Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 36


Saran Boye 36
Viral

No. 36

………….“Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan ita ta gaza baku. Amma kuyimin afuwa idan ya kasance na shiga hurumin da ba nawa ba”.
Gaba ɗaya suka juya suna kallon bakin ƙofar har Nu’aymah data fara ganin dishi-dishi cikin idanunta.
Ba kowa bane mai maganar face ɗaya daga cikin amintattun almajiran baba malam mai suna Hamisu. Hamisu ɗan anguwar su Nu’aymah ne, hasalima maƙwaftan junane. Mahaifin su baba malam yayi zaman mutunci da girmama juna da kakansu Hamisu, dan takai harda ɗaukar nauyin karatun mahaifin Hamisun a wancan lokwcin. Sai dai ALLAH bai masa tsahon rai ba, dan ya rasu tun su Hamisu suna ƙanana sosai. Wannan dalilin ne ya saka zuri’ar gidan su Hamisu ta dawo ƙarƙashin kulawar zuri’ar ɗan Jibiya bisa wasulcin da ya barma ƴaƴansu su baba malam.
Tabbas baba malam ya cika wannan wasiyya, dan babu irin ɗawainiyar da bayayi da gidan su Hamisun, har takai Hamisu yana ɗaya daga cikin amintattun almajiransa da sukasan abubuwa masu yawan gaske da ya shafesa, kuma Hamisu har cikin gidan yakan shigo bisa yarjewarsa musamman akan aiko da wani abu cikin gidan idan babu ɗaya daga yaran gidan a tare da shi…

A fusace Yah Ab ya miƙe yana nunasa da yatsa. Har tdallaken kalma yake wajen faɗin, “Amma kasan wannan matsalace ta family da bata shafekaba ko malam. To ta yayama akai kai kasan cewar ana wannan zancen a gidan nan? da har zaka wani shigoma mutane tsulum batare da neman izini ba sai kace wasu sa’anninka. Wannan ma ai raini ne da keta haddin mutane”.
Nasir da shima baƙin ciki ya lulluɓe ya miƙe a fusacen yana cewa, “Tabbas maganarka gaskiyace Abdallah, mi zaisa ya………”
“Kunga ya isa haka” baba malam yay saurin dakatar dasu ganin yanda Hamisu duk ya muzanta abin tausayi. Ya cigaba da cewa, “Tabbas yayi kuskuren shigowa kai tsaye, amma ina ganin mu bashi dama ƙila mu sami bakin zaren matsalar tamu. Hamisu ya akai kasan da wannan issue ɗin?”.
“ALLAH ya gafaeta malam ka gafarceni, tabbas nima a yanzu na fahimci nayi kuskuren shigowa babu izininku. Ba komai ya jawo hakanba kuma sai ɗunbin ruɗanin dana tsinci kaina a ciki. Abinda yasa kukaji zancen nan a gareni jiya da daddare na dawo daga inda ka turani kai saƙo. Duk da dare yayi sai naga ya dace nazo na kawo maka saƙon koda ban samu damar maka bayani ba. Da ƙyar ma na samu maigadi ya barni na shigo, to a lokacin dana shigone na samu duk jama’ar gidan a sashenka, na iskeku cikin tashin hankali shine na juya da saƙon gidanmu, sai da safe na dawo kawowa nakejin abinda ke faruwa bisa fahimtar da nai daga maganganun ku. Har fitarsu asibiti akan idonane, wlhy da farko naso ɓoyewa nima, sai dai tashin hankalin danaganka a ciki ne naga ya cancanci na bayyana abinda na sani kodan ka samu nutsuwar warware al’amarin yanda ya dace, ku fita daga ruɗani kuma”.
Duk da sun gamsu da jawabinsa Naser da Abdallah sai zabga masa harara sukeyi. Baba malam ya bashi izinin ƙarasowa ciki. Da ga ɗan gefe ya durƙusa, ya miƙama Abban Adawiya dake kusa da inda yake Envelope ɗin dake a hannunsa.
Amsa Abban su Adawiya yayi, batare da ya buɗe ba ya miƙama baba malam. Nuni baba malam ɗin yay masa daya buɗe kawai. Abban su Adawiya ya buɗe Envelope ɗin ya ciro hotuna dake a ciki guda uku. Ba ƙaramin razana yayi ba matuƙa, har ta kai yana dubawa hannunsa na rawa.
Hoton Nu’aymah ne da Yoohan, a ranar farko da tsautsayi ya saka shi taimaka mata lokacin da zata faɗi a ranar salla, har ta kaisa ga kissing ɗinta saboda baki data wage zata masa ihu. Sai rana ta biyu itama ranar daya musulunta. Saina ukun shima dai a ranar farko ne, ya ranƙwafa a kanta suna kallon juna.
Yanda baba malam yaga ɗan uwan nasa ya shiga wani haline ya sakashi zare hotunan daga hannunsa. A take jinsa ya ƙauracema kunnensa. Hakama ganinsa neman kuɓucema idanunsa yake neman yi. Saurin fara ambaton UBANGIJI yayi yana ƙoƙarin ajiye hotunan Abban Abdallah ya amsa. Shi kam ma na farko kawai ya iya kallo ya miƙama hajjo. Itakam ta jima tana kallon hotunan ko ƙyaftawa batayi, ta haka ne Nu’aymah da ke gani dishi-dishi ta samu damar ganin hotunan gaba ɗayansu a hannun hajjo.
Babu wanda ya lura da ita. Sai ganinta kawai sukai kwance ƙasa wanwar. A take falon ya sake rikicewa gaba ɗaya. Duk suka rufu a kanta banda Baba malam da Umm da ko motsi basuyi ba da ga inda suke. Hajjo ma da bata tashiba sai ta maida hotunan a Envelope ɗin batare da ta sake bama kowa ba. Sai ma miƙewa tai ta shiga bedroom ɗinta da su. Babu jimawa ta fito lokacin anata ƙoƙarin zubama Nu’aymah ruwa dan son aga ta farfaɗo. Sai dai kuma ko motsi batai ba balle suyi tunanin dacewa.

Gidan ya sake cakuɗewa fiye da farko, sai da baba malam ya musu magana sannan suka ɗan nutsu. Tamkar bai damu da halin da Nu’aymah ke a ciki ba ya kalli Hamisu dake zaune tsuru-tsuru yana zare idanu. “Hamisu su waɗanan hotunan ina ka samesu ne haka?”.
Kansa a ƙasa yace, “Baba malam nine na ɗaukesu da waya gaba ɗaya”.
“Hakan na nufin komai ka gani kenan Hamisu? Ina nufin duk abinda ke a cikin hotunan nan a gaban idonka aka yisa?”.
“Eh wlhy duk na gani”.
“To miyasa baka taɓa sanar minba kuma?”.
Jimmm Hamisu yayi kafin yace, “Wlhy ina tsoron ɗaga maka hankaline, tare da gudun abinda zai iya zuwa ya dawo malam. Amma ka gafarceni nayi kuskure ”.
Nannauyan numfashin baba malam ya sauke. kafin a sanyaye yace, “Shike nan jeka abinka. na gode sosai”.
Godiya shima Hamisu yayi ya tashi ya fita.

Hajjo da duk kejin komai na neman kufce mata tace, “A kaita asibiti, koma minene sai a yisa da ga baya, ciki kuwa harda neman yaron shima. Da yawan mutane wannan suke tsoro ga taimako, shiyyasa bahaushe ke faɗin kasa mutun inuwa ya saka rana. Ko a fuska bazaka taɓa tunain yaron nan zai aikata makamancin hakanba duk da kuwa a farkon shigarsa jikinmu kafiri ne. Ashe ya lulluɓe mune kawai yazo jikinmu ya cutar damu, da alama dama yarinyar nan ya biyo bawai alkairin da muke tsammani daga garesa ba. To kansa yay mawa, ALLAH kuma ya saka mana da gaggawa indai muna da haƙƙi a kansa”.
A tare duk suka amsa mata da amin. Banda baba malam da yay wani ɗan murmushi ya ɗauke kansa kawai. Abdallah ne ya ɗauki Nu’aymah dake a sanƙame ya fita da ita bisa umarnin Hajjon.

_________________

An musu ƙarɓar gaggawa saboda halin da Nu’aymah ke a ciki. Musamman ma da suka sami mace ce Doctor ɗin dake dutyn lokacin.
A yanda suka ga likitocin na kai kawo ɗakin da aka saka Nu’aymah hankalinsu ya daɗa tashi sosai. Duk kuma sanda wani ya fito suka tambaya baya basu amsar komai yake wucewa da sauri. Tun suna ɗaukar al’amarin ƙarami har suka fahimci yanada girma sosai, dan Doctors har uku sun ƙaru bayan ta farko. Sai faman yin ƙus-ƙus kuma sukeyi a tsakaninsu.
Cikin ƙarfin hali Abba Musbahu ya dubesu yana faɗin, “Bayin ALLAH inaga idan yarinyar nan ta rasa ranta ne ya kamata ku sanar mana, dan kunata sake ɗaga mana hankali da rashin cewarku komai da kai kawon nan naku”.
Ɗaya da ga cikin likitocin ne ya sadda kansa ƙasa cikin girmamawa yace, “Ai mana afuwa malam, ba muna ɓoye muku komai baneba. Kawai muna akan aikine shiyyasa, amma insha ALLAHU zakuji komai nanda ƴan mintuna kaɗan”.
Shiru wajen yayi babu wanda yace komai, sai dai a zukatansu sam basu gamsu da zancen likitan ba.

★★★

Tunda aka fita da Nu’aymah asibiti baba malam ya koma sashensa. Zaune yake a study room ɗinsa saman wata kujera da ke ɗan lilasa idan yana kanta. Duk da rana ce ɗakin yayi duhu sosai kasancewar bai ɗaga labule ko guda ɗaya ba a ɗakin. Bai kuma kunna fitila ba sai ɗan hasken da ake gani kaɗan kasancewar na hasken rana. Kwance yake a jikin kujerar idanunsa a lumshe ya faɗa duniya mafi nisan zango a tunani.
Tun daga daren jiya har zuwa yanzun zuciyarsa a ruɗani take. Ruɗani irin wanda ƙwaƙwalwa bata iya rarrabe gaskiya da ƙarya, fari da baƙi, haggu da dama……..
Motsin da yaji a kusa da shine ya sakashi buɗe idanunsa da ƙyar. Umm ce ya gani cikin ɗan hasken da ɗakin ke da shi. tsaye take a gefensa dafe da kanta alamar tana a cikin matsala. Zumbur ya miƙe ya riƙota ganin tana layi, ga hakki tanayi kamar wadda tayi gudu a cikin sahara.
Kujera doguwa dake a ɗakin ƙwara ɗaya kacal ya nufa da ita, ya kwantar da ita jikinsa sai tsuma ya keyi. “Jannat miya sameki?”.
Duk da halin da take a ciki itama sai da tausayinsa ya kamata jin a yanda yay magana. Tasan ƙarfin hali kawai ya keyi tun jiya akan al’amarin nan, amma shima a ruɗanin yake. Hannunsa ta kamo da ɗayan hannunta, ɗayan kuma na akan ƙirjinta da ke mata azabar zafi tamkar zai buɗe.
“Sooraj inaji a jikina mutuwa zanyi, a wannan karon zuciyata bazata iya ɗaukar wannan al’amarinba. Abban Nu’aymah akwai ruɗani a cikin zancen nan, amma ni kaina na kasa banbance mai gaskiya tsakanin ƴarmu da likitocin nan. Idan da ace likita ɗaya ne ya faɗa sai muce ko haɗa baki akayi da shine, amma kaga harsu uku, ɗayan ma bamu santa ba tunda asibiti suka sameta. Sannan Sooraj a kwanakin cikin nan da aka ambata ya kasance jikin Nu’aymah ban taɓa ganin wani alama na mai ciki tattare da yarinyarta ba, babban tashin hankalina kuma shine tabbas watan da ya shige na azumi banga Nu’aymah tayi jini ba har suka wuce saudia, wancan watan kuma a farkon wata tayisa. Kasan dai ita jininta baya ɓoyuwa a gidan nan saboda lalurar da yake zuwa mata da shi. Sooraj na shiga ruɗani wlhy”.
Ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
Shima sai ya ji hawaye na ziraro masa batare da ya shirya yin hakan ba. Dan zuciyarsa ta karye gaba ɗaya. Ya rungumeta a jikinsa sukayi mai isarsu kafin ya ɗagota yana kallon yanda take faman dafe ƙirjin nata har yanzun.
“Jannat bazaki mutuba, bana fata ki tafi ki barni cikin wannan tarnaƙin, nima zuciyar tawa ba iya ɗauka zatai ba. Ki daure dan ALLAH muyi imani da ƙaddara. Amma kamar yanda kike cikin ruɗani a wannan al’amarin wlhy nima haka nake a ciki. Na ƙiyasta duka zuwan Yoohan cikin gidan nan gaba ɗaya ban iya tunano ta yanda har ya samu keɓancewa da Nu’aymah ba. Wlhy zuciyata ta kasa yarda Nu’aymah da Yoohan zasu aikata wannan ɓarnar. Idan kuma nace ban amince sun aikata ɗinba yaya xanyi da waɗan nan hujjojin bayyanannu kuma Jannat? Ya ALLAH ka bayyanar da gaskiyar al’amarin nan koda a cikin Zukatanmu ne ya Rabbi”.
Haka sukaita hawaye har sai da baba malam ya fahimci Umm na neman rasa numfashin ta. Sake ruɗewa yayi ya shiga girgiza ta jikinsa na rawa. Yama rasa miya kamata yay mata, kiran sunanta kawai yake iya yi da iya ƙarfinsa.
Hakanne ya jawo hankalin su Hajjo da ke zaune jigum-jigum suna jiran jin halin da Nu’aymah dake a a sibiti take a ciki. Har rige-rigen shiga sashen sukeyi, gashi duk mazan gidan sun wuce asibiti tare da Nu’aymah, dama baba malam ɗinne kawai ya rage.
A hankali inuwar mutum dake a jikin windown tana kallon su baba malam ta kafar labule ta janye daga wajen. Hakan yay dai-dai da fara shigowar matan gidan. Babu wanda hajijiya bata kusan kwasa ba ganin da gaske Umm bata numfashi, ga baba malam yau duk jarumtarsa da kawaici yana zirar da hawaye…………

_____________★★★

A asibiti bayan sallar la’asar Doctors ɗin suka buƙaci ganin wasu a cikin su Abba. Su duka ukun suka shiga office ɗin, aka bar su Abdallah kawai a waje.
Sai da aka nuna musu wajen zama kafin likitar mace tai ɗan gyaran murya tana kallon sauran ƴan uwanta uku likitocin. Kawuna suka ɗaga mata alamar bata damar magana. Ta amsa musu da kai itama tana sake gyara zamanta.
Cike da girmamawa a garesu tace, “Dama munason muku bayani ne akan abinda ke faruwa idan bazaku damu ba”. Babu wanda ya iya ce mata komai a cikinsu. Dan haka ta cigaba da faɗin, “Maganar gaskiya yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali, duk yanda mukaso ceto rayuwarta ma mun gagara, dan aikin yafi ƙarfinmu. Amma a yanzu dai abinda muka iya kawai shine jawo numfashin ta da wasu na’urori kafin a samu mafita. Muna da likitan da zai iya duba matsalarta, sai dai kuma ganinsa shine tashin hankalin musamman da ya kasance yau kwanakinsa goma sha ɗaya kacal da barin nan, sannan aikinsa yana da ƙa’ida bana waje ɗaya bane balle muce muku kai tsaye ga inda zaku iya samunsa. Amma yanzu dai in taƙaice zance matsayinku na iyaye a garemu masu daraja da kima bazamu iya ganin matsala a gareku ba mu kauda idanunmu, dan haka munyi ƙoƙarin nemansa dan muji ko zai iya mana alfarmar ganinsa amma bai ɗaga wayar ba, sai dai mun kira amintaccen sa da ke a garin Lagos a yanzu haka ya tabbatar mana zai bincika mana shi, idan har ya amince zaizo zamu iya ganinsa a koda yaushe. idan bai aminceba yana da wani uzurin kuma shi zaizo ya ga yarinyar ko zai iya bada wata mafita akan matsalar tata dan shima babban likita ne”.
Cike da gamsuwa da bayaninta duk suka karɓa mata da “ALLAH yasa a dace” tare da musu godiya sosai akan wannan taimako da sukai musu. Daga haka suka tashi suka fito kowa yana addu’ar dacewa a cikin ransa da jin tausayin ɗiyar ɗan uwan nasu dama ɗan uwan nasu shi kansa fiye da ko yaushe a yau.

Kamar da wasa sai ga su Abbah sun shafe fin awanni bakwai amma babu labarin likitan da ake tsumayen jira. Su kuma likitocin basuce musu komaiba. Haka suka cigaba da zama jugum-jugum suna addu’oi a zukatansu har tsahon wani lokaci. Shigar lokacin sallar la’asar ne ya sake tadasu suka nufi massallaci, bayan an idar da salla suka sake fitowa suka sake zaman jiran tsammani.
Wata cikkakkiyar awa biyu suka sake sharewa gangariya, Abban Abdallah na ƙoƙarin miƙewa zuwa office ɗin Doctor ɗin nan mace mai suna Doctor Ai’sha yaji yaya ake ciki? sai ya hangota tana fitowa da ga office ɗin nata fuskarta washe da murmushi.
Kafin ya samu damar mata magana yaga ta nufi ƙofar fita da hanzarinta. Kamar zai bita sai kuma ya fasa, ya cigaba da tsaiwa a wajen yana jiran ganin ko zata dawo.
Tsayuwar tasa tayi dai-dai da shigowarsa cike da takunsa na ƙarfi da lafiya, wanda idan baka saniba zaka iya ɗauka tsabar isa ce da izza ke ɗawainiya da shi. Amma sam ba haka baneba, halittar tasa ce kawai haka.
Kansa duƙe yake sakamakon file ɗin Nu’aymah da ke a hannunsa yana dubawa. Ya ɗan rame, hakan ya saka sake fiddo hasken fatarsa da ƙyawun da ALLAH yay masa. Ga wani annuri na hasken ibadar ALLAH tattare da shi, wanda ya sake ɗaukaka ƙwarjininsa da cikar haiba kai kace farin watane ɗan daren sha biyar. Kamar kullum sanye yake cikin suit, na yau ɗin sun kasance Coffee color, sai farar shirt da ke a ciki babu necktie, dan maɓallan Shirt ɗinma kusan uku a buɗe suke.
Doctor Aysha na daga gefen damarsa duk da yaɗan zartata kaɗan a tafiyar kasancewar ya fita tsayi, da alama bayani take masa akan matsalar. Sai Solomon dake ɗauke da jikkarsa a hannu, da Doctor Sa’ad da wasu likitoci biyu da Nurse kusan huɗu na biye da bayansa. Har suka zo suka gitta Abban Abdallah bai ga fuskarsa da ƙyau ba, dan har lokacin kan nasa a sunkuye yake ga file ɗin. A dai-dai ƙofar ɗakin da Nu’aymah ke ciki suka ja birki, su Abdallah da duk suka zuba nusu ido duk suka miƙe, sai dai kafin wani cikinsu yace wani abu. Ya tura ƙofar ɗakin ya shige har lokacin hankalinsa nakan file ɗin.
Iya shi da Doctors ɗin suka shiga, yayinda Solomon da Nurses ɗin suka ja birki a bakin ƙofar.
Sai da ya ƙarasa gab da gadon da Nu’aymah ke kwance sannan ya ajiye file ɗin ya kai dubansa gareta, bai ganeta ba sam, saboda na’urar da aka saka mata mai taimakama numfashinta fita. Ya ɗan ranƙwafo kanta kaɗan ya kai hannu ya zare na’urar mai haɗe da oxygen. Ba ƙaramin tsirgawa zuciyarsa tayi ba, amma saboda son sake gaskta abinda yake tunanin sai ya zare Glasses ɗin idonsa da ya ƙara ƙawata fuskar tashi. ‘Kamar dai itace’ ya ayyana a zuciyarsa cike da kokwanto.
A fili kam sai yay saurin maida mata na’urar saboda ganin yanda ƙirjinta ke sama da ƙasa da sauri-sauri ga jikinta na vibration har gadon kansa na motsawa. Luuu ya ɗanyi da idanunsa ya lumshesu ya sake buɗewa a kanta. murya a cinkushe ya dubi Doctor Aysha a ɗan faɗace ya ke faɗin, “Anyi matuƙar sakaci da lafiyar yarinyar nan da har take neman shiga matakin ƙarshe, ina mamakin yanda mutane suke abu tamkar basu san muhimmacin lafiya ba. Mtsoww!!. Su Iyayenta fa?”.
Dr Sa’ad ne ya bashi amsa da “Haka suke wlhy Doctor, sai kuma an mutu suce likitoci ne da sakaci bayan tun farko sune da matsalar su………”
Cikin sauri Dr Aysha ta katse Dr Sa’ad ɗin dan bata son ya sake tunzura Dr Yoohan, “Ayi haƙuri sir, duk family nata suna waje, duk da kasancewarsu manyan mutane suna tare da ita tun ɗazun fiye da awa tara wlhy”.
Baice komaiba, ya dai sake kai dubansa ga Nu’aymahn, sai kuma yay azamar ɗauke kansa batare da nasan dalilin yin hakan ba. Juyawa yay zai fita. Doctor Aysha tai saurin ɗaukar file ɗin da ya ajiye su ka sake bin bayansa ita da su Doctor Sa’ad da ke ta faman cika yana batsewa saboda haushin kare dangin Nu’aymah da tayi.
Yanzun ma bai duba kowa ba a cikin su Abdallah yay wucewarsa. Duk da kallo suka sake binsa suma, yayinda Abban Adawiya yaso gane sa, sai dai baiyi magana ba jin suma su Abban Abdallah basu ce komai ba.
Da ga shi sai Solomon suka shiga office ɗinsa, komai ƙal yake, dan tunda Dr Aysha ta tabbatar da zuwan nasa ta saka aka sake tsaftace office ɗin duk da dama ƙa’ida kullum sai an share an goge. Ƙaramin ɗakin hutun dake cikin office ɗin Solo ya ƙarasa. Ganin nanma komai dai-dai yake yanda yasan Yoohan ɗin na buƙata sai ya ajiye jikkar ya fito.
Tsaye ya iske sa yana ƙoƙarin zame rigar suit ɗinsa, har Solomon ɗin ya kai ƙofar fita ya tsinkayi muryarsa ya na faɗin, “Kiramin Dr Aysha”.
“Okay sir”.
Solo ya faɗa da sauri yana ficewa. Hanging ɗin rigar yayi bayan kujerarsa ta zama, sannan ya fara ƙoƙarin kunna Computer ɗin da ke a saman desk ɗin na sa. Yanda yay matuƙar zuba idanunsa ga Computer ɗin zai tabbatar maka abunda yake yi a ciki yana da matuƙar muhimmanci. A haka Dr Aysha ta turo ƙofar bayan tayi knocking ta shigo, dan tasan ba lallai ta samu amsa ba musamman a irin wannan lokacin da ta tabbatar hankalinsa gabaki ɗayansa nakan patient ɗin da ke jiran taimakonsa.
Batare da ya ɗago ya kalleta ba yace, “Matsalar yarinyarnan babba ne, sai dai zan mata wani ƙaramin theatre yanzun, dan haka ku shiryata zuwa theatre room”.  Ya miƙa mata file ɗin gabansa yana cigaba da faɗin, “Wannan mahaifinta zai saka hannu anan, ko mahaifiyarta ko mijinta. Kuma dole ɗaya da ga cikinsu ake buƙata kawai”.
Ɗan jimm Dr Aysha tayi. sai kuma komi ta tuna oho, ta gyaɗa masa kai da faɗin “Okay sir”. Daga haka ta fice shi kuma ya miƙe ya nufi ɗakin da ke a cikin office ɗin………✍

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/26, 3:26 PM] +234 806 269 3623: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply