Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 43


Saran Boye 43
Viral

No. 43

…………Ajiyar zuciya ya sauke a hankali jin yanda Aymah take sake tura kanta cikin ƙirjinsa. Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe akan dogon gashinta dake ta uban ƙamshi ga ƙyallin mai daya sha masha ALLAH. “Silly girl!” ya faɗa a hankali yana kai bakinsa dai-dai kunnenta. Batare da ya jira amsarta ba ya sake miƙewa da ita ɗauke a hannunsa. Zama ya farayi saman kujerar sannan ita kuma ta koma saman cinyarsa da ƙyau batare da tasan mi takeyi ba. Syringe ɗin da Ahmad ya ajiye ya ɗauka, ɗan guntun ruwan allurar dake ciki ya kalla, ya ɗan yamutsa fuska kaɗan da zare hular kansa ya ajiye gefe. Ya sake kallon Aymah ya girgiza kansa, cikin ƙwarewa da sanin makamar aiki ya kuma turata jikinsa da ƙyau tare da ranƙwafowa ya ɗaura bakinsa akan kunnenta. Wata irin sassanyar iska ya shiga hura mata cikin kunne a hankali, yayinda can kuma hannunsa ke saita inda zai mata allurar batare da ta saniba.
A hankali ta saki wani irin nannauyan ajiyar zuciya da sake shigewa jikinsa, saboda ƙamshinsa na sake jan hankalinta. Hakane ya bashi dama tsira mata allurar dai-dai inda ya dace. Da masifar ƙarfi ta zabura tare da fasa ƙara ta sake damƙesa da ƙyau jikinta na wani irin karkarwa.
Zare allurar yay yana sakin wani lallausan murmushi daya sake fidda annurin fuskarsa. “I am sorry”. ya faɗa a hankali cikin kunnen nata.

Ihun Nu’aymah duk sai da ya shiga cikin kunnen su baba malam. Duk rumtse idanu sukayi tausayinta na tsargama zukatansu. Sai dai babu wanda yay yunƙurin shiga cikin falon.
A ɓangaren Yoohan kuwa idanunsa ƙyam akan Aymah dake ta juyi a jikinsa tamkar wata macijiya, sai zufa dake ta faman tsatstsafo mata a goshi. Handkerchief ɗinsa fari ƙal ya fiddo cikin aljihun gaban rigarsa ya shiga share mata zufar, tsahon mintuna biyar suna a haka kafin ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere, a hankali kuma sai jikinta ya fara saki alamar barci. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sauke numfashi. Kwanciyar ya gyara mata a cinyarsa yanda zataji daɗi sosai, sai kuma ya kai hannu saman gashinta daya barbaje ya tattaresa cikin hannunsa. Ribbon ɗin ya ɗauka ya ɗaure mata shi a tsakkiya ya nannaɗesa da ƙyau yanda bazai takura mata ba. Baya yayi ya kwanta jikin kujerar shima, ya lumshe idanunsa da sakin sassanyar ajiyar zuciya.
Shirun da su baba malam sukaji babu motsinsu har tsahon wasu mintuna ne ya saka Ahmad faɗin, “ALLAH yasa dai lafiya naji shiru”. Ɗan murmushi baba malam yayi, ya kalli Ahmad ɗin yana faɗin, “Ai tunda kaji mamana tabar kwakwazo na tabbatar anyi alluran”.
Kusan a tare duk suka murmusa. Hajjo tace, “Raguwar amarya ba, sai tsiwa a baki amma cikinta fal tsoro, gashi kuma ta zama matar likita sai su ƙarata ai”. Yanzun kam duk dariya suka ɗanyi. Ananah tace, “Ai irinsu dama hakane, zakiga akwai tsiwa amma matsoratane a bugun farko. Ahmadu leƙa kagani”.
Da to Ahmad ya amsa yana nufar falon. Sallama kusan uku yayi baiji an amsa masa ba. Hakane ya sakashi tura ƙofar a hankali ya shiga. Sai dai daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallonsu. A take murmushinsa ya sake faɗaɗa.
Buɗe idanu Yoohan yayi a hankali tare da ɗagowa zaune sosai yana kallon Ahmad ɗin. Sai kuma ya yunƙura ya ɗaga Aymah cak daga cinyarsa zai miƙe.
Da sauri Ahmad yace, “No Doctor, kayi zamanka dama na leƙone kawai naga idan komai lafiya. To ashema har tayi barci”. Yoohan daya ƙarasa miƙewa baice komaiba, sai da ya shimfiɗe Nu’aymah a kujerar da ƙyau ya gyara mata kwanciya sannan ya ɗauki hularsa ya maida bisa kai yana bama Ahmad ɗin amsa. “Barrister wannan ƙanwar taka ta cika raki da ragwantaka, saboda allura kawai duk ta jigatani tamin Squeezing ɗin kaya”.
Ƴar dariya Ahmad yayi yana ƙoƙarin tattare syringe ɗin da komai da sukai amfani dashi. Yace, “A’a Doctor karmuyi haka da kai. Ni na tabbatar maka sai kazo wataran ka sanarmin Aymah jarumace, ballema itama likita zata zama insha ALLAH ”.
Idanu Yoohan yaɗan waro yana gyara zaman rigarsa, yace, “A hakanne zata zama likita tana tsoron allura tamkar bindiga ɗin? Tab za’aga likitoci kam”.

Da haka suka fito Ahmad na dariyar zancen Yoohan, shiko Yoohan ya fiske abinsa tamkar ba shine yay maganar ba.
Kusan duk a tare su Abbah ke tambayar jikin Nu’aymahn. Ahmad yace, “Ku kwantar da hankalinku ita harma ta tafi duniyar barci. Dama ihun na allura ne”.
Duk kallon Yoohan sukai cike da farin ciki, suka shiga jera masa sannu da godiya. Shi dai kansa a ƙasa yake faɗin, “Uncle karku damu aikina ne ai. Insha ALLAH zata tashi kamarma komai bai faruba dan amfanin allurar kenan. Sai dai a dinga kula dan abu kaɗan ita yanzu zai iya birkita ta, ruɗanin kuma shine ba’a so dan zai maida cigaban da ake murnar samu bayane. komai a ringa mata shi da lallashi”.
“Insha ALLAHU za’a kiyaye. ALLAH ya saka maka da alkairi, ita kuma ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne”.
A tare suka amsa da amin, harsu hajjo da Ahmad ya fassara musu abinda Yoohan ɗin ya faɗa.

A cikin gida kuwa dai hidimar bikinsu suke tayi, babu wanda yasan abinda ke faruwa da Nu’aymah sai shaƙiƙan Umm da suke a bedroom ɗinta kawai. Suma kuma tunda Umm taje ta sanar musu likitan da zai duba Aymah yazo duk sai suka samu kwanciyar hankali.
Bayan wucewar Yoohan duk suka shiga har falon baba malam suka ganta. Hakan ya ƙara musu nutsuwa sosai, dan haka suka dawo ɗakin Umm suka cigaba da hirarsu ta zuminci tare da tattaunawa akan auren na Aymah.
Koda suka koma can baba malam da kansa ya ɗauki Nu’aymah dake barci hankali kwance ya maida bedroom ɗinsa. Sannan ya fito shi da ƴan uwansa suka fice massallaci gabatar da sallar magriba.

Biki yayi biki masha ALLAH, dan Addah ta samu alkairi sosai daga wajen abokan arziƙinta. Hakama sauran matan gidan bisa al’adar biki da kowa ya sani suma sun samu rabonsu ga abokan arziƙansu. Harma da Umm da kowa sai yanzu yasan harda gudan jininta. Ana idar da sallar isha’i kuma aka shiga shirya amare. Hajarah da Kubrah. Nu’aymah dai babu wanda yay magana maybe ba yau ba kenan.
Kamar yanda kowa ya sani baba malam shike raka duk ƴaƴansu gidan aure. Babu wani gayyar ƴan kai amarya. Duk wanda yake da buƙatar ganin ɗaki yakanje da rana bayan ɗaurin aure ko washe gari idan amarya ta kwana a gidanta. To gasu Hajarah ma tsarin bai canja ba. Dan ana idar da sallar isha’i su baba malam duk suka shigo gida. Sashen Hajjo aka kai amaren, Hajarah nata kuka kamar zata shiɗe. Kubrah kam idanunta ƙyar cikin lifayar da aka naɗa musu. Sai uban ƙamshi suke kamar gidan turare.
Duka iyayensu da shaƙiƙan ƴan uwa suka taru a sashen Hajjo aka shiga musu nasiha. A yanzunma dai Hajarah kuka take, Kubrah kam kanta dai a ƙasa tana saurarensu. Bayan nasihar da akai musu da gargaɗi mai ratsa jiki akai musu doguwar addu’a da fatan alkairi sannan aka fito dasu. Da motoci uku kacal za’a kai amaren. Motar farko amaren ne a baya sai baba malam da Omar da zaiyi driving. Mota ta biyu iyayene mata na ɓangaren Addah su huɗu, sai yayun Umm biyu, su kuma Malam ƙarami ne zai jasu. Sai motar ƙarshe da Yah Ahmad zai ja ita kuma tsoffin iyaye ne dangin su baba malam a ciki su biyu, sai Umm da momy da amaryar Abba Musbahu. Motar ƙarshe, Abban Abdallah, Abba Musbahu, Abubakar da zai jasu, Uncle Kabeer mahaifin Nasir, sai Uncle Babangida shima dai shaƙiƙinsu ne.
Haka suka fita a jere ana bin amare da addu’ar tafiya a sa’a. Dama mafi yawan ƴan biki na kusa duk sunata guduwa suma. Zuwa goma na dare sai hayaniyar gidan ta ragu sosai, wasu sunyi barci, wasu sun tafi.
★★★

Su baba malam sun fara miƙa Hajarah ne dan itace ƙarama. Gidanta mai ƙyau da tsari a anguwar GRA, kowa ya yaba da addu’ar zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba. Sun sami tarba ta mutuntawa daga dangin ango su bakwai da sukazo tarbar amarya daga can gidan surukan Hajarah. Kasancewar sunsan dokar su baba malam ɗin suma cikinsu harda maza uku. Bayan sun ɗan zauna a falo akai addu’a baba malam ya kama hannun Hajarah har cikin Bedroom ɗinta ya kaita, zaunar da ita yay a bakin gado yay mata addu’a da saka mata albarka. Ya juyo zai tafi ta riƙe hanunsa. Tsayawa yay tare da juyawa jikinsa duk a sanyaye yana dubanta. Haka yake shi, yanada son yara, shiyyasa har ƴayan ƴan uwan nasa ƙaunarsu yake har cikin ɓargonsa. Duk kuma sanda yay irin wannan rakkiyar sai yayi ƙwalla dajin ɗacin rabuwa da yaran nasu ta dalilin aure ƙanin mutuwa.
Hajarah data buɗe fuskarta ta share hawayen dake silalo mata. Cikin dasashshiyar muryarta tace, “Abbah dan ALLAH inason in roƙeka wani abu”. Kansa ya jinjina mata, yace, “Komi kikeso zan miki inhar baifi ƙarfina ba Hajarah, dan haka faɗamin koma miye kinji”. Sake share hawayenta tayi tana jinjina masa kai. “Abbah dan ALLAH idan yah Abdallah yace bazai maida aurensa da su Adawiya ba karku takura masa”. Jimmm baba malam yay yana kallonta. Sai kuma yace, “Uhm Hajarah miyasa kika buƙaci hakan? Bayan kinsan shi ɗin mai laifine”. “Abbah zan faɗa maka dalilina amma ba yanzu ba, dan ALLAH kuyi mani wannan alfarmar, suma su Abba zan kirasu duk na roƙesu har Hajjo”.
Numfashi baba malam ya ɗan sauke, sai kuma yace, “Karki damu zan duba na gani, kibar kukan nan haka karya saki zazzaɓi. ALLAH ya baku zaman lafiya”.
Daga haka ya fita ya barta tana cigaba da rabzar kukanta.
Daga gidan Hajarah saina Kubrah. Itama dai gidan ya haɗu masha ALLAH. Sai dai ita tana da abokiyar zama harda yaranta uku. Amma kowa da sashensa dan gidan babbane. Itama dai an tarbesu da mutuntawa. Baba malam kuma ya rakata har nata ɗakin ya ƙara mata addu’a sannan ya fito suka wuce gida kowa aka barsa da halinsa kuma.

____________________

A ɓangaren Yoohan kam tunda suka baro gidan su baba malam sai ya koma Hotel ɗin da su papa suka yada zango. Babu yanda baba malam baiyiba akan su sauka a ɗaya daga cikin gidajen baƙinsu amma papa ya ƙi fir. Wajen ɗaurin aurenma da yake jirgin 12 suka shigo suna isowa ana idar da sallar juma’a, hakan yasa saida ma aka ɗan jirasu kafin su iso wajen ɗaurin auren daga airport. Yoohan ne kawai yazo tun goma na safe. Bayan an ɗaura auren aka ɗunguma har dasu hall ɗin da su baba malam ɗin suka tanada domin gudanar da walimar cin abinci. Anan akaci aka sha cike da farin ciki. Babu wanda zai kalli baba malam da papa yace akwai wani abu na rashin jituwa a tsakaninsu. Suma su papan sun sake sosai a cikin mutane bazaka taɓa cewa ga daga addini ko ƙabilar da suka fito ba. Musamman ma daya kasance a cikin manyan mutanen ƴan ɗaurin aure akwai waɗanda suke da alaƙa dasu sosai musamman ma ƴan siyasa. Wasuma papan ya sake gayyatarsu bayan gayyatar da baba malam yay musu.
Bayan an kammala walimar ne mafi yawan baƙin suka kama gabansu, su kuma su papa da tawagarsa suka nufi hotel bayan sunƙi amsa tayin baba malam. Hakan yasa yanzun acan Yoohan ya iskosu. Sai dai kasancewar jirgin ƙarfe bakwai da rabi zasu bi zuwa Abuja duk ya iskesu sun fito shi ma suke jira. Basu wani zauna zaman ɓata lokaci ba duk suka shiga motocinsu. zasu kaisu airport ɗinne su dawo su kwana da safe suma su ɗauki hanya. Dama da safe suka taho kafin su papan.
Ko mintuna goma cikakku basuyi da zuwa airport ba jirginsu ya lula birnin tarayya abuja. Inda a canma dai ɗaukarsu akazo akayi. Abokan papa kowa ya nufi gidansa, papa da Gebrail, Richard, Joseph, Godwin, Osin, Uncle Marcel, Uncle Anthony, kuma suka nufi gidan papan. Sai Solomon jelar Yoohan😂.
Sun iske gidan a hargitse da rikicin da suka bari su Mama Debora nayi akan auren Yoohan ɗin. Faɗa mai lasisi sosai akasha tsakanin tsofin biyu. Kuma duk akan sufa basu yarda jikansu ya aure bahaushiya mai salla ba. Momy da papa ya gama sanar mata komai akan manufar auren tanata ƙoƙarin fahimtar da su duk da kuwa jitake kamar tafi kowa shiga tashin hankali, amma sun ƙi fahimta. Sai kiran dangi suke na nesa a waya suna sanar musu. Miracle kam yanke jiki tayi ta faɗi a sume dama tunkan su Yoohan su wuce. Akace kuma ya dubata ya tsallake yay ficewarsa batare daya ko tanka musu ba.
Hakan daya aikatane ya sake fusata kakanninsa sabon wutar bala’i ya ƙara ruruwa. Sai asibiti aka kai mira bayan wucewarsu ɗaurin auren.

Tunda Yoohan ya shigo idonsa ya sauka akan kakannin nasa sai ya sake tsuke fuska fiye da yanda take. Ɗauke kansa yayi ya nufi upstairs duk da yaga yanda suka miƙe zumbur suna kallonsa cike da wutar masifa.
Cikin yare, mama Debora ta shiga ƙwala masa uban kira kai kace gidan zata fasa. Ko waiwayensu baiyiba ya buɗe ƙofarsa ya shige bayan ya amshi babbar rigarsa a hannun Solomon dake biye da shi a tsorace. Ruf ya rufe ƙofar ya murza mata key yama barshi a ciki dan kar wani yay tunanin amfani da wani key ɗin.
A falo ya zube yana sauke numfashi da jan dogon tsaki. Jin an fara buga ƙofar tasa da ƙarfi ana masifa ya kuma jan wani tsakin ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa. Bai zaunaba anan, kayansa dake ta zuba ƙamshinsa dana Nu’aymah ya cire yanata faman lumshe idanu. Dan a matuƙar gajiye yake. Babu abinda yake buƙata a yanzu sama da kwanciya. Ya gaji harma baisan tataya zai faɗa ba a tausaya masa. Ga ihun su Mama debora da yake jiyowa sama-sama yana neman saka masa ciwon kai. ‘Nasan maganinku ai. Kwanan nan zaku bar gidan nan ku koma inda kuka fito’. Ya faɗa a fili yana harar ƙofar kamar sune wajen tsaye.
Daga haka ya shiga yay wankansa kamar yanda ya saba. Ya jima bai fitoba daga bayin kamar mai naƙuda🙄😏. Sai kuma gashi ya fito a yanayin gajiyar da yake ciki. Sama-sama yay shirin barci cikin tausasan kayan barci, yana fesa turare wayarsa tai ring. Kallon wayar yay, ganin Richard ne sai ya basar ya cigaba da hidimarsa. Sai da Rich ya sake kira bayan ta katse sannan ya ɗaga. A dakile yace, “Kana damuna fa”. A fusace daga can shima Richard yace, “An damekan, shine dan tsabar wulaƙanci ka wani kullema mutane ɗaki? Da ace babu wasu ɗakunan ina kake tunanin zamuje mu kwanta?”.
“Oho muku” Ya faɗa a taƙaice da yare.
“Zakace oho kuwa tunda mun gama maka wahala, mtsoww! Ka wani saka mutane zuwa cikin…..” Katse wayar Yoohan yayi batare da ya bari Richard ya ƙarasa ba. Ya taɓe bakinsa yana cilla wayar saman gado. Yanaji Rich ya sake kira bai kulaba. Sai da ya kammala shirinsa tsaf yay sallar magriba da isha’i da shafa’i da wutiri da addu’oinsa sannan ya mike ya haye gadon. Wayarsa daya cillar gefe ya ɗauka. Number baba malam ya lalubo yay dailing. Ring uku kuwa ya ɗaga.
Tamkar Yoohan yana gabansa haka ya risina cikin girmamawa yana gaishesa. Daga can kuwa baba malam na amsa masa da kulawa.
“Abba mun iso babu jumawa. Ina fatan jikin nata babu wani matsala zuwa yanzun?”.
Murmushi baba malam yayi da duban Nu’aymah da Umm ta gama canjama kaya zuwa na barci. Ya ɗauke kansa yana sauke numfashi. “Alhmdllh Yahya. ALLAH ya huta gajiya, ya kuma saka albarka. Dama yanzun nan muka gama waya da baban naka shima ya kira ya sanarmin isar taku. Mamana kuwa har yanzu barci ma take batako farkaba tun bayan allurar”.
Sassanyan murmushi Yoohan yayi babu shiri, yace, “Alhmdllh Uncle, insha ALLAH zuwa da safe zata farka normal, ALLAH ya ƙara lafiya. Bara na barka ka kwanta sai da safe”.
“To Yahya ALLAH ya huta gajiya”.

Daga haka sukai sallama. Baya yay ya kwanta ƙafafunsa a ƙasa yay filo da hannayensa. Idanunsa ya lumshe a hankali ya faɗa duniyar tunanin da shi kaɗai yasan akan abinda yake yi.

__________★★★★_________

*_To masu karatu sace shin ina Abdallah da Nasir😱🤗?._*

Tam nima dai tsayawar wannan tambayar a raina ce taja ra’ayina shiga bulayin nemansu a cikin gidansu Nu’aymah. Sai dai na karaɗe ko ina da ina tsaf babusu babu mai kama da su ɗin. Sai acan bakin su Omar dana tsinkayi yana faɗama Momynsu yanda ɗaurin auren ya kasance naji.
Ashe faɗan da Abdallah da Naser suka tafka ne a daren shekaran jiya daya bama kowa tsoro yajawo su baba malam canja shawara akan zaɓin Nu’aymah. Ananah da hajjo sukai dogon nazari da shawarar canja komai. Dan yanda abubuwan ke nan canja salo tabbas zumincinsu zai iya girgiza akan matsalar Naseer da Abdallah. Dan haka suka kira su baba malam a wannan daren tare da Abban Naseer daya iso suka tattauna. Abban Nasir shine ya bada shawarar hana Abdallah da Nasir gaba ɗaya. Ya kuma bada shawarar aurama Yoohan kamar yanda ya bukata dan a samu zaman lafiya. Hakan zai kawo masalahar Abdallah ya maida matansa. Nasir kuma yaje ya auri wata.
Kowa yayi na’am da wannan tunani na Abban Naser. Babu ɓata lokaci ko jinkiri suka kira Yoohan suka sanar masa. Yoohan kuma bai ɓata lokaci ba wajen sanarma papa. Sai dai yayi matuƙar mamakin ganin yanda Papa ya bashi goyon baya babu wani ja inja ko ƙalubalantar lamarin, ya kuma gargaɗesa karya sanarma Momynsa (Madam Chioma😸) shi zai sanar mata.
A wannan daren papa ya bada akai masa invitation na layin waya aka turama duk wanda yake da buƙatar gani a wajen ɗaurin auren ɗan nasa. Washe gari kuma ya ƙarasa dukan kai kawo da yake buƙata tare da bincikar duk yanda al’adar auren hausawa yake. Duk abinda ake buƙata sai da papa ya saya aka shiryasu a mota.

Anan kuwa kano su Abdallah basusan wace wainar ake toyawa ba. Kowannensu dai ya ɗauki alwashi akan ɗan uwansa tsakanin shi da Nasir. Hakan yasa sukaje ɗaurin auren kamar kowa cikin kwalliya ta musamman. Sai dai kuma ganin Yoohan da tawagar ƴan uwansa da abokai ya basu matuƙar mamaki. Gashi waje ya ƙure balle su tambayi iyayen nasu. Basu fita daga ruɗanin ganin Yoohan ba aka fara ɗaurin auren. An fara ɗaura na Kubrah da angonta Al-ameen yuseef durɓi, sai Hajarah da angonta Dawood Sulaiman Rano. Naseer na jiran yaji shi da Nu’aymah sai yaji Zainab Sooraj Hashim jibiya da Yahya Goshpower”.
Turƙashi zance ya girma. Ba Nasir kawaiba ne a ruɗani, Abdallah kansa hajijiya yaji tana ɗibarsa. Hakan yasa Omar dake kusa da shi ya taimaka masa suka fito daga cikin hayaniyar ya kaisa mota. Shima acan Nasir sai Ahmad ne ya kamashi ya fito da shi. Sun koma sanarma su baba malam, Abdallah ya tada motar da Omar ya sakashi ciki ya bar wajen batare da kowa ya sani ba. Nasir kam da ƙafa ya bar wajen shima a birkice.
Daga wannan tafiyar ne har yanzu babu wanda yasan ina suke. Su baba malam sunyi neman a waya harsun gaji. Dan duk wayoyinsu a kashe suke. Halin da suka ahigo suka iske Nu’aymah a gidane ya sakasu yin shiru da zancen rashin su Abdallah ga kowa. Duk da kuwa Hajjo nata tambayarsu bataga Abdallah da Nasir ba.

WASHE GARI……….✍

 

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply