Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 38


Saran Boye 38
Viral

No. 38

………….Duk yanda su Abdallah sukaso a tuhumi Yoohan tun a asibiti game da zancen Nu’aymah baba malam ya hana, hakama su Abba basu bada goyon baya ba.
Zuwa yanzu dai Yoohan ya fahimci alaƙar baba malam da patient ɗinsa. Ya kuma gane Nu’aymah. Sai dai taka maimai abinda bai gama fahimta ba shine hotunan da Abdallah ya kawo masa da tsantsar ɓacin ran da yake ganni tattare da samarin gidan su baba malam ɗin gaba ɗaya harsu malam ƙarami da ya fara sabo da su.

Bayan samun damar shiga ɗakin da Nu’aymah ke kwance da sukayi ɗai-ɗai suka dubata duk da bata farfaɗo ba baba malam ya tattarasu su duka suka bar asibitin. Dan Yoohan ya tabbatar musu ba’a buƙatar wani mai jiyya tattare da ita har sai ta farfaɗo.
Suna tafiya baifi da mintuna talatinba shima ya amshi key ɗin motar Dr Mubarak Solo ya jashi zuwa gidansu baba malan ɗin. Kamar yanda yay tsammani ya iske kowa a gida da alama ma zaman jiransa sukeyi. Omar ne ya fito yay masa iso har sashen Hajjo. Hajjo ce kawai a sashen sai su baba malam su duka. Omar ma yana shiga da shi fitowa yayi.
Duk da Hajjo najin haushin Yoohan sai ta danne ta amshesa da fara’a kamar ranar salla dasu Ahmad suka shigo da shi wajenta. Ta kuma kawo masa ruwa da lemo. Yaji daɗi kuwa sosai, tare da sake jin ƙaunar ƴar tsohuwar har cikin ransa.
Bai iya sakin jiki ya sha ruwan yanda ya kamata ba, ya ajiye kofin tare da sake nutsuwa yana jiran ji daga garesu.
Bayan shuɗewar shiru na wasu mintuna Abba Musbahu yay gyaran murya idonsa akan Yoohan da kansa ke a rissine. Ba bu wani kwalo-kwalo ya shiga zayyano masa duk abinda ke faruwa.
Sosai mamaki ya kusa kashe Yoohan, ya sake tsuke fuska yana girgiza kansa. Idanunsa da suka kaɗa sukai jajur ya ɗago ya duba baba malam, “Uncle ni a rayuwar turai da nayi ma ba taɓa aikata haka da wata mace da yardarta ba ma balle anan ƙasata. Nasan anyi hakane kawai don shiga tsakanin alaƙarmu, ko kuma kasancewata musulmi a yanzu. Sai dai kuma ko wanene bai samu nasara ba, dan babu wani ɓatanci da za’aimin koda yafi wannan da zai girgiza zuciyata daga barin bautama UBANGIJINA shi kaɗai. Ban musulinta domin kowa ba, ba kuma zan fita domin wani ba. Nasan zaku yarda da ni, Tunda har kuka yarda da dani alokacin da ba addininmu ɗaya ba ma, dan kuɗin nagartattun mutanene masu ƙyawawan zukata. Zan faɗa muku ainahin gaskiyar abinda ya faru”. Cikin nutsuwa da ɗacin rai ya bayyana musu tun daga haɗuwarsa da Nu’aymah ta farko har zuwa ranar da ya musulinta. Bai iya ƙarya ba tun yana kafirinsa, balle yanzun da ya ƙara sanin muhimmancin gaskiya a harshen ɗan adam. dan haka ko kissing ɗin Nu’aymah da yayi bai ɓoye musu ba ya faɗa. Ya ɗora da faɗin, “Zan koma asibiti yanzun insha ALLAH, na muku alƙawarin bincike akan cikin da akace itama ya zuba a jikinta, dan sam ni dai banga wannan matsalar tattare da itaba saboda ba akanta na fuskanci matsalarta ba. Amma zan kawo muku hujja a yanzu da yardar ALLAH”.
Gaba ɗaya sun gamsu da bayaninsa har Hajjo da Abba Musbahu ke fassarama maganar Yoohan ɗin dan da turanci yay bayaninsa.
Baba malam ya ɗanji nauyin zuciyarsa ya ragu sosai da bayanin Yoohan, a yanzu kuma hankalinsa ma yafi kwanciya da binciken Yoohan ɗin fiye da na likitocin farko. Sannan tunaninsa ya fara karkata akan wani abu da ban kuma.
Ko mintuna goma Yoohan bai ƙara a gidanba ya fice ya koma asibiti. Sam baiji zafin su baba malam ba akan wannan maganar. Sun ƙarama mutunci a idanunsa ne, haka yake son iyaye su kasance akan ƴaƴansu. Ya sake fahimtar addinin musulinci addinine abin koyi, domin yana ƙyamatar abinda wasu addinan su a wajensu ado ne, Wayewace. Hasalima zuciyarsa wani hasashe take masa daban akan wannan ƙullin da akai musu. Duk da bai tabbatar ba amma zuciyarsa na kinsa masa papa.

Tare suka koma asibiti da su Abdallah da har yanzu su dai basu wani gamsu da Yoohan ɗinba.
Shi da Doctor Aysha suka gudanar da duk wani bincike akan Nu’aymah da har yanzun tana cikin halin sumar allurar da sukai mata. Dr Aysha ta tattara komai zuwa lab ta danƙama wanda ta aminta da shi. Daga haka ta dawo ta sanarma Yoohan.
Kansa kawai ya iya ɗaga mata, dan yana lafe jikin kujerarsa ne idanunsa a lumshe. Fuskar nan tasa kuwa a tsuke take matuƙa. yana cigaba da nazarin komai dalla-dalla. Babu abinda ya iya taɓukawa a wannan yinin sai zuwa salla idan lokaci yayi da leƙa Nu’aymah da suke tsumayen farfaɗo warta a kowane irin lokaci.
Misalin ƙarfe biyar saura na yamma Dr Aysha ta kawo masa duk results ɗin bincikensu. Ko buɗewa baiyi anan ba ya miƙe da shi ya fito, su Abdallah da suka zame masa bodyguard shi da Nasir da Ahmad biye da shi.
Har zuwa yanzun su baba malam duk suna gida suna jiransu. Yanzun dai saɓanin ɗazun, duk mazan gidan ne suka taru banda ƴammatan da yaran da su Umm, dan hajjo ce kaɗai mace ma a cikinsu. A maimakon Yoohan ya buɗe yanzun ma sai ya bama Abdallah damar buɗewa dan ya tabbatar musu zai gane.
Tun a result ɗin farko Yoohan yaji saɓanin abinda yay tsammani. Hakama sauran ƴan gidan, aka tafi na biyu dana uku, Abdallah baima ƙarasa na ukun ba Yoohan ya miƙa hannu a hankali ya zare file ɗin da takardun results ɗin ke a ciki yana binsu ɗai-ɗai da kallo. Tabbas babu ƙarya dai-dai Abdallah ke faɗa. Dan kuwa duk Results ɗin sun nuna Nu’aymah tasan ɗa namiji, ta kuma ɗauki cikin sati shida da wasu kwanaki, cikin kuma tayi ɓarinsa kwana biyu kenan.
Dimmm kan Yoohan yayi na ɗan wani lokaci, sai kuma ya sake duba duka takardun sannu a hankali. Su baba malam dai babu wanda yay magana sunata binsa da kallo. Sai Abdallah ne da Naseer ke jifansa da wani mummunan kallo tamkar zasu hau kansa da duka.
A harzuƙe Abdallah yace, “Yanzu kuma wace ƙarya zakai mana dan ka kare kanka?”. Yay maganar yana riƙo rigar Yoohan.
“Abdallah!!!!” Abbansa ya daka masa tsawa yana miƙewa. Ransa a ƙololuwar ɓace yace, “Sake sa”.
Kamar Yah Ab ya kashe Yoohan haka yakeji, amma kasancewar an musu tarbiyyar jin maganar magabatansu sai ya saki Yoohan ɗin da shi sam hankalinsa ma bawai yana tare da su baneba. Dan gaba ɗaya zuciyarsa ta shige a wani sabon nazari ne. Ɗan hankaɗashin da Abdallah yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa. Ɗagowar da zaiyi sai idanunsa suka sauka jikin Windown falon hajjo. Inuwar mutum ya gani, yay ma wajen kallon kusan seconds goma kafin wanda ke a tsaye ya farga ana kallonsa yay saurin barin wajen.  A take kan Yoohan ya kawo masa wuta kasancewarsa mutum mai kaifin tunani da basira.
Kallon sashen da baba malam yake yayi, ya ɗanyi luuuu da idanunsa da haskensu ya ɗan sirka yana wani bahagon murmushi, kamar zai lumshe su sai kuma ya ɓuɗesu a hankali. Cikin muryarnan tasa mai kauri da amo data hadu da ɓacin rai a yanzun yace, “Uncle wannan tatsuniyar akwai marubucinta kusa da mu daf. Amma mizai hana ka bani damar yankar ticket ɗin fara game da shi? Dan ni bana wasa a saman ruwa tunda ba masinci bane. Nafi yarda da shiga ƙarƙashin ruwan kasancewata mai yawan bincike akan ma’adanai. Kasan masu iya magana kance idan ka hango biri bisa tsumagiyar reshe ba gangancine ya kaisa ba, tsabar ƙwarewa ce a iya hawan bisa. Ko zaka amince ka bani aurenta idan ta girma?”.
Kowa a falon sai da ya zaro idanu waje, harma da masu zabura. Nasir da Ya Ab kam ai dingangan suka tsaya akan ƙafafunsu tare da hassalowa lokaci guda kamar zasu haɗiye Yoohan da ko kallo basu ishesaba. Sai dai kafin su ƙarasa Abban Adawiya ya daka musu tsawa. Tilas suka ja burki badan rayukansu sunso hakanba.
A karon farko baba malam yay tattausan Murmushin da har haƙwaransa sai da suka bayyana. idanunsa ƙyam akan Yoohan. zamansa ya gyara da ƙyau yabi duk jama’ar falon da kallo, su Abban Adawiya ma duk murmushin sukeyi, hadda hajjo da malam ƙarami ke fassarama maganar yoohan ɗin.
Murmushi baba malam ya sakeyi a karo na biyu, kafin yace, “Yoohan maganar aure ba abin wasa bace a musulinci, dan haka bazan iya baka amsar bukatarka a yanzun kai tsaye ba. Amma kaje zanyi magana da ƴan uwana, duk hukuncin da muka yanke zamu sanar maka insha ALLAHU”.
Duk da Yoohan yaso samun amsar baba malam take a wajen sai kawai ya jinjina masa kai alamar ya amince da hakan. dan haka ya miƙe yay musu sallama ya fice abinsa yana jifan Naser da Abdallah da wani irin kallon na ban ƙyaleku ba kuma, kamar yanda suma suke binsa da kallon kishi da tsana.

A yanzun kam zamu iya cewa komai ya harmutse musamman a gidan su Nu’aymah. Dan tun bayan barin Yoohan gidan baba malam ya kasa zaune ya kasa tsaye da fashin baƙi akan kalaman yaron mai hikima. Kai kawo kawai yake a bedroom ɗinsa tamkar mai safa da marwa. Hakama Abdallah da Naser hankalinsu a matuƙar tashe yake, dan su dukansu suna tsananin son Nu’aymah har cikin ransu. Umm kam da hajjo bama a maganar halin da suka tsinci kansu a ciki. Umm ba maganar wa Nu’aymah ya kamata ta aura bane damuwarta. Abinda likitocin keta tabbatarwa ga ɗiyarta shine tashin hankalinta. Itace ta haifi Nu’aymah, itace tai mata tarbiyya, sannan a gabanta ta tashi har zuwa yanzu da ake akan rikicin. Tunda take da yarinyarta bata taɓa kamata da kuskuren sauka akan turbar tarbiyyar data ɗorata ba. To tayaya za’ace hakan ta faru?  Kanta ya kulle gaba ɗaya, tama rasa wazata gaskta tsakanin likitoci da Nu’aymah. Dan zuciyarta taƙi aminta ƴarta zata aikata haka, to sukuma likitocin mizaisa su musu ƙarya? Ta yama zasu musu ƙarya bayan sun kasance daban-daban?.

A ɓangaren Yoohan kam yana fita yaci karo da Solomon. Bai wani zaman tunanin yanda akai ya biyisaba ko inda ya samo motar da yazo ɗaukarsa kawai ya shiga kusa da mazaunin driver.
A tsorace Solomon ya dubesa, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru. saurin zagayawa yay mazaunin driver ya tada motar suka bar anguwar. Har suka isa hotel babu wanda yace uffan a tsakaninsu. Solo yay masa rakkiya har ɗakin da ya kama masa. Yana ganin ya shiga shi kuma ya koma da baya. Wayarsa ya zaro yay kiran papa. Bugu biyu kuwa Papa ya ɗaga saboda muhimmancin da Solo yake da shi a wajensa. Cikin girmamawa ya gaishe da shi, kafin suyi magana mai tsajo wadda bilyn ku bataji saboda da yare Solo ke magana. Sun kusa mintuna talatin sannan Solomon ya yanke wayar yana wani cizon lips da yin ƙwafa.

Ƙarar waya ce ta saka Yoohan dake zube saman gado idanu a lumshe ko takalmi bai cire ba buɗe idanunsa. Kasancewar ring ɗin daya sakama iyayensa da banne yasa ya fahimci papa ne. Sai da wayar ta kusa katsewa sannan ya ɗaga. Ya saka a kunne batare da yayi maganaba.
Daga can Papa yace, “Yoohan kana lafiya?”. “Uhhm!” Yoohan ya amsa a taƙaice. Papa da keta ƙoƙarin danne fushinsa yace, “Ni bansan lokaci daka fara zama maƙaryaci ba. Ni nasan dagajin muryarka akwai matsala ai, dan an kirani daga asibitinku an sanarmin duk abinda ke faruwa”. Kamar Yoohan zaiyi magana sai kuma yay shiru abinsa yana sake tsuke fuska. Takaici ya kuma kume papa, yace, “John kana jina kuwa?”. Yanzunma kamar bazai amsa ba, sai kuma ya nisa muryarsa a harɗe yace, “Papa inason nayi aure! Kuma ɗiyar Sheikh Sooraj Hashim jibiya zan aura, sai dai yarinyar ta cika ƙankanta”.
Wani irin bugawa ƙirjin Papa yayi a lokaci guda. Tamkar wanda aka ƙwaɗama guduma a saman kai ya miƙe zumbur da faɗin, “What?!. John! Are you Mad?!!”. Yanda papan yay maganar da tsananin tsawa ne ya saka Yoohan janye wayar daga jikin kunnensa yana matse idanu tam-tam. Sai kuma kawai ya yanke wayar yay wurgi da ita ta tarwatse ƙasa kamar wani zararre. Harya ɗan zabura zai miƙe sai kuma ya koma baya ya sake zubewa a gadon yana ambaton addu’ar da Manager Hamza Ibrahim da a yanzu suka sake zama abokai sosai ya koya masa. Ita ya shiga maimaitawa a cikin ransa. Cikin amincin UBANGIJI a hankali yaji ƙirjinsa ya fara rage nauyi, sai kuma wani irin barci ya fara fisgarsa a hankali.

Gaba ɗaya papa ya haukace a gaban abokansa da ƙanninsa. Dan suna a tare lokacin wajen wani meeting ɗinsu na manyan ƙauyensu, dan dama yaje ƙauyensu ɗinne tun jiya da daddare saboda meeting ɗin mai muhimmanci ne suka shirya yi.
Uncle Godwin ne ya kama hannunsa ya zaunar da shi yana faɗin, “Hah Friend. Please calm dawn ”.
Papa ya furzar da wani zazzafan huci jikinsa na wani irin tsuma, ya doka sandar hannunsa a ƙasa yana cizar lip ɗinsa na ƙasa da masifar ƙarfi. Da turanci yace, “Tayaya kake tunanin hankalina zai kwanta Godwin? Ko nauyin faɗamin Yoohan baijiba wai zai auri ƴar arewa, ɗiyar hausawa masu sallah?”.
Da sauri Uncle Mike yace, “Ah!Goshpower wani lokacin kana abu kamar ƙwaƙwalwarka baya aiki da kyau. kai nefa ka sanar min yaron nan ya sanar maka yana da manufa akan duk abinda ya keyi. Mizai hana ka amince masa ya aureta ɗin. Muma wata damace tazo hannunmu akan mahaifinta…..”
A fusace papa yace, “Sai kuma akace muku da ɗana kawai zamu iya samun wannan damar? Salon suje su maidashi mai salla, to ni……”
Saurin ɗaga masa hannu wani da suke kira Chief yayi da sauri. Ya juya maganarsa zuwa yarensu da ayanzuma bilynku bataji ba😪. Magana ya farayi kamar zai haɗiye harshenshi cikin maida gaba ɗaya hankalinsa ga papa. A mamakina kuwa sai naga gaba ɗaya papa ya nutsu yana saurarensa tamkar ƴan uwansa. A hankali na ga fushin papa ya fara sauka daga fuskarsa. Saima ya koma sakin wani mugun murmushi yana gyaɗa kai. Kafin ya miƙe cike da wani irin farin ciki ya rungume Chief ɗin. Suma sauran duk tsantsar farin cikinne ya bayyana a fuskokinsu. Da alama dai shawarar Chief ta zauna da ƙyau a zukatansu.
Tashi papa yay ya shiga neman Number Yoohan. Sai dai kusan kira goma bata shigaba. Canja akalar kiran yay ga Solomon.
Yoohan na kwance har yanzu a gadon Solomon yay knocking. Bai motsaba balle ya amsa masa. Shikuma Solo jin yayi har kusan sau huɗu babu amsa sai kawai ya tura ƙofar ya shigo. Ƙarasawa yay inda Yoohan ɗin ke kwance cike da tsoro da girmamawa yace, “Am sorry sir. Boss ne yace na baka waya”. Kamar Yoohan bazai tankaba ya watsar da shi. sai kuma zuwa can ya miƙa masa hannu alamar ya basa wayar. Yana bashi ya fice abinsa. Yoohan ya ɗora wayar a kunne batare da yayi magana ba.
Cikin sanyin murya papa daga can yace, “I am so sorry my son. Raina ne kawai ya ɓaci dan ina tsoron su canja min kai su cuceni. Amma kuma sai nayi tunani da sake tuna bayanin da kaimin kwanaki sai na fahimci kaima ba ƙaramin abune mai muhimmanci zai saka yin hakan ba. yanzu yaya kaso ayi to?”.
A karon farko Yoohan yayi wani munafukin murmushi ya kai hannu ya shafi sumar kansa har zuwa sajensa. Idanunsa ya buɗe a hankali ya sauke bisa frame ɗin da akai adon ɗakin hotel ɗin da shi. Magana ya farama papan nasa da yare cikin taushin murya.

To su dinɗin dinkum balkisu saina koma gehe kawai ina zare idanu dan anzo dai-dai wajen. Turancinma da yaya nake haɗosa nake masa fassara🙄😜🚶🏻.

Papa da Yoohan sun ɗauki lokaci mai tsaho suna waya. Dan har sai da na ƙosa kafin su kammala. Yanda naga Yoohan ɗin ya ɗan rage buyagin nasa ne ya sakani fahimtar maybe har sun gama tsara wani abune.

★★★★★
Kusan ƙarfe tara na dare Nu’aymah ta farfaɗo. Dr Sa’ad dake tare da ita dan duty ɗin dare ne da shi yay azamar kiran Dr Yoohan da har yanzu yana a hotel ɗin bai kuma waiwayar asibitin ba.
Cikin kuwa mintuna ƙalilan ya shigo asibitin. Tsabar yanda ransa ke a jagule sai ya toshe idanu da baƙin Glasses da yay masifar sake fiddo masa ƙyawun fuskarsa da kwarjinin hasken musilinci dake mamaye da shi. Tunda ya shigo asibitin baiyi magana da kowa ba. Ko gaidashi da Nurses suke da sauran ma’aikatan  hannu kawai ya dinga ɗaga musu kansa a ƙasa ya rufe rabin fuskar da p-cap bayan glasess ɗin. Shi dai Solomon na biye da shi kamar jela.
Ɗakin da Nu’aymah ke a kwance ya tura a hankali ya shiga da sallama ƙasa-ƙasa. Dr Sa’ad da Nurses guda biyu dake a tare da shi suka amsa suna ɗagowa. Da girmamawa Nurses ɗin suka risina suna gaishesa. Batare da ya amsa musu ba suma ɗin ya ɗaga musu hannu kawai. Kafin ya miƙama Dr Sa’ad hannun sukayi musabaha shi kuma.
A hankali ya juya kansa zuwa ga sashen da kan Nu’aymah ya ke. Ya ɗan ranƙwafa kanta ƙaɗan ya janye wani igiyan na’uran dake a gefen kanta gab da kunne.
Yanda ƙamshin turarensa ya buga mata hancine ya saka ƙirjinta harbawa. Buɗe idanun nata tayi da ƙyar saboda bala’in nauyin ciwo da sukai mata. Dai-dai Dr Yoohan ya dubeta shima yana ƙoƙarin zare glasess ɗin idonsa. Kallon ido cikin ido sukaima juna, duk da ita ɗin dishi-dishi take ganinsa hakan baisa ta gagara ganesa ba.
Wani irin juyawa kanta ke mata, daga ciki tanaji kamar ana karta mata ƙarfe, zabura tayi, ta yunƙura zata tashi Sai kuma tai saurin dafe kan nata tace, ‘Aushhh kaina!’.
Yoohan da shima zuciyar tasa ke wani irin harbawa, da sauri ya wani ɗauke idanunsa daga kanta cike da basarwa, tamkar bai fahimci halin da take a ciki ba.
Yanda jikinta ke wani irin ɗan karkarwa ga kanta data riƙe da duka hannayenta tana jujjuyawa ya saka Nurses ɗin nufarta da sauri tare da Dr Sa’ad. Yoohan dai na tsaye baiko motsaba. Sai dai yana kallonsu ne ta ƙasan ido. Yanda duk sukaso Nu’aymah ta nutsu hakan ya gagara, dan ganin Yoohan ɗin ya sake dawo mata da komai cikin memory ɗinta, wanda hakan ke mata barazana cikin kanta tamjar ƙwanyarta zata tarwatse.
“Ku barta” ya faɗa a hankali tamkar ba shine yay maganar ba. Baya Nurses ɗin suka ja domin cika umarninsa, amma tausayin Nu’aymah fal ransu. Dr Sa’ad kam sai ƙoƙarin son riƙo hannun Nu’aymah data riƙe kanta da shi gam ya keyi. A bazata yaji an riƙe masa hannun lokacin da yake gab da ɗorasa saman nata…………..✍

 

Ni dai nace ‘Hummm’.😶 inji mai tsoron gulma.

__________________________
ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

BARKA DA JUMA’A

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply