Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 66


Saran Boye 66
Viral

No. 66

………….Da sauri madam Chioma ta shiga ɗakinsa ta kwaso spare keys ɗin gidan ta kawo masa. Amsa yay ya nufi sashen Yoohan ita da Solomon biye da shi. Kai tsaye ɗakin Nu’aymah suka shiga. Ɗakin yayi ƴar ƙura, dan ma Yoohan duk ya tattare abinda yasan ƙurar zatai masa illa. Buɗe-buɗe suka shigayi a lungu da saƙo na ɗakin. Har cikin Wadrobe ɗin kayanta dan tsabar rashin mutunci. Duk abinda idonsu ya gani bai musu ba sai sun masa filla-filla. A haka Madam Chioma ta dinga tiɗo kayan Nu’aymah a ƙasa har hoton nan data ɗaukko ɗakin papa ya faɗo.
Duƙawa tai ta ɗakko farar envelope ɗin, ta ɗaga bakin zata buɗe kira ya shigo wayarta. Gajeren tsaki tayi da ɗora hotan a kan fallen Wadrobe ɗin ta zaro wayar a aljihunta, ganin Madam Rebecca ne ya sakata ɗan juyawa ta dubi papa. Sai tai saurin barin gaban Wadrobe ɗin tama fice falo danta amsa kiran.
Faɗowa hoton yay ƙasa kasancewa bata ɗaurashi da ƙyau ba. Hakan yayi dai-dai da isowar Solomon wajen. Take hoton yayi ya matsa jikin Wadrobe ɗin ya cigaba da tiɗo kayan ƙasa shima yana bincike dalla-dalla kamar yanda madam Chioma yaga tanayi.
Tsaf suka gama harmutsa ɗakin basu sami komaiba. Kayan sakawarata ne kawai sai turarurruka da buks ɗinta na addini dana boko. Shiru sukai kowa ransa cike da jin zafin rashin samun komai. Papa ya fara jan tsaki ya fice. Solomon ma ya bi ɗakin da harar ya takema papa baya. Madam Chioma suka bari ƙarshe tanata dube-duben inda zataga envelope ɗin nan amma ta rasa. Ta ɗan juyo zatama Solomon tambayar koya gansa ta shuresa da ƙafa batare data saniba. Kasancewar santsin tiles dana envelope ɗin ya sakashi tafiya suuuu sai ƙarƙashin gado. Taji ƙaran wucewar abu, hakan yasa tahau waige-waige. Sai dai kuma bataga komaiba. Tana niyyar fita ta hango farin takarda a ƙasa mai kama da envelope ɗin. Ɗauka tai ta buɗe sai taga zane ne Aymah tayi a ciki na teddy bear. Cike da takaici tai wurgi da takardan tare da shurar kayan Aymah da suka watso ƙasa tai ficewarta itama.

Cike da jin zafi suka yini a wannan yini. ga Yoohan yaƙi ɗaga kiran kowa a gidan hatta da su Uncle Mike da papa ya saka su kira masa Yoohan a bisa wayonsa.
Sai dai baisan Yoohan duk a lure yake da komaiba. Ya kumayi shirin tsaf akan ƙin amsa wayar kowa tunda yasan dai bai wuce zancen Solomon. Shi kuma ya riga da ya gama yanke hukunci dan yana buƙatar farin cikin matarsa da mallakar zuciyarta yanda ya kamata. Hakan kuma bazai tabbata ba har sai ya faranta mata kamar yanda iyayenta suma suka faranta masa a rayuwa. Sannan shi kansa a yanzu yaga kasancewar Solomon tare da shi a ko’ina babu wani tsari ai. Kodan kiyaye martaba da mutuncin iyalinsa. yana da kishi kuma gaskiya.
Kiran da yaso kawai ya dinga ɗagawa a wannan yinin. Gefe ɗaya kuma yana manne da matsarsa sarkin taɓara suna shan sharafin soyayyarsu. Dan duk hanyar da yasan zata saki jiki da shi ita ya kebi da kulawa a gareta.
Da gaske kuwa aikinsa na yin ƙyau ga jikar ɗan jibiya. Dan sosai karatun nasa ke tasiri akan Nu’aymah yanda ya kamata. Tasan taso Yah Ab kamar zata mutu. Amma lallai da gaske soyayyar ƙuruciyace tai ɗawainiya da zuciyarta a wancan karan da kuma darajar jininsu daya kasance guda. A yanzune take banbance minene ma soyayyar ga mahaɗin rayuwarta.
A hankali ta fara sabawa da yanayin ƙasar U.S ɗin. Ƙasar ƴan gatan duniya masuyin yanda suka gadama a cikinta babu ƙasar data isa nuna musu yatsa. Hatta da U.K ɗin ma data rainesu a yanzu shakkarta suke saboda hatsabibanci da tsaurin ido irin na ƙasar ta Amuruka.
Kwannsu biyu da zuwa Yoohan ya fara aikin daya kawosa. Hakan yaɗansa ta koma yini ita kaɗai a gidan. A rana ta huɗu ma sai kusan gabannin asuba ya dawo gidan. Nu’aymah bata da tsoro sam tun fil’azal. Sai na Duhu da allura kawai. Hakan yasa Yoohan bai taɓa ganin damuwa a fuskarta na barinta gida da yake ita kaɗaiba. Duk da shi duk inda ya shiga tana nan manne da ransa da zuciyarsa.
Kaɗaicin da yake tunanin tana a cikine ya sakashi kaita tai register ɗin sabon layinta ya ɗora mata akan waya. Tare da saita mata duk wani folder na yanar gizo ta koma harkokinta da ƴan uwa da abokan arziƙi. Takoji daɗin hakan dan har ya fahimta akan fuskarta bayan runguma da sumbata daya sha da godiya.
Samar da Sim card a wayar Aymah ya ƙara nutsar da ita. Dan kullum Umm da Hajjo cikin mata nasiha suke da ɗorata akan abinda ya dace. Harma baba malam da Ananah da Addah ba’a barsu a bayaba. Hakama Aunty Hajarah wata shaƙuwace take ƙara shiga tsakaninsu tana koyama Aymah dabarunsu na ƴan zamani akan gidajen aure. Dan tasan wautar ƙanwar tasu.
Alhmdllh aikinsu na ƙyau kuwa. Dan huɗubar tasu nama Nu’aymah tasiri sosai. Har shi kansa Yoohan na fahimtar hakan. Dan randa suke cika sati guda da zuwa U.S da kanta ta samesa da zancen ya kaita tayo shopping dan ta ringa musu abinci. Ita ta gaji da jagwalgwalon turawan nan gaskiya.
Kallonta yayi da kulawa yana ajiye wayarsa da yake dannawa. “Uhm yaushe kika iya girki?”.
Yay mata tambayar da iya gaskiyarsa. Dan shi dai harga ALLAH ba taɓa sanin ta iya yayiba. Ya dai fahimci a fanin gyaran gida yarinyar gwarzuwa ce. Dan yanda gidan nan yake shan gyara a wajenta yana sakashi farinciki matuƙa. saboda a rayuwa yanason tsafta.
Cike da ƙwaɓe fuska take dubansa daga kwancen da take a shakkiyar falon akan carpet. “Amma wlhy ka ragemin daraja. Girkinne kake tambayar yaushe na iya? Kira Umm ko Abbana kaji to. To ALLAH har Abba inama girki, dan nafi Umm ma data koyamin iyawa. Dan ni idan naso a yanzun sai in haɗa maka idea ɗin kalar girkin da zaisa ka manta kunnenka a cikin plate”.
Da ƙyar ya iya danne dariyarsa ya murmusa kawai. Sakkowa yay daga kujerar da yake zaune ya zauna a gefenta ya jingina jikinsa da kujerar tare da ɗan karkatawa. Hakan yasa ta dawo kamar a jikinsan take dan ya miƙe hannunsa ta bayanta a jikin kujerar. Anan kuma ya tanƙwashe ƙafarsa ɗaya, ɗayar ku a ajiye ya ɗaura ɗayan hannunsa bisa gwiwar ƙafar.
“Sweet girl! Dan ALLAH da gaske kin iya girki?”.
Wayarta ta ɗauka batare data bashi amsaba ta shiga ma’ajiyar hotunanta. A take ta ƙwaƙulo masa pictures ɗin abincin da tayi lokacin da yay tafiyar nan. babu musu kuwa ya amsa yana kallo ɗaya bayan ɗaya a tsanake. Harga ALLAH yaji abincin ya birgesa harma yaji ƙwaɗayin abincin 9ja. Amma dai kuma bai gaskata ita ɗin tayiba. Dan haka ya mannata da jikinsa tare da saƙalo hannunta saman cikinta yana shaƙar ƙamshinta ta jikin dokin wuyanta.
“To muje muyi shopping kenan, dan nidai sai anyi a gabana zan yarda. kuma nine zan zaɓi abinda za’a dafa idan kin yarda. Idan kinyi dai-dai kinada ƙyauta ta musamman. Idan kika kuskure akwai hukunci na musamman”.
Cike da gatsen sanin ta iya ɗin ta juyo kanta da ɗora hannunta saman fuskarsa ta shafi sajensa. Da wani salo tace, “Na yarda da wannan game ɗin Mr Man”.
Hannu yasa shima ya tallafo fuskarta tare da ɗora laɓɓansa akan nata yaɗan tsotsa. Jin zai zirma ya saka Aymah galla masa mintsini mai zafi a cinya. Sakin mata kai yayi yana sosa wajen da ɓata fuska kamar zaiyi kuka. Ta miƙe da sauri tana dariyar shakiyanci da faɗin, “Maganin mai kwaɗayin bakin mutane kenan”. Ta ƙare maganar da shigewa bedroom ɗinsu tana dariyarta.
Murya ya ɗan ɗaga yanda zata jiyosa da ƙyau. “Silly girl! ALLAH kinci bashi, nasan ta inda zan fanshe muguntarnan da kikafi ƙwarewa a kai ai”.
Dariya Aymah dake jiyosa daga ɗaki tayi tana zira skirt pink a jikinta irin mai bajewa gaba ɗaya ɗin nan. (Buje inji hausa😂lol). T-shirt yellow sosai da tambarin heart a gaba ta saka a saman skirt ɗin. Sannan ta gyara fakin din gashinta ta ɗaure a tsakkiya tare da naɗa gyale baƙi maiɗan girma sannan ta ɗaura pink jacket mai ƙyau a sama. Sosai tayi ƙyau, musamman yanzu datake ƙara yin wani uban haske jikinta na bajewa da ƙyau ƙibarta na dawowa. Ga ƙirji ya sake cika masha ALLAH. Taɗan saka hoda da lipstick pink kaɗan. Tana saka turare dai-dai misali ya shigo ɗakin. tsayawa yay kawai yana kallonta dan ta masa masifar ƙyau. Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe a kanta da sakin ajiyar zuciya. A ransa kuwa yana ayyana sirrin dake cikin auren ƙaramar yarinya mai yawan gaske. A fili kam baice komaiba sai ida shigowa da yayi ya ɗauka riga shima ya saka a saman singlet ɗin jikinsa. Sannan ya ɗora jacket baƙa shima data sake fidda masa sirrin ƙyau na angwanci dake ɗawainiya da shi.
Gaban mirro ɗin da Aymah ke ƙoƙarin saƙala sidebag ta wuyanta tana daidaitata a gefen cikinta ya ƙaraso. Hannu yaɗan buɗe mata batare da yayi magana ba. Sanin abinda yake nufi ya sakata ɗauka gwangwanin turare batare da tace komaiba itama ta shiga fesa masa. Sannan ta ɗauki comb ta taje masa sumarsa data sake cika kan sosai saboda ƙaunarta da yakeyi, sai dai kuma yanzu askin arzikine a kan ba irin na daba. Sajenma gyara masa shi tayi tana magana cike da tsogumi.
“Nifa karya zam inama kaina ramin muguntane ma. Inje na gama gyaraka wasu tambaɗaɗɗu can suyita kallemin miji. Wlhy duk wadda ta kalla ALLAH ya isana ban yafe ba”.
Cike da neman magana yaɗan waro idanu waje da faɗin, “Uhm uhm fa Sweet girl. Matan U.S ɗin nan shegen ƙarfine da su ba irin na 9ja bane da kika gama rainawa kina karya musu ƙafafu da fasa musu baki. Su laƙaɗa miki shegen duka zasuyi babu ruwana”.
Sosai ta turɓune fuska tana zuba masa harara. Tace, “To na rantse kuwa zakaja kafin mu dawo gidannan a fara wucewa damu police station ɗin garin nan, saboda ɓalla ƴaƴan jama’a zanyi na zubar a banza. Dama gasu ba ƙwariba girman ƙanƙara da Ice-creem da biscuits”.
Ransa fes da fahimtar soyayyarsa dake tattare da matarsa ya rungumota ta baya dan tana gama maganar ta juya tana ajiye turaren data fesa masa. A cikin kunnenta yace, “I love you irin trillions ɗin nan My Cutie”.
Hannu tasa zata ture masa fuska danfa taji haushin zancen ƴammata da yayi mata. Harda Miracle da tuni ta manceta a babin rayuwarta. tunda ita dai tasan itace ta taɓa ɓallama ƙashi da fasama baki.
Da sauri ya riƙo hannunta yana dariya. “Na tuba wasa nake. Ai wannan Zenabu ɗin har abadan a bada, insha ALLAHU ita kaɗaice da Dr Yahya goshpower har ƙarshen numfashi. My angel kece kaɗai uwar ƴaƴana da yardar UBANGIJI. Ke kaɗaice sirrin Yoohan in ALLAH ya yarda. Daga ke babu wata mace data isa sanin koda sirrin murmushin Yoohan ne balle ma ta raɓu miki miji My Noorunnisa”.
Cike da jin daɗin jin kalamansa da suka sanyaya mata jiki ta juyo a hankali ta jingina da mirror ɗin, shi kuma tana fuskantarsa. Ƙwallar da suka taru mata a ido suka ƙarama idanun ƙyau ta zuba masa. A hankali ta motsa laɓɓanta wajen faɗin, “Idan nace kai na dabbane, ina nufin na dabban har ƙasan zuciya da bugun numfashina My boo. Tabbas bani kaɗai bace haske a gareka. Kaima haske ne a rayuwata. Dan ka cetoni daga wahalhalun jarabawar rayuwa da ƙaddara ta tilasta zamansu a tafin hannuna. I love you so very much Yah Yoohan”. Ta ƙare maganar da faɗawa jikinsa ta rungumesa.
Idanu ya lumshe a hankali yana mai ƙarɓarta da hannu biyu. harga ALLAH yanama yarinyarnan soyayya da ƙauna mai tsanani. Wanda ɓata lokacine wajen zama yayta faɗa da fatar baki. Tana riƙe da wasu darajoji da martabobi da mace tagari ce kawai ke iya samunsu a wajen ɗa namiji.
“I love you more…. More…. More and more Zeeynab ”.  Ya faɗa shima cike da shauƙi da sarƙewar harshe a cikin kunnenta. A tare suka sauke ajiyar zuciya sannan ta ɗaggo daga jikinsa. Sumbatar laɓɓanta yayi yana lumshe idanu da sake buɗewa a kanta. Kafin ya juyata suka kalli mirror ɗin yay musu hoto. Sosai sukayi ƙyau kuwa. Tamkar ka sacesu ka gudu dan tsabar dacewa da sukai da juna. Daga haka yaja hannunta suka fice a gidan gaba ɗaya. Cab suka samu zuwa wani haɗaɗɗen shopping mail da Amerikawan ke ji da shi. Dan yasan zasu samo duk abinda zasu iya buƙata a can.
Aiko sosai wajen ya birge Nu’aymah. Babu kunya balle damuwa tattare da ita ta shiga kashe kwarkwatan idanunta tana jinjina jin daɗin duniya da turawan nan keyi. tare da ɗunbin jin tausayin Africans da wahalar Yunwa da kashe-kashe ta gama jigatawa da fiddamu a hayyacinmu gaba ɗaya.
Yana riƙe da hannunta suke duba duk abinda zasu iya buƙata. Kasancewar kowa harkar gabansa ya keyi babu ruwan wani da wani sai suke komai kansu tsaye. Bayan sun kammala shopping ɗin suka fito ta ɗan wajen mail ɗin kafin a gama musu packaging ɗin kayan zasusha coffee.
Sosai Nu’aymah yanzu take bala’in son coffee. Ta rasa dalilin hakan. Dan dacan har haushi takeji yanda Yoohan ya ɗauki amanar kansa ya bama coffee ɗin. Amma tunda suka dira U.S ta koma tamkar mayya akan coffee.
Shi dai Yoohan yakanyi dariyane idan yaga yanda take bankarma cikinta. Cike da shakiyanci yake faɗin, *_Bugun daga kai sai mai tsaron gida kenan_* duk yanda Aymah taso fassara kalmar nan tasa ta kasa. Da taga ma wahala kawai take bama kanta sai ta daina damuwa da sanin. Daya faɗa sai ta zuba masa harara kawai ta cigaba da hidimarta.
Sunsha coffee suna ƴar hirarsu cike da farin ciki. Dan kayansu tuni an tura musu gidansu. Kusan zaman awa guda sukayi a wajen sannan suka miƙe. Gaba sukai wani shagon sai da tsuntsaye dake tsallaken mail ɗin. Aymah ta zabi wasu kyawawan tsuntsaye mata da miji dake cikin keji. Yoohan ya biya yana tausayama ƴan kuɗaɗensa da yau Nu’aymah kema ɗibar karan mahaukaciya😂🤣. Zata ƙara nuna wasu yay saurin riƙo mata hannu yana magana da ƴar hausar daya fara iyawa a wajenta.
“Hy madam ki taimaka mani karki ƙaremin kuɗi anan. Bakiga munyi shopping ba, kalli wallet ɗinafa”. Yay maganar yana nuna mata cikin wallet ɗinsa kamar zaiyi kuka.
Ƴar dariya tayi ƙasa-ƙasa da cewa, “Humm sarkin raki na haƙura. ALLAH zai baka wasu masu albarka tunda ka farantama iyalinka rai ne. Kaima ALLAH ya faranta maka da ƙyaƙyƙyawan sakamako My boo”.
Murmushi yay cike da jin daɗi. Dan duk wautarta ya shaideta da iya lafazi mai daɗi a garesa. Ko tsiwa take masa zaka samu babu kalaman raini a ciki sam. Sumbatar laɓɓanta yayi da kashe mata ido ɗaya, yace, “ALLAH yay miki albarka my Sweet girl”.
“Amin my Boo”. Ta amsa masa cike dajin daɗin addu’arsa. Daga haka suka fito yana riƙe da cage ɗin ƙyawawan tsuntsayen masu daddaɗan kuka. A ƙafa suka ɗan ringa tafiya suna hira kamar yanda Aymah ta bukata. Ya fahimci tanason ganin kanta a inda bata saniba. Shiyyasa yake biye mata wajen ɗan fita da ita dan tai farin ciki, ya kuma rage mata kewar ahalinta daya rabota a cikinsu ya kawo nan ya ajiye.
Saida suka gaji da tafiyar sannan ya tare musu abin hawa suka ƙarasa gida. A barandar gidan suka iske shopping ɗinsu. dan haka ya buɗe gidan suka dinga kwasa suna shiga da kayan ciki har suka kammala.

Sallar la’asar data riskesu a hanya sukai ƙoƙarin gabatarwa. Bayan sun idar Aymah ta fara wucewa kitchen ɗin. Kayan da duk suka siyo ta fara buɗewa tana ajiye komai inda ya dace da zamansa. Tana kammalawa kenan ta ɗakko tukunya zata ɗauraye Yoohan ya shigo waya manne a kunnensa yana magana. Idonsa a kanta ya dafe kitchen cabinet ɗin dayin ɗan tsalle ya haye samansa ya zauna. Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke idanunta ita dai, dan ta fahimci wayar tasa mai muhimmanci ce.
Sai da ta gama wanke duk abinda zatai aikin da shi sannan ta jawo rigan girki ta ɗaura. Dai-dai kuwa da kammala wayar Yoohan. Sauka yay ya nufeta da ɗan alamun gajiya tattare da shi. “Wlhy duk kin gajiyar da ni Sweet girl. Inata murna yau zan huta a gida bazanje asibiti ba. Amma sai da kika sakani yawo”.
Hararsa ta ɗanyi tana riƙe ƙugu da duk hannayenta. Cike da rigima tace, “Uhm uhum uhmyy. Wani aiki sai rago dai wlhy”.
“Oh nine ma ragon?”. Ya faɗa yana wani hangame baki.
Gira ta ɗage masa tana wani juya idanunta manya masha ALLAH. Tace, “Na gaske ma”.
Wata dariyar mugunta yayi yana matsota, da sauri ta manne jikinta da cabinet ɗin tana marairaice fuska. Kafin ta samu damar magana yazo dab da ita. Matseta yay a wajen ya hanata ko guntun space yana wani ɗage gira sama da ciskule fuska. Hannayensa na a gefe da gefenta ya kai fuskarsa gab da tata suna shaƙa da busama juna numfashi. Ga idanunsu cikin na juna kowa kwarjini da sirrin na ɗan uwansa na ratsa masa jiki da zuciya. Da wani irin karya harshe na ma’abota shauƙin soyayya yace, “Yarinya kema kinsan ni ɗin ba rago bane. Amma zan sake tabbatar miki kuwa a yau ɗin nan da iznin ALLAH. Sai wannan bakin rakin naki ya kai titi saboda neman agaji”. Ya ƙare maganar da ɗallar laɓanta da yatsunsa biyu.
Da sauri ta dafe bakin hawaye na cika mata idanu. Ta kai hannu bisa damtsen hannunsa yay saurin kaucewa yana wata shaƙiyyar dariya ƙasa-ƙasa dan yasan muguntar da zatai masa.
Kumbura tayi tai fam. Cike da haushi ta kama rigar zata kunce ya riƙe hannunta. “Ai yarinya baki isa ba. Kin riga da kin yarda da game ɗin nan dan haka girki dole ne”.
Baki ta tura masa tana kwaɓe fuska da faɗin, “Na fasa game ɗin. Girkinma sai dai kay…..”
“Hhh daga baya kenan hajjaju Zenaba ƴar farar bakanuwa ƙyaƙyƙyawa”.
Yay maganar da riƙota hannunta ya maida ɗaurin rigar yana mata wani dariyan iya shege a gefen wuya.
Gaba ɗaya neman susuta mata jiki yake da salonsa. Saurin zame jikinta tai ta koma gefe tana faɗin, “Ai inba yau a kwai gobe indan ALLAH ya kaimu. Ka ɗauka yau ɗin kaine a sama ni a kwana. Sai dai kuma zaka dawo kwanar ne ni na koma ciki…”
Ta ƙare maganar da wani salo tana kashe masa ido ɗaya.
Da gasken gaske saƙonta ya iso inda ta turosa. Dan gaba ɗaya jijiyoyin Yoohan suka saki dama kwana biyun nan rakinta ya sakashi ɗan bata ƙafa. Lip ɗinsa ya cije da ƙarfi yana wani jan ajiyar zuciya ya ɗauke kansa. Batare da yace komaiba ya jawo wayarsa ya miƙa mata. Yana mata wani kallo ƙasa-ƙasa. Amsar wayar tayi da tura baki gaba tana ƙunƙuni. Ta kalli hoton abincin da ƙyau sannan ta ɗan dubesa ta ɗauke kanta tana murmushi.
Kujerar dake gaban tebir ɗin tsakkiyar kitchen ɗin yaja ya zauna. Ya wani miƙe ƙafafu da bajewa da ƙyau, irin fa shine boss ɗin nan.
Nu’aymah bata sake bi ta kansa ba ta fara ƙoƙarin ɗaura girkin tana addu’a a ranta da fatan yin komai yanda ya kamata.

Ko ɗauraye cokali bai tayataba, tunda ta fara. Yama ɗauke kansa gaba ɗaya daga gareta sai danne-dannen waya yake yi hankalinsa kwance. Duk da kuwa a baɗini duk wani motsinta nakan idonsa ne.
Kasancewar ta kwana biyu batai girkin ba yasa takeyin komai cike da ɗoki. Kafin cikar awa ɗaya kuwa sai ga ƙamshi ya gama gauraye kitchen ɗin gaba ɗaya har falo. Shi kansa Yoohan shaƙa yake cike da jin daɗi da kwaɗayin son cin abincin. Tsaf ta kammala komai ta gyara kitchen ɗin da ɗauraye duk abinda ta ɓata duk yana zaune dai yana kallonta. Abincin ta zuba a plate tare da ɗan ɗora kwalliyar data ƙara ƙawatashi ta ɗauki cokali tazo ta dire gabansa tana wani shan ƙamshi.
Idanu ya tsirama abincin dake ta tashin ƙamshi mai saka yunwa. Kafin ya ɗago ya kalleta. Ɗauke fuskarta tai gefe murmushi nason kufce mata. Sai kuma taje ta tsiyayo apple and orange juice ɗin data haɗa a glass cup tazo ta ajiye shima a gabansa. dai-dai yana gyara zamansa. Bai fahimci minene ba, amma yaga sanda take markaɗa abu dai. Cokalin ya ɗauka ya ɗiba abincin kaɗan ya kai bakinsa tare da yin bismilla. Duk da daɗin daya ratsa masa baki da kunne da ƙwaƙwalwa sai ya wani yamutse fuska harya haɗiye. sake ɗiba yay yaci nanma fuska a yatsine. Aymah dai na kallonsa baki a ɗage dan tasan wlhy ƙarya yake yace abincinta babu ɗanɗano.
Cike da son danne dariyarsa na ganin yanda tai da fuska ya kai lauma ta uku. A hankali ya lumshe idanunsa da sauke wata sassanyar ajiyar zuciya. Sai kuma yay mata alamar jinjina da kashe ido ɗaya ya haɗe yatsunsa biyu👌🏼 alamar komai zam.
Itama ajiyar zuciyar ta sauke a hankali da juya bayanta idanunta na cika da ƙwallar farin ciki dajin ƙaunar Umm ɗinta mai tsanani. Dan itace ta maidata tauraruwa wajen tsayawa akanta tun tana ƴar mitsitsiyarta. Ƙanƙantarta baisa Umm ta taɓa rangwanta mata ba akan aikin gida duk da sunada mai aiki. Kamo hannunta da Yoohan yayi ya ɗora bisa cinyarsa ne ya sakata sauke ajiyar zuciya a karo na biyu.
“K ta dabance Cutie”. Ya faɗa a cikin kunnenta yana tura hannunsa cikin rigarta.
Idanunta ta lumshe itama da kai hannunta ta shafo kwantaccen sajensa mai laushi dake cin kuɗaɗe wajen gyaransa. Kiss ya bata a wuya tare da ɗagowa ya kamo fuskarta ya manne bakinsu waje ɗaya. Bata hanashi ba. Dan ya riga da ya koyar da ita wannan sirrin.
Sai da taga wasan na neman canja salone ta ƙwace kanta da ƙyar tana masa dariya. Sai ko ya ƙwaɓe fuska tamkar zaiyi kuka dan da gaske ya zurma da yawa.
Plate ɗin abincin ta ɗauka ta ƙaro musu tare da ɗakko juice ɗin gaba ɗaya shima. Sai lokacin Yoohan ma ya ɗauki wanda ta fara kawo masa yasha yana sauke ajiyar zuciya. Cike da ɗage gira yace, “Kin haɗu a abubuwa da dama Hausa girl”.
Murmushin jin daɗi tayi, dan har ranta tanajin nishaɗi idan ya kirata Hausa girl. Tana son yarenta tana alfahari da shi fiye da zaton mai karatu. Tanaji a ranta komi ta zama dolene duniya tasan itaɗin ƴar ƙabilar HAUSA ce gaba da baya.
Sunci abinci cike da farin ciki, yana bata tana bashi har suka kammala. Da taimakonsa yanzu kam suka tattare wajen suka fice a kitchen yana faɗin ta zaɓi ƙyautarta.
Ita dai dariya take masa kawai. Sai da suka fito falo ya zauna da ita a jikinsa sannan ta dubesa tana murmushi. “Soyayyarka da kulawarka a gareni kaɗai ta isheni tukuyci my sweet boo”. Tai maganar cike da salon da take ƙara ƙwarewa wajen koya a hannun Aunty Hajarahn mai sonta da ƙaunarta.
Rungumeta yay a jikinsa ƙaunarta na sake ratsasa. A ƙasan ransa kuwa godiya yakema ALLAH da samunta tare da jin girma da darajar iyayenta a cikin ransa. Fatansa ALLAH ya basu ƴaƴa masu albarka suma su basu irin wannan tarbiyyar tata abin son kowanne ɗa nagari.

__________★★

Haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa ga Nu’aymah da Yoohan cike da farin ciki da tattalin juna kasancewar har yanzu a amarci da ɗokin juna suke. (Kunsan shi farkon aure dama haka yake. Za’aita nunama juna soyayya cike da zalama. Ku kanku jin kanku kuke tamkar babu ya ku a duniya. Sai rayuwa ta fara nisane abubuwa ke fara tsauri. Sai dai da yake UBANGIJI mai rahama ne da jinƙai sai kaga hakan baya hana a nunama juna soyayya da kulawa koda saɓani na shiga. Duk da jarabawa kan ratsa a zamantakewar ma’aurata kaga matsalolin nata yawaita fiye da hasashe. ALLAH ya cigaba da zaunar damu a gidajenmu lafiya tare da mazajenmu da ƴaƴanmu da abokan zamanmu baki ɗaya mata sarakunan gaskiya a fadar gaskiya😘😍🤗).

Kwansu goma sha uku a U.S Yoohan yay shirin zuwa Oman yin wani aiki na kwana biyu. Daga can kuma zai wuce Nigeria insha ALLAH.
Yasha taɓara kuwa a wajen Aymahn sa. Dan kuka sosai ta dinga yimasa akan saita bisa. Da ƙyar ya lallaɓata da tabbatar mata Juliet matar Omar (Rich) tana zuwa daga 9ja a daren yau. Idan ma batason zaman anan gidan ita kaɗai sai ya kaita gidan Juliet ɗin ta zauna a can harya dawo.
Da ƙyar ta amince kuwa. Shima sai da aka haɗa da hajjo wajen lallashi. A ranar kuwa Juliet ɗin ta iso. Sun tarbi juna da mutuntawa. Kuma har cikin zuciya Nu’aymah taji zata iya zama tare da Juliet ɗin. Musamman yanda taga itama Juliet ɗin na nuna mata ƙauna da yaba komai nata tana sake taya Yoohan murna. Shi dai murmushi kawai yakeyi yana bin mutuniyar tasa da kallo ƙasa-ƙasa.
Washe garin da zai wuce sai da ya rakata gidan Juliet sannan ya wuce ya barta da kewarsa kamar yanda shima ya tafi cike da tata kewar.

★★★★

Tamkar jira jikin Aymah keyi Yoohan ya wuce ta fara ƙananun ciwuka. Kullum da zazzaɓi take wayar gari, zuwa ƙarfe ɗaya na rana kuma sai ya gudu. Tun Juliet bata fahimtaba harta fahimta saboda shaƙuwar dake ƙara shiga tsakaninsu da Nu’aymah. Dan Juliet tanada sauƙin kai sosai. Bata taɓa kuma nuna ƙyamar addinin Nu’aymah ba koda kuwa akan fuskartane. Wani lokacinma idan Aymah na salla ko karatun Al-qur’ani har zama take taita kallonta. Dan itama zuwa yanzun tasan mijinta Omar (Richard) ya musulinta…………✍

*_Gaba ɗaya na manta yau monday fa😥🤦🏻🏃😂_*

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[7/1, 2:39 PM] +234 806 331 2486: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply