Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 39


Saran Boye 39
Viral

No. 39

………….Ba Dr Sa’ad ba hatta Nurses ɗin da Dr Aysha dake ƙoƙarin shigowa da drip a hannu sai da suka kalli Dr Yoohan ɗin. Amma a mamakinsu ya fiske abinsa tare da sake tsuke fuska tamkar ba shine ya aikata ba. Sai tura tattausan nasa hannun yay ƙarƙashin kan Nu’aymah da dogon gashinta ke a tsefe duk ya baje a saman filon.
Da sauri ta sake buɗe idanunta, dan kusancin da suka samu gaba ɗayansu neman haifar da barazana yake a bugun Zucikatan su, cikin rawar jikinta daya ƙaru ta sake buɗe baki zatai magana, sai dai kuma hakan kamar da wuya a gareta. Dan saɓanin yin maganar sai hawaye sharrrr!! Suka fara bin kumatunta. Yanda damshin ruwan hawayen nata suka sauka bisa fatar hannunsa ne ya sakashi lumshe idanu yana wani jan numfashi da sassarfa. Sai kuma a hankali ya janye hannun nasa daga cikin kanta dama jikinta gaba ɗaya ya ɗan matsa baya kozaiji sauƙin yamutsawar da dukan gaɓɓan jikinsa ke masa.
Da sauri Dr Aysha tace, “Doctor akwai matsala ne?”.
Shiru mai amsa mata ba. Sai idanu da ya zubama Nu’aymah da jikinta ke vibration a hankali, har zuwa yanzun kuma riƙe take da kan nata da duka hannayenta tana ɗan mirginashi bisa filon. Kusan mintuna biyu yana kallon nata, kamar yanda su Doctor Aysha ke kallonsa a tsorace, kafin ya ɗauka file ɗin Nu’aymah yaja da baya daga gaban gadon. jikin Window ya koma tamkar halin da take ciki bai damesaba. Ya shiga buɗe shafukan takardun dake a ciki file ɗin  yana bin rubutun ciki daki-daki da nazari a nutse.
Su Dr Sa’ad kam duk sun rikice, sai dai sun kasa fahimtar wane taimako ya dace su bata ne. Dawowar da yay gaban gadon riƙe da file ɗinne ya sakasu zuba masa idanu su duka. Ya ajiye file ɗin a saman drawer’n gefen gadon da take sannan yay magana a ɗan kausashe yana kallon Aymah. “Malama ki nutsu”.
Ai maganar tasa tamkar zuga Aymah ma ma tayi, dan gani kawai sukai tayi wani irin masifar zabura zata miƙe. Cikin sassarfa Dr Aysha ta ƙaraso ta tareta. Da ƙyar ta iya dannata saman gadon ta kwantar, duk da hakan kuma fisge-fisge takeyi har yanzun. Batare da Yoohan ya ƙara magana ba ya matsa jikin makunnar wutar ɗakin ya kashe. a take duhu ya mamaye ko ina. Wata razananniyar ƙara da ta amsa duka Word ɗin Nu’aymah ta ƙwalla. Duk firgita su Dr Aysha sukayi, dan haka suka shiga lalube a cikin duhu kowa na neman wajen ɓuya. Shiko yana tsaye ko gezau, duk da kuwa ƙarar tata jiyay tamkar zata tarwatse masa kayan cikin kansa. Lumshe idanu yayi ya buɗe a hankali sannan ya kunna wutar. Baiko kalli inda su Dr Sa’ad suka maƙalƙale ba ya taka zuwa ga Nu’aymah dake yashe a ƙasa alamar faɗowa tayi ƙasa.
Duƙawa yay yasa hannu biyu ya ɗauketa cak ya maida saman gadon, a kallo ɗaya zaka fahimci batama yin numfashi. Sai da yaja bargo ya lulluɓa mata sannan ya maida mata duka na’urorin da ke manne da kanta ɗazun. Juyawa yay yayima su Dr Aysha alamar su fita. Suna gaba yana biye dasu riƙe da file ɗin Nu’aymah.

★★★★★

Tun barin Yoohan gidan su Nu’aymah babu wanda ya sake samun nutsuwa. Musamman ma Naseer da Abdallah. Dan furicin Yoohan akan Aymah ba ƙaramin girgiza musu zukata yayi ba.
A yanzu hakama Naser ne zaune can bayan sashen samarin gidan. Waya ce mane a kunnesa alamar magana yake da wani. Muryarsa cike da rauni yace, “Ananah wlhy ina sonta, dan ALLAH karku bari wannan karon na rasata. A wancan karonma na haƙura ne saboda duk kun goyama Abdallah baya. Ni kuma banason abinda zai kawo rikici a cikin zuminci ta dalilina. Amma a yanzu wlhy babu abinda zai sakani na janye, dan ALLAH kizo kano, nasan Hajjo duk abinda kikace zatayi, dan kece ke sakata tayi abu koda bataso matsayinki na babbar yayarta”.
Shiru ya ɗanyi yana sauraren abinda take cewa daga can. Sai kuma naga ya saki lallausan murmushin daya sake ƙawata ƙyawun fuskarsa ta jinin katsinawa, ya kai hannu ya shafi kwantaccen sajensa da faɗin, “Na gode sosai Ananah, furucinki ya koremin dukkan damuwata da tashin hankali, wlhy ba cikiba ko ƴaƴa goma Zainab ta haifa ina sonta a hakanta, kema kuma shaida ce akan hakan Ananah”. Ya sake jim na saurare sannan yace, “To nagode sosai, sai kun iso”. Daga haka ya yanke wayar yana sake faɗaɗa fuskarsa da murmushi. Yanaji a ransa insha ALLAHU a wannan karon ya gama mallakar farin cikin rayuwarsa Nu’aymah ya gama, musalta irin son da yakema yarinyar ɓata bakine, amma wlhy ko rantsuwa yay babu kaffara a cikinta yafi Abdallah son Nu’aymah.

(To masu karatu kun yarda😉😂?).

A can sashen su Abdallah kuwa Abdallah ne zaune a gaban Momy a karo na farko tun dawowarsa gidan, dan daya gaisheta baya ƙara ko minti ɗaya yake barin wajen. Tun tana damuwa da hakan harta zuba masa ido kawai da kaima UBANGIJI kukanta. A yau kan tun bayan watsewar kowa daga falon hajjo bai zame ko inaba sai sashen iyayen nasa. Momy na zaune a bedroom ya sameta. Ganinsa kawai tai a gabanta ya ɗora kansa bisa cinyarta yana hawaye.
Cikin tsoro da mamaki tace, “Abdallah lafiya kuwa?”. Da muryar kuka yace, “Momy wannna karonma zasu rabani da ita. Wlhy ina sonta, dan ALLAH karki bari su rabamu, itama tana sona Momy”. “Ikon ALLAH Nu’aymahr dai?”. Da sauri ya gyaɗa mata kansa, kafin ya shiga bata labarin duk abinda ya faru yanzu a falon hajjo.
Cike da al’ajabi Momy tace, “Nikam wannan lamari da ɗaure kai, har raina zuciyata ta kasa aminta da zancen likitocin nan akan Nu’aymah. To amma yanda duk bakin nasu yake zuwa ɗaya ne zai sakama kowa ruɗani, sannan shi kuma yaron yanzun yazo da batun cewa zai aureta. Kodai….? Kai ina ba haka bane, hakanma bazata taɓa faruwa ba”. Ta ƙarasa faɗa tana girgiza kanta.
Abdallah yace, “Momy wlhy koma hakan gaskiyane ni inasonta a hakanta, ƙilama fyaɗe yay mata”. Murmushi Momy tayi a karon farko, tace, “Humm Abdallah zuciyata na hasashen abubuwa da yawa a gidan nan, sai dai bazan furtaba har sai zargina da zatona sun zama gaskiya a idanun kowa”.
“Momy kamar ya?”. Abdallah ya faɗa da sauri yana kallonta. Kanta ta girgiza masa. “No, bazaka ganeba share kawai. Yanzu kai da kake batun auren Nu’aymah su Adawiya daka yima aika-aika fa? Kasan kowa a gidan nan ciki yake da kai harni wlhy. Abinda ya hana ace maka komai wannan tashin hankalinne kawai. Abdallah kodai ka fara shaye-shaye ne bamu sani ba?”.
“Momy shaye-shaye kuma? Ni ban fara shaye-shaye ba wlhy. Kawai dai na rushe katangar da sukace itace zata hanani mallakar burina ne, kema kin sani momy Nu’aymah farin ciki nace, da sonta na fara sanin kaina, tayaya lokaci ɗaya za’ace za’a ruguzashi. Itama tana sona. Batason a rabamu”.
“Nasan duk haka Abdallah, shawarar da zan baka kawai kabi komai a hankali, ka kuma saka a ranka wani ramin rijiyar yafi gaban tsallakawa saboda faɗin baki, a kuskure kaɗan zaka iya afkawa ciki ka halaka. Zan tayaka da Addu’a, insha ALLAH kai da Nu’aymah sai kunyi farin ciki. Daga ni har mahaifinka kuma sai inda ƙarfinmu ya ƙare wajen ganin ka mallaki Nu’aymah a wannan karon kodan samun farin cikinku kai da ita”.
Sosai yaji daɗin kalaman mahaifiyar tasa. Yay mata godiya sannna ya fice daga sashen cike da ƙwarin gwiwa.

________★★★________

Baba malam na zaune a falonsa hannunsa riƙe da Littafin gawurtaccen barubucin malamin addinin nan Sheikh: Salihu bn Fauzan bin Abdallahil Fauzan yana dubawa, sai dai sam hankalinsa bama ya tare da fahimtar abinda littafin ya ƙunsa. Karantawa kawai ya keyi. Kiran da akaima wayarsa ne a karo na biyu ya saka Umm dake kwance cikin kujera idanunta a rufe an cire mata drip ɗin da aka saka mata kallonsa. Ganin sam bama yajin kiran wayar ya sakata miƙewa a hankali zaune. Hannu ta miƙa ta taɓashi.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke da juyowa ya kalleta da sauri, sai kuma ya maida ga wayarsa data nuna masa da hannu. Sake sauke numfashin yayi, ya gyarama Muhammad dake kwance jikinsa yayi barci kwanciya, sannan ya ɗauka wayar dai-dai ta tsinke. Ganin wanda yay kiranne ya sakashi kiransa babu jinkiri. Sai dai kuma bai ɗaga ba harta tsinke shima, tana tsinkewa kiransa ya sake shigowa wayar baba malam ɗin. A karon farko baba malam yay ɗan murmushi, wannan ɗabi’ar Yoohan ce, baya taɓa yarda baba malam ya kirashi sai dai shi ya kira. Koda kuwa baba malam ne ya fara kiransa zai bari har sai ta katse sannan shi ya kirasa.
Kamar yanda ya saba cike da ladabi yayma baba malam cikkakkiyar sallama da harshensa da baya fita da kyau. Baba malam ya amsa masa da kulawa tamkar yanda ya saba, bazaka taɓa cewa wani abu ya faru tsakaninsu ba. Gyara zama sosai Yoohan ya sakeyi a kujerar office ɗinsa kafin ya farama baba malam ɗin bayani a nutse.
“Uncle Alhmdllh patient ɗin ta farfaɗo, sai dai kuma…….” Sai yay shiru kuma. Cike da dauriya da kawaici irin na baba malam yace, “Yahya! Sai dai me? Karkaji komai kai min bayani akan duk halin da Nu’aymah take, domin UBANGIJIN daya jarabceta a wannan yanayin ya fimu sanin dalilin hakan, ita rayuwa da ƙaddara duk suna cikin kundin jarabawa ne, mai ƙarfin imani da ƙwaɗayin rahama ne kuma kawai ke iya juriyar cinyesu komai tsanani da zafin da sukazo masa da shi. UBANGIJI ya fimu sonta ai, bai kumayi shawara damu ba sanda ya bamu, idan ya ƙarɓeta a yanzu sai dai mu gode masa da ni’imar da yay mana na samunta tsawon shekaru sha bakwai a gabanmu. Dan haka faɗamin kawai”.
Baki Yoohan ya cika da iska ya fesar, zuciyarsa da ruhinsa na ƙarajin ƙauna da son baba malam har cikin jini. A komai nasa yana fatan yin koyi da baba malam. Cikin harshen turanci yace, “Uncle tanama da ranta, sai dai dama bawai mun mata aikin ainahin matsalarta bane kamar yanda nai maka bayani ɗazun kafin mu taɓata. Aikin da mukai mata zai bata taimakone kawai wajen hana ƙwaƙwalwarta goge komai da take barazanar yi, sannan zai sassauta mata raɗaɗin da takeji a duk lokacin da matsalar ta motsa, insha ALLAHU zai hana ta iya rasa hankalinta. Nayi tunanin aikin zai bata kariyar da zamu iya ɗaukar kamar watanni biyar kafin ai mata aikin gaba ɗaya, dan dole sai an fita da ita waje, a ƙasarnan bamu da isassun kayan aikin matsalarta, koma muna dasu zaka samu bana zamani bane tunda shuwagabannin namu bawai hankalinsu nakan abinda ya dace suyi bane. To a yanzu dai matsalar dana fahimta dolene ai gaggawar yimata aikin koda nan da wata ɗaya ne insha ALLAH, inba hakaba zata iya loosing memory ɗinta a koda yaushe”.
Ɗan rumtse idanu baba malam yay yana ambaton sunayen ALLAH, muryarsa da ƙoƙarin jarumta yace, “Shikenan Yahya, duk yanda kake ganin ya kamata akai kayi tunda aikinka ne, yanzu zamu iya zuwa mu ganta?”.
Ɗan jimm Yoohan yayi, kafin yace, “Eh to amma karkuzo da yawa dai”. “Babu damuwa”. Baba malam ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya.

Batare da kowa ya saniba a gidan Umm da baba malam da Hajjo suka tafi asibiti duba Nu’aymah. Yoohan da yake wani irin jin kunyarsu da nauyinsu ne yay musu rakkiya har ɗakin da Nu’aymah ke kwance. Ba ƙaramin tashi hankalinsu yayiba ganin yanda aka jajjone kan Aymah da na’urori, Hajjo da Umm harda hawayensu. Basu wani jimaba suka fito. Office ɗin Yoohan suka sake komawa. Inda ya sake musu bayanin komai dalla-dalla a nutse. Sosai suka gamsu da bayaninsa, wanda a take duk murmushi ya baibaiye fuskokinsu, suka shiga saka masa albarka da jera masa addu’oin fatan alkairi. Har wajen mota ya rakosu, sai da yaga tafiyarsu sannan ya koma ciki, dan yau a asibitin zai sake kwana saboda Nu’aymah zata iya farkowa a kowane irin lokaci.
Zamansa babu jimawa Solomon ya shigo ɗakin ɗauke da takeaway da yayo masa acan hotel ɗin da suke sauka. Dan idan yazo kano abincin can kawai yake ci, sai ko yanzu da suka haɗu da su baba malam. Ganin yana waya ya saka Solomon komawa gefe ya tsaya yana sauraren yanda Yoohan ɗin ke wayar a nutse.
Magana suke da wani likita abokinsa dake a ƙasar Canada. Yana buƙatar a aiko masa da wasu allurai ne masu matuƙar tsada da zaima Nu’aymah amfani da su. Kuma yana buƙatar sune da gaggawa daga nan zuwa yammacin gobe idan ALLAH ya kaimu. Shine suke maganar ta yanda za’a kaisu airport ɗin ƙasar a damƙawa wani abokinsa matuƙin jirgi da Yoohan ɗin yasan kayan zasu iso yanda yake fata. Sai da suka kammala maganarsu har Yoohan ɗin yayma Dr Androi transfer ɗin kuɗaɗen allurar take anan masu yawa daga asusunsa sannan ya ajiye wayar.
Solomon dake kallonsa cike da takaici da mamakin ganin kuɗin daya biya na alluran tamkar baisan ciwonsu ba yay saurin faɗin, “Good evening sir! Ga abinci na amso maka, naga bakaci komaiba tun breakfast ɗin safe”.
Ɗan luuuu da idanu Yoohan dake miƙewa yayi, kamar zai lumshesu sai kuma ya buɗe su akan Solomon ɗin. “Karka damu banajin yunwa. Haɗamin coffee kawai is ok for me”.
Ganin yanda ya tsuke fuska sosai ya saka Solo amsa masa da “To” kawai. Cikin bin umarni yayi masa yanda ya buƙata, acan rukunin kujerun office ɗin daya koma yana aiki a lap-top yaje ya kai masa coffee ɗin. A hankali yace, “Thanks”. Shiru office ɗin yayi na wasu mintuna, Yoohan nata aikinsa da shan coffee kamar ya manta da Solomon. Sai kuma ya ajiye kofin ya ɗago yana kallon solo ɗin. “Kaje ka kwanta, basai kazo nan da safe ba, inaga zuwa dare zamu wuce Abuja, sai ka mana booking ɗin jirgi”.
Cike da girmamawa yace, “Okay sir”. Daga haka yay masa sallama ya fice.

Solomon na isa hotel ɗin wayar Papa ya fara kira. Ba a ɗauki lokaciba kuwa ya ɗaga. Bayani ya shiga yimasa da yarensu wanda sam ban fahimci akan minene ba. Sunja lokaci mai tsaho suna wayar sannan ya kira madam Chioma itama. Itama ɗin dai magana sukai ta tsahon lokaci da wani yaren ba irin wanda sukai da papa ba. Batun yau ba na fahimci Solomon najin yare ba ɗaya ba. Kamar yanda na kula shima Yoohan ba yare ɗaya kawai yake jiba bayan turanci. Shiyyasa a lokuta da dama nakan gaza banbance shin su wane yarene wai?.

*_WASHE GARI_*

Washe gari da safe ƴan gidan su Nu’aymah sukaje asibitin suka duba Nu’aymah data sake farfaɗowa. Sai dai har suka gama abinda zasuyi suka taho basuga Yoohan ba. Yana office yana duba marasa lafiyar da suke da tsananin buƙatarsa duk da da da farko baiyi niyyar hakanba.
Suna dawowa gida kuma suka iske baƙin da basu san da zuwansu ba. Kakar Nasir data haifi babansa ce tazo daga katsina mai suna Hajiya Hassana. Sai dai suna kiranta Ananah, yayar Hajjo ce uwa ɗaya uba ɗaya, wadda ita kaɗai ce ta rage mata a duniya. Hajjo na tsananin girmamata dan itama tana ƙaunar hajjon, batason abinda zai taɓa hajjo da zuri’arta, ta zame mata tamkar uwa da uba. Itama ta tsufa sosai fiye ma da Hajjo, sai dai da yake ALLAH ya basu lafiya sosai ga jin daɗin rayuwa, ko ina suna zuwa, garama hajjo tana fama da ciwon ƙafa. Ananah kuma idanuntane dan sai da galashi take gani da ƙyau.
Tare take da jikokinta da yaranta biyu ƙannen mahaifin Nasir ɗin mata. Dama duk babbar salla anan take salla kano, ita kuma hajjo sai gab da azumi take zuwa mata can katsina tai kamar wata guda. Hakan na sakasu farin ciki sosai.

‘To yanzu kuma Nasir ya ɗaɗɗago Ananah akan batun Nu’aymah. Ko yaya zata kasance?. saimu bisu muga wane mai rabo ne zai ɗauki wannan allurar ta cikin ruwa😉?’.

Ba ƙaramin farin ciki hajjo dama duk jama’ar gidansu Nu’aymah sukaiba da zuwan Ananah. Dan yanda take son kowa a gidan haka kowa ke sonta da ƙaunarta har surukan Hajjo. Take gidan ya rikice da murna dan duk tunaninsu ta iso da wurine saboda bikin su Kubrah nan da kwanaki goma. Ciwon Nu’aymah ne ma yaɗan sanyaya shirye-shiryen da akeyi.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka shirya abinci gabansu kala-kala daga kowanne sashe. Da mamaki Ananah tace, “Wai ni banga ƙawalliyata ba ita?”. Kowa yasan Nu’aymah take nufi. dan suna shiri sosai-sosai da Ananah, saboda Nu’aymah nada sunan hajjo ma take cemata ƙawalliya.
Rufaidah ce tai caraf ɗin cewa “Ananah tana asibiti babu lafiya” a rikice Ananah take tambayar, “Asibiti kuma? Miya sameta ni Hassana ɗiyar malam Haruna”. Shiru kowa yayi ya gaza bada amsa. Sai hajjo ce tai ɗan murmushi da cewar, “Ciwonta ne ya motsa, amma Alhmdllh da sauki ma”.
Cikin jimami Ananah ta share ƴar ƙwallar data taru mata a ido, tace, “Kai duk wanda yay sanadin shigar wannan yarinya a bala’innan yayi asarar rayuwarsa wlhy, ALLAH ya saka mata, ko wanene kuma ALLAH ya hanashi farin cikin duniya dana lahira”.
Kusan a tare duk falon suka amsa da amin.

★★

Bayan sallar magriba Ananah sukaje asibiti suma suka duba Nu’aymah, a lokacin Yoohan yaje airport amso saƙon da aka aiko masa daga ƙasar canada. Hakan yasa har suka kammala suka wuce yanzunma basu haɗu da shi ba. Sai bayan wucewarsu da kamar awa guda ma ya dawo.
Kansa tsaye ɗakin da Nu’aymah take ya nufa. Solomon biye da shi ɗauke da wata madaidaiciyar bag. A ciki ya samu Nurse ɗin data gama gogema Nu’aymah dake barci jiki.
Da girmamawa ta gaida shi, Solomon kuma ya ajiye bag ɗin ya fice. Matsawa yay gaban gadon lumsassun idanunsa akan Nu’aymah da fuskarta tai wani irin fayau. Sai uban haske data ƙara tamkar mai yaron ciki. Ya kafe Laɓɓanta da sukayi wani irin jajur gwanin sha’awa, gashi taɗan tsuke bakin ya sake komawa mitsitsi.
Huci ya ɗan furzar ya janye idanunsa daga kallonta, yana faɗin ‘Bakin tsiwa’ a zuciyarsa. ya gyara kujerar gefen gadon ya zauna tare da ɗaukar bag ɗin da Solo ya ajiye ya buɗeta. Madaidaicin abu ya fiddo cikin kwali mai kama da kula, ya buɗesa sai ga ƙanƙara a sama tanata huci. a ƙasan ƙanƙarar ya zaro kwalaben alluran kusan guda guda bakwai ƴan ƙananu, yanda kwalaben suke ƴan mitsitsi sai ka ɗauka wani tarkacen banza ne. Nanko kuɗaɗene masu shegen nauyi zaune da ƙafafunsu. Sai da ya gama duba takardar dake a cikinsu kafin ya maidasu ciki ya fiddo ɗaya kawai.
Miƙama Nurse ɗin dake a ɗakin yayi, murya a daƙile yace “Kiyi mata allurar nan yanzun nan”. Amsa tayi da girmamawa. A gabansa ta buɗe syringe ta kwashe ɗan ruwan allurar da ko ganinsa bama ayi sosai cikin syringe ɗin. Shine ya nuna mata a inda zatayi. (A raina nace da idon Aymah biyu sai anyi ƙaramin yaƙin duniya na uku kafin ayi allurar na kuwa🤣).
Mintuna uku ba’a rufa dayin allurarba wani irin mahaukacin zufa ya fara tsatstsafowa a kowacce ƙofar gashi ta jikin Nu’aymah. Kafeta da kallo Yoohan dake zaune ƙafa kan ɗaya ya harɗe hannayensa a ƙirji yayi. Yanda take wani irin mutsu-mutsu kamar macijiya mai tsohon ciki ne ya sakashi sakin wani tattausan murmushi daya ƙawata cikar haibarsa da kwarjinin bautar UBANGIJI. Ya ɗan lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta yana jan ajiyar zuciya………….✍

‘Saura naji wani yace ɗan kaɗan ne😣😒. Da gobe saina ƙara rage mudu🚶🏻😑😚’.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

*Ga breakfast nan aci a hankali har dinner ɗin gobe idan ALLAH ya kaimu sai ku ɗumama😎😁⛹🏻‍♀️*.

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply