Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 48


Saran Boye 48
Viral

No. 48

…………..Kallo ɗaya tai masa ta kauda kanta. Dan daga shi sai wando gajere fari dako cinyoyinsa bai gama rufewa ba. Sai singlet kalar gwaiduwar ƙwai hannunta mai faɗi fiye dana singlet data sani. Shikam dai kansa tsaye yake ƙare mata kallo cikin kayan barcin wando da riga pink masu taushi. Duk da basu kama mata jiki ba sun mata ƙyau, musamman daya kasance kanta ko hula babu. Gashin dake a ɗaure a tsakkiya duk ya zazzame a gaba ya tashi.
Cike da ƙosawa da kallon ƙurillar da yake matan tace, “Good morning”. Kamar dama abinda yake jira kenan. Ya janye idanunsa daga kanta yana sakin handle ɗin ƙofar da faɗin, “How are you feeling now?”. “Alhmdllh”. Ta amsa dai-dai lokacin da yake tura glass ɗin dake bangon kudu a falon ƙofa ta bayyana. Ita duk zatonta ma an sakashine kawai domin ado. Amma sai taga ya shige ƙofar ta koma da kanta ta rufe. Shiru tayi tana ta kallon wajen kamar wata sokuwa…….
“Good Morning Maa!”.
Aka faɗa a bayanta. Da sauri ta juyo danjin muryar gardi. Solomon dake ta wani ɓata fuska yay saurin sunkuyar da kansa ƙasa bayan ya gama ƙare mata kallo tun shigowarsa. Wani irin mugun takaicine ya turnuƙe Nu’aymah, taya ƙaton banza da shi zai shigo musu babu wani neman izini. Lallai dolene ta saitama ma’aikatan gidan nan zama, dan bazata ɗauki wannan iskancin ba sam. Da ƙyar ta iya haɗiye bala’in dake a harshenta. Murya a daƙile tace, “Ince dai lafiya?”. “Yes maa! Zanyi sharane. Dan nine mai yima oga gyara”. ‘Zan saita muku layi kai da ogan ai’ ta faɗa da hausa tana zuba masa harara kamar idanunta zasu faɗo. Shi dai Solomon bai ji mita faɗa ba, amma yana kallon harar da take zuba masa. Kuma harga ALLAH sai yaji wani irin shakkarta da ganin ta cika masa idanu da kwarjininta duk da kuwa inda aure yayi sai ya haifi wadda ta fita ma.
“Kaje bana buƙatar sake ganinka ka shigo mani nan, ka ajiye min kayan sharan hannuna zai iya yin komai”.
“Okay maa! I’m sorry”.
Banza tai masa, sai harar da taketa cigaba da antaya masa hannayenta riƙe da ƙugunta kamar mai shirin yin dambe. Kamar walƙiya Solo yabar falon. Ta dafe goshi cike da takaici. ‘Shegu dangin ƴan sama jannati, duk saina muku sabon kaciya tunda idonku bai iya daina kallon mutane. Yanda kasan mayu, suyi maka ƙuri da idanu’.
Haka taita banbamin jaraba ita ɗaya kamar wata zararriya. Ta gyara falon tsaf harma kitchen da ba komai aka taɓa yi aciki ba. Ta kwaso turarenta na ƙamshi haɗin da miss xoxo tai mata ta baje ko’ina da su, (Da gaske masoya, duk mai buƙatar turarurrukan su khumrah da makamantansu ya tuntuɓemu zai samu. Kuma a kowane gari kake muna aika kayanmu insha ALLAH) sannan ta ɗora da Air Fresheners ɗin data gani. Yanda gidan ke tashin ƙamshi tuni zai saka ka barci baka shirya yi ba. Yunwan da takejine ya sakata nufar inda taga an shirya kayan tea cikin wata drawer glass dake a dining ɗin. Sai da ta gama ƙarema kayan shayin kallo da su biscuits dake ciki kala-kala, sai su cornflakes, gyaɗa soyayya a cikin kwalabe, dabino, zuma, kayan ciye-ciye ne dai iri-iri wasuma ko ganinsu bata taɓa yiba. ‘Oh ALLAH, amma guy ɗinnan mugun makwaɗaici ne yasin. Kaga yanda ya haɗa kayan ƙwalama kamar wani sa’an Muhammad. Amma dai anji jiki yasin’. Tana mita tana zagurar waɗanda ta gani a buɗe tana jefawa a baki (makwadaitan sun ƙaru kenan😂lol).

★★

Sosai Solomon yaji zafin abinda Aymah tayi masa, ya kuma ɗauki alwashin sai ya saita ta a layi duk da matar ogansa ce. Da wannan takaicin yaje kitchen ya amshi tatattun kayan itatuwan Yoohan ɗin a wajen Blessing data kammala haɗawa. Ta waccan ƙofar yabi ya shiga Gym ɗin. Inda ya tarar Yoohan ko rabin motsa jikinma baiyi ba. “Good Morning sir”. Ya faɗa ransa har yanzu najin zafin Aymah. “Morning?”. Yoohan ya amsa masa yana dubansa da tunanin ko baida lafiya ne. Yanzun ma cike da ɗacin murya yace, “I’m Good sir”. Komai Yoohan bai kuma ce masa ba. Ya cigaba da harkokin gabansa har ya kai lokacin da yake tsayawa. Towel Solo ya miko masa. Amsa yay yana furzar da huci ya ƙarasa kujerar zamansa ya zauna. Solomon ya karaso ya miƙa masa juice ɗin. Sannan ya ɗauka remote ya kunna television.
Sai da Yoohan ya sha kusan rabin juice ɗin, hankalinsa nakan program ɗin yace, “Ka bama su SJ kayan dana ce?”. “Sir wane kaya? Bansan ka ajiye kaya na basu ba ai”. Da mamaki Yoohan ya juyo ya ɗan kallesa, sai kuma ya maida ga television ɗin yana faɗin, “Baka gyara min ɗaki ba kenan?”.
A take abinda Aymah tai masa ya dawo masa a rai. Murya a cinkushe yace, “Sir naje zan gyara Madam ta hanani. ta kuma min gargaɗin ma karna sake shiga sashen gaba ɗaya”.
“Madam? Wace madam?”.
Yoohan yay maganar da tsatstsare sa da idanu. Kan solo a ƙasa yace, “Madam Nu’aymah”. A take ya zayyane masa duk yanda sukayi da Aymah kafin yazo nan wajensa. Ya zata zaiga ɓacin rai tattare da ogan nashi, dan ya saka aiki aƙi masa ko wani ya hana a masa yana ɗaya daga cikin abinda ya tsana, ko madam Chioma ce sai ya nuna ɓacin ransa koda ba zaiyi magana ba. Amma a mamakin Solo sai yaga Yoohan ɗin yayi wani ɗan munafukin murmushi yana ajiye kofin hannunsa. Batare da yace komaiba ya shiga zare takalman ƙafarsa. Yana kammalawa kuma ya miƙe ya fito solo na binsa da kallon tsoro dan ya wuce na mamaki kam.

Har yanzu Aymah na a falon, dan tsabar ƙwarewa a ƙwaɗayin da take cema wani yana yi ita kofi ma ta ɗakko ta haɗa madara da zuma da yawa, tasa ruwa ɗan kaɗan. Ta kwaso biscuits kala-kala kusan shida tazo ta zube a dining tana faman ci da lumshe idanu. Dan babu ƙarya biscuits ɗin duk sunyi uwar haɗuwa.
Cak Yoohan dake ƙoƙarin fitowa ya tsaya kawai yana kallonta da maɗaukakin mamaki da al’ajab. Yayi tsayuwar kusan mintuna uku yana kallonta da ita da falon da ƙamshinsa ke neman saukar masa da kasala kafin ya cigaba da takowa a hankali ya iso inda take. Kamar zaiyi magana sai kuma ya wuce a binsa zuciyarsa fal mamakinta. Ya tabbatar ta gansa amma ta basar.
Tunda ya tura ƙofar ɗakinsa yaga yanda ya barsa haka yake sai ya juyo bai shiga ba. Wajen Aymah dake cigaba da party ɗinta ya dawo. Yanzun kam a bisa tsautsayi ta ɗago kanta, dan batai tunanin shine ya dawoba duk da taji ƙamshinsa sai suka haɗa ido. Saurin kauda nata tayi tana tura biscuit cikin baki.
Shikam yana tsaye hanayensa duka cikin aljihun wandonsa, cikin ƙasa da murya sosai, kamar baya son yin maganar yace, “Hy Smally, tuda kin korarmin maimin aiki sai ki je ki min dan bana iya wanka a toilet ba’a wanke ba”.
Kamar Aymah zata sharesa sai kuma ta kasa, dan yanda yay maganar ƙasa-ƙasa da kiranta sumoli yaja hankalinta wajen son maida masa murtani. Sai dai kuma tana ɗagowa ta sami fuskarsa a tsuke mayun idanunsa kuma ƙyam a kanta kamar zasu haɗiyeta. Kumbura baki tayi da faɗin, “Wlhy niba smally bace, dan ko a yanzu dai shekarata goma sha bakwai da wata tara”.
A ransa yace, ‘Ai fa sai sha bakwai ɗin’.
Ta cigaba da faɗin, “Kuma da kake cewa na korar maka mai aiki, ta yaya zanbar wannan ƙaton gardin yana tsayamin a kai kamar wani mala’ikin dake tsaron ƙofar wuta. Baga ƙannenka nan ba wani yazo ya gyara maka”.
Harga ALLAH maganarta ta bashi dariya, amma sai ya danne. Takawa yay gab da ita. Hakan yasa ta miƙe zumbur tana ajiye ledar biscuit ɗin hannunta, ta tura kujerar baya danta samu hanyar guduwa. Caraf ya riƙo hannunta ta faɗo jikinsa. Duk da yaji ɗan zafin yanda ta faɗo masa bai damuba. Sai ma hannunsa daya ɗora akan ƙugunta ya sake matsota ta manne masa sosai.
“Ouch!! Wannan muguntar fa?”. Ta faɗa tana ƙoƙarin ɗago fuskarta dake saman ƙirjinsa gab da haɓarsa, dan har ɗan gashin gemunsa na gogar gashin kanta. Kallon ido cikin ido sukaima juna. Tana ƙoƙarin son kauda nata amma ya hana, da wani irin yanayi yace, “Miyasa ke bakinki baya iya daina magana? Kowacce amsa kinada ita?”.
“To sai in zauna a ringa cutata, ku mutane ai kunason mutum ya zama banza ku dinga takashi kamar wani tiles kuna wucewa”.
Shi sam bama ya fahimtar mi take faɗa, hankalinsa gaba ɗaya yana kan bakinta ne da idanunta da suka ciko da ƙwalla. Hakan yasa baice mata komaiba, sai saukar babban ɗan yatsansa taji akan gefen bakinta. Saurin kauda fuskarta tai ƙoƙarin yi tana zaro ido. yayinda shi kuma ya ɗaga mata yatsan yana nuna mata ɓurɓushin biscuit daya goge mata. Haɗiye abinda zata faɗa ɗin tayi da ƙoƙarin san zamewa daga jikin nasa. Babu musu ya saketa kuwa.
Daɓar ta faɗa saman kujerar da take zaune da. “Wayyo Abbana!”. Ta faɗa saboda zafi da taji.
Dafe tebirin yayi da hannu biyu ya ranƙwafo kanta har tanajin saukar numfashinsa. Cikin kunnenta yace, “Silly girl, wannan shine maganin masu bakin magana kamar akku”.
Hawaye na silalo mata akan fuska ta sa hannu kan damtsen hannunsa ta turesa. Fuskarsa ɗauke da murmushin mugunta ya riƙe hannunta, “Tashi muje ki gyaramin ɗaki kona sake ɗagaki sama na dire a kujerarnan har sai…….. ” Sai kuma yay shiru bai ƙarasa ba
Zatai magana ya ɗora yatsansa saman bakinta yace, “Shiiii!!!!”. Sai kuma yaja hannunta dake cikin nasa ya miƙar da ita. Tanaji tana gani ya jata har ɗakinsa. Ganin ya nufi hanyar da take ƙyautata zaton toilet ne ta tirje da faɗin, “Nifa bana shiga toilet babu ɗan kwali”.
Baice komaiba, sai sakin hannunta da yay ya nufi Wadrobe ɗinsa, sai gashi riƙe da babban handkerchief. Gani tai kawai ya warwaresa yay masa linkin ɗankwali ya ɗora mata bisa kai. Tsaf ya ɗaura mata shi kuwa duk da bawai ya buɗe bane da ƙyau yanda ya kamata, amma dai ya rufe gashin. Sake kama hannun nata yay zuwa cikin toilet ɗin.
“Ki fara wanke nan, wanka zanyi na fita”. Daga haka ya saketa ya fita.
Dubansa tayi kamar zatai magana sai kuma tai shiru dan harya gama ficewa. Tsaf ta gama bin toilet ɗin da kallo, dan babu ƙarya ya haɗu, gashi an zuba kayan toilet ɗin irin kalar, garai-garai ɗin nan kamar ƙanƙara, sai dai sunfi ƙanƙara duhu dan sunyi ɗan kalar ash da fari-fari. Komai tsaf a tsare inda ake buƙatar ganinsa babu wani dattin da yake faɗa akansa bazai iya wankan ba. Da yake neman aikin yin take saboda jikinta da yay mata nauyi sai gashi ƙara gyarashi tsaf, kamar taje ta ɗakko turaren toilet ɗin da miss xoxo ta haɗa mata mai shegen ƙamshi na wanke toilet sai kuma ta fasa. A cewarta kada ta cika zaƙewa ya ɗauka ya sameta ne a ɓagas.
Fitowa tai riƙe da ƙugu alamar ta gaji, Yoohan dake zaune a kujerar dake tebirin karatunsa ya ɗago yana kallonta jin tana nishi. Dan shi a zatosa ko faɗuwa tayi a toilet ɗin ma. “lafiya?”.
Baki ta kumbura gaba da faɗin, “Na gaji ne, bayana kamar zai ɓalle”.
“Kaɗanma kenan, tunda kika koramin mai mini ai”. Ya faɗa yana ɗauke kansa daga gareta ya maida ga lap-top ɗin gabansa da yake aiki a ciki. Haushin maganar tasa ya hanata tanka masa, ta ƙarasa ga makeken gadonsa ta faɗa a kai tana faɗin, “Wash Umm na gaji, nima bara na rama hawar min gado da kayi”.
Miƙewa yay idonsa a kanta. Batare da yace mata komaiba ya nufi bayi yana wani murmushin daya zo masa babu shiri. Harga ALLAH ta burgesa da tai aikin, dan baiyi zaton zatayin ba saboda sanin tsiwarta. Iyawarma baiyi zaton ta iya ba. Amma daya shiga bayin sai yagama gyaran natama yamafi na Solomon ɗin.
Sai da taja kusan mintuna uku a kwance tana shaƙar ƙamshinsa daya manne bedsheet ɗin, kafin ta miƙe ta fara gyarawa duk da harga ALLAH ta gaji da gaske. Amma batason ya fito ya isketa. Kuma tanama buƙatar zuwa tayi wanka itama dan cikinta dam yake da ciye-ciyen da tayi.

Tana tsaka da mopping kuwa ya fito. Kallo ɗaya tai masa tai azamar maida kanta ƙasa ta duƙar tana ƙunƙunin wai mara kunya ne mutumun nan. Yasan da ita amma ya fito da towel.
Oho shi baimasan tanai ba. Dan mirror ya nufa bayan shima ya mata kallo guda ya dauke kansa. kansa tsaye yake komansa duk da kuwa yasan tana cikin ɗakin. Ta gama tana fesa fresheners data gani shi kuma ya ɗakko kaya zai saka. Juyowar da zatayi idonta ya sauka a kansa yana ƙoƙarin ƙwaye towel ɗin. Cikin subutar baki tace, “Babbar bala’i a gabana?”. Kafinma ya fahimci mitake nufi ta jefar da roban freshener ɗin ta kwasa da gudu ta fice.
Da kallo ya bita ransa fal tunanin lafiya kuwa? Sai kuma yay saurin kallon hannayensa biyu dake riƙe da gefe-gefen towel ɗin. Ai baimasan sanda ya fashe da dariya ba. Ya saki towel ɗin yana zama bakin gadon har sannan dariyar yake hannayensa riƙe da kansa. Pant ɗin dake jikinsa fari ƙal ya shafa yana faɗin, ‘Silly girl, an gaya miki zan fito gabanki babu pant’.
Oho Aymah tuni takai ɗakinta ita dai, ta faɗa toilet tana hakki idanunta a rufe kamar ance gashi gabanta. Taja kusan mintuna biyu sannan ta sami nutsuwa, ta ɗan dafe kanta a ranta tanajin da sakamakon abinda zata gani kenan da bata biye masa tai wannan shararba. Dan dama tayine kawai saboda an koya musu biyayya gana gaba dasu, sannan nasihar iyayenta a gareta tana nan daram cikin ranta babu abinda ta manta a ciki. Daga haka itama ta zame kayanta ta hau yin wankan.

Ta kammala shirinta kenan cikin baƙar doguwar rigar jallabiya data ji stones ya shigo. Saurin juya masa baya tayi tana ɓata fuska. Kansa ya girgiza kaɗan ya cigaba da takowa cikin ɗakin. A kan laɓɓanta ta furta, ‘Mayen suit ’ dan tsaf ta gama ƙare masa kallo ta cikin mirror ba tare da ya sani ba. Shima ɗin dai kallonta yake daga sama har ƙasa dan rigar ta mata ƙyau sosai. Idonsa akan dokin wuyanta da kananun gashi ke kwance luf-luf yace, “Ni zan wuce porthercout, sai gobe idan ALLAH ya kaimu zan dawo”.
Da sauri ta juyo tana kallonsa idanu a buɗe, tace, “Ni kuma ka barni a ina?”.
Da mamaki yace, “A ina kike anan?”.
“Gidanku”.
ta bashi amsa kansa tsaye.
“Oh to anan zaki zauna kenan, tunda kinsan ni dai aiki zanje ko”. Yanda yay maganar a dakile ne ya bata haushi. Cike da tsiwar tata data motsa tace, “He’em. Wlhy to nima ka kaini gidan Abbah dan bazan zauna ni ɗaya ba. Sannan kuma nama Abbana maganar ƴar aiki daga can kano yace babu ruwansa saika amince. Please ka kirashi kace ka yarda”.
Necktie ɗinsa dake rike a hannu da rigar saman suit ɗin ya gyarama zama yana tsatstsare ta da idanunsa, “Duk waɗanan masu aikin dake gidan nan su menen amfaninsu da har sai an kawo mai aiki daga kano?”. “Toni bana buƙatar aikinsu, ni dai kawai a akawomin YARENA ADDININA hankalina zaifi kwanciya. Amma ta ina zan yarda waɗan nan garadan na shigomin kai tsaye gasu da shegen kallo kamar ƴaƴan mayu”.
Ƙala baice da itaba, dan shima ya tafi wani kuma tunani daban. A ganinsa zaiyi amfani da wannan damar wajen binciko abinda yay alwashi. Dan dole kam ya yarda sai sun sami kusanci da wani ɗan gidansu Aymah anan sannan zai fahimci abinda yake zargin. Kuma ya tabbata idan aka kawo mai aikin duk wanda yayma Nu’aymah wancan ƙullin zai haɗa alaƙa mai ƙarfi da wanda za’a kawo musun saboda samun bayanai akanta. Shi kuma wannan shine mabuɗin bincikensa………..
“Na shirya” data faɗa ne ya maidosa hankalinsa. Yay saurin dubanta da ƙyau yana bin handbag ɗin hannunta da kallo da ƙaramar leda. ‘Lallai kan yarinyar nan da motsi’ ya ayyana a ransa yana ɗauke idonsa a kanta. Duk da take masa kallon ba bahaushe ba duk yanda al’adunsu da dokokin musulinci sai da Hamza manager ya bashi haske a kansu daki-daki. Shi kuma ya ɗauki ɗammarar bi da ita akansu kodan ta samu nutsuwar zama da shi.
“Karki ma ɓatama kanki rai dan babu inda zakije. Idan abokan hira kike bukata gidan nan cike yake da mutane”. “To ni……..” ta kasa ƙarasawa saboda matsota da yayi. “Ke me?”. Ya faɗa yana tsuke fuskarsa da ƙyau. Bata sake magana ba dan kwarjinin da yay mata da cika idanu. Ga kuma zuciyar ta gado ta yunƙuro tazo gab da maƙoshi ta tsaya. Harya juya ya fita bata sake magana ba sai hawayene da suka cika mata idanu. Yana rufe mata ƙofar kuwa ta matsosu suka zubo.

Duk da yaji tausayinta a ransa haka ya fice daga sashen nasu, a falo ya iske duk a halin gidan suna breakfast a babban dining ɗinsu. Cike da girmamawa yaran duk suka shiga gaishesa. Ya amsa sau ɗaya shima yana gaida su Momynsa dake binsa da wani irin kallo da ya kasa bama fassara. Da yake tasan kullum itace ke saka masa necktie indai yana gida saita taso. Amsa tayi ta saka masa, tare da taimaka masa ya ɗora rigar saman itama. Yanda batai magana ba shima sai baiyi ba. Sai da ta gama saka masa sannan yace, “Mu an daina bamu breakfast ne a gidan Momy?”.
Da sauri tace, “No my boy, dama na sanarma Blessing ne takai muku tunda har yanzu kaga dota tana tare da baƙunta”.
Idanunsa yaɗan lumahe ya buɗe a kanta. Hakan ba karamin sumar da ita yake ba, dan tana masifa-masifar son wannan salon da ya zame ma ɗan nata ɗabi’arsa. Yace, “Wasa nake nima Momy, ga amanar matana nan na bar miki, ni zanje porthercout ne, amma zan dawo gobe”.
Da ƙyar ta danne zafin da takeji a zuciyarta. Ta kai hannu bisa tattausan sajensa ta shafa tana lumshe idanu, “Babu damuwa My Son, kaje lafiya ka dawo cikin nasara”. Hannunsa yasa ya janye nata daga fuskar tasa. Ya sumbaci bayan hannun yana jinjina mata kai da faɗin, “Thanks you sweetheart”.
Daga haka ya juya ga kakaninsa. Fuska ya tsuke da ƙyau yana kallonsu. “Granny’s na dawo gareku, dan nasan kunfi kowa tarin matsala a gidan nan yanzun. Baku barma kanku ba balle wani. Ga matata nan zan bari, idan na dawo naga ko ƙwarzanen damuwa a fuskarta nasan maganinku”.
Cike da hayaniya Momy Debora ta hayayyaƙo masa cikin yarensu, dan dama da yare yay maganar shima. Itama Mama miƙewa tai tana zazzaga masa nata. Bai kulasu ba ya duba kannensa suma yay muau nasa gargaɗin da idanu, sannan ya duba ƙanen papa su Momy Destiny. A girmame yace, “Auntys kuma na baku amanar matata, karku bari waɗanan tom and jerry ɗin su mata ko kallon banza”. Cike da kulawa suka karɓa masa. Dan sukam har cikin ransu suna ƙaunar ɗan ɗan uwan nasu, musamman daya kasance Yoohan tsaye yake akan bukatunsu na yau da kullum harma da ƴaƴansu.
Har mota ƙannensa da Momy sukai masa rakkiya, Gebrail ma motar ya shiga zai bisa har airport dan yanason ya tambayi kuɗi a wajensa. Solomon dai nata faman cin maganin da shi Yoohan ɗinma bai san yanayi ba. Sai da motocin suka fice sannan suka koma cikin gidan.

Hawaye sosai Aymah ta dingayi dan kewar gidace sosai ta dawo mata sabuwa fil. Daga ƙarshe ma sai ta koma gado ta kwanta abinta. Tun tana tunanin mafita akan wannan auren har barci yay awon gaba da ita batare data shirya hakanba.
Barcin kusan awa guda da rabi tayi kafin ta tashi, koba komai taji sakayau bakamar ɗazunba. Ganin lokacin walha ya wuce sai kawai ta shiga toilet tai uzirinta ta fito. A ranta take ayyanawa bazatai zaman takura kai ba, gara ta fitama ta zagaya gidan kar masu gidan su ɗauka ko tsoronsu takeji su sami nayi a kanta. A falo taci karo da breakfast da Blessing ta kawo mata tun ɗazun. Ta matsa gaban tray ɗin tana buɗe kwanikan. gasashen plantain ne, sai miyar ƙwai da ruwan tea da farfesun kifi. Ba yunwar take jiba. dan haka ta ɗauki gasashshen plantain ɗin guda biyu tasa miya a gefe ta zauna taci, koda ta gama saita ɗauka trayn gaba ɗaya ta fito da shi.
Tunda ta fara sakkowa daga steps ɗin benan duk suka zuba mata idanu. Babu wanda bai yaba ƙyawunta ba a cikin ransa. Tare da ganin dacewarta da Yoohan ɗin nasu. Miracle ce ta fara jan tsaki tana kauda kanta gefe. Karaf kuwa a idon Aymah dake sakkowa. Wani ɓoyayyen murmushi ta saki a ranta tana ayyana ‘kece zaki fara ɗaukar lesson kenan ƴar lukuta’. A fili kam saita dubi Blessing data hangota tazo wajen da saurin domin amsar tiren hannunta. Yanda Blessing ɗin ta gaidata da girmamawa haka itama ta amsa mata da girmamawa tana miƙa mata tiren..
Cikin falon ta ƙarasa fuskarta ɗauke da ɗan murmushi, ta zauna a kujerar data rage. Su mama debora ta fara gaidawa, suka amsa mata fuska a ɗaure. Bata damuba ta gaida Momy, ita dai babu yabo babu fallasa ta amsa. Daga haka ta gaida su Momy Favour da suka amsa mata sukam da fara’a, har suna tambayarta ya baƙunta?. ko kallon inda su Joy suke batai ba, sai da su Victoria na gaisheta ne ta amsa musu da kulawa tana tambayarsu ya school?.
Wani wawan tsoki Miracle ta sake ja tana miƙewa tana wani fifita fuska da hannu alamar wulaƙanci dai.
Tana zuwa saitin Aymah tasa ƙafa ta taɗeta batare da kowa ya lura da yanda akai ba, sai ganin Miracle sukai a ƙasa wanwar bakinta ya daki gefen centre table aiko ya fashe………….✍

Tofa, mutuniyarku zata fara taro mana world cup a gidan Pastor goshpower😱😣😂.

yanzu haka an kusa kai ƙarhe, gamai buƙata zai iya garzayawa ya biya zafafa kar agama shanye romo babu shi😋😋😋.

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No. 49

_____________

_Ina ma’abota karance karance littafin hausa? Wanda ke nishadantar wa ya fadakar? Kana ya tsunduma ku a kogin lobayyar kauna..?_

_*REAL FEEDO* hazikar marubuciyar nan ta zo muku da wani gangariyar littafi mai suna: *BA AMO…!* *BA AMO* wani nazartaccen littafi ne daya zo da wani irin salo na daban…_

_Labarin *BA AMO* ya faru akan wata yarinya da d’an sarkin garin su, yarinyar gidan su gidan yawa ne…Baban su yana auri saki ya tara ‘ya’ya da mata da yawa. Tirqashi! To ita yarinya sunan ta KHAIRAT… Tun farko dangin mahaifin su sun tsani mahaifiyar tasu,Bayan ya auro ta, Ta haifi yara mata zallah suna kiran ta da uwar mata kuma kwata-kwata basa kaunar ita da ‘ya’yan nata. To ita yarinya ta gama karatun ta…. wato KHAIRAT.. shekarun ta 22 matan gidan nasu suna mata gorin tayi kwantai tak’i aure. Kwatsam wata rana yarinyar ta samu labarin d’an sarkin garin su ya bude sabon company ya fara daukan sabbin ma’aikata, 🧚🏻‍♂️😍cikin ikon Allah ta zuwa ta samu aiki. Ta fara zuwa aikin ta, a karshe su kansu da suka fahimci kwazan ta da nutsuwar ta samu karin matsayi. To a lokacin ne kuma Yarima da PA dinsa suka sami matsala aka kore ta a ma’aikata sai aka daura ita Khairat d’in a matsayin P.A dinsa. Tafiyar tasu batama yi nisa ba! Aka yi makiya suka yi masu sharrin wai karuwar sa ce, har labarin yaje gun mai martaba. Itama Khairat d’in labarin yaje ga mahaifin ta har ya nemi korar ta daga gidan sa, da kyar aka lallashe shi ya hakura.._

_Tab rungutsumi din fa kenan🤮Ya zata kaya ne ga YAREEMAH GA KHAIRAT..a roof d’aya? Ya rabbi😢 labarin kauna yayi.. Amma fa Za’a sha rikici.. Karku manta khairat daga gidan yawa tafito🥺Ga basuda wani hali.. Shin sarki zai yadda da Khairat amatsayin personal assistant din yareemah ko kuwa.? Duk wannan ruguntsumi n REAL FEEDO ce kadai zata iya warware mana.._

_BA AMO::::: (Ba Labari…)_

_DOMIN MALLAKAR NAKI/‘NAKA sai ku baza idanu domin free ne yana nan yana yawo a kowane group_😘😘

___________

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply