kunyaba”. Yanda Umm tai maganar cikin ɓacin rai yasa Addah saurin faɗin. “Dan ALLAH karki tsaurara harshenki akan wannan abun, mudaibi komai a sannu muji inda matsalar take. Nu’aymah har yanzu yarinyace, kuma sanin kankine duk rashin ji da tsiwar Nu’aymah batayinsa ita kaɗai sai da gudunmawar su Adawiya dama, tunda halin nasu ai duk ɗaya ne…..”
“Humm Addah kema kinsan indai gaskiya zaki faɗa Nu’aymah ta fisu kaifi, dan duk abinda zasu aikata itace jagora”. “To kowa ya zauna akan ra’ayinsa danni bawai yarda zanyi ba, inaga dai bara nakira su Yusrah muji minene ya faru?”. Umm dai batace komaiba, tanata kuma ƙoƙarin danne damuwar dake cizon ranta da kukan dake yunƙuro mata a rai. Duk da Alhmdllh zuwan Addah a gareta ya sanyaya mata fushinta bakamar sanda ta shigoba.

Sallamar Yusrah da Amal ce ta saka Umm da Addah ɗagowa suna kallonsu. Basai an faɗaba, daga gani kukama sukeyi. Hakan da Umm ta gani sai ya sake karya mata zuciya, tai ƙasa da idanunta tana karanto7 addu’ar neman sauƙi da sassauci wajen UBANGIJI.
Zama su Yusrah sukai kansu a ƙasa suna sharar ƙwalla. Addah tace, “Kuka ba shi bane mafita Amal da Yusrah, ku sanar mana mikuka sani game da hakan dan musan hanyar data dace mu kama wajen amso ƴar uwarku”.
Share hawayensu duk sukai, cikin nutsuwa sukaima su Umm bayanin abinda ya faru aranar ƙunshi, sai dai sun ɓoye cewa Nu’aymah ta fasama guards ɗin kai, sundai ce ta wulwula dutse bisa tsutsayi ya daki glass ɗin motar. Hakan da tayine kuma ya saka mutanen tsayawa amma da guduwa zasuyi.
Shiru babu wanda ya iya cewa komai tsakanin Umm da Addah, sai da kusan mintuna uku Addah ta sallamesu suka tafi.

“Umm! Inaga lokaci yayi da zamu fara aiwatar da shirinmu a gidan nan gameda waɗanan abubuwan. Na kula al’amarin ƙara zurfi yakeyi kullum”.
Murmushi Umm tayi idanunta akan Addah, ta ce, “Addah wannan ai babu saka hannun kowa a ciki, itace ta jama kanta. Ni wlhy a yanzuma naji bana sha’awar sanin wanda ke aikatawar………”
“Me yasa?”
Addah ta faɗa da mamaki.
Murmushi Umm ta sake yi har haƙoranta na bayyana, tace, “Addah to minene amfanin sanin? Babu abinda sanin zai amfanar sai fitina. Idan a gidan nan yake zai zama sanadin lalacewar zumincin da aka gina bisa haƙuri da juriya. Idan kuma a waje yake za’a jawo masa tsana daga mutane a tozarta iyalansa. Addah hakan baida wani amfani a gareni, dan wlhy bana fatan kwana da wani musulmi a cikin raina koda na kwana ɗaya ne, dan bani da tabbacin wayar gari. Koma wanene UBANGIJI ya rufa masa asiri na tsahon lokaci, ya kuma fimu sanin hikimar yin hakan. To mu haƙura kawai mu barsa da UBANGIJIN ya ishesa komai”.
Ba ƙaramin ƙurama Umm ido Addah tayiba, har sai da takai Umm ɗin ta taɓata da faɗin, “Ina kika tafi kuma?”. Murmushi Addah tayi da sauke ajiyar zuciya. Tace na tafi duniyar mamaki ne da tsarkake sunan ALLAH, Umm ki godema ALLAH ya azurtaki da ƙyaƙyƙyawar zuciya wlhy……..”
“Kema ai ya azurtaki da ita Addah, dan ina koyi da wasu ƙyawawan halayene daga gareki. Hakan yasa ƙaunar da nake miki ta dabance a zuciyata wlhy, fatar bakima bazata iya kwatantawa ba, kun bani gudunmawa ke da Baba wadda har na koma ga ALLAH bazan gazaba wajen roƙa muku rahama da yardarsa”.
Hawayene ya cikama Addah ido kamar yanda ya cikama Umm itama, suka kama hannun juna suna murmushi cike da ƙaunar juna da ta ginu tun ƙuruciya…………..✍

(ALLAH ya bar ƙauna Umm da Addah😅😘🤗)

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*

*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*

*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*

*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
*_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
*_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
*_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.

*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
*_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA… SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
*_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

__________________________________

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply