Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 6


Saran Boye 6
Viral

No. 6

…………….Baba malam na tsaka da sallamar abokan arziƙinsa kira ya shigo wayarsa. Kamar zai share karya duba sai kuma ya cirota daga cikin babbar rigarsa. Ganin Number da akai kiran da ita yasashi ɗagawa da sauri ya ɗora a kunne yana faɗin, “Assalamu alaikum. Innah!”. Batare da Hajjo ta amsa masa sallamarba cikin kuka take faɗin, “Duk inda kuke ku taho gidan nan babu lafiya ɗan Malam”.
“I…in…innah miya faru halan?”. A zafafe Hajjo tace, “Sai kaji abinda ya faru zaku taho? To Firdausi ce aka fita da ita babu rai”.
Ba ƙaramin bugun ƙirjin Baba malam wannan kalma tayi ba, kafin ya samu damar yin magana Hajjo ta yanke kiran. ‘Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un’ Baba malam ya fara ambata akan laɓɓansa, atake damuwarsa da yaketa ƙoƙarin dannewa take ƙoƙarin fitowa fili, ya share zufar data taru masa a gaban goshi yana busar da iska mai zafi. lumshe idanunsa yay na wasu mintuna yana ambatar addu’a. Sai da yaɗan samu nutsuwa sannan ya juya zuwa cikin hall ɗin. Ruwa ya samu ya sha zuciyarsa ta ƙara nutsuwa kafin ya tattara su Abbah da samarin gidan suka bar wajen.
Suna fara tafiya sai ga kiran Omar, shine ya sake sanar masa da abinda ke faruwa, tare da asibitin da suke a yanzu haka. Kai tsaye can suka nufa, inda suka tarar da Addah da yayun Umm sun haɗe kai sunata sharɓan kuka.
Hankalinsu Baba Malam sai ya sake tashi fiye da farko, amma da yake shiɗin kamilin mutum ne sai fuskarsa bata nuna yanda yake a rikice ba. Addu’oi ya keta ambata a ransa yana cigaba da miƙama UBANGIJI kukansa.

Sun kai tsahon mintuna arba’in suna jiran fitowar Doctor kafin ya fito. A kusan tare suka sauke ajiyar zuciya ganin fuskar Doctor ɗin da ɗan sassauci ba kamar ɗazunba. Kallonsu yay cike da girmamawa yace, “Alhmdllh ta farfaɗo. jininta ne ya hau sosai, ALLAH ma ya taƙaita mata wahala, dan irin wannan faɗuwar ga mai hawan jini babbar matsalace, musamman yanda jininta yay ƙololuwar hawa”.
Sake sauke ajiyar zuciya duk sukayi, Baba Malam ya kauda kansa gefe tare da ɗauke ƴan ƙwallar da suka taru masa a cikin ido.

Baba malam ne kawai aka bari ya shiga ya ganta, tana kwance idanunta rufe an saka mata ƙarin ruwa. Tai masa wani irin masifar haske a ido. Ya jima yana kallonta tausayinta na sake faɗaɗa a zuciyarsa, ya kai hannu ya shafa kanta yana magana a hankali. ‘ALLAH ya baki haƙuri Jannat kinji, ALLAH ya bamu ikon cinye jarabawar nan, kiyi haƙuri ki daina damuwa’. Ya ƙare maganar da sumbatar goshinta.
Ya kai tsahon mintuna goma yana cigaba da kallon ƙyaƙyƙyawar matar tasa kafin ya juya ya fita a ɗakin.

Gaba ɗaya kan baba malam ya ƙara ɗaukar zafi, gashi dama shima yana da hawan jinin. Gudun kar gazawarsa ta bayyana ya sashi samun Doctor ya nema a sallamesu su koma gida da Umm. Family Doctor ɗinsu zai cigaba da kula da ita.
Doctor baiyi musu ba ya basu sallama, dan yasan su ɗin manyan mutanene, bazasuso cigaba da zama a asibitinba kodan yanayin da ƙasar yake na rashin tsaro.

Bayan kammala duk abinda ya dace aka saka Umm a Ambulance. Addah ta shiga tare da Nurse ɗin da aka basu, su kuma suka shiga motocin da sukazo a ciki.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

__________________
________________________

Sosai hankalin mutanen gidan da ƴan biki ya ƙara tashi ganin Ambulance har cikin gida. Da yawan gwiwoyin wasu ya sare a zatonsu ko Umm ta rasu ne. Sai da sukaga an fito da ita zuwa sashensu harda ƙarin ruwan da ake mata sannan aka fara sauke ajiyar zuciyoyi da ambaton Alhmdllh.
Bayan an shiga da Umm Bedroom ɗin Baba Malam dangi suka shiga jajantama juna da addu’ar samun lafiya a gareta tare da fatan dawowar Nu’aymah gida cikin ƙoshin lafiya. Daga haka dangi na kusa suka fara zare jiki suna barin gidan, dan kam ko masu gidan basuce dasu komaiba sunsan suna buƙatar a basu wuri suji da abinda ya damesu.
Kafin sallar magriba gidan ya ragu sosai. dan irin dangi na katsina, kaduna, jigawa ma duk sunyi sallama sun tafi tunda ba wani nisa bane mai yawa. Balle kuma ƴan cikin kano da ƴan gayyar aci shinkafa asha zoɓo😏🤐.
Yayun Umm su Maman Nanah dai suna nan basu tafi ba sukam duk da anan cikin kano suke aure su duka. Sai kuma wasu a cikin dangin Momyn Abdallah da suma sukaƙi barin gidan.

Har bayan sallar isha’i Umm nata barci, yau Baba malam ko wajen karatu bai zauna ba, sai Abba Mustapha ne yayma magidantan dake ɗaukar karatu bayan sallar isha’i ƙari. Shima daga ƙarin ya sallami kowa ya shigo gida.

★★★★

Zuwa bayan isha’in ne hankalin kowa ya koma kan sanin ina Abdallah?, dan duk wannan rugun tsumin da akeyi babu wanda yaji ɗuriyarsa. Nemansa aka shigayi a waya amma bai ɗagaba. Hakan yasa samarin gidan suka fara didduba ɗakunansu. Har hankali ya fara tashi na rashin ganin nasa sai gashi Abubakar ya samosa a ɗakinsa yana barci.
Fita yay ya sanar musu. A tare duk suka ɗura kai cikin ɗakin, inda suka sami Abdallah kwance cikin matsanancin zazzaɓi. Da yake Doctor yazo sake duba Umm sai aka kirasa yazo ya duba Abdallah shima. Shikam damuwace ta saukar masa da zazzaɓin, sai kuma yunwa. Magunguna Doctor ya haɗa masa harda wanda zai sakashi barci, yace a bashi abinci ya ci kafin yasha.
Haka kuwa akayi, Hajjo ta basa abinci da kanta duk da yanata cewa shi ya ƙoshi. Da dai lallashi da ban baki aka samu yaci kaɗan yasha magani. Ahmad ne ya taimaka masa yay wanka sannan aka maidasa ɗakinsa da Hajarah ta gyara ya kwanta.
Ganin barci ya ɗaukesa sai duk suka fito, aka barsa da Ahmad kawai da zai kwana tare da shi dan ba’asan mi dare zaizo da shiba.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

___________________________
___________________________
WASHE GARI
___________________

Daga Umm har Abdallah sun tashi jikinsu Alhmdllh, sai dai damuwa irin ta zuciya da fitarta farat ɗaya bazai yuwuba. Bayan kammala karin kumallo aka haɗu aka tsaftace gidan, sauran baƙi duk suka kama gabansu. Su Sumayya kawai ne duk suna nan basu koma gidajensu ba.

Bayan sallar azhar Baba malam da su Abba suka zauna tare da Hajjo, sun daɗe suna tattaunawa kafin su buƙaci ganin matan gidan suma da Abdallah.
Cikin nutsuwa Baba Malam yay musu bayanin da zasu fahimcesa akan wannan canjin da yayi, da kuma dalilinsa na aurama Abdallah su Yusrah. Ya kuma sake nuna fushinsa sosai akan abinda Nu’aymah ta aikata. Har saida takai ƙannen nasa da matansu na bashi haƙuri.
Umm dai batace da kowa komaiba har aka gama aka sallami kowa. itace farkon tashi ta fice a falon. Dan haka duk suka bita da kallon tausayawa. Banda Baba malam da yay kamarma baisan mi sukeyiba, yanata ƙoƙarin cigaba da danne damuwarsa a rai.

____________________
BAYAN SATI ƊAYA
____________________

Bayan sati ɗaya da faruwar komai gidan ya koma normal a zahiri. A baɗini kuwa kowa shi kaɗai yasan damuwarsa da matsalarsa.
Kasancewar ita Adawiya sun kammala secondary baba malam ya yanke hukuncin Abdallah zai tafi da ita can ta cigaba da karatunta, ita kuma Yusrah saita ƙarasa watannin da suka rage mata sai yazo ya tafi da ita. Kowa yayi na’am da wannan magana, dan harma an kammalama Adawiya duka shirye-shiryen tafiya.
Kwatanta muku irin farin cikin da Adawiya take cikima ɓata lokacine, sai dai tanata ƙoƙarin dannewa saboda tsoron Addah data sanyama duk wani motsinta idanu yanzun, sannan ta daina sakar mata fuska gaba ɗaya..
Ganin yanda Addah taketa share Adawiya daƙin yin komai game da ɗan gyarata yasa Umm ta maidota sashenta. Gyaran da bazai cutar da itaba ta shiga mata. Musamman fatarta da kuma maganin sanyi. da koya mata dabarun zaman aure. Ɓangaren girki da aikin gidan tasan bata da matsala, tunda su duka tsaye suke akan yaransu ta wannan fanin duk da kowane sashe akwai ƴan aiki. Dan danan cikin sati guda ta canja tai fes abunta. Idan tana ɗaki ita kaɗai tata kallon kanta a mirror kenan tana tiƙar rawa da gwada yanda zata kasance da Yah Abdallah. Duk da kuwa a yanzu ko kallo basu ishesaba daga ita har Yusrahn. Ko yarda ya haɗu da suma bayayi sam, idanko yaga ɗaya daga cikinsu a waje yata fama haɗe fuska kenan tamkar an aiko masa da saƙon mutuwarsa. Hakan bai dametaba, dan tasan lokaci zaizo da sauyi wataran, kamar yanda a yanzu yazo da shi a garesu suka kasance matansa batare da mafarkinsu ya taɓa hasaso musu hakanba.
Tana tsananin takaici a ranta na haɗata da Yusrah da akayi matsayin matansa, amma ta wani ɓangaren hakan bai damunta, musamman da akace itace zata fara binsa, ta barma kanta yanda sauran aikinta zai kasance tsakaninta da kishiyar tata (😖Adawiya!!!!!💣).

Yusrah kam dai tana cikin damuwa sosai. kullum cikin kuka take da roƙon Abbanta a warware auren ita bataso. Sai dai kowa yaƙi saurarenta, Amminta ce dai take tayata kuka dan tasan da gaske Yusrah bataso ɗin. Amma yaya zasuyi da ƙaddara?.

A washe garin da aka cika kwanaki goma da faruwar al’amarine tafiyar Adawiya da Abdallah ta kama.
Umm da kanta ta samu Addah har ɗaki tai mata ƙorafi akan yanda take share Adawiya. Sai da ta nuna mata ɓacin ranta akan hakan sosai sannan ta ɗora da mata nasiha akan ta yarda da ƙaddara mana.
“Addah Minene laifin Adawiya tunda ba itace ta saka a ɗaura mata aure da Abdallah ba. Ba kuma itace tabama Nu’aymah shawarar ta gudu ba. A ganina addu’a ya kamata mubi yarannan da shi tare da fatan alkairi bawai tsangwama da hantara ba dan su basu da laifi”.
“Umm bazaki ganeba wlhy, ke dai kibar……”
“Naji bazan ganeba Addah”. Umm ta dakatar da Addah da sauri. Ta cigaba da kallonta tana faɗin, “Baki da wani abinda zaki faɗamin da zaki kare kanki, ni dai kawai ki dawo rayuwa da yaran nan kamar yanda kikeyi da. Ki kuma yima Adawiya fatan alkairi kodan sabuwar rayuwar da zata fuskanta a yau dan girman ALLAH”.
Shiru Addah tai tana sake jinjina ƙyawun zuciya irin na Umm, haka take ita komai tana ɗaukarsa da sauƙi a rayuwarta bata zafafama kanta. Tunda abinnan ya faru babu wanda ya taɓajin furucinta kosau ɗaya akai. Ko a fuska ƙoƙarin ɓoye damuwarta takeyi. Tausayin aminiyar tata kuma ƴar uwarta sai ya sake kamata fiye da da can.

Umm da kanta ta fita taje ta shigo da Adawiya, zaunar da ita tai kusa da Addah itama ta zauna. Su biyu suka shiga yima Adawiya nasiha kamar yanda sukeyi a duka sauran ƴaƴan Addah uku da aka aurar. Sumayya, Maryam, Badariyya. Sai da sukai mata nasiha sosai kafin Umm ta tashi ta fita ta bar Adawiya da Addahn.

★★★★

Kamar yanda tsari da al’adan mutanen gidan yake bayan sallar la’asar iyayen suka sake haɗuwa aka rufu kan Adawiya da Abdallah akai musu faɗa da nasiha sosai. Tare da gindaya musu sharuɗa masu tsauri akan duk wanda wani al’amari mara ƙyau ya ɓullo daga wajensa a cikinsu to lallai zai fuskanci ɓacin rai da fushinsu sosai. Daga ƙarshe aka sake musu doguwar addu’a aka sallami Adawiya da ko sau ɗaya batai hawayeba da iyayensu mata.
Umm ta tafi da Adawiya sashenta danta kimtsata, suka bar Abdallah tare dasu Baba Malam da Hajjo da suka sake ɗora masa da Nasiha kasancewarsa shine babba.

Ƙarfe 7:30pm gayyar yaran gidan harna ma’auri su Aysha sukaima Abdallah da Adawiya rakkiya airport dan jirgin 8:30 zasu bi zuwa ƙasar Dubai. Sai sunyi kwanaki goma acan kamar yanda Abdallah ya tsarayi da Nu’aymah sannan su wuce Saudia.
A yanzuma dai idanun Adawiya ƙifi-ƙifi babu ko ɗigon hawaye a cikinsu. Hakan ba ƙaramin ƙona ran Addah yayiba. Hakama Momyn Abdallah al’amarin ya bata tsoro, taita kallon Adawiyar cike da alamomin tambaya a ranta, sai dai bata furtaba.

Ko kaɗan Yusrah bataji komai a rantaba, dan ko kusa bata kawo Adawiya ma a cikin matsalolinta saɓanin Adawiyar dake jin zafin Yusrah babu gaira babu sabar. Ita Yusrah dama za’a warware nata auren da tayi matuƙar farin ciki. Amma ta ɗauka alwashin cigaba da addu’oi tana gayama ALLAH kukanta akan hakan kafin lokacin da akace zata tare.
Basufi zaman mintuna talati da huɗu ba aka sanar da tafiyarsu. Sai yanzune Adawiya taɗanji babu daɗi a cikin ranta na kewar ƴan uwanta. Amma saita fuske ta shiga binsu ɗai-ɗai tana rungumarsu. Da tazo kan Yusrah saita wuce batace mata komaiba. Ba ƙaramin mamaki hakan ya bama kowaba, duk suka bita da kallo har Yah Abdallahn. Tsarguwa da tai ne ganin yanda ƴan uwan nata ke binta da kallon tuhuma ya sakata buɗe jakkarta ta ɗakko wani abu ta nufi Yusrah, hannunta ta kama ta saka mata abin sannan ta rungumeta kamar yanda taima kowa.
A kusan tare duk suka sauke ajiyar zuciya, dan da da yawansu abun yay musu cak a ƙirji hatta da ƴan uwanta da suka fito ciki ɗaya. Musamman Hajarah da taga abinda ya faru a ranar ɗaurin auren tsakanin Addah da Adawiyan.
Sallama suka sakeyi da juna. Kafin tabi bayan Yah Abdallah da yay gaba abinsa batare da ya saurareta sun jera tareba kamar yanda taso.

“Hummm!! Wasa farin girki Adawiya👁👎🏻”.

___________________
NU’AYMAH
______________

Tun randa aka barota daga gida bata sake sanin halin da take a ciki ba sai washe gari da yamma. Farkawa tai a tsananin firgice. Sai dai nauyin masifa da kanta yay mata na azabar ciwo ya sakata sakin ƴar siririyar ƙara da dafe kan nata da hannu bibbiyu tana sakin numfashi a wahale.
Sake ƙoƙarin buɗe idanunta tai da ƙyar saboda nauyin da sukai mata suma. Tabi ɗakin da take ciki da kallo mai ƙaracin haske, sai dai ba dunɗum yakeba. Katifa ce kawai a ɗaki da wasu lalatattun akwatuna guda uku kalar ruwan ƙasa. Sai takalma na maza da aka jera a gefe kusan ƙafa shidda. Sai hanger a jikin bango anyi hanging farar jallabiya ta maza guda ɗaya da wanduna uku duk baƙaƙe. Sake lumshe idanunta tai ta buɗe a hankali dabin jikinta da kallo.
Hijjabin tane dai a jikinta har ƙasa da ta saka lokacin da zata fita neman wayarta. Ta kai hannu da ƙyar ta laluba jikinta. Towel taji wanda shima shine tasan ta ɗaura a jiyan, sai dai yanzu ya kwance duk ya zazzame daga ƙirjinta ya dawo saman cikinta.
Juya mata da garin ya farayine ya sakata yin baya ta sake kwanciya a katifar hawaye masu a zabar zafi na silalo mata a saman kumatu. A haka ta cigaba da kwanciya tana zirarar da hawayen jikinta duk babu wani ƙarfi. Tafi mintuna talatin da kwantawa sannan aka buɗe ƙofar.
Kasa buɗe idanu tai balle taga wanene ya shigo ɗin, tsahon mintuna biyar kafin ta buɗe idon kaɗan ta saukesu akan wanda ke tsaye jikin ƙofa sanye da baƙaƙen kaya, hatta da hannunsa akwai safar hannu baƙake. Hakama fuskarsa da facemask, idanunsa kawai take iya gani. Suma ganin kallon da take masa ya sashi ciro glasess ya toshesu.
Basket ɗin dake riƙe a hannunsa ya tako gaban katifar ya ajiye batare da yace da ita uffanba ya juya ya fita. Maida idanunta tai da ƙarfi ta rumtse zuciyarta na zafi. Kukanma yanzu sai ya kasa fita mata. Haka ta cigaba da zama a wajen har bayan mintuna kusan goma da fitarsa. Sai kuma ga mace ta shigo sanye cikin dogon hijjab har ƙasa. Itama fuskarta sanye take da niƙaf.
Batare da tama Nu’aymah magana ba ta kamata ta tayar. Bata da wani ƙarfi ko iya yin magana, dan haka ta cigaba da bin matar kawai a yanda taso. Ƙofa ƙwara ɗaya ƙarama dake a cikin ɗakin suka nufa, sai da suka shiga Nu’aymah ta fahimci toilet ne. Fas yake babu ƙazanta a cikinsa, saima ƙamshin omo da hypo daketa tashi.
“Kiyi wanka”. Matar ta faɗa a taƙaice batare da ta jira amsar Nu’aymah ba ta fice abinta. Da kallo kawai Nu’aymah ta bita, sai dai bakinta ya mata nauyi ta gaza cewa uffan a yanzunma. Kamar bazatai wankanba sai kuma wani tunanin yazo mata. Rabonta da salla tun ta isha’in jiya. Ga shi a yanzu da alama har anyi sallar la’asar ma. Tana buƙatar ƙarfin jiki sosai, hakan kuma bazai yuwuba sai tayi wankan.
Cikin ƙarfin hali ta zare dogon hijjabinta da towel ɗin, duk da tsaftar banɗakin a ɗarare tai wankan. Taji ƙarfin jikinta sosai, sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi a jajjere. Alwala tayi ta fito tana daddafa bango, dan akwai yunwa tattare da ita.
Da mamaki ta kalli kayanta da aka ɗaura a saman katifar, ta bi ɗakin da kallo kamar ɗazun, babu kowa sai kayan a ajiye da kuma kwanikan abincin dake cikin basket ɗin suma an fiddosu ƙasa an ajiye.
Bata da wani zaɓin daya wuce canja kayan tai sallolin dake kanta. Harta kammala rama sallolin babu wanda ya sake shigowa, ta kwanta saman abin sallar tana hawaye da tunanin ko wane hali yanzu Umm da Abbanta da Muh’d dama duka sauran ƴan gidansu suke ciki a yanzu na rashin ganinta?. Yah Abdallahn ta, tasan zaifi kowa shiga tashin hankali bayan Umm da Abbanta. ‘Minayi suka kawoni nan? Su wanene su? A ina nake?’. Ta faɗa a fili tana sake fashewa da kuka. Taja tsahon lokaci tana ribzar kukanta, har kanta yana masifar sara mata fiyema da ɗazun. Barcine ya fara figarta na wahala. Jin motsin shigowar mutum ya sakata tashi zaune zumbur. Matar ɗazunce, yanzuma batai mata magana ba ta ɗakko kwanikan abincin ta kawo gabanta da mata alamar taci.
Yunwa Nu’aymah takeji sosai, dan haka batai musu ba taja abincin tahau cinsa. Taci sosai har matar tai mamakin hakan. Matar ta miƙe zata fara tattare kwanikan Nu’aymah ta kalleta cike da rashin tsoro tace,
“Su wanene ku? Miyasa kuka kawoni nan? Minai muku kuma?”.
Kallonta matar tayi sosai, amma sai batace da ita komaiba ta tattara kwanikan tai ficewarta.
Tashi Nu’aymah tayi ta nufi ƙofar da sauri, sai dai tana taɓawa tajita a kulle, fashewa tai da kuka ta koma saman katifar ta sake kwanciya tana sambatun kiran Umm da Abbanta da Yah Abdallah.

Tun daga wannan ranar kullum hakan ta cigaba da faruwa, zasu kawo mata abinci sau uku a rana, matarnan zatazo ta gyara ɗakin ta wanke mata bayi da kayan data cire. Sannan ta haɗa mata ruwan wanka ta sakata cin abinci. Tambayar duniya tai mata bama bata amsa, haka shima namijin idan zai shigo sau goma tai masa magana baya ko mata tari. Iya kacinsa ya leƙo ya ganta ya koma.

Haka Nu’aymah ta cinye kwanaki goman nan cikin matsanancin damuwa da tashin hankali. Babbar damuwarta halin da ahalinta zasu shiga na rashinta. Musamman ma Umm ɗinta da Abbanta da Yah Abdallah da Hajjo. Tayi kuka harta gaji ta bari ta koma gayama UBANGIJI kukanta. Dan tasan shine mai rahama mai jinƙai. Ya fita sanin dalilin da yasa ya jarabceta da wannan al’amari a daren ɗaurin aurenta da yayanta masoyinta.

Ranar data cika sati biyu a ɗakin bayan sallar la’asar sai ga matar nan, kamar kullum yauma batai mata magana ba, saima kwashe kayanta data cire tai ta fita dasu. Bayan kamar mintuna goma sai gata ta dawo ɗauke da hijjabi wankakke gogagge. Miƙama Nu’aymah tai da mata alamar ta sanya. Babu musu Nu’aymah ta fisgi hijjabin daga hannunta tana watsa mata harara ta sanya. Ita sam bata wani jin tsoronsu, damuwarta kawai family nata.
Matar bata kulataba, bayan ta saka hijjab ɗin ta zagaya ta bayanta ta riƙe mata hannaye. Fisgewa Nu’aymah ta fara ƙoƙarin yi amma ta kasa saboda ɗaure hannayen da matar tayi. Kafin ta samu damar magana namijin ya shigo shima. Gaban Nu’aymah yaje ya tsaya tare da fiddo baƙin ƙyalle a aljihunsa ya ɗaure mata idanu.
Duk tsiwar da take masa bai kulataba balle ya tanka. A haka suka fita da ita a ɗakin batare da tasan ina za’a kaitaba………….✍

_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba’a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_Typing📲_*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply