Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 31


Saran Boye 31
Viral

No. 31

…………..Ta ƙaramin gate Yoohan yay ficewarsa. Hakan yasa Kubrah data biyo bayansa ta rasa ina ya nufa. Har babban gate taje bayan ta gama dube-dube a harabar gidan bataga wata baƙuwar mota ba duk saina ƴan gidan.
Yanda ta iso gate ɗin a rikice tana tambayar maigadi sai abin ya bashi mamaki. Amma sai kawai ya bata amsa da cewar babu wanda ya fita.
“What?! Yama zakace dani babu wanda ya fita a gidan nan? Bayan nasan tabbas idan ba fitaba babu inda zai nufa”.
“Hajiya Kubrah wlhy babu wanda ya fita kamar yanda na sanar miki. Shin kodai ɓarawo ne ya shigo gidan ban sani ba?”.
Wani takaicine ya sake tuƙe Kubrah, batare data bashi amsaba ta bar wajen tana zuba masa harara. Shima tsit yayi bai sake magana ba, sai dai zuciyarsa fal saƙe-saƙe.

★★★★

Yoohan na fitowa waje yay turus dan mamakin ganin motocin gidansu da alamu suka nuna tsayawarsu kenan. Dan yanzu suke ƙoƙarin fitowa. Mamaki yay masifar sake kamashi ganin papa harda d.p.o Emanuel da yaransa. Tsuke fuska ya sakeyi ya nufesu ganin yanda suka tafi kai tsaye ga gate ɗin gidan dan su basu ganshi ba.
“Papa!” ya faɗa dai-dai lokacin da papa ya kai hannu zaiyi knocking gate ɗin. A kusan tare duk suka juyi garesa domin shigar muryarsa mai amo da kauri cikin kunnuwansu.
Wata wawuyar ajiyar zuciya suka shiga saki a jajjere, musamman ma guards ɗin Yoohan da suka san suna a cikin gagarumin tashin hankali inhar ba’a samesa anan ɗinba.
Papa har yi yay tamkar zai kifa dan saurin zuwa ga Yoohan ɗin. Yay wani bala’in rarumosa jikinsa ya rungume yana faɗin, “Thanks you lord. my son are you okay?
“Yes Papa! What is happening? Mi kakeyi anan? Miya kawoka kano?”. Yoohan ya jerama papa tambayoyin yana zare jikinsa daga nasa tare da bin guards ɗinsa da ƴan sandan dake zagaye da su da kallon tuhuma suma.
Sake jawosa jikinsa papa yayi, batare daya bashi amsar ko ɗaya daga tambayoyin ba, ya shiga duba jikinsa sama da ƙasa kamar mai tunanin an masa wani abu. Sai kuma ya kama rigar shaddar jikinsa yana faɗin, “Yoohan minene wannan?”.
Wani irin luuuu da idanu Yoohan yayi tare da huro iska daga bakinsa. Cikin ƙosawa da abinda ke faruwa yace, “Papa kaya ne mana. Wai mi kukeyi anan wajen ne? Miya kawoka kano?”.
Cikin tsananin nuna ɓacin rai papa yace, “John! Yau kaine da kayan hausawa a jiki? Mike damun kanka da tunaninka?”.
Sake shiga wani takaicin shima Yoohan ɗin yayi, dan a take fuskarsa ta sake nuna fusata. Tayaya yana tambaya amma batare da an basa amsaba papa kuma na masa wasu tambayoyi mara kangado sai kace wani ƙaramin yaro. A tsawace ya kalli su Solomon da faɗin, “Mi kukazo yi anan nace?!!”.
Yanda ya daka tsawar basu Solomon kawai ba, hatta Emanuel da yaransa duk da suke ƴan sanda saida suka razana. Balle kuma ƴan anguwa da suka fara taruwa kallo. Gashi Yoohan yayi maganar ne da yare.
Solomon ne cikin rawar jiki data baki ya fara masa bayani,
“Sir! Dama mun zata ko wani abu mara ƙyaune ya sameka. Tunda muka tashi muka fahimci baka a cikin hotel ɗin. Gashi an duba ko ina amma babu alamarka. Ma’aikatan kuma duk sun tabbatar mana basuga fitarka ba, ga kuma wayoyinka mun samu baka fita dasu ba. To shine mukai tunanin ko anyi kidnapping ɗinka ne shine muka kira boss muka sanar masa…….”
“To da kuka kawosu nan, sune sukai kidnapping ɗin nawa kenan?”. Yoohan ya faɗa cikin katse Solomon.
Kasa bashi amsa Solomon yayi, dan harga ALLAH ba ƙaramin gulma da munafincin su baba malam sukai wajen papa ba akan gaba ɗaya sun janye ra’ayin Yoohan ɗinma, amma sunyi bakin ƙoƙarinsu suga tun a zuwan farko bai sake zuwa gidanba sai dai hakan ya gagara. Kuma jiya a yanda suka bar gidan yana cikin wani yanayi yasa sukai suspecting ɗin kosu baba malam ɗinne suka turo aka saceshi. Shiyyasa papa na isowa maganar gidan suka fara faɗa shiyyasa yace su kawosa…….

★★

Baba malam da Kubrah kusan a tare suka shiga falon. Shi ya fitone wajen Yoohan ɗin dan yanason su tattauna ta yanda ya kamata Yoohan ya fara neman ilimin dazai taimakamasa wajen bautar ALLAH. A tunaninsa zuwa lokacin ya kammala cin abincin da Nu’aymah taje kai masa. Dan rashin dawowar tata baisa sun zargi komaiba da ga shi har Umm. A tunaninsu ko bayan takai masan ta shiga sashen Hajjo ne ko kuma Addah.
Da sauri ya ƙarasa ga N’aymah daya hango ƙasa wanwar, ga kuma falon babu alamar Yoohan ɗin sai ƙamshin turarensa kawai. Tiren abincin data kawo yana a ajiye a inda ta ajiyesa.
“Ya ALLAH! K lafiya kuwa mamana? Mikikeyi kwance anan haka?!”. Baba malam ya faɗa yana kai hannu ga Nu’aymahn. Da sauri ya zabura dan jin jikinta yayi sanyi ƙalau ya saki. Yay azamar maida yatsunsa biyu wajen ƙofar hancinta. ‘tabbas bata numfashi’ ya ambata a zuciyarsa yana ɗagota gaba ɗayanta.
Hakan yayi dai-dai da ƙarasowar Kubrah da tun shigowar baba malam tana biye da shi, sai dai shi bai gantaba sai yanzun data ƙaraso garesu da dauri tana faɗin, “Abbah lafiya? Miya faru da ita ne?”.
Cikin tashin hankali baba malam yace, “Ban saniba nima Khadijah, kinga miƙo ruwa dan bata numfashi”.
A hanzarce ta ɗakko masa ruwan da Yoohan yasha ya bari, ya miƙa hannu ta tsiyaya masa. shafama Nu’aymah yay a fuska. sai dai ko motsi batayiba balle ai tunanun zata farko. Hankalin baba malam ne ya sake tashi matuƙa. Ya ɗago idanunsa da sukai jajur ya kalli Kubrah.
“Khadijah maza kiramin Ahmad ko malam ƙarami ko Omar. duk wanda kakaci karo dashi cemasa ya fiddo mota”.
Amsawa tai da to tana fita da sauri. Sai dai maimakon ta wuce aiken da akai mata saita samu waje ta laɓe abinta tana wani taɓe baki da sakin murmushin mugunta. Zuciyarta fes take akan halin da Nu’aymahr ke ciki. Ita ta mutu kota rayu hakan ba damuwarta bace a yanzu. Dan ita kaɗai tasan miyasa take bala’in jin zafin yarinyar.

Baba malam da baisan Kubrah bata tafi aikansa ba ya ɗakko Nu’aymah gaba ɗayanta ya fito. Da sauri Kubrah data hangosa ta sake maƙewa tana zaro ido waje. dan batai tunanin baba malam zai fito da Nu’aymah ba yanzun, a tunaninta ko saita kira ɗaya daga cikin wanda ya aiketan.
Oho shi hankalinsa ma bai kai gareta ba. Jikinsa na tsuma bakinsa na ambaton ALLAH ya nufi harabar gidan. cikin sa’a kuwa sai hakan yay dai-dai da fitowar malam ƙarami daga sashin su Kubrahn hannunsa ɗauke da leda da key ɗin mota.
“Abba lafiya? Miya sameta?”. Malam ƙarami ya faɗa a ruɗe yana nufo baba malam dake ɗauke da Nu’aymah.
Da sauri baba malam ya bashi amsa da, “Maza buɗemin mota malam ƙarami, yanzu ba lokacin sanin mafari bane ba”. Cikin sauri malam ƙarami ya cika umarnin baba malam. ya karasa ga motarsa ya buɗe. Baba malam na ƙoƙari sakata a ciki Kubrah ta ƙaraso wajen. Tamkar an kira Hajjo sai gata itama ta fito daga sashenta ita da Husnah da alama ma fita zatayi.
A rikice ta nufesu tana tambayar ba’asi. Dan taga yanda baba malam ya saka Nu’aymah a motar tamkar bata da rai. Babu yanda baba malam ya iya dole yayma Hajjo bayani a taƙaice. Kubrah na ƙoƙarin shiga motar dan a tafi da ita Hajjo ta tureta gefe ita ta shi. Yayinda Husna ta ƙirƙira cikin gidan da gudu tana ƙwalama Umm kira tana kuka. Dan ita a zatonta Nu’aymah kota mutune. Yarinyace ƙarama bata wuce 9years ba. Itace autar amaryar Abbah Musbahu.
Fara fitowar mutanen gidan saboda ihun Husna yay dai-dai da ficewar motar da aka sakata daga gidan. Sai dai suna fitowa idon Baba malam ya sauka akan su Yoohan. Da mamaki ya tsaida malam ƙarami dake ƙoƙarin hawa titin layin. buɗe motar yay ya fita yana faɗin, “Malam ƙarami kuje asibitin ina zuwa. da alama wajen nan babu lafiya dan kamar Yahya ne”.
Daga malam ƙarami har Hajjo dake baya riƙe da Nu’aymah tana faman jijjigata da tofa mata addu’a basu fahimcesa ba. Sai malam ƙaramin yabi umarni.

Cikin nutsuwarsa ya ƙarasa garesu tare da yin sallama duk da alamarsu bai nuna na waɗanda ya dace yayma sallamarba. Sai bai saniba ko akwai musulmai a cikinsu. Ai ko cikin sa’a sai gashi wasu daga cikin ƴan sandan sun karɓa masa. Harda ma risinawa suna gaishesa dan darajar da ALLAH yay masa ta babban mutum kuma jagora.
Ya amsa musu ne idonsa akan Papa da sukema juna kallon sani. Kusan a tare papa da baba malam suka ambaci sunan juna.
“Pastor Goshpower!”.
“Sheikh Sooraj Hashim!”.
Sai kuma kawai sukaga Papa ya kece da dariya yana tafa hannu. Ya sake nuna Baba malam yana faɗin, “Da gaske Sheikh Sooraj nake gani anan?”.
Kafin baba malam dake kallonsa fuskarsa babu yabo babu fallasa ya bashi amsa Solomon yace, “Sir! Ai shine mutumin da…….”
Malalacin kallon da Yoohan ke masane ya hanasa ƙarasawa, yay saurin duƙar da kansa ƙasa yana haɗiye sauran maganar.
Kallon Yoohan baba malam yayi. Sai kuma ya sauke wani lallausan murmushi. Cikin halin dattako irin na masu ilimi da sanin ya kamata yace, “Yahya ka sanshi ne?”.
Kai Yoohan ya jinjinama baba malam, kafin a hankali yace, “Mahaifina ne”.
Sosai alamar mamaki ya bayyana ga baba malam, dan fuskarsa ta nuna ƙuru-ƙuru. Yace, “Yahya da gaske?”.
Kafin Yoohan yay magana Papa da yay matuƙar tsuke fuska ya matso gaban baba malam ɗin yana faɗin, “Mizaisa ya maka ƙarya?”.
Kamar baba malam zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana sake dai-daita nutsuwarsa. Kusan sakanni goma kafin yace, “Okay! Alhmdllh. Inaga to muƙarasa ciki tunda yau gashi kazo gidana…..”
“Never!”. Papa ya faɗa cikin saurin katse baba malam ɗin.
Da sauri Yoohan yace, “Papa saboda mi?”.
Kallonsa papa yayi da tsananin ɓacin rai. Kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru ya sake maida kallonsa ga baba malam dake murmushi.
Baba malam yace, “Kayi haƙuri, dan kai yau sunanka baƙona. Ka cancanci na karramaka da masauki da abin ci da sha. Dan koba komai kazo ƙasata ne, yankina, gidana kuma”.
Tsaki papa ya ja. Tare da kallon d.p.o Emanuel yace, “D.p.o kama shi, inason sanin dalilin alaƙarsa da yarona”.
“What!!?” Yoohan ya faɗa a zabure yana ƙarasowa gaban papan. Cikin nuna fusata yace, “Papa mi kake shirin yi haka? Dammi zakasa a kamashi bayan ba’a cikin gidansa ka ganniba. Sannan ba tare da shi ka ganni ba”.
“Rufema mutane baki!!. Karna sake jin bakinka anan. Wannan wasane tsakanin manyan daji guda biyu. Ka shiga mota yanzun nan zamu koma Abuja da kai”.
“Babu inda zanje papa. Domin aikina ne ya kawoni nan. Banga kuma dalilin dazaisa na barshi ba akan dalili mara tushe. Ku kuma (ya faɗa yana nuna police ɗin) duk wanda yay gigin matsowa koda kusa da shi ne na rantse da ALLAH sai ya rasa aikinsa. Idan kunji ƙarya zaku iya gwada hakan kuma”.

Tashin hankaline ƙarara ya bayyana a fuskar d.p.o Emanuel. Dan shi kam an sakashi a tsaka mai wuya. Matsayin papaa a garesa ya wuce duk yanda mai karatu zaiyi hasashe. Sannan ɗansa Yoohan basai an faɗaba, yanada faɗa aji ga gwamnatin kowacce jaha saboda rawar da yake takawa akan harkar lafiya dama matsayinsa na babban likita da duniya gaba ɗaya ke ji da gani a yanzu. Dan tabbas yaron yana lokaci da lokacinsa.
“Yahya! Iyaye nada matuƙar daraja ga ɗa. Ka daina tsaurara harshenka ga mahaifinka kaji. Karka damu da tsakanina da shi, dan a yau a yanzu ya fini gaskiya tunda a wajena ya sameka. Ba’a wasa da iyaye. Dan haka karka sake maida masa magana kaji”. Baba malam ya faɗa idanunsa akan Yoohan dake ta faman haɗiyar zuciya da sauri-sauri.
Kai kawai ya ɗaga ma baba malam, dan zuciyar tazo wuya bazai iya magana ba. Ya watsama guards ɗinsa wani shegen kallo. Kafin ya raɓa papa da baba malam ya bar wajen batare da yayima kowa maganaba.
Papa da yasan minene fushin Yoohan yay saurin bin bayansa yana kiransa. Amma ko kallonsa baiyiba balle ya saka ran amsawa. Ya buɗe murfin motar a fusace ya shiga baya, shima Papa ɗayan gefen ya zagaya ya shiga yana cigaba da kiran sunan sa. Hakanne ya saka drivern sa da Solomon saurin shiga suma, sauran guards ɗinsa da su Emanuel da suka sami mafita suma suka nufi nasu motocin batare da suncema baba malam komaiba.

Nannauyan numfashi baba malam ya sauke lokacin da mitocin suka harba kan titi. Yayinda can ƙasan zuciyarsa ke mamaki da jinjina al’amarin UBANGIJI. ‘Yoohan ɗan Pastor Goshpower ne da gaske? Lallai UBANGIJI mai yin yanda yaso, a lokacin da yaso, ga kuma wanda yaso’. Baba malam ya faɗa a fili. Yasan tabbas UBANGIJI shike fidda rayayye a cikin matacce, ya kuma fidda matacce a cikin rayayye. Amma al’amarin akwai ɗunbin ban al’ajabi a cikinsa, dan yasan abubuwa masu yawa game da papa tun shuɗaɗen lokaci kafin yakai haka.
Da wannan tunanin baba malam ya koma cikin gidan, inda ya tadda duk jama’ar gidan sun fito sunata tararrabin abinda akace ya faru da Nu’aymah. Su Abban Abdallah ma shirin shiga mota suke zasubi bayansu asibitin.
Ganin baba malam ya sakasu dakatawa, duk suka nufesa hankali tashe suna tanbayar yaya Nu’aymahn.
Tausayinsu ne ya kamashi. dan haka cikin taushin murya ya kwantar musu da hankali, tare da sanar musu shima yanzu zai bisu. Basu zauna ɓata lokaciba suka ɗunguma a mota ɗaya Omar ya jasu, akabar su Umm a gida na binta da addu’a.

Yoohan da tunda suka tafi ya ƙi kula papa daketa so yayi magana yay kwance jikin kujera hannunsa dafe da goshinsa cike da tsananin takaicin abinda ya faru tsakaninsa da Nu’aymah yauma. Yarasa mike jan hankalinsa ga aikatama yarinyar nan wannan banzan ɗabi’ar?. Abinda ba halinsa ba amma yana ƙoƙarin ɗabi’antar da shi a gareta. Saima yaji na yau yafi masa zafi a rai fiye da na jiya.
Da sauri ya kwanto jikin papa saboda wata hajijiya-hajijiya dake neman kwasarsa. Sake rikicewa papa yayi. A matuƙar ruɗe ya shiga girgiza Yoohan kai kace gani yay baya numfashi.
Sosai takaici da hayaniyar papa ta sake rufe Yoohan ɗin, amma sai ya daure cikin taushin murya da sanyayata yace, “Papa Please relax. Ina lafiya fa”.
Da sauri ya rungumeshi yana sauke numfashi a jajjere. Su dai su Solo suna kallon ikon ALLAH daga gaba. A haka suka ƙarasa hotel ɗin da har yanzu akwai sauran yaran Ema… Da taimakon papa Yoohan ya fita, shine ya kamasa har ɗakin da yake. Su kuma su Solomon suka dakata wajen manager ɗin hotel ɗin suna musu bayani akan anga Yoohan ɗin su kwantar da hankalinsu.

Papa na zaune kusa da Yoohan dake kwance idanu a lumshe, hannunsa har yanzu dafe yake da kansa. Yama rasa wane kalar tunani ya dace yayi akan matsalarnan guda biyu. Alaƙalar Papa da Baba malam. Abinda ya aikatama Nu’aymah a karo na biyu. Buɗe idanunsa yay a hankali kan papa da yay shiru shima yana wani tunani can daban, sai da yay masa kusan kallon sakan goma kafin cikin nuna kulawa ya kamo hannunsa cikin nashi da faɗin, “Papa!”.
Firgigit ya dawo hankalinsa tare da kallonsa. Yoohan ya sake lumshe idanu ya buɗe a kansa. “Papa dama kasan malamin nan ne?”.
“Yoohan! Wannan tambayar taka bata da muhimmancin samun amsa. Kai ya kamata nasan minene alaƙarka da shi?”.
Kamar Yoohan ya faɗi ainahin gaskiya sai kuma wata zuciya ta gargaɗesa dayin hakan. Yunƙurawa yay ya tashi zaune sosai ya jingina da fuskar gadon. Hannunsa ya sake maidawa cikin na papansa, cikin kwantar da murya yace, “Papa akwai abinda nake buƙata a wajensa, shiyyasa na kwantar da kaina nake binsa a sannu harna cimma burina. Sai dai kuma gashi kai kazo cikin mintuna goma kacal kana shirin rusamin shiri na. Miyasa zaka biyema su Solomon da shirmensu? Ai koda suka sanar maka na ɓata ko tunanin inda za’a’a sameni kamata yayi ka jira harna dawo kaji ta bakina. Haba papa da girmanka a ƙasarnan amma kake abu tamkar wani mara…….”
Saurin katsesa papa yayi ta hanyar ɗaga masa hannu. hakanne ya saka Yoohan haɗiye sauran maganar tasa. Papa ya gyara zamansa sosai da cewa, “Naji nayi kuskure, amma kaima harda laifinka. Miyasa tun tuni baka sanarmin ba, bayan kasan niɗin mai baka goyon bayane akan kowanne irin business naka musamman a wannan yakin”.
“Nima naji nayi kuskure to. Amma ina da dalilin ɓoyewar ai. Da ace na sanar maka mi nake shirin yi zaka iya ɓatamin aiki dan kanada gaggawa papa. kai kafi son komai da zafi-zafi a lamarinka. Hakan kuma na taɗiyeka daga nasarorinka. Yanzu da ace bakazo ba da cikin satin nan zan kammala aikina. Amma yanzu kaga ka kawo min togaciya dan zai fara kokwanto a kaina. Kaga kenan saina sake sabon ginin da zai ƙara yarda dani hundred percent kamar farko”.
Cikin tsananin jin daɗi papa ya rungume Yoohan yana faɗin, “I am sorry my sweetheart, kai ɗinne ba’a gane kanka sai kaso. Yanzu dai na maka alƙawarin da kaina zan gyara abinda na ɓata a yau ɗinnan kaji”.
Ɗagowa Yoohan yay da sauri, yace, “Papa da gaske kakeyi?”.
“Ƙwarai kuwa my dear son”.
Wani lallausan murmushi Yoohan ya saki najin daɗi. Dan ya fahimci lallai sai ya nunama papa akwai manufa a tafiyarsa da baba malam sannan zai samu nutsuwar samun damar fahimtar ilimin addinin islama da zai kare kansa anan gaba a wajensu dama duk wani dake a cikin ahalinsa da yasan zai kawo masa togaciya. Amma a yanzu yasan duk yunƙurin da zaiyi sai sun taɗesa saboda rauninsa na kasancewa sabo cikin addini mai ɗunbin haske irin musulinci. A yau kawai daya kasance a ciki jinsa yake tamkar sabon mutum. Tamkar darajarsa ta ƙaru. Duk wani nauyin zuciya da ƙunci da yakan tsinta kanshi a ciki a baya yau sai yaji tamkar ansa kwano an kwashesu tas.
Jikin papa ya sake lafewa tare da lumahe ido. Papa ma dake jin daɗin Yoohan ya fara ɗaukar huɗubarsa ya shiga shafa kansa cike da jin daɗi da annashuwa. Dan shima har zuciyarsa ta gama shirya masa babban aiki akan baba malam tsaf…………✍

Tofa masu karatu. Yanzu za’a fara wasan😎 dan haka kumuje zuwa filin daga😉😱🚶🏻.

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/23, 10:10 AM] +234 816 133 8078: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

*_BARKA DA JUMA’A. ALLAH yasa muna cikin bayin da zasu sami gafara a cikinta😭🙏🏻_*

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply