Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 23


Saran Boye 23
Viral

No. 23

…………….Tun sakkowar Yoohan daga sashensa Momy tai saurin ajiye kofinta na barasa, dan Yoohan ya daɗe da hanata shan giya, kuma ta masa alƙawarin dainawa. Sai dai wani lokacin damuwar da take ciki kansa tasha abinta musamman da daddare idan zata kwanta barci. duk da dama wani mai yawa take sha ba. Binsa tai da wani shegen kallo tamkar idanunta zasu faɗi ƙasa, yayinda fuskarta ma ta nuna shauƙi sosai fiye da yanda suke zaune. Yunƙurawa tai zata tashi amiyarta madam Monecca tai saurin riƙe mata hannu tana girgiza mata kai cikin hikima. Duk da bataso hakanba saita koma ta zauna tana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciyar da harsu Papa da fira ya ɗaukema hankali basusan da wucewar Yoohan ɗinba suka juyi suna kallonta.
“Lafiya Darling?” papa ya faɗa cike da kulawa a gareta. Murmushi yaƙe ta masa da cewar “Babu komai, bara naɗan rage kayana dai sun fara min nauyi”. Murmushi yay mata da aika mata kiss daga inda yake. Ta miƙe tana fadin, “Thanks Honey”.
Rakata da idanu yay cike da so da ƙauna harta haye sama sashen bedrooms ɗinsu. Sai da ta wuce da kusan mintina goma kafin Madam Monecca ta miƙe itama tana neman excuse ɗin zuwa toilet. Duk da kowa yasan dama amintarsu tafi zuwa ɗaya da madam Chioma babu wanda yay zargin komai a sauran matan. Sai ma maida hankalinsu ga hirar mazajen su da sukayi kawai.

A bakin gado Madam Monecca ta iske Momy zaune ta dafe kanta. Ta ƙarasa kusa da ita ta zauna, cikin harshen nasara take tambayarta damuwarta?.
Ɗagowa Madam Chioma tai idanunta cike da hawaye tana kallon ƙawarta, tace, “Monecca! Ina cikin damuwa sosai akan Yoohan, gaba ɗaya ya sake canjamin, ɗan kusancin da nake murnar ya ƙara shiga tsakaninmu a yanzu neman hanyar kakkkaɓar da shima ya keyi. Rungumarsa ma yanzu bayason yaga nayi, sai kiga ya kama ɗacin rai. Nifa na gaji da ɓoye-ɓoyen nan, dan gashi Honey harya fara tunanin wai yay masa maganar aure.…..”
“Aure!?” Monecca ta faɗa cikin tashin hankali.
“Ki bari kawai, jiya da yay maganar naji kamar na bindige shegen nan nama huta da wahalansa, Monecca zan fitoma Yoohan a mutum kawai da buƙatata, duk da kuwa nasan shegen taurin kansa”.
Cikin sauri Madam Monecca tace, “Karkiyi haka, dan zaki samu babbar matsala. kidai bari muyi tunani akai. Wai ita Mira bazata koma gidansu ba ne. sai naga kamar itace ke ɗauke masa hankali?”.
Cikin dariyar da Madam Chioma batai niyyar yiba tace, “Miracle fa? An gaya miki kalloma ta ishesa ne a gidan nan. Dama fa Zamani ne keta son ganin Yoohan ɗin ya aureta. kuma ni na gama fahimtar shima akwai tasa manufar akan hakan, shi kuma Yoohan ɗin duk da ƙyan Miracle ɗin bata gabansa shiyyasa nima zamanta a gidan bai taɓa damunaba”.
Ɗan taɓe baki Monecca tayi tana hararar Madam Chioma a kaikaice. a ranta kuwa rayawa take duk rintsi saita bi hanyar mallakar Yoohan ɗin, dan itama wani Masifaffen sonsa take, tana dannewa ne a gaban ƙawar tata kawai. Sun tattauna sosai ta yanda suke ganin ya dace a samu Yoohan ɗin a hannu. Kafin su fito wajen sauran ƴan uwansu a cigaba da hira.

Haka gidan ya cigaba da karɓar baƙi har dare, dan yau ranace ta ziyara a garesu, musamman ma gidan papa daya kasance babban mutum a wajensu.
Yoohan bai dawo gidanba sai yamma lis, ya samu giyar dasu Osen suka sha ta ɗan sakesu, harma sun fito daga sashensa Solomon ya shiga ya gyara. Duk suna harabar gidan zaune dan wasu abokan nasu sun ƙaru saboda jin Yoohan ɗin na gari, shima sai kawai ya zauna a wajensu duk da ba firar yakeba sosai.

______________________________
*_SAUDIA_*

Duk da Adawiya na ƙoƙarin ɓoye halayenta hakan bai hanata sakin layi a wasunl lokutan, dan babu abinda ke sakata takaici da ƙunar zuciya kamar yanda Nu’aymah taƙi nuna damuwarta akan duk abinda take mata. Gaba ɗaya Nu’aymahr ma ta maida hankalinta ga ibada ne kamar yanda ta ɗauro niyya tun daga gida.
Tayi mugun yin watsi da shirmen Adawiyar dan ta gama karantarta tsaf akan lamarin nata, to dama tasan tun suna secondary ma Adawiya tasha haɗata faɗa da ƙawayensu, ta kuma koma ta noƙe ta nuna ba ita tayiba. Amma sai bata taɓa nuna mata ta gane komaiba akan hakan, dan duk sanda taje ta sanarma Umm Adawiya ta mata kaza sai Umm ta lallasheta da nasiha da nuna mata muhimmancin haƙuri da ɗan uwa. Hakanne ke daƙile Nu’aymah daga ramuwa ga Adawiyar gashi har hakan ya zame mata jiki.
A wannan tsukun kuma data fahimci Adawiya ta canja sabon salon halaye sai itama ta canja takunta a kanta tana binta da gashi cikin ruwan sanyi, a ranta tana zargin kenan dama Adawiya na son Yah Ab komi?. A duk sanda tai wannan tunanin takanyi ƙoƙarin ganin ta ƙaryata zuciyarta, dan bata taɓa ganin alamar hakan ba ga Adawiya a dacan baya. A ganinta yanzu dai daɗin aurene yasa take ganin tafita kusanci da Abdallahn shiyyasa take shirya yaƙarta a kansa.

Yau ma kamar kullum Nu’aymah na ɗan yin barcin rana a falo, dan da daddare tafi maida hankalinta ga ibada ne, Abdallah ya shigo gidan. Adawiya ta wuce makaranta. daga hajjo sai Nu’aymah. Da tare suke da Hajjon a falo zaune suna ɗan hira sai barci ya kwasheta, itama hajjon saita nufi ɗaki ta kwanta danta huta.
Kafe Nu’aymah da idanu Abdallah yayi ko ƙyaftawa ba yayi, ya ƙaraso inda take yay tsaye kanta yana cigaba da kallonta tamkar mai nazarin wani abu. Cikin barci Nu’aymah taji alamar tsayuwar mutum a kanta. A ɗan firgice ta buɗe idanu saboda barcin nata baiyi nisaba sosai. Ganin Yah Ab tsaye a kanta ya sakata sake zabura tana binsa da kallon tuhuma itama. Sai kuma ta kumbura baki tana ɗauke kanta cike da takaicinsa.
Fuskarsa a haɗe ya zauna a kujerar da take kwance, hakan ya saka Nu’aymah saurin miƙewa sosai tana faɗin, “Yah Ab minene haka wai?”.
“K kika cancanci wannan tambayar ai?”. Ya faɗa shima yana miƙewa yasha gabanta fuskarsa a haɗe, ya cigaba da faɗin, “K harkin isa ki dinga wulaƙantani akan wani banza can Nu’aymah? Kinzo inda nake amma sai wani basar dani kikeyi”.
Cikin rashin fahimta take kallonsa, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta raɓashi zata wuce. Sake shan gabanta yayi yana mazurai, “Nabaki izinin tafiya ne?”.
Idanunta cike da ƙwalla tace, “To idan na zauna mizan maka? Kodan kaga nazo na zauna a gidanka kakeson ƙuntata rayuwata?”. Hannu ya ɗaga tamkar zai ƙwaɗa mata mari sai kuma ya fasa ya dunƙulesa yana taune lip ɗinsa jikinsa na tsuma. Yace, “Uban wanene Ameer?”.
Cike da takaici Nu’aymah ta kallesa ta watsar, kamar karta bashi amsa sai kuma mamakin abin nasa yasa ta kallesa da ƙyau. “Ban gane mikake faɗa ba Yah Ab?”. A hasale yace tayaya zaki gane mara mutunci. Nu’aymah wai harni zaki iya gudammawa a daren aurenmu saboda wani jaki? Kinsan baƙya sona miyyasa kika yarda aka saka mana ranar aure?”.
Sallamar Adawiya da batai zato ko tsammanin Abdallah zai dawo gidan a wannan lokacinba ya hana Nu’aymah da mamaki ya kume bashi amsa. Turus Adawiyan tayi tana kallonsu, dan wanda bai saniba zai ɗauka ne wata maganar arziƙi sukeyi da juna.
Binsu take da kallo tamkar idanunta zasu zubo ƙasa, Abdallah yay ƙaramin tsaki yana barin wajen ya nufi ɗakinsa. Har Nu’aymah ta cira ƙafa itama zata bar wajen Adawiya ta dakatar da ita ta hanyar riƙo mata hannu. Juyawa tai tana kallonta fuska a haɗe sosai, “Malama sakeni”. Nu’aymah ta faɗa a hasale.
“Anƙi a sakekin, idan kin isa kiyi duk abinda zakiyi. miya haɗaki da mijina?”. Kallon tsantsar mamaki Nu’aymah kema Adawiya, sai dai kuma a fili saita saki lallausan murmushi da har ya bayyana haƙoranta. Tace, “Tunda kinsan mijinkine mizai hana shi kije ki tambayesa miya haɗashi dani? Inaga kamar hakan zaifi birgewa a gareki shashasha kawai”. Ta ƙare maganar da fisge hannunta tai gaba tabar Adawiya da huci.
Hajjo data hango tahowar Nu’aymah saita saki labulen cikin ɗakin ta zauna a bakin gado. A haka Nu’aymah ta shigo ta sameta. “Hajjaju kin tashi ashe?”. Nu’aymah ta faɗa tamkar babu wani abu daya faru. Murmushi Hajjo tayi tana kallonta, “Ba dole na tashiba tunda kin gaza zuwa ki tadani mu wuce massallaci”.
Kusa da ita ta zauna tana dariya, “Ho hajjonmu, yanzu kuma dana tadakin cazaki ban barki kin rintsa ba, gara mu maidake da ƙwarinki karsu Abba suga kin sake rugurgujewa”.
Duka Hajjo ta kaima Nu’aymah da filo. Hakanne ya sakata tashi ta shige bayi da gudu tana dariya. Cike da tausayinta Hajjo ta sauke ajiyar zuciya, a ranta kuma tana ƙulla abubuwa da dama game da rayuwar Nu’aymahr

A falo kam Nu’aymah na shigewa Adawiya ta nufi ɗakin Abdallah a fusace, babu ko sallama ta tura ƙofar ta shiga. Sai dai ganinta yay kawai a kansa kamar an jehota. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Hakan ne ya sake hasala mata zuciya, sai ta fashe masa da kuka. “Yanzu Yah Ab abinda kakemin kana ganin adalcine? Ni dake matarka baka da lokacina amma kanada lokacin dawowa gida da wuri dan ka kasance da Aymah? Badan ALLAH yasa yau na shigo gidan da wuri ba bama zansan hakan na faruwaba tsakaninku. Shin wai da mi Nu’aymah ta fini ne? Wlhy sai ALLAH ya sakamin duk cin amanata da akeyi, kuma ni na gaji zan kira baba malam na faɗa masa komai tunda naga ita hajjo goyon baya take baku ma, ƙilama wataran a gabanta zaku shiga ɗaki ku rufo bazata tankaba saboda tana tsoronku……”
Wani wawan mari ya sauke mata a fuska da saida taga stars na mata kaikawo, balle dama ga azumi. A take ta zube ƙasa da sakin wata ƙarar kuka data kai har kunnen Hajjo.
“Kai Abdillahi lafiya kuwa? Mike faruwa hakane nakejin kukan Adawiya?”. Ta ƙare maganar tata dai-dai lokacin da take ƙarasowa cikin ɗakin. Ganin Adawiya kwance ƙasa dafe da kunatu ya saka hajjo zaro idanu, “Mikai mata Abdullahi?”.
Cikin ɓacin rai yace, “Hajjo barni da ƴar iskar nan kawai, wlhy tai wasa wataran saina karya ƙasusuwanta a gidan nan tunda ita kamar dabba take”.
“Ya isa haka”. Hajjo ta faɗa tana ɗago Adawiya dake ƙasa tana cigaba da sakin gunjin kuka. Saida ta zaunar da ita saman kujera sannan ta sake tambayar Abdallah miya faru?. Faɗa mata komai yayi amma banda tsayuwarsu da Nu’aymah, baisanma ita taji komaiba.
Cikin ɓacin rai Hajjo tace, “Adawiya dama baki da wayo haka? Ita ƴar uwar takice kuma tazama abar kishi a gareki? Har kike jifansu da wannan mummunan lafazin ita da mijinki? Adawiya yaushe kika bari ƙawayen banza suka canja miki tarbiyya ne? Har haka. To wlhy ki shiga hankalinki, idan kuma ba hakaba ni bazan ɗauki wannan banzan halayen a cikin zuri’ata ba, saina ɓatama kowa rai a cikinku har iyayen naku ni babu ruwana. Bandama iya shege kowa na fama da ibadar ALLAH a baki ke kina biyema sheɗan yana ɗoraki akan dokin zuciya. To idan na sakejin makamancin wannan zancen lallai sai kinyi nadama shashasha kawai. Banda ƙaddara da yanzu ita wadda kike cin zarafin ba itace matsayin matar tasa ba”.
Haka Hajjo taima Adawiya tas sannan ta fito ta barsu. Duk abinda akeyi Nu’aymah najinsu, sai dai ko tari bataiba balle a fahimci ta sani ɗin. Daga ƙarshema sukai shiri suka wuce massallaci, suda gidan kuwa sai anyi sallar asuba kuma.

Tun daga wanan ranar Adawiya ta shiga fishi da kowa a gidan. Daga gaisuwa bata sake tankama wani. Ahmad yamata nasiha harya gaji ya watsar da ita shima. Bayan kwana biyu da yay dai-dai da cikarsu kwanaki biyar da zuwa, ashirin kuma ga watan azumi Nu’aymah ta tattara inata-inata ta koma massallaci zaman ittiqafin.
Abdallah yaso hanata, sai dai Hajjo tace ya barta tai ibadarta yamafi zaman nata a gidan aita fitina. Badan yasoba ya haƙura, dan yaso a wannan zaman suyi magana ta fahimta da Nu’aymahr ya samu ya lallaɓa hajjo dasun koma a ɗaura musu aure.
Bayan barin Nu’aymah gidan sai ga Adawiya ta saki jikinta, ashe dama Nu’aymahr ce natsalar rayuwarta. Babu wanda yace mata komai. Saima hajjo ce taima Abdallah magana akan su shirya shi da Adawiyan dan tare zasu wuce Najeriya ayi bikin salla. Kai tsaye Abdallah ya nuna cewar bazaije ba, sai dai Adawiya, dan shi bai manta ALLAH ya isan da mahaifiyarsa tai masa akan zuwan nasaba.
Balbalesa da masifa sosai hajjo tai dan ita batasan dalilinsa na bijirewarba. da taga dai ya tirje ɗin saita kira baba malam ta faɗa masa komai. Shine ya kira Abdallahn cikin bada umarni ya sanar masa ya shirya suzo salla gida tunda suna samun hutu a wannan lokacin.
Abdallah ya shiga tsaka mai wuya sosai akan hakan, dan yasan dai umarnin mahaifiyarsa dana baba malam babu wanda yake da damar tsallakewa a ciki, dan duk sunada daraja da kima a idanunsa da rayuwarsa.

_________________________
*_NIGERIA_*

A kwanaki biyun nan abubuwa sun sake tsamari akan Yoohan, gaba ɗaya neman birkicewa yake saboda rashin samun barci, tun daga jiya zuwa yau yaƙi magana da kowa a gidan, yama kulle kansa a ɗaki ya hanama kowa ganinsa. Momy tayi kukan tayi roƙon amma yaƙi buɗewa. Hakama su Gebrail sunyi nasu ƙoƙarin ya sharesu.
Amma saboda ƙarfin hali da burinsa nason cika alƙawari sai gashi a safiyar yau talata yayi shirin tafiya kano. Tunda safe ya bama Solomon umarnin faɗama guards ɗinsa su tafi kano. Su kuma ya nema musu ticket guda uku. Solomon nason tambaya akan hakan yanajin tsoro, dan haka yaja bakinsa yay shiru yaje dai ya cika umarninsa

Kusan ƙarfe huɗu na yamma sai gashi ya sauka ƙasa cikin shigarsa ta suit blue mai haske. sun masa bala’in ƙyau duk da yana a yanayin da a kallo ɗaya zaka fahimci akwai damuwa tattare da shi.
Momy ce kawai zaune a falon sai Victoria da Abraham. Cikin girmamawa a garesa yaran suka shiga gaishesa. Hannu ya ɗaga musu kawai tare da ƙarasowa inda suke duk ya shafa kansu batare da yayi magana ba..
Ya maida dubansa ga Momy da idanunta suka kumbura saboda kuka, ɗauke kanta tayi ita a dole fushi take da shi. Baice komaiba ya ƙaraso inda take ya tsaya a gabanta tare da riƙe kunnuwansa da hannayensa alamar ban haƙuri.
Bata iya dogon fushi da Yoohan ɗinta. Dan haka tai murmushi tare da miƙewa ta rungumesa. Yau dai ya daure bai tureta ba, sai da ta gaji dan kanta ta sakesa sannan, ta amshi tie ɗin hannunsa ta ɗaura masa tana faɗin, “My Boy nikam yaushe zaka fara saka necktie da kanka?”.
Bai bata amsaba, sai dai ya sake ɓata fuska alamar shagwaɓa. Da ƴar dariyarta ta shafa masa kwantaccen sajensa da yasha gyara yau, ya kama hannun nata ya sumbata kaɗan.
“Ina zakaje ma wai?”. Ta tambaya tana tsatstsaresa da idanunta manya. Da ƙyar ya buɗe baki wajen bata amsa da “Kano”. “Kano!! kuma Yoohan? Mizakayo a kano kaida kake cikin wannan halin? Badai aiki ba?”. Kansa ya girgiza mata, batare daya bata wani ƙarin bayani ba yace mata, “Bye” yana nufar ƙofa.
Saurin binsa tai tana kira, amma sai yaƙi tsayawa, saida ta haɗa daɗan gudu ta cimmasa, duk da kuwa tafiyarma ba wani sauri yakeba saboda rashin ƙwarin jikinsa. Yanda ta riƙosanne ya sakashi waigawa ya kalleta. Tace, “Ina tambayarka mizakayo acan amma ka taho baka kulaniba Yoohan”.
Kansa dake faman masa ciwo ya dafe kaɗan, kafin cike da ƙosawa yace, “An gayyaceni ne” danshi baison yin ƙarya a rayuwarsa, kamar yanda ya tsani kuma saɓa alƙawari. Yana gama faɗa ya zare hannunsa zai juya ta kuma riƙewa. Yanzunkam bai juyoba sai da yaja wasu sakanni. Muryarta da damuwa ta zagayo gabansa tana magana. Amma maimakon ya bata amsa sai ya saka yatsansa akan baki yace “Shiii!!!”.
Shirun kuwa tayi tana kallonsa, ya ɗaura yatsunsa saman baki yay mata alamar *_Smile_* kamar yanda ya saba mata aduk sanda ya ganta a damuwa tun yana yaro. Duk da batason yin hakan saita murmusa. Yay mata jinjina yana ɗan lumshe idanunsa dake a kumbure sosai.
Tanaji tana gani ya shiga mota driver ya jasu shi da Solomon suka bar gidan, gashi Papa bayama ƙasar jiya sukai tafiya shi da Uncle Zamani.

★★★★★

Airport driver ya kaisu. inda acan suka haɗu da Manager Hamza Ibrahim yana jiransu. Sun gaisa cikin mutunta juna Hamza na mamakin ganin Yoohan ɗin a ƙunci fiye da waccan ranar. Ga idanunsa da fatarsu tai jajur hakama farar fuskarsa. Haka kawai yaji a ransa akwai abinda ke damun Yoohan ɗin. amma sai baiyi magana ba suka nufi ciki.

Ƙarfe biyar da rabi jirginsu yabar Abuja zuwa birnin dabo kodami kazo mun fika🤗😜.
Kamar yanda Yoohan ya iske Guards ɗinsa na jiransa haka suka iske motoci biyu na tarbarsu kuma. Hakan ya sai ya sake birge Yoohan matuƙa, dan haka bai shiga tasa motarba ya shiga wadda aka aiko musu, Guards ɗinsa kuma suka bisu a baya………….✍

[5/28, 3:14 PM] Q

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply