Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 33


Saran Boye 33
Viral

No. 33

……….Koda suka isa can ɗinma wasu jerin motocinne sukazo tarbarsu tare da bodyguard ɗin papa. Haka suka nufi gida zuciyar Yoohan sam babu daɗi.
Sun sami tarba da ga ahalin nasu, musamman ma Yoohan da ya jima dama baya ƙasar. Shima yaji daɗin ganinsu sosai, musamman kakarsa data haifi Papa da ƙannen papan su uku mata da yaransu da ya gani sunzo musu, ga kuma kakarsa data haifi Mom itama dai bata komaba har yanzun.
Madam Chioma sai tattalinsa take kamar ta haɗiyesa dan farin cikin ganinsa, gashi taga ya wani ƙara mata ƙyau da kwarjini da cikar haiba kamar wanda akaima wankan iji.
Haka dai ya daure yana biye musu sama-sama dan kamar ko yaushe fuskar dai babu walwala. Ƙasan ransa ma basusan cike yake da tashin hankalin ganin yanda suka cika gidanba tamkar masu biki, musamman da ya san baƙar ƴar tsamar dake tsakanin kakanninsa guda biyu. A yanzu ma haka ya tabbata wannan zuwan na kakar tasu yanada nasaba da zaman mama Deborah Abujan.
Da ƙyar ya iya zaman mintuna goma a falon ya gudu sama a cewarsa zai watsa ruwa ya dawo. Yana shiga ya ja tsaki tare da dafe kansa. Zama yay cikin kujerar dake ɗakin ya zaro wayarsa a aljihu, sai faman yamutse fuska yake dan har yanzu ransa a ɓace yake akan dawowar dole da papa ya sakashi yi. Wayar ya shiga sarrafawa cike da ƙwarewa. Kansa tsaye yay kiran number baba malam dan yana buƙatar yin magana da shi. Cikin sa’a kuwa bugu uku ya ɗaga.
Sai da suka gaisa Yoohan yace, “Uncle mun iso gida, amma nifa gobe zan dawo kano”.
“Alhamdulillahi, barkanku da hanya. Amma mizaisa ka dawo Yahya?”.
Fuska ya ɓata kamar yana gaban baba malam ɗin, cikin nutsuwarsa da taurin kai irin na samari masu ji da lokacinsu yace, “Uncle ina buƙatar neman sani akan addinin musulinci. Ta wannan hanyarne kawai zan iya yaƙar duk wani ƙalubalen da nake hange da ga ƴan uwana. Ta hanyar neman ilimin ne kuma kawai zan bautama UBANGIJINA. Ba tsoro nake duk wanda ya sanni yasan na zama musulmi ba. Kawai ina buƙatar kwankwaɗar madarar ilimine nima cikin kwanciyar hankali”.
Sosai baba malam yay murmushi har Yoohan na jiyo sautinsa. “Yoohan karka damu kaji, bama sai ka dawoba, inason kabi komai a hankali kamar yanda ka faɗa. Akwai ƙanina dake anan zaune abujan amma yana nan basu koma bikin salla ba, dama na shirya masa magana kawai zaka ringa ɗaukar karatu a wajensa tunda anan kafi zama fiye da nan kano, kaga zaifi maka sauƙi ko kuwa?”.
Ɗan jimm Yoohan yayi alamar tunani, bawai hakan bai masa baneba. A’a tunaninsa shine yanayin aikinsa, dan ya tabbatar a nan abujar ma ba samun zaman yake ba. Yanzu haka kwanaki biyar kawai zaiyi ya wuce Lagos. daga can kuma zai shiga Maiduguri. Yana da tabbacin kuma da wahala ya ƙulla wata guda bai sake barin ƙasarba ma……..
“Yahya ko akwai damuwa ne?”. Baba malam ya katse masa tunaninsa.
Ajiyar zuciya ya sauke, tare da miƙewa ya taka jiki a sanyaye zuwa bakin gadonsa ya sake zama. “Uncle babu komai. Kawai dai ina duba yanayin aikina ne da baya barina zaman waje ɗaya, sai nake gani kamar hakan zaiyi wahala a gareni. Inba dai ajiye aikin zanyiba kawai na fuskanci karatun…..?”.
“A’a Yahya bazai yuwuba, duk da bansan ya aikin naka yake ba bazan baka shawarar ajiye aikinka ba. Dan mu musulinci addini ne dake son mutum mai neman na kanka. Ta hakane zaka kare mutuncinka da tarbiyyarka, ka kuma nema halalinka harka tausayama na ƙasa da kai da marayun ALLAH. Yahya karka manta kaifa bawan ALLAH ne mai yawan hidima, sannan bayane goya marayu. Idan ka ajiye aiki yaya masu jira daga garekan zasu kasance kuma?. Kaf Annabawan ALLAH tun daga farkonsu har zuwa MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su tabbata a gareshi, tarihi ya nuna mana nauyin dake kansu na yaɗa kalmar ALLAH baisa sun rayu a rashin neman na kansuba, balle ai tunanin zama daga jiran na wani ko taskar masu mulki. Dukansu sunada sana’oinsu. To inhar mutane masu daraja irinsu sun yi gwagwarmayar neman halalinsu mu su wanene da bazamu tashi munema na kanmu ba”.
Ajiyar zuciya Yoohan ya sauke. Murya a sanyaye yace, “Hakane Uncle. Tunanin hakan baizo min a rai ba shiyyasa”.
“Karka damu ALLAH yana tare da mu. Insha ALLAHU mafita zatazo daga UBANGIJIN rahama da jinƙai”.
“To shike nan Uncle nagode sosai. ALLAH ya ƙara lafiya da tsahon rai. Bara na barka ka huta dan yanzu na sami nutsuwa, ɗazu kam hankalina a tashe yake sosai”.
Ƴar dariya baba malam yay masa sukai sallama ran Yoohan fes. Da ƙarfin zuciyarsa kuwa ya miƙe ya fara zame kayansa dan son watsa ruwa.

★★★

Tunda suka ajiye wayar baba malam ya shiga dogon nazari, harga ALLAH yana jin son Yoohan cikin ransa. hakan har mamaki yake bashi wani lokacin. Duk da yasan UBANGIJI kan jefa soyayyar wani a zuciyar wani batare da wata alaƙa ba a tsakaninsu
Har yanzu baisan abubuwa da yawa ba dangane da Yaron ba, amma sai ya keji zuciyarsa na tsananin ƙyautata masa zato akan abubuwa da dama na rayuwar yau da gobe. Haɗuwarsu ta uku kenan kacal. Amma ya fahimci wasu ƙyawawan halayya da ko a cikin musulman ma ba kowane ke da su ba. Ga ƙyauttawa da yarda da yaron ke bashi ɗari bisa ɗari.
Numfashi ya ɗan sauke wani gefen zuciyarsa na sake ƙarfafa masa gwiwa akan alkarin da yake shirin aikatawa. Yayinda can kuma wata ke gargaɗarsa musamman akan ahalin da Yoohan ɗin ya fito………
“Malam lafiya kuwa ka zurfafa a tunani haka?”. Umm data shigo tun ɗazun tanata sallama bai jiba ta faɗa tana mai katsesa.
Ajiyar zuciya ya sauke da sauri tare da kallonta. Gefensa ya nuna mata da hannu alamar ta zauna. Batare da tayi musu ba ta zauna kuwa idanunta a kansa. Hannunsa ya saƙala cikinnata yana ɗan sake furzar da huci. “Jannat wani al’amarine yanzun nan UBANGIJI ya saƙaminshi a cikin tunanina akan yaron nan dana sanar miki jiya ya musulunta. Sai dai kuma wani sashi na zuciyar tawa yana gargaɗina dason jefani a kokwanto game da al’amarin”.
“Tom nidai a nawa tunanin sai naga kamar shaiɗanne Malam. mizai hana ka bama al’amarin wani ɗan lokaci haka, sai ka duƙufa neman zaɓin ALLAH akan yuwuwarsa ko barinsa”.
“Eh tabbas kinzo da shawarar hankali Jannat. Insha ALLAHU kuma zanyi amfani da ita. Amma kema inason ki tayani dan ALLAH”.
“Insha ALLAHU zan tayaka Abban Nu’aymah, ALLAH ya tabbatar mana da alkairinsa”.
“Amin ya rabbil-alamin”. Ya faɗa cike da jin nutsuwa da gamsuwa akan shawararta”.
______________★★★

Kwanakin Nu’aymah uku a asibiti aka sallamota. Alhmdllh jikinta yayi ƙyau sosai, sai dai haɗarin da Doctor ya tabbatarma iyayenta tana a ciki akan iya fuskantar loosing mamory shine ya jefasu a cikin matuƙar damuwa.
Yayinda ita kuma da batasan mike faruwa ba sai tata matsalar ta zama Naser. Dan a kwanaki biyun nan daya ɗauka da zuwa gaba ɗaya ya takurama kowanne irin motsinta. Duk da daga gaisuwa babu abinda ke sake haɗasu sai magana kamar kowa. Amma kallon da yake jifanta da shi da tarewa a asibiti da yayi ya tabbatar mata cewar zuwan nasa akwai manufa.
Tun bayan dawowarsu gida Umm ta taimaka mata tai wanka taci abinci da magungunanta ta kwanta danta huta. Shine ta samu damar yin tunani akan Naser ɗin. Kamar daga sama ta dinga jiyo hayaniya na tashi a gidan, sosai mamaki ya kamata, duk da ta tabbatar hayaniyar bata faɗa bace tasan wannan ba ɗabi’ar mutanen gidansu baceba hakan. ‘To minene ya faru?’ ta faɗa a fili cikin sake zurfafa mamakinta.
Kusan mintuna ashirin sai kuma taji hayaniyar ta lafa. bata ko motsa ba balle ai tunanin zata fita ta ganoma idanunta, haka ta cigaba da kwanciyarta tun tana tunani har barci mai nauyi ya ɗauketa saboda a maganin nata akwai na barci daman.

Kiran sallar magriba ne ya saka Umm shigowa ɗakin Nu’aymah ta tadata. Da ƙyar ta samu ta tashi dan barcin nata yayi nisa sosai. Taimaka mata tayi tai alwala kafin tai yunƙurin fita zata barta…..
“Umm wai hayaniyar mi naji anayi ɗazun?”. Ta faɗa cikin katse hanzarin Umm dake ƙoƙarin fita.
Batare da Umm ta juyo ta kalleta ba tace, “Su Abdallah ne, sunma shigo dubaki kina barci”.
Sosai gaban Nu’aymah ya faɗi, sai dai kafin ta sake cewa wani abu Umm ta fice abinta. Shiru tai tsaye hannunta riƙe da hijjab, dan zuciyarta cike take da tambayoyin miya kawo su Yah Ab ɗin gida a yanzun bayan kuma shine da kansa yacema Hajjo sai bikin su aunty Hajarah daya rage saura kwanaki ashirin cif yau ayi. Ganin bata da mai bata amsarta sai ta saka hijjab ɗinta ta kabbara salla kawai.
Koda ta idar bata fitaba tai zamanta a ɗaki, sai da tai sallar isha’i da shafa’i da wutiri sanna ta fito falonsu danta ɗansha iska. Umm kawai ta tarar zaune. Ta zauna kusa da ita tare da ɗora kanta a gefen kafaɗarta.
Ɗan kallonta tayi, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta ɗaura hannunta a wuyanta. Jin jikinta babu wani zafi ya saka Umm sauke ajiyar zuciya da janye hannunta.
“Umm nafa warke”. Nu’aymah ta faɗa tana murmushi dajin ƙaruwar ƙaunar mahaifiyar tata a cikin rai. Itama Umm Murmushin tayi, ta shafa kumatun ɗiyar tata da faɗin, “Ai haka muke fata Nu’aymah, ALLAH ya ƙara miki lafiya dai damu baki ɗaya”.
“Amin Umm”. Ta amsa mata zuciyarta cike da damuwa. tasan iyayenta suna cike da damuwar halin data tsinci kanta, basu da damuwa sama da lafiyarta, basu kuma da burin da ya wuce su wayi gari suga ta warke………
Sallamar Adawiya ta katse tunanin Nu’aymah. Ta ɗan ɗago daga kafaɗar Umm tana amsawa. Sai dai ganin harda Yah Abdallah ya sata maida kan ta sake kwantarwa zuciyarta najin zafin kishi a kansa.
Rungumeta Adawiya tayi cike da munafincin data saba nunawa idan suna a gaban mutane. Itama sai Nu’aymah ta tarbeta fuskarta fes. Umm dai cike da jin daɗi take dubansu. Yayinda Abdallah kam kallonsu kawai yakeyi.
Bayan sun gaisa da Umm, Nu’aymah ta gaida Abdallah batare data yarda sun haɗa ido ba duk da kuwa shi hakan yake buƙata tun ɗazun. A tunaninta zasu tafi ne, amma sai taga sunyi zamansu sunata hira da Umm. Kusan mintuna talatin basu da ko niyyar tafiyar, takaici ya cika Nu’aymah, dan haka kawai yau itama sai takejin zafin Adawiya akan Abdallah. Shiyyasa hirarma bata saka baki, tana lafe jikin Umm tamkar wata mage.
Basu bar sashen ba har sai da Baba malam ya shigo gidan, dama shi suke jira. Zama kuwa yay suka gaisa a ransa yana mai jin daɗin ganin yanda Adawiya ta kwantar da hankalinta. Yanda tai ƙiba ta ƙara ƙyau kawai ya isa fahimtar da mai kallonta hankalinta a kwance yake sosai. Barci ne ya sake kwashe Nu’aymah har suka bar sashen bata saniba. Koda Umm datai tunanin anan Adawiya zata kwana amma taga saɓanin hakan sai da ta tashe Nu’aymahr ma ta rakata ɗakinta saboda barcin da tayi.

Washe gari Nu’aymah ta tashi ne duk a takure. Ba komai ya jawo hakanba sai zuwan su Yah Ab da zaman Naser a gidan. Maƙalewa tayi a sashensu taƙi fita har rana. Sai da Umm ma ta takura mata ɗaukar abincin Hajjo ta kai mata sannan ta fita badan taso ba.
Tunda taga takalma birjik a ƙofar Hajjo taji kamar ta juya. Amma gudun kar Umm tai mata faɗa sai ta daure tayi sallama. Sai da aka bata izinin shiga sannan ta shiga da wata sallamar a bakinta. Duk samarin gidanne a she. Sai Rufaida da Hajjo. Nu’aymah ba wani shiri sukeyi da Rufaidah ba itama, dan ta girmesu, gata kuma da shegen son girman tsiya, shiyyasa take ganin sai dai su bita. Ita kuma Nu’aymah tsiwa.
A tare kawai tace dasu “Ina yinin ku”. batabi takan dawa-dawa ya amsa ba ta nufi Hajjo daketa binta da kallon jin daɗin ganin jikinta ya sake warwarewa.
“Hajjo barka da gida. Ga abinci inji Umm na”.
“To takwara sannu kinji, yaya jikin naki?”.
“Naji sauƙi Hajjo”.
“Alhmdllh ai haka akeso dama. Tun ɗazun nake tsumayen ganinki amma shiru. Tashi ki duba a firiji na ajiye miki fura”.
Sosai daɗi ya kanata. Cike da ɗoki ta nufi fridge ɗin hajjo ta ɗakko kofin furar tana sakema hajjo godiya. Har zata fice Naser ya kirata. Badan tasoba ta amsa tare da juyowa tana kallonsa. Ya sakar mata sassanyan murmushi tare da miƙewa ya nufo inda take tsaye. Bayare da yay magana ba yay gaba da mata alamar ta biyoshi.
Bataso hakanba, amma sai ta bisa kawai gudun kar yaga kamar ta masa wulaƙanci. Ɗaya daga rumfar bunun da aka jera guda uku a harabar gidan ya nufa. Nu’aymah ma dai na biye da shi. Kujera ya ja mata baya yace ta zauna. Nanma bata musaba tayi yanda yake buƙata. Sai da ta zauna sannan shima yaja wata ya zauna.
Yana zama Abdallah na isowa wajen kamar daga sama. Daga ita har Naser kallonsa sukai. Yayi kicin-kicin da fuska tamkar zai fasa ihu. Batare da yace dasu uffanba yaja kujerar ɗanyan gefen Nu’aymahn ya zauna suka sakata a tsakkiya.
‘Ikon ALLAH ’. Nu’aymah ta faɗa a cikin ranta tana kallonsu da mamaki.

“Alhaji lafiya kuwa?”. Naser ya faɗa a lalace yana kallon Abdallah. Murtani Yah Ab ya maida masa cike da dizgi. “Itace ta kawo haka”.
“Humm!” Naser ya faɗa yana ɗauke kansa daga garesa ya maida ga Nu’aymah da mamaki ke cigaba da nuƙurƙusarta a zuciya.
“Kayi haƙuri ka bamu waje magana nakeson yi da ita Abdallah”.
“Wannan isar ce kuma baka yiba. Duk abinda zaka faɗa mata inhar kasan ba mara ƙyau bane ka faɗa a gabana mana”.
“Mtsoww! Ai kasan baka isa sakani yin abinda banyi niyya ba. Nu’aymah tashi muje can…”
Batayi niyyar binsaba a yanzu. Tayi niyyar kawai tabar musu wajen. Sai dai tana yunƙurawa zata miƙe Abdallah ya daka mata tsawa. “Koma ki zauna kona mareki!!”. Ya faɗa yana ɗaga hannun tamkar zai maketa.
Ɓata fuska sosai tayi tamkar zata fasa kuka. Dan ita kam sun sakata a tsaka mai wuya.
A fusace Naser yace, “Abdallah karka bari nakai bango da kai, wai shin ina ruwanka dani ne? Naga dai Nu’aymahr nan ba matarka bace balle kace zakama mutane iko. Idan ada kayi ikon saboda akwai alƙawarin aure a tsakaninku yanzu saika tuna babu wannan. Ita ɗin allura ce cikin ruwa mai rabo ka ɗauka……..”
“Nine mai rabon kuma insha ALLAHU!!, dan haka ka kama kanka karka bari a jimu da kai Naseer”.
“Hhhhhh! Abin dariya. Sannu Abdallah ubana mai bani umarni. ai ka sani kayi sake tun a farkon dama, a yanzu kuma ta suɓuce maka har avada. A da canma dan ba’a bata dama bane akaso mata auren dole da kai, amma sai UBANGIJI yay dubeta ya hana hakan…..”
“Naser!!!”
Abdallah ya kirashi cikin ƙaraji da fusata tare da dunƙule hannu tamkar zai kai masa naushi. Ƴar zabura baya Naser yayi kamar irin yaji tsoro ɗin nan. Sai kuma ya kwashe da dariya ya kuma ɗaure fuska duk a lokaci ɗaya. “Oh to ko dukan nawa zakayi ne?!”.
Bai gama rufe baki ba kuwa Abdallah ya kai masa naushi. Da sauri Naser ya duƙe naushin yabi iska. Ya sake kai masa wani Baba malam da ke bayansu shi dasu Abbah ya daka musu tsawa.
“Kai!! wane irin shashanci ne haka kukema mutane a cikin gida da hankalinku?. Ko kunya bakujiba kuka zauna faɗa a gaban ƙaramar ƙanwarku, wannan ai rashin hankaline da sakarci”.
Duk ƙasa sukai da kawunansu kowa na huci. Abban su Adawiya yace, “Ku wuce muje ciki. Kema Nu’aymah shige”.
Sum-sum ta wuce tana danne dariyar dake cinta a rai tun fara rigimar yayun nata. Tana shiga falonsu kuwa ta fashe da dariya. Da sauri Umm da Rabi dake a kitchen suna aiki duk suka leƙo.
“K lafiyarki kuwa kike wannan dariyar ta rashin hankali?”.
Hannu Nu’aymah tasa da sauri ta danne bakinta, da ƙyar ta haɗiye dariyar tata sannan ta kalle su. “Wlhy Umm su Yah Ab ne suka bani dariya”.
Batare da Umm ta tsaya jin ba’asi ba tai tsaki ta koma kitchen. Rabi kam sai ta nufota tana tambayarta wai miya faru?. Da sauri Nu’aymah ta haɗe fuska tare da zuba mata harara tabar wajen. Itama Rabin da harara ta raka Nu’aymahn, a ranta kuwa faɗi take, ‘Zaki gane shayi ruwa ne yarinya, shegiya mai kama da ƴaƴan aljanu’.
Oho Nu’aymah batasan tanai ba. Dan tuni ta shige ɗakinta. Sai dai itama a ranta tana matuƙar mamakin munafunci irin na Rabi. amma sam Umm ta kasa fahimtar akwai wani abu a zuciyar Rabi, dan ita ta jima da fahimtar hakan, harma a ranta tana zargi Rabin da ɗaukar sirrin Umm tana fitarwa. Dan akwai ranar data taɓa ganinta bayan ɗakinsu tare da wanda bata fahimci namiji ne ko mace ba suna magana. Sai dai kafin ta zagaya taga wanene ta iske sunbar wajen Rabin ma harta shigo ciki. Tun daga lokacin ta saka mata kahon zuƙa. Taso fahimtar da Umm amma saita hauta da faɗa akan batason wannan halin banzar, dan Rabi a haife ta haifi Nu’aymah harma wanda ya fita. Kuma tun Nu’aymah na ƙarama suke tare ita bata taɓa ganin wani abu mara ƙyau daga gareta ba.
Tsaki tayi kawai da kauda zancen Rabi a ranta ta koma tuno su Abdallah. Haka kawai takejin al’amarin nasu na sakata nishaɗi. Ba sai an faɗa ba kowa yasan tana tsananin son Abdallah, ƙaddara ce kawai ta shiga tsakanin al’amarinsu. Amma a yau sai kawai yanda Naser yay sai shima ya birgeta. Har takeji zata iya aurensa duk da zuciyarta bawai tana sonsa bane ba. Amma tunda ta haƙura da Yah Ab zata iya maye gurbinsa da Naser ɗin. Sai dai fa tasan lallai akwai ƙura a cikin faruwar hakan kuma.

★★★

A ɓangaren su Abdallah kuwa faɗa sosai su Baba malam sukai musu akan abinda suka aikata. Dan a gabansu mafi yawan rigimar ta faru shiyyasa basu bi takan jin yanda akai ba. Sai da baba malam ya tabbatar jikinsu yayi sanyi sannan ya ɗora musu da nasiha kuma, ya kuma sakasu bama juna haƙuri sannan suka sallamesu.
Suna fitowa kowanne ya wurgama ɗan uwansa harara da jan tsaki………….✍

Kuyi manage Please, inada baƙi😒🚶🏻.

 

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

 

[5/22, 10:26 PM] +234 809 502 2953: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply