Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 19


Saran Boye 19
Viral

No. 19

…………..“Khadijah tabbas kin cancanci ki damu, amma karki manta nima fa ina cikin damuwarne har kashi biyu. Ta shi da taki kema, dan farin cikinki shine nawa dana sauran yarana. Akasin haka duk a wani hali zaki sakamu. Ko yau ke baki lura da yanda Omar ya yini sukuku ba saboda yanda yake ganinki?. Kofa makaranta bai fitaba sai da nai masa magana”.
Zaune ta tashi sosai tana share hawayenta. “Kayi haƙuri to na daina, amma kodan Adawiya ka sakashi ya biyo Hajjo idan zata dawo suzo suyi salla a gidan dan ALLAH itama iyayensu su ganta, sannan musan yaya zaman nasu yake tafiya”.
Ɗan murmushi yay mata da shafa kumatunta. Yace, “Karki damu zanyi ƙoƙarin hakan insha ALLAH, nima gobe idan ALLAH ya kaimu zanje kanon, inaga Omar ne zaiyi tafsir ma gobe idan ALLAH ya kaimun insha ALLAH”.
Kanta ta jinjina masa da addu’ar fatan ganin wayewar garin lafiya.

_____________________________

Washe gari Abban su Abdallah ya nufi kano domin yin sallama da hajjo da suke shirin wucewa nan da kwanaki biyu. Yako isa da wuri, dan sanda ya shigo gidan ma duk ƴan uwansa na nan, baba malam yanama barci bai tashiba tun ɗazun daya ɗan kwanta. Yaran sun baibayesa da oyoyo kamar yanda suka saba a sashen hajjo, kowa na tambayar ɗan uwansa da suke sa’anni. Yayinda shi kuma yake tambayarsu azuminsu nawa-nawa.
Ya jima yana biyema shirmensu kafin ya nufi ɓangarensu da babu kowa a ciki, sai dai zuwan nasa Hajjo ta saka Amal da Nu’aymah zuwa su gyara duk da yace ba kwana zaiyi ba. Wanka yaɗanyi ya kwanta kafin azhar ya samu ganawa dasu baba malam, dan yama iske Abba Musbahu yana wajen tafsir danshi na safe ya keyi.

Bayan gama gaisuwa da Abban su Abdallah Nu’aymah ta nufi sashensu ranta duk a cinkushe, ko kaɗan bata sha’awar wannan zuwa Umrah duk da tana buƙatar hakan fiye da komai a ƙasan ranta. To amma fitinar da take hangoma kanta a tafiyar ta fahimci sai tafi daɗin yawa.
“Lafiyarki kuwa Nu’aymah? Kina tafiya kamar hankalinki baya jikinki?”. Umm dake zaune a falo tana duba littafin KITABUT TAUHID ta faɗa tana kallonta.
Zama Nu’aymah tai kusa da ita, tare da ɗora kanta gefen kafaɗar Umm ɗin. “Umm azuminne fa yau nikan tun yanzu na fara jinsa ALLAH, ni koma wajen tafsir bazanjeba yau barci zanje nayi”. Shiru Umm tai kawai tana kallon Nu’aymah, dan gaba ɗaya a watannin nan tana kula da ita kamar akwai abinda ke damunta. Ta zaunar da ita yafi a ƙirga tana tambayarta amma sai tace mata babu komai. Da yake ta san akwai damuwar Abdallah tattare da ita har yanzu sai take danganta yanayin Nu’aymahn da hakan. Shiyyasa ta duƙufa gayama ALLAH akan lamarin. Idan da rabon aure a tsakaninsu ALLAH ya kawo mafita ayi, idan babu kuma ALLAH ya saka musu salama su duka itama ya bata miji nagari.
Jin Umm batace komaiba itama sai bata sakeyin magana ba, tama lumshe idonu kamar mai barci.
Sun jima a haka, kafin Umm da taji Nu’aymah ta mata nauyi a kafaɗa taɗan ɗago ta kalleta, numfashi take saukewa a hankali na barci. ta girgiza kai kawai da ɗagota a hankali ta gyara mata kwanciya a kujerar tare da ɗaura kanta saman cinyarta. Aiko kamar jira take saita sake gyara kwanciya da ƙyau a cinyar Umm ɗin.
“Ita wannan lafiya take kuwa?” Baba malam da Umm bataji fitowarsa da isowarsa wajenba ya faɗa yana ɗaura hannunsa saman goshin Nu’aymahn. Ɗago ido Umm tai ta kallesa dai-dai ya janye hannun ya sake maidawa a gefen wuyan Nu’aymah.
“Lafiya lau take, barcine kawai”. Janye hannun yay yana sauke ajiyar zuciya da faɗin, “To Alhmdllh, bara na leƙa massallaci Mustapha yasanar min da zuwan baƙi”.
Kanta ta jinjina masa cike da girmamawa, tare da masa addu’ar dawowa lafiya. Da amin ya amsa yay gaba. Harya kusa ficewa a falon sai kuma ya tsaya tare da juyowa. “Banji motsin Muhammad ba, shi yana inane?”.
“Inaga yana ɓangaren Hajjo, dan tun isowar Abbansu na Abuha ya fice”. Umm ta bashi amsa. “Oh Rizwan ɗin yazo ne?”. Yay maganar yana ficewa batare daya saurari amsa daga Umm ɗinba. Itama ganin ya fice ɗin sai batace komaiba ta maida hankalinta ga kallon tafsir ɗin da takeyi yanzun a WISAL HAUSA.

________________________

Kasancewar baba malam da anyi magriba yasha ruwa yake barin gidan sai suka yanke shawarar ganawa bayan sallar zuhur shi da sauran ƴan uwansa biyu dan Abba Musbahu yana Lagos.
Bayan ya kammala da baƙin da sukazo ganinsa bai shigo gidanba dan lokacin salla yayi. Sai da suka idar da salar zuhur ɗin sannan suka shigo gidan a tare ta ƙaramar ƙofa abin sha’awa. Kansu tsaye sashen mahaifiyarsu suka nufa. Inda suka isketa ita kaɗai sai Kubrah dake fashin salla tana barci a kujera. Sallamarsu kuma ta sakata farkawa. Sai ta koma bedroom ɗin hajjo ta kwanta bayan ta gaishesu.
Duk a ƙasa suka zauna suka zagaye mahaifiyarsu, dan wannan al’adarsu ce inhar suna wajenta basa zaman kujera sai dai ƙasa. Sun gaisheta ta amsa cike da farin cikin ganunsu kamar yanda ta saba. Harda ɗan barkwancinta akan autanta. “Kunzo duk kun zagayeni babu autana”. Dukansu murmushi sukayi, Abbansu Abdallah yace, “Inna ai tunda kin gammu kin gansa”. Dariya taɗanyi irin tasu ta manya. Tace, “Gara dai shima na gansa ɗin dai yaji ɗumina”.
Dariya suke mata cike da ƙaunarta. Kafin su tsagaita su fara tattauna abinda ya tarasu game da abinda suke tsarawa na hidima bayan tafiyarta. Sun shafe kusan awa ɗaya suna ƙulla abubuwa masu muhimmanci da amfani. A cikin maganganun nasu ne Abbansu Adawiya ke kawo shawarar ya kamata su gayyato bawan ALLAH nan daketa hidima a garesu shan ruwa idan a cikin kano yake inhar yanada halin zuwan.
Baba malam da shawarar taima daɗi sosai yace, “Mustapha kaga kuma fa kazo da shawara mai ƙyau gaskiya. Dan wlhy bazan ɓoye mukuba inajin matuƙar son ƙwaɗaituwa da ganin wannan bawan ALLAH. Akwanakin nan kodan na saka lamarinsa cikin raina sai nakanta mafarki da shi duk da ban taɓa ganinsaba. Sai dai yanda mafarkin nasa ke zuwamin sai abin yakan zauna cikin raina sosai. Shiyyasa nakeson mu ƙara ƙaimi wajen masa addu’ar fatan alkairi, idanma wani al’amarine ke damunsa ALLAH ke nunamin ta hakan ALLAH ya warware masa”.
Duk da sun fahimci mafarkin akwai abu mara ƙyau a ciki sai basu takura kansu nason saniba, suka shiga addu’a a garesa da alƙawarin sakashi a duk ibadunsu insha ALLAH. Sunja kusan awa biyu da rabi a wajenta sannan suka fito dan la’asarma tayi. Basu koma ciki ba sai suka nufi massallaci kawai.

________________★

Shirye-shiryen tafiyar hajjo da Nu’aymah da Yah Ahmad Umrah ya gama kammala tsaf, insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zasu wuce. Ta kama dai-dai da cikar azumi kwana goma sha biyar kenan.
Duk hanyoyin da Nu’aymah zatabi nason ganin tafiyar bata yuwu da itaba tabi amma bata samu mafita ba. Hakan yasa taci kukanta ta haƙura ta barma UBANGIJI ikonsa, dan ta miƙa kukanta wajen ALLAH akan wannan tafiya har batasan iyakaba. Ganin al’amarin ya kasa gagara saita ɗaurasa a mizanin hakan shine mafi alkairi a gareta shiyyasa.

Zaunar da ita Umm tayi tai mata doguwar nasiha akan wannan tafiya, tare da tunatar da ita manyan ibadu da idan taje zata maida hankali a kansu ba shashanci ba. Tsaf Nu’aymah ta riƙe komai a ranta, tareda ƙarfafa ranta akan insha ALLAH zata zama mai himma. Saboda ma ta gujema abinda take gudun ganin daga Adawiya da Yah Abdallah saita ƙudiri niyyar shiga ittiqafin idan sun isa.

Washe gari ƙarfe biyu na rana jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki ita da Yah Ahmad da Hajjo. Ta tafi cike da kewar Umm da Muhammad harma da baba malam da sauran jama’ar gidan. Musamman ma su Amal da badan basu ƙarasa jarabawarsu guda biyu data rageba da tare zasu tafi.

To Nu’aymah a sauka lafiya. Duk da muna tare dake dan muji yaya wasan zai kaya ke da Adawiya da Yah Abdallah🤔🤗🚶🏻.

_______________________________
*_DOCTOR YOOHAN_*

Kwance yake acan cikin garden ɗin gidan nasu daya ƙawatu da korayen ciyayi da furanni kala-kala, tare da ƴaƴan itatuwa da ALLAH yayma bayinsa ni’ima da su. Kwanakinsa biyu kenan a Abuja ya ɗauki hutu na kwanaki goma ne saboda jikinsa daya ɗan motsa masa.
Fuskarsa a cinkushe take matuƙa, dan rashin walwalarsa ta yau ta ɗara ta kullum ma. Sosai zuciyarsa ke a matuƙar ƙuntace, shiyyasa ma ya waro kansa daga cikin gidan ya dawo nan cikin garden ɗin a gaban swimming pool dake gefe ya kwanta. Haka yake, a duk lokacin da abin nasa ya motsa yakan tsinci kansa cikin wani irin ƙunci da takuruwa. Komai na rayuwa yakan koma masa baƙiƙƙirin. Yaji ya tsani komai da kowa har aikinsa na taimakon al’umma da yake matuƙar so fiye da komai. Idan yana a wannan halin ko magana baya sonyi da kowa ciki harda iyayensa kuwa. Shiyyasa da ya motsa sai yay wuf ya ɗauki hutu domin samun damar zuwa ya keɓance kansa batare da ya shiga haƙƙin wani ba.
Duk yanda iskar garden ɗin dana ruwan pool ɗin ke kaɗawa da ƙamshin furanni masu daɗi sam bayajin wani nishaɗi tattare da shi. Hasalima yazo wajen ya zaunane badan yay farin cikiba ko yaji daɗi. Hannayensa da yay filo dasu ya sake gyarawa yana yamutsa fuska kaɗan. Sai kuma yaja tsaƙi tamkar wanda akaima wani abu.
A haka Solomon ya shigo cikin garden ɗin a ɗarare, dan yafi kowa sanin idan ogan nasu na irin wannan yanayin babu mai raɓarsa a gidan har iyayensa, suko wani lokacinma sallamarsu yake daga gidan gaba ɗaya ma…….
Duk da Yoohan yaji motsin mutum a wajen baiko motsaba, har sai da Solomon yay magana cike da rawar baki, “O…Oga good everning, dama saƙone aka kawo maka daga hannun manager ɗin com…….” kasa ƙarasawa yay saboda yanda Yoohan ɗin ya buɗe fararen idanun nan nasa da suka rine suka koma jajaye a kwanakin nan uku da ciwon nasa ya motsa.
Yanda yake jifansa da kallon ba ƙaramin tayar masa da hankali yayiba, ya ɗanja baya kaɗan dan yana shawarar juyawane kafin abinda baiyi zatoba ya afku yanzun nan.
Yoohan da duk yake kallonsa ta ƙasan ido ya maida idanunsa ya lumshe batare da ya nuna alamar yama san da zaman Solomon ɗin a wajen ba. Juyawa Solo yayi da sauri yabar garden ɗin, dan zuciyarsa ta bashi shawarar gwara ya juya yaje ya ajiye masa saƙon a ɗaki idan ya gadama ƙila ya duba daga baya.

Shigowar Solomon falon ya saka madam Chioma dake cike da tsantsar damuwar halin da Yoohan ɗin ke a ciki ta ɗago tana kallonsa. Risinawa Solomon yay ya gaidata yana nuna mata abinda ke hannunsa da faɗin, “Ma’am zan ajiyema oga wannan a ɗakinsa”.
Muryar Madam Chioma a cinkushe tace, “Yana ina?”. “Yana garden kwance Ma’am” ya bata amsa cike da girmamawa. Batace komaiba sai miƙewa da tai ta nufi ƙofa, shi kuma Solomon ya nufi sama dan ajiyewa.

A yanda Solomon ya tafi ya barsa haka Madam Chioma ta shigo garden ɗin ta iskesa itama. Duk da tana tsoron abinda zai iya biyo baya haka ta ƙarasa garesa cikin sanɗa. A gaban kujerar da yake kwance irin wadda ake ajiyewa a gaban swimming pool ɗin nan ta tsugunna saitin kansa. Duk da a yanzunma yanajin motsin sarai bai buɗe idanunsa ba harta kai hannunta kan sumarsa dake a hargitse yau tamkar ba itace ke masifar ɗaukar gyara ba. ta ranƙwafa kanta saman fuskarsa tamkar zatai masa kiss. yanda takai bakinta gab da nashi ya sakashi saurin saka hannunsa ya ɗaura saman bakinsa yay musu katanga. Sannan ya sake saka ɗayan hannunsa da sauri ya riƙe nata data tura cikin gashin kansa, ya buɗe jajayen idanunsa sosai a kanta. A take taga wani fushi na tattaruwa saman fuskarsa mai saka bantsoro ga duk mai kallonsa. Saurin girgiza masa kai ta shigayi cike da kame-kame tana faɗin, “Relax my baby”. Tai maganar jikinta har ɗan rawa yake na tsorata da yanayinsa dan tayi zaton barci yakeyi da farko.
Batare da yace mata komaiba ya miƙe zaune tare da sakin hannunta daya damƙe, sai kuma ya miƙe ya saka Slippers ɗinsa yabar garden ɗin gaba ɗaya batare da ko waiwayarta yayiba.
Binsa tai da kallo idanunta na cika da ƙwalla, babu abinda zaka iya hanga a gareta sai tsantsar damuwa da tashin hankali. Kasa tashi tai a wajen har tsahon wani lokaci. Sai da tai kuka sosai kafin ta iya miƙewa tabi bayansa.

Yoohan da tuni ya shige ciki yana shiga sashensa ya maida ƙofar ya kulle tare da barin key ɗin a ciki dan karma Mom ɗin tace zata biyosa. Kai tsaye ɗakin motsa jikinsa ya shige ya farayi da wani irin yanayi maiban tsoro. Dan komai yana aiwatar da shine fiye da yanda yakeyi idan yana cikin nutsuwarsa.
Tsahon lokaci ya kwashe a ɗakin, duk da yanda yay bala’in fita hayyacinsa saboda wahala ya kasa bari ya huta. Sai da yay wujiga-wujiga da shi, daga ƙarshema ya yanke jiki ya faɗi.
A take wasu hawaye masu zafi suka shiga gangaro masa a fuska, ya shiga taunar lip ɗinsa ƙirjinsa na sake zafafa, abinda ke kusa da shi ya rarimo yay wurgi da shi, ya sake ɗaukar wani ya ƙara wurgawa. A haka yayta jefe-jefe da kayan ɗakin yana hawaye cike da jin ɗacin da fushi mara dalili.

Hankalin madam Chioma yay masifar sake tashi fiye da farko. Tunda Yoohan ya fara jefe-jefen nan akan kunnenta ne, taje ta kira su Solomon amma kowa na tsoron shiga ɗakin. Waya ta ɗauka ta kira papa shima. Bugu biyu kuwa ya ɗaga. Da kukanta shaɓe-shaɓe ta sanar masa da duk abinda ke faruwa.
Duk da papa yasan da yanayin na Yoohan sai hankalinsa ya sake ƙololuwar tashi fiye da da can. Wannan al’amari na Yoohan na bashi tsoro. Sunyi addu’oin a church, sunyi maganin, sunyi na aaibitin amma abu yaƙi barinsa. Tunda suke basu taɓa gamo da mai kalar matsalar Yoohan ba. Shi ciwon nasa bawai wani waje ne ke masa ciwo a jikinsa ba, likitocima kansu sun sanar musu su basa ganin kowacce irin matsala tattare da Yoohan ɗin, ƙwaƙwalwarsa lafiyarta lau.
UBANGIJI shine yasan gaibu game da matsalar Yoohan. Dan haka kawai yake tsintar kansa da kasa yin barci. Sai ya jera kwanaki sama da biyar bai rintsaba koda kuwa yanajin son yin barci, ada sanda abin ya fara masa sai ake yimasa allurar barci mai shegen ƙarfi, a kuma haɗa masa da magani. Idan har akai haka yakan samu barci kona awa ɗaya zuwa biyune ya farka. A hankali kuma yana ƙara girma matsalar na hauhawa, sai yazama kobabu ciwon ma baya iya barcin sai yasha maganin ko anyi allura, kuma baya wuce awa biyu zai tashi. Al’amarin sosai ya fara neman taɓa masa rayuwa da karatu, amma da yake yanada ƙwazo sai akaita lallaɓawa.
A lokacin da karatunsa na likitanci ya fara zurfi sai ya fahimci shan maganin barci da yin allurar barci illace a lafiyarsa da hankalinsa da kuma aikinsa dake cikin manyan burikansa na rayuwa. Ballema da ALLAH ya taimakesa shaye-shaye baya cikin abin sha’awarsa, dan ya jima da fahimtar inhar zaiyi shaye-shaye koda na giyane to bafa zai kai labariba akan burin zamansa likita, sai kuma Asthma da yake da ita, itama ta taka rawar gani wajen sakashi ƙyamatar bushe-bushen hayaƙin samarin zamani. A ɗan tsakanin da ya daina yarda amasa allura, ya kuma daina shan maganin barci yasha matuƙar wahala, komawa yay tamkar wani ƙaramin mahaukaci, (kunsan rashin barci matsalane). Ya koma babu abinda ya keyi sai baƙin rai, abu kaɗan zai hau fushi, baya walwala sam, baison hayaniya, magana ma sai yaso ya keyinta. Karatunsa ma sai ya fara neman yin tangal-tangal.
Baya son zuwa aji, akoda yaushe yafi buƙatar zamansa a hostel shi kaɗai, idan kuma ya fito sai ya koma can gefe guda ya zauna inda mutanema basa gilmawa. Duk da wannan tashin hankali da Yoohan yake a ciki yana nan akan bakansa na daina yarda ayi masa allurar barci ko yasha magani, ya yarda zai jure duk wani matsi da rayuwa zatazo masa da shi dan ya samu ya sai-saita rayuwarsa kodan samun cikar burinsa. Aikam ya jigatu, dan a tsakanin badan Rich ba da ƙwaƙwalwarsa ma zata iya taɓuwa.
A cikin wannan yanayin da ya tsinta kanshi a wata ƙasa suka sami hutun sati biyu. A wannan karon sai ya haɗa kaya yace shi zaije gida 9ja hutu. Rich yayi mamaki matuƙa, dan yasan burinsu shine bazasu taɓa zuwa gidaba sai sun kammala karatu. Duk yanda yaso tunama Yoohan wannan alƙawarin yaƙi saurarensa sam, haka dole ya barsa ya shirya ya taho Najeriya. Da yazo Najeriyar ma bata canja zaniba. Dan sai addu’in coci da kullum papa yake kan kaisa ai masa bayan nashi, sai kuma masu magani da basu maraba da a kirasu da matsafa kowa na gwada tasa fasahar.
Ahaka ya kusan cinye hutun babu wani ci gaba, saima gaba al’amarin yakeyi dan yanata ƙara nisanta kansa da zama cikin mutane, ya kuma daina fara’a sam balle walwala. Cikin amincin ALLAH ana saura kwana biyu zai koma makaranta ALLAH ya haɗa shi da wani bawan ALLAH da wani yammaci, ya ɗauka mota ya ɗan fita daga gida suka kusayin taho mu gama da motar mutumin. Hankali a tashe waɗanda suke a waccan motar suka fito, amma shi Yoohan sai yaƙi fita yay zamansa a mota yana cika yana batsewa. Su duk zatonsu wani abun ya samesa, sai da suka buɗe motarsa dansu duba sai suka samesa lafiya lau. Sai dai kuma mutumin kallo guda yayma Yoohan ɗin ya fahimci yana tare da damuwa sosai, duk da wani kallon banza dana takaici da Yoohan ke musu sai yay murmushinsa daya ƙarama kamilar fuskarsa kwarjini, cikin kwantar da murya ya kama hannun Yoohan ya fiddosa a motar, ya saka drivernsa ya ja motar gefe dan a tsakkiyar titi suke. Danma titine na anguwa babu yawan shiga da fitar motoci.
Da farko Yoohan yaso bijirewa, sai dai kwarjinin mutumin ya cika masa idanu har yaji bazai taɓa iya masa musu ba. Can gefe bawan ALLAH nan yasa suka zauna, ya amshi ruwan da yasa drivern sa ya ɗakko masa a mota ya bama Yoohan yace ya sha. Nanma sai bai musaba ya amsa yasha kusan rabin robar yana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Sai da ya huta na wasu mintuna sannan mutum nan ya shiga masa tambayoyi cike da nutsuwa da kulawa. Wasu Yoohan ɗin na bashi amsarsu, wasu kam sai yay masa shiru.
Duk da bawan ALLAH nan ya fahimci Yoohan ɗin ba musulmi bane sai ya dubesa cike da kulawa yace, “Idan na baka wani magani ka gwada zaka amsa kasha?”. Kallonsa Yoohan ɗin yayi na wasu mintuna yana nazari, kamar bazai amsaba sai kuma can ya ɗaga masa kai alamar “eh”. Murmushi wancan mutumin yayi a wancan lokacin, ya ɗauka goran ruwan da Yoohan ɗin yasha ya rage yay addu’oi a ciki ya bashi. Yoohan ya jima yana kallon ruwan kamar bazai sha ba, sai da yaja lokaci mai tsayi sannan ya kafa baki ya shanye. Murmushi mutumin ya sakeyi, ya kama kan Yoohan yay masa addu’oi ya tofa masa. Daga haka yace masa ya koma gida ya kwanta, insha ALLAH yau sai an gaji da dogon barcinsa a gidansu an tadashi. Da izinin ALLAH kuma indai matsalar barcice ya daina fuskantarta sai dai idan hakan yana cikin doguwar ƙaddararsa.
A lokacin Yoohan ya tashine kawai ya bar wajen amma ko godiya baima mutuminba dan bawai ya yarda da zancensa bane, tunda shi yasan faɗi tashin da iyayensa keta famanyi akan matsalar. Shi kuma mutumin bai damuba sai kallo kawai ya bisa da shi a ransa yana fata da sakankancewa UBANGIJI zai amsa masa addu’arsa tai tasiri akan Yoohan ɗin………….✍

_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba’a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

*_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*

*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*

*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*

*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
*_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
*_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
*_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.

*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
*_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA… SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
*_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

__________________________________

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply