Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 40


Saran Boye 40
Viral

No. 40

…………Ƙarfe sha ɗaya na dare Yoohan da Solomon suka bar kano zuwa Abuja. Tafiyar da bata kulle awa guda ba jirginsu ya sauka. Sun iske guards ɗinsa tuni suna a airport ɗin ma, dan haka basu ɓata lokaciba wajen wucewa gida.
Kamar yanda yay tsammani ya iske gidan nasu shiru, alamar duk sun kwanta, madam Chioma kawai suka iske a falo zaune cikin kwalliyar riga da wando da sukai mata ƙyau sosai. Yanda ta zubamasa ido haka shima kallonta yake babu yabo babu fallasa. Cikin takun nasa ya ƙarasa gareta, itama sai ta miƙe tana mai buɗe nasa hannayenta alamar yazo gareta.
Gabanta yaje ya tsaya batare da ya shiga jikin nata yanda ta buƙata ba. Ya kamo hannunta ɗaya yana ɗan shagwaɓe fuska kaɗan. Cikin sanyin muryar da tabbatar da agajiye yake, da yarensu yace, “Mom na girma ni”.
Ɓata fuska tayi itama cikin wani yanayi, muryarta na harɗewa wajen fita tace, “Please my boy”. Karan farko ya saki lallausan murmushin da ya nema sumar da ita a wajen. Ya ɗora hannunsa na haggu saman tattausan sajensa ya shafa yana ɗan kauda idonsa daga gareta zuwa ƙafar benen dake a falon inda Miracle ke tsaye cikin kayan barci, ƙirjinta rungume da madaidaicin teddy bear ta wani kafesa da idanu tamkar zata haɗiyesa ta huta.
A hankali ya janyesu gareta yay wani luuuu da su kamar zai rufe sai kuma ya buɗesu yana sakin hannun Mom yaja baya. Hannayensa duka biyu ya ɗaga mata da faɗin “Sweet mom gudnit”. Kafin tace wani abu harya fara hayewa upstairs ɗin da ɗan sauran kuzarinsa batare da ya sake duban Miracle ba ya raɓa ta gefenta ya wuce.
Su duka da kallo suka bisa harya ɓacema ganinsu, mira ta share ƙwallar data cika mata idanu ta juya da gudu zuwa ɗakin barcinsu ita da joy. Wata malalaciyar harara Mom ta raka Mira da ita. Kafin ta taune lip ɗinta na ƙasa da ƙarfi zuciyarta na ƙuna fiye da yanda gangar jikinta ke tsuma.

Yoohan daya iske ɗakinsa kamar yanda yay fata komai fes bai wani zauna ba ya shige toilet. Bayan wasu mintuna masu ɗan tsaho ya fito jikinsa na ɗigar da raɓar ruwan wanka. Da sauri yaja ya tsaya ganin Mom zaune bisa sofa. A ɗan daburce yace, “Mom lafiya kuwa?”. Saurin ɗago idanunta dake akan wayarta tayi ta dubesa, dai-dai shi kuma yana ƙoƙarin saka farar t-shirt ɗin daya ɗauka. Miƙewa tai ta nufosa tana wani sakin tattausan murmushi, ta ɗauka ƙaramin towel ɗin daya fito da shi a hannu ta nufi sumar kansa alamar zata tsane masa gashinsa dake ɗigar da ruwa. Da ɗan hanzari yaja baya kaɗan yana tsuke fuska.
“Mom!!”
Ya faɗa aɗan tsawace. Jin a yanda yay maganar ne ya sakata tsayawa cak daga yin abinda tai niyya.
Da ɗan shagwaɓa yace, “Haba Mom! Miyasa kike son maidani baya ne kullum? Nifa ba Abraham bane ko Victoria Please”.
Ƙanƙance mayatattun idanunta tayi tana ɗan matsosa, cikin muryarta dake wani irin rawa tace, “Kaine kake ɗaukar kanka babba John! Ita uwa ɗanta kullum yaro ne a gareta. Ina sonka Yoohan fiye da yanda kake tunani, kai ɗin farin cikinane fiye da sauran ƙannenka”.
Ɗan lumshe idanu yay ya buɗe a kanta, ya ɗan sassauta muryarsa da fuskarsa dake a tsuke. Dan shi harga ALLAH bai fassara maganarta da komaiba face soyayyar ɗa da uwa. “Na sani Mom, nima ina sonku da ƙaunarku fiye da zato ke da papa da ƙannena. Amma Please ki ringa rage cewa zakimin wasu abubuwan. Bama ni ba ko Abraham ɗan shekara goma ba komai zaiso kimasa ba yanzun. Mun rigada mun girma, hidimar da kikai mana muna ƙanana ta wadatar uhmyim?”.
Yanda yay maganar cike da lallashi ne ya sake narkar da ita a wani irin yanayi mai wahalar fassara. Ta buɗe baki zatai magana aka turo ƙofar aka shigo. Gaba ɗayansu ƙofar suka kalla. Papa ne cikin kayan barci da alama ma ya fara barcin tashi yayi.
Cikin ƴar shagwaɓa Yoohan yace, “Yauwa papa Please kwashi matarka ku wuce dama ta sakani a gaba nikam”.
Papa dake bin Mom da wani irin kallo ya haɗiye yawu da yin guntun murmushi yana maida idonsa akan Yoohan ɗin da ya sake ƙwaɓe fuska. Muryarsa da alamun barci ya tashi yace, “Yaushe ka dawo?”.
Mirror Yoohan ya nufa yana faɗin, “Yanzun nan babu jimawa nazatama baka gida ai”.
Komai papa bai ceba ya kama hannun Mom suka fice yana faɗin, “Huta abinka sai da safe”. Suna fita Mom ta fisge hannunta da ga na papa tana kumbura kumatu. Baice mata komaiba yay gaba abinsa dan jin Yoohan yana sakama ƙofarsa key. Yasan ko mi zatayi bazai sake buɗe mataba kuma. A ransa kuwa mamakin yanda Matar tasa ke nuna tsananin so ga ƴaƴansu yakeyi. shi bai taɓa ganin mahaifiya mai ƙulafucin ƴaƴa irin Madam Chioma ba.

Yoohan kam koda ya kammala kimtsawa falo ya fito ya haɗa tea ya koma bedroom ɗinsa. Zaman sha yay zuciyarsa da tunaninsa duk na wajen Nu’aymah. Ji yay yana buƙatar sanin yaya take yanzun, dan haka yaja wayarsa ya nema Dr Aysha a karo na farko a rayuwarsa.
Ita kanta Dr Aysha ba ƙaramin mamaki tayi ba ganin kiran Dr Yoohan a wayarta. Abinda bai taɓa faruwa ba. Jikinta har tsuma yake wajen saurin ɗauka. Ta kara a kunne murya a narke tace “Hello! Doctor good evening”. Maimakon ya amsa mata sai cewa yay “Assalamu alaiki”. Idanu taɗan zaro waje jin sallama yayi, saɓanin da da sai dai ya ce maka hii. Itafa dama gaba ɗaya a wannan zuwan nasa abubuwa da yawa taga idan yanayi tamkar ba shiba. Shekaranjiya ma har ganinsa tai kamar ya fito massallaci……
Sallamar da ya sake maimaita matace ta katse mata tunaninta. “I’m sorry sir. wa’alaikissalam. Kunje lafiya?”.
“Humm”
ya faɗa a taƙaice yana lumshe idanu da kai kofin tea ɗin bakinsa. Sai da ya kurɓa ya haɗiye kafin yace, “Ya yarinyar nan ta farka ne?”. Ta gane Nu’aymah yake nufi, dan ita kaɗaice patient ɗin daya kwantar dai. Cikin sanyaya muryarta tace, “A’a har yanzu tana barci, amma an saka mata drip ɗin daka ce ɗin yanzun babu jimawa”. “Okay night” ya faɗa a taƙaice da yanke wayar batare da ya ƙara komai ba.
Nannauyan ajiyar zuciya Dr Aysha ta sauke tana ɓata fuska kamar zatai kuka. Akan laɓɓanta ta furta, ‘Ɗan wulaƙanci’.
Oho baimasan tanai ba, dan shi tea ɗinsa ya ƙarasa sha kafin ya miƙe ya nufi toilet. Alwala yayo. Ya saka sallayarsa sabuwa da baba malam ya bashi ya tada salla kamar yanda ya keyi yanzu a kowanne dare. Idan har ya samu dama yakan fara daga ƙarfe ɗaya ko biyu, zuwa uku sai yaɗan kwanta kafin asuba.
*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply