Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 44


Saran Boye 44
Viral

No. 44

……….WASHE GARI normal Nu’aymah ta tashi kamar yanda kowa yay fata. Sai dai rashin ƙarfin jiki da damuwar maganar auren da ta sake tabbatar an ɗaura mata shi. Dan bayan baba malam ya dawo daga massallaci zaunar da ita yay ya ringa mata nasiha mai ratsa jiki da ɓargo. Tun tana hawayen zuci, harta koma na zahiri. Hawaye suka dinga kwarara mata daga ido suna sauka saman fuska.
Fuskar baba malam ɗauke da murmushi ya kai hannu ya share mata hayen. Ya kamo hannayenta duka cikin nashi yana sake kwantar mata da hankali. “Kukan ya isa haka kinji mamana. Duk abinda kikaga ya shigo cikin rayuwarki saɓanin tunaninki ki ɗauka hakan shine mafi alkairi a gareki. Idan kuma har kika rasa abinda ke shine burinki da fatanki, ki saka a ranki UBANGIJI bai baki shi bane saboda ba naki bane, hanakin kuma shine yafi alkairi. Akwai abubuwa da yawa dana san suna damunki a cikin rai. Amma inason ki ɗaukesu ki watsar da su acan nesa, ki kuma manta da su ki shafe babinsu a tunaninki. Dan jiyanki ta wuce, kina cikin yau ɗinki ne. Kinga yafi kamata ki maida hankali wajen hangen gobenki. ALLAH yay miki albarka. Ya yaye miki damuwarki. Ya share hawayenki. Yay riƙo da hannunki. Yay miki jagora a gobenki da jibinki”.
“Amin Abbah na gode, ALLAH ya ƙara maka lafiya da tsahon rai”.
“Amin mamana nima na gode. Kije ki kwanta ki sake hutawa kinji. Sai dai ki zama cikin shiri dan zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu kema za a miƙaki gidan mijinki”.
Kanta kawai ta ɗaga masa. kamar zata tambayesa waye mijin nata sai kuma tayi shiru. Ɗago idanunta dake jajur tai ta kallesa. Muryarta na rawa tace, “Abba dan ALLAH ka yafemin dukan abinda kake ganin na maka a sanina ko saɓanin haka. Sannan wlhy kaji na rantse ban aikata abinda likitocin nan suka tabbatar ba. Abinda ke a cikin hotunan nan kuma ya farune bisa ƙaddara……..”
Duk abinda ya faru a waɗan nan ranakun biyu sai da Nu’aymah ta sanarma baba malam. hatta da farkon haɗuwarta da Yoohan. Sosai baba malam ya gamsu da dukan bayaninta. Dan duk abinda Yoohan ya faɗa shine ta maimaita. Inda sukai saɓani kawai shine ita tana ganin da gangan ya aikata mata. Shi kuma ya sanar dasu baba malam duk akan taimakonta zata faɗi komai ya faru. Ya san Nu’aymah tun tana yarinyarta da wahala kaji tamaka ƙarya akan abu. Koda kuwa za’a daketa idan tai laifi aka tambayeta saita faɗa.
“Na yarda da ke Mamana. Insha ALLAHU kuma zamu ƙara sanin gaskiyar daga ina zancen ya fito. Dan wasu kalaman mijinki akan maganarnan suna nan tsaye bisa ƙwalwata ina musu fashin baƙi a hankali. Kuma lallai da gaske na fara ganin haske a ciki”.
“Abba na gode daka fahimceni”. Ta faɗa tana kuka da dariya lokaci ɗaya. Shima Murmushin ya keyi cike da tausayinta. Daga haka suka fara cin abincin da Umm ta shirya masa na breakfast shi da ita. Tana bashi a baki shima yana bata abin sha’awa.
Janyewa inuwar dake jikin windown tayi, baba malam da sai yanzu ya farga yay tsai yana kallon jikin Window ɗin cike da mamaki da al’ajabi. Sai dai kuma a zahiri ya maida hankalinsa ga Aymah ne. Daga can wani gefe na zuciyarsa yace, ‘Taya zakai zargin an muku laɓe ne bayan gidan cike yake da baƙi. Maybe wanine ke wani abu a wajen dai’. Ɗari bisa ɗari ya gamsu da hakan har cikin ransa. dan haka ya sake maida hankalinsa ga ɗiyarsa da tausayinta ke cike taf da ransa.

Bayan baba malam ya shirya ya fita Nu’aymah ta koma sashen Umm. Ƙannen Umm ɗin da yayunta duk suna nan. Breakfast ma sukeyi. Sai wasu daga ƴan uwan Adda da suma anan suka kwana. Cike da jin daɗin ganinta ras duk suke kallonta. Ta risini ta gaidasu. Daga haka ta fito sashen hajjo. Nanma sunyi farin cikin ganin ta tashi lafiya kamar ba ita ba. Gaishe da baƙin dake a sashen tayi sannan ta shige bedroom ɗin hajjo. Acan tai wankanta tsaf, Yusrah data shigo taje ta amso mata kaya. Bayan ta shirya tare da Yusrahn suka fito. Hakan yayi dai-dai da shigowar Adawiya falon hannunta ɗauke da bokiti ruwan goro.
Tunda sukazo ƙasar wannan shine gani na uku da Aymah tai mata. Adawiyan duk ta rame, tayi duhu kamar ba itace sukazo tayi ɗam da ita kamar zata fashe ba dan ƙyau. Ɗauke kanta tayi tamkar bataga Aymah da Yusrah ɗinba. Ta ƙarasa gaban Ananah ta ajiye bokitin tana faɗin, “Ananah gashi inji Addah na ƴan katsina ne da zasu wuce yau”.
“To. To masha ALLAH, ALLAH ya sanya alkairi yasa albarka. Kice mata angode ALLAH yayi albarka”.
“Amin” ta faɗa tana ƙoƙarin gitta su Nu’aymah zata fice. Murmushi Aymah tayi, tare da cewa, “Adawiya an tashi lafiya?”. Da mamaki Adawiya ta juyo ta kalli Nu’aymah. Kamar bazata amsaba sai kuma tace, “Alhmdllh”. Daga haka ta fice abinta.
Yusrah tace, “Humm ALLAH ya ƙyauta. Wlhy lamarin Adawiya har mamaki yake bani Aymah. Ita yanzu dai abinda take nunawa ta raba zuminci damu. Nifa tunda sukazo ƙasarnan batamin magana. Idan na mata kuma saita amsani kamar wata kashi. Koda yake kema da kuka shaƙu da ita fiye da kowa tana ɗaga miki hanci bare mu”.
Murmushi kawai Aymah tayi, amma batace komaiba. Daga Ananah har hajjo duk suna jinsu suma. Amma sai sukai kamar basujinba.

An ƙarasa gudanar da shagalin biki yau. Zuwa bayan azhar sukaje gidan amare akai buɗan kai. duk baƙi masu tafiya daga can suka kama gabansu. Sai ɗai ɗai kune suka dawo nan gidan waɗanda su sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Nu’aymah dai tana gida bataje ko inaba. Cikin ranta kam fal damuwa dason sanin wanene ita aka ɗaura mata aure da shi?. Anya kuwa Naser ne datai fata? A ganinta idan shine yaci ace ta gansa ai. Amma tunda ta tashi daga Naseer har Abdallah bataga kowa ba a cikinsu. Kuma duk sauran samarin gidan ta gansu.

_________★★★★_________

*_FCT ABUJA_*

A birnin tarayya kam taƙaddama ake bugawa sosai tsakanin Yoohan da kakanninsa. Harma da wasu a cikin ƴan uwansa da suke nuna borensu akan auro Nu’aymah da yayi. Hayaniyarsu da haukarsu duk bata damesa ba. Yamayi kunnen uwar shegu da su tamkar baiji akan mi sukeyi ba. Babban tashin hankalinsa da damuwarsa kawai halin da Momynsa ke a ciki.
Dan tun daren jiya jininta ya hau sama sosai saida ya danna mata allurar barci, har kuma yanzun bata farka ba saboda mai ƙarfi sosai yay mata. Su Richard ne kawai da suma suka so tasashi gaba da magana akan auren yay azamar taka musu burki. Dukansu sunsan halinsa, idan rashin mutuncinne da buyagi duk ya fisu iyawa. Sannan suma ɗin kowanne allazi da nasa amanu ai. Kuma babu wanda sirrinsa ba’a tafin hanunsa yake ba. Haƙuri suka bashi akan masa katsalandan ɗin da sukayi. Suka kuma nuna masa zasu basa goyen baya tunda yana son matarsa.
Uffan baice da su ba daga haka. Su kuma duk suka tashi suka fice suka barsa. Fita sukai daga gidan duka, sai da sukasha gulmarsu iya iyawa a waje kafin su tattauna akan shagalin biki da suke son shirya masa tunda auren nasa yazo musu da salo na daban ba irin nasu ba.

A cikin gida ma bayan su mama Debora sun turza sun turza akan Yoohan ɗin sunga babu mafita sai suka sakko dan kansu akan zasu amince da auren, sai dai da sharaɗin duk sun dawo da zama gidan papa. dolene kuma Nu’aymah ta zauna itama a gidan Yoohan bazai kaita ko ina ba.
Sai dai a mamakinsu sai sukaga Yoohan yayi murmushi tare da lumshe idanunsa ya buɗe a kansu. Sai da yay musu kallon tsaf na wasu mintuna kafin ya miƙe cike da basarwa yace, “Na amince”. A ransa kuwa dariya ya tafi yana musu, dan yasan indai nu’aymah ce sun sami dai-dai dasu.
Kusan duk a tare sukai wata irin zabura. Dan sam sun zata zaice bai yardaba su kuma su sake tada wani billin. Sai gashi sunga saɓanin tunaninsu. Kafin su gama dawowa hayyacinsu ya dawo falon ɗauke da takarda.  A tebirin dake tsakkiyar falon ya ajiyeta. Ya bisu da kallo fuska a murtuke yana faɗin, “Wannan takarda ce ta agreement tsakanina da ku. Zaku cigaba da zama a gidan nan, matata ma zata zauna. Sai dai da sharaɗin duk randa na kama wani da laifin mata koda maganar banza a cikinku ko cikin yaranku sai mutum yabar gidan nan koda ace kuwa cikin su Gebrail ne. Itama kuma na muku alƙawarin bazata shiga rayuwarku ba bayan mutuntawa da girmamaku”.
Cike da wani mamakin suke kallonsa. Zasuyi magana papa yay saurin faɗin, “Wannan tsarin na John yayi dai-dai. Dan shine zai kawo mana masalaha da kwanciyar hankali a zuri’ar mu. Mukuma sake tabbatar da kowannenmu nada ƴancin aikata abinda bai saɓamana ba”.
Babu wanda ya iya sake cewa komai. Sai singing ɗin da Yoohan ya fara yi ya basu suma duk sukayi. Ɗaya ya ɗauka ya basu ɗaya. Ɗayan copy ɗin kuma da aka saka cikin frame ya nufi bangon falon daga kusurwar d/table ya kafesa jikin ginshiƙin wajen daya zama kwalliya.
Wannan abu da Yoohan ɗin yayi ya kuma girgiza su matuƙa. Gashi babu damar magana dan ya tsuke fuskar fiye da ɗazun.

Wannan takardar Agreement itace ta zama makullun rufe bakin duk wanda keda ƙarfin faɗa a ji a family ɗin su Yoohan. Sai ma zaman shirya biki sukai dan nuna bajintarsu ga gudan jininsu tamkar yanda akema kowa.
Shi dai Yoohan bai tanka kowa a cikinsu ba akan shirin bikin, ranarma yini yayi a asibiti shi da Richard. Basu dawo ba sai dare. Gajiyar da sukayi ce ta sakasu ko zaman hira basuyi ba Yoohan ya shige sashensa. yau ma tsabar wulaƙanci hana su Rich shiga yayi. da sukai magana yace shi yanzu yayi aure baya buƙatar su a sashensa. Suje can su ƙarata a sashen baƙi suyita loda kwalaben barasarsu.
Aiko sun hayayyaƙo masa tamkar zasu cinyesa. Ya fice yana murmushi bayan ya musu gwalo.

______★★★_______

*_KANO_*

A kano kam tunda garin ALLAH ya waye yau da shirye-shiryen tahowar su Nu’aymah aka tashi. Dan zasu taho abuja gidan su Abdallah. washe gari sai a miƙata ɗakin mijinta daga nan gidan. Saboda ma baba malam baya buƙatar ayi wata gayya jirgi zasu biyo.
Jin abuja zasu wuto yasa Nu’aymah fara tunanin ko dai yah Ab aka ɗaura mata aure da shi? Ko burinsu na mallakar juna ya tabbata ne? To amma idan har hakane mizaisa a ringa ɓoye mata?. Har yanzu babu wanda ya sanar mata wanene mijinta. sai dai kowa na zaunar da ita yay mata nasiha dai-dai gwargwadon saninsa. Haka ne yasa yau taci kuka harta godema UBANGIJI. Mai ƙunshi ma da Addah tasa aka kawo da ƙyar Aymah ta yarda akai mata. Hakama da za’a kaita gyaran jiki sai da baba malan ya saka baki wajen lallashinta sannan ta amince. Ai ko sai gata tayi ɗas tamkar ka saceta ga gudu. ƴar ramar da tayi saita sake ƙara fiddo mata da ƙyawunta da haskenta. Sai dai a kallo ɗaya kaɗai ya isa ka tausaya mata duk tayo laushi kamar ba Nu’aymah tsiwa ba. Duk ta zama shiru-shiru, ta kuma nanema Umm taƙi barinta sukuni.
Lokacin da aka idar da sallar la’asar Ananah tazo har sashensu tajata dan taje a kimtsata tunda jirgin 5:30pm zasu bi saita saka musu sabon rikici. Babu wanda bai lallasheta ba amma taƙi tai shiru. Sai da baba malam ya fito yay mata jan ido da nuna mata ɓacin ransa sannan. Aiko tana kuka tana sharɓar hawaye. Koda ta fito ma sai Aunty Kulu yayar Naser ce tai mata kwalliya ka ɗan dukda kuwa ba wai gidan su Yoohan ɗin zata sauka kai tsaye ba.
Tsaf ta sakata ta shirya cikin atamfa lass ƴar ubansu, ɗinkin zani da riga. Kasancewar atamfar baƙa ce da kwalliyar golden sai tai bala’in zama mata a jiki tamkar ka saceta ka gudu.
Iyayenta sun sake taruwa a kanta sun mata nasiha da gargaɗi mai faɗi akan rayuwar da zata fuskanta ta aure mai cike da ƙalubale. Dan aure ibadane. Ita kuma ibada a koda yaushe tana a cike ne da jarabawa kala-kala. Daga haka aka miƙata wajen Umm tai mata sallama. Ba Umm da Nu’aymah kawaiba, hatta duk wanda ke a wajen sai da ya matse hawayen tausayinsu. Da ƙyar aka ɓanbare Aymah jikin Umm. Hakama Muhammad dake taya yayar tasa kuka abin tausayi. Daga haka aka kaita kowane sashe tai musu sallama sannan aka shiga da ita ɗaya daga cikin motocin da zasu musu takkiya zuwa airport. Abban Abdallah da duka yaransa duk sun fito dansu daga haka zasu koma kenan sai kuma anyi hutun makaranta. Sai matan Abba Musbahu duka biyu da zasu mata rakkiya. Sai Ananah da Aunty Kulu. Aunty Aysha, Sai ƙanen Umm biyu da yayarta ɗaya. Sai Yusrah da Adawiya da taso tirjewa bazataje ba. Sai da Hajjo ta zageta tas sama da ƙasa sannan ta yarda da binsu badan taso ba. Sai Nanah, da Rufaidah autar su Naser.

Tunda motocin suka ɗauki hanyar airport Aymah ta kwantar da kanta jikin Aunty Hibbah ta cigaba da raira kukanta a hankali. Aunty Hibbah dai nata shafa bayanta cike da lallashi amma batace uffanba.
Basu wani ɓata lokaci ba a airport ɗin jirginsu ya ɗaga zuwa Abuja. Tafiyar mintuna ƙalilan kuwa ta kaisu. Anan ɗinma dai tarbarsu akazo akayi, daga gani dai daga company ɗinsu ne masu tarbar. Zuwa yanzun jikin Nu’aymah yayi zafi zau da zazzaɓi, hakan yasa suna isa Momy ta kama hanunta zuwa ɗakinta, sai da ta sakata tai sallar magriba da aketayi lokacin da suke shigowa gida, tana idarwa ta haye gado ta kwanta Momy ta lulluɓa mata bargo saboda rawar sanyin da taketa faman yi.
Ganin yanda rawar sanyin nata ke ƙaruwa Momy taje ta sanarma Abban su Abdallah dake shirin fita massallaci sallar isha’i. Biyota yay suka dawo ɗakin tare. Shima sai hankalinsa ya tashi jin yanda jikin Aymah yay masifar zafi. Ga rawar sanyin na ƙaruwa harma tana roƙon a ƙara mata wani bargon.
“Khadijah inaga bara na dawo masallaci sai a kira Yahya zaifi, dan yayi gargaɗin bata magani kai tsaye. Nasan yanzu kuma a duk inda yake yana ƙoƙarin yin sallar isha’i ne tunda kiji gashi can za’a tayar”.
“Eh gaskiya, hakan zaifi Abbansu. Bara nayi sallar nima kafin ku shigo”.

Bayan an idar da sallar isha’i Abba ya shigo gida. Kai tsaye waya ya ɗauka yay kiran Yoohan. Sai dai harta katse bai ɗaga ba. Ya sake kira nanma bai ɗaga ba. Ajiye wayar yayi yana faɗin, “Maybe baya kusa. Amma idan ya gani nasan zai kira”. Kai Momy ta jinjina masa kawai.

A lokacin da Abbah ke kiran wayar Yoohan yana massallaci, wayar kuma na mota, dan suna wani hotel tun kafin magriba shi da su Joseph akan dinner ɗin da za’a gudanar gobe idan ALLAH ya kaimu bayan kawo amarya. koda ya fito kuma wajen nasu ya koma dan dama yace musu ne kawai yana zuwa, sukuma tsare-tsaren da sukeyi ya ɗauke hankalinsu basubi ta kansa ba akan inda zaije ɗin.
Kujerar daya tashi ya ja ya zauna yana harar Osin da aka ajiyema kwalbar giya da yayi oda. Bai dai ce komaiba, sai Osin ɗinne yay murmushi yana faɗin, “Duk iya hararka dai ba ƙinsha zan ba. Kaima koda ɗura gobe sai ka shata domin farin ciki, koba komai kaji daɗin cin soyayyarka da amryarka”. Dariya suka kwashe da ita gaba ɗaya. Richard yace, “No, bazai shaba a wajen dinner sai ya koma gida, so kake y……” bammm kakeji Yoohan ya dokema Rich baki da bayan hannu kafin ya karasa faɗa. Aiko mizasuyi inba dariya ba. Tsabar mugunta Godwin har faɗuwa yake ƙasan korayen ciyayin da akaima wajen shimfiɗa da su. Richard daya ɓata fuska yace, “Mr X da zafi fa”. “So..” Yoohan ya faɗa a wani salo yana ɗage kafaɗa.
“Aiko na rantse sai kaji a jikinka yau” Rich ya faɗa yana rarumo kwalbar giyar da Osin bai kai ga buɗewa ba. Da gudu Yoohan ya tashi yana dariya shima saboda yasan mi Richard ke shirin aikata masa. (a karan farko dana taɓa ganin dariyarsa mai faɗi irin haka). Suma gaba ɗaya dariyar sukeyi, dan Rich bin Yoohan ɗin yayi shima da gudu. Mota Yoohan ya buɗe ya shige ya saka lock yana yima Rich dake ƙoƙarin ganin ƙofar ta buɗe daƙƙuwa. Da ɗan ƙarfi yace, “Stupid boy”. “Same to you”. Shima Rich ya faɗa yana masa daƙƙuwar.
Gwalo Yoohan ya sake masa yana ƙoƙarin ɗaukar wayarsa dake haske. Da mamaki yake kallon sunan wanda yay kiransa har 3missed call. Bai kula Rich dake masa knocking glass ba ya shiga ƙoƙarin dailing Number Abban Abdallah.
Bugu biyu kuwa ya ɗaga. Kamar yanda yake gaida baba malam da girmamawa haka ya gaida Abbah. Shima Abba sai ya amsa da kulawa, sannan yayma Yoohan ɗin bayanin abinda ke faruwa. Ɗan lumshe idanunsa yayi ya buɗe a hankali tare da kwanciya jikin kujera. “Uncle bara nazo na dubata kawai”.
Cikin jin daɗi Abba yace, “To shikenan ALLAH ya kawoka lafiya. Ai kana da address ɗin gidan ko?”.
“Eh Uncle inada”.
Daga haka suka yanke wayar. Glass ɗin motar ya sauke yana kallon Rich da ke jiransa ya kammala wayar. Da ƴar damuwa yace, “Sorry Rich ina zuwa, bazan jimaba insha ALLAH ku cigaba kawai”.
Richard yace, “Lafiya dai ko?”.
“No, babu damuwa dear, wani ɗan uzirine idan na dawo zan maka bayani”.
“Ban yardaba gaskiya muje tare kawai”. Richard ya faɗa yana buɗe motar ya shigo shima.
Yoohan ɗin baice da shi komaiba, sai waya daya ɗauka yay kiran Godwin, yana ɗagawa yace, “G-boy muna zuwa Please, just 30minutes”. “Okay no prob..” ya amsa masa da salon iya shege na gayu.
Motar ya tada suka fice daga hotel ɗin. Yanda yake driving ɗin a hankaline ya sa Rich faɗin, “X-man are you ok?”. Ɗan murmushi Yoohan yayi kawai bai ce komaiba.

Tafiyar mintuna ƙalilance ta kawosu gidan. Sun iske Omar tsaye a bakin gate da alama zuwan nasu yake jira. har ciki Yoohan ya shiga da motar. Da ga shi har Rich bin gidan suke da kallo dan kuwa ya haɗu. A ransa kuwa ayyanawa yake lallai su baba malam sunada ƙuɗi. Sai dai sun iya takunsu dan basu da fariyya akan ni’imar da ALLAH ya basu.
Ƙofar da zata sadasu da cikin gidan suka nufa. Omar na gaba suna biye da shi, shi dai Rich ransa fal mamaki dan baisan ina suka zo ba. Su Aunty Hibbah na baje a falo zasuci abincin da Omar ɗin ya fita yayo musu takeaway suka shiga da sallama.  Cikin girmamawa Yoohan da yay musu kallo ɗaya yay ƙasa da kansa ya shiga gaishesu. Hakan yasa shima Richard da ke binsu da kallon tsaf ya gaida su. Daga haka suka wuce falon Abba dake zaman jiransu.

Aunty Aysha ce tai ƴar dariya bayan shigewar su Yoohan. Duk kallonta sukai na alamar tambaya. Tace, “Wannan angon namu dai akwai kunya, abokinsa yay mana ƙuri da idanu, amma shi ya kasa kallon ko sashen da muke”. Aunty hibbah ta karɓe da cewa. “Sai kace jinin hausawa, inma ba faɗa maka akaiba bazaka taɓa cewa ba bahaushe bane wlhy. Musamman wanda yasan yanda ƙabilun nan suke da shegen tsaurin ido”.
Haka suka cigaba da hirarsu ƙasa-ƙasa akan Yoohan. Har Umm tazo ta wuce ta fito da Aymah zuwa falon Abbah basu lura ba. Adawiya ce kawai da Amal babu a falon. Adawiya dai ƙin fitowa tai, tunda suka iso gidan ta shige ɗakin Amal bata sake leƙo waje ba. Amal kuwa kanta ke ciwo shiyyasa tasha magani ta kwanta tana idar da sallar isha’i.

Tunda Momy dake riƙe da Aymah data langaɓe mata a jiki tai sallama duk suka ɗago kansu. A hankali Richard ya furta ‘Woow kaga wata ƙyaƙyƙyawar halitta’. Akan laɓɓansa ba tare da kowa ya jisa ba. Dan Yoohan ma dake kusa da shi zaune hankalinsa gaba ɗaya akan Aymah data takure cikin kujerar da Momy ta ajiyeta ya ke. Cikin rawar sanyi tace, “Momy Please ki bani bargo sanyi”.
Kafin Momy tai magana Abba dake kallonta da tausayawa ya duba Omar da shima duk yay wani iri da tausayin ƙanwar tasa. “Omar kaga rage gudun ac nan”. Da sauri yace, “To Abba” yana ɗaukar remote ɗin.
Murya ƙasa-ƙasa Rich ya cema Yoohan, “X-man who is she?”.
Fuska Yoohan ya ɗan tsuke tare da ɗauke kansa batare da ya bama Rich amsa ba, saima maida hankalinsa yayi ga Abba da ke faɗin ga Nu’aymah ɗin nan. Yana gama faɗa ya bar falon Momy biye da shi. Har Omar ya juya zai fita shima Yoohan yace, “Excuse me Fharook”.  Dawowa Omar yayi fuska ɗauke da murmushi yace, “Yayah kana buƙatar wani abu ne?”.
Ɗan murmushin kaɗan shima Yoohan yayi, yace, “Kaɗan samo mata tea tasha first”.
Kai Omar ya gyaɗa ya fita.
Yana fita Rich ya bugi kafaɗar Yoohan da yare yace. “Kaifa banza ne! Ina tambayarka kana basar dani. Ina ka kawomu nan, gidan ƙyawawan mutane wai?!”.
Dariya yaba Yoohan, amma sai ya gimtse bai yiba. Da gatse yace, “Gidan kidnappers ne” tare da zuba masa harara. Hakan yayi dai-dai da dawowar Omar falon ɗauke da ƙaramin tire an ɗoro mug dake ta turiri………….✍

 

ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

 

I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply