Hausa Novels Saran Boye Hausa Novel

Saran Boye 73


Saran Boye 73
Viral

No. 73

………….A yau kam su Nu’aymah da duk wanda yasan da wannan shirin sun tashi a shirye tsaf bisa yaƙinin tarkon da suka ɗana ya ɗanu. Kasancewar sanyi da akeyi duk sauran jama’ar gidan da ƴan biki suna can a sassan gidan a maƙale, duk da madai ƴan bikin da suka rage duk na jikine babu bare. Babu kowa a tsakar gidan sai yaran Jay dake ɓoɓɓoye.
Yau kam Jay ya shiga har falon baba malam tare da lauyan malam mahaifin su baba malam a zuwan zasu tattauna akan kaddaririn baba malam ɗin. Acan kuma ta waje little bee ce da wasu jami’a a harabar gidan a mabanbanta wajaje duk da Jay yasan akwai camaras ɗin da Afrah ta saka masa a wancan zaman. Yafi buƙatar gani ga ido ga kowa kafin ya bankaɗa sirrikan dake a cctv ɗin. An kira Aymah da Yoohan falon, sai su Abban Abdallah da hajjo data san komai itama. Sai Omar da yazo matsayin lauyan Nu’aymah shima.
Bayan buɗe taro da addu’a baba malam ya fara da nasiha a garesu duk dai a cikin salon tarkonsu, dan a zahiri fa babu wani maganar mallakama Nu’aymah kaddarorinsa da yakeyi. Shirine kawai irin nasu Jay.
A gefe kuwa idanun su Yoohan gaba ɗaya na’a Windows ɗin falon a kaikaice. Baba malam kuwa na cikin nasiha sai ga abinda suke jira ya bayyana. Kallon juna sukai shi da Jay dasu Yoohan sukayi murmushi. Daga haka ya cigaba da bayaninsa hankali kwance.

Acan waje kuwa su Little bee na mammaƙale a maɓoyarsu sai ga mutum sanye cikin dogon hijjab har ƙasa da niƙab ya fito daga tacan bayan gidan yanda babu mai iya fahimtar daga ainahin sashen da aka fito. Basu da tabbacin mace ce ko namiji, dan komai an rufe ba’a gani.
A yanda mai laɓe ke tafiya da dabaru zaka san cewar lallai an ƙware, sannan aikine da akeyi tunba yanzuba. Cikin salon iya aiki Little bee taima abokan aikinta wani salo da yatsun hannunsa suka bada ɗass!! Sau ɗaya. A take duk suka ƙara shiryawa dan suma dai suna biye da mai laɓe akan idanunsu.
Sai da suka tabbatar mai laɓe ya isa dai-dai sashen Malam marigayi alamar dai ɗan gidanne, tunda har ansan a ina su baba malam zasuyu taron nasu aiko sai wanda yasan gidan. Kamar yanda mai laɓe ya saba a koda yaushe ya isa jikin Window. Wani siririn abu ya saƙa a tsakanin glasess ɗin Window ɗin da alama na ɗaukar magana ne. Dan yana gama turashi ya kai hannu ya taɓa kunnensa alamar tabbatar da daidaitar komai. Ƙaramin tsaki akaja jin Nasihar da baba malam ya fara dan ba ita ake buƙataba a yanzu. Jin baba malam zai fara jawabinsa mai laɓe ya ƙara nutsuwa da maida hankalinsa ga window ɗin domin saurare..
Da wannan damar su Little bee sukasamu isowa wajen cike da ƙwarewar aiki suka toshe gaba da baya na ɗan siririn lungun bayan ɗakin malam marigayi. Ƙarar saƙon daya shigo wayar Little bee daga Jay ne ya fargar da mai laɓe ya juyo da sauri. Sai kawai ganinsa yayi zagaye da mutanen da baisan ta ina suka ɓullo ba.
Tashin hankali ba’a saka maka rana. Wannan shine ɓoyayyar kalma a zuciya da bakin mai laɓe duk da bai fito ya furta manaba a zahiri. Dan kuwa dai gabas da yamma kudu da arewa babu wajen guduwa. Katanga a bangon gabas. Ginin sashen malam a bangon yamma. Little bee da jami’ai uku a bangon kudu duk sun nunasa/ta da bindiga. Dawood da jami’ai uku shima a bangon arewa duk sun nunata/sa da bindiga nanma.
Wannan itace kwana casa’in da tara ta barawo ɗaya tak ta mai kaya. Little bee ta ciwo wayarta da hannu ɗaya a aljihu ɗayan kuma riƙe da bindigar data nuna mai laɓe. Kiran Jay tayi a waya. Yana ɗagawa tace, “Sir! Aikinmu ya kammala zaku iya fitowa”.
“Woow!” Jay ya faɗa yana miƙewa idonsa akan su baba Malam. Takawa yay jikin windown da yake hango inuwoyinsu ya zuge gilas ɗin tare da net. Abinda mai laɓe ya saƙala ya faɗo. duƙawa yay ya ɗauka yana jujjuya shi a hannunsa kafin ya kalli su baba malam da suma duk shi suke kallo.
“Malam zama ya ƙare ai, suspect ɗinmu yazo hannu zamu iya zagayawa”.
Harga ALLAH sai da gaban baba malam da Umm ya faɗi. Hakama Aymah duk sai taji tsoro kuma. Su Abba Musbahu da basusan mi akeyiba suka shiga kallonsu da tuhuma. Ko a jikin Yoohan da Umar. Dan sunema farkon ficewa a falon.
Baba malam dake kallon su Abban Abdallah yace, “Kuyi haƙuri wannan itace kawai mafita a garemu gudun kar wataran a kai ga rasa rai bisa makircin da bamusan wake ƙullasa ba”. Daga haka yay gaba ya barsu da kallon kallo ma juna sai dai ganin kowa ya fice suma sukabi bayansu jiki a sabule.
Ganin duk sun iso Little bee ta dakama mai laɓe tsawa da faɗin, “Cire Niƙaf”. Ko motsi ba’ayiba. Sai dai yanayin tsayuwar ya tabbatar da koma wanene a tsorace yake kuma cikin ƙololuwar tashin hankali da firgici.
“Inada cikaken dama nayin harbi, hakan na nufin bullet ɗin zasu iya fita a cikin bindigarnan zuwa jikinki/jikinka a koda yaushe. Zan irga iku kawai bisa lasisin dama a gareki ko a gareka. *_Ɗaya! Biyu! Uku!!”_* ta fita daga bakin Little bee tare da bullet ɗinta zuwa ƙafar mai laɓe da ko motsi baiyiba balle ya nuna kota nuna zata cire nikab din da aka bada umarni.
A take ƙarar muryar mace ta karaɗe gidan saboda azaba shigar bullet. Ƙasa ta durƙushe jiki na rawa. Da wannan damar Little bee ta ƙarasa gareta tasa hannu ta fisge niƙab ɗin ta jefar gefe. Baba malam da Umm da sauri suka kauda kawunansu gefe da tsananin fargabar tsoron ganin koma wanene. Sai da Nu’aymah ta furta,
“Illalillahi wa’inna ilaihirraji’un Addah!! Kece dama?!!!”.
Sannan su Umm suka juyo a firgice. A take wajen gaba ɗaya ya ɗauki salati. Dan duk jama’ar gidan kururuwar ihun Addah da Little bee ta harba dama duk ya fito dasu a hautsine.
Cikin girgiza kai hawaye na sakkoma Umm a guje tace, “Inaa bazai yuwuba. Addah ki sanar musu ba abinda suke zargi bane ya kawoki nan. Dan ALLAH ki tabbatar musu domin bamu kariya kema kika zo nan. Ki tabbatar musu bake bace kike laɓen nan dama can dan ALLAH, kicemin yau kika farayi……”
“Bata da bakin baki waɗan nan amsoshin domin wanke kanta Umm-Muhammad. Domin kuwa duk saɓaninsu da baki eson ji daga bakinta sune gaskiyar amsoshin naki da ma kowa dake anan wajen”.
Bily dake kusa da Jay tsaye ta bama Umm amsa kanta tsaye.
“Karkice dani haka Maman Awwab. Dan ALLAH karkice haka. Wannanfa Fauza ce, wadda muka tashi tare tun ƙuruciya tamkar uwa ɗaya uba ɗaya ta haifomu. Ban taɓa ɓoye mata sirrinaba, itama bata taɓa ɓoyemin nata ba. Tare muke raba farin ciki, sannan mu raba kuka tare idan ya samemu…..”
Murmushi Bily tayi da takawa a hankali zuwa gaban Addah daketa faman magowar azabar ƙafarta dake zubda jini. Ta nunata tana mai kallon Umm ɗin, “Tabbas a zahiri haka take a gareki Umm-Muhammad. Amma a baɗini itace babbar maƙiyyarku. Idan kuna buƙatar tabbatarwa mu a shirye muke wajen nuna shaidar gani da ido a gareku dan duk mun tanajesu dama”. Ta ƙare maganar tana duban su baba malam da alamu ya nuna tamkar duk sunyi sumar tsaye ne har yaran Addah da duk suma suna a wajen.
Daga haka Jay ya bama Yoohan da Omar damar cire bullet ɗin jikin Addah. Cike da ɗacin murya Yoohan ya dubi Jay ɗin idanunsa jazur. “Uncle ka gafarceni, hannuna bazai taɓa iya aikata jinƙai ga maci amana ba”. Daga haka ya kama hannun Nu’aymah da jikinta ke karkarwa suka bar wajen.
Murmushi kawai Jay yayi. Baba malam zaiyi magana Jay yace, “Karka takura masa Malam. Umar Please ka cire mata sai mu wuce da ita. Malam sai ku samemu a statlon ɗinmu nan kano mu ƙarasa maganar”.
Da sauri baba malam yace, “A’a Jawaad ina neman alfarma komi zai faru muyisa anan cikin gidan domin rufin asirinmu, wannan itace alfarmar da zan nema a gareku”.
Ɗan jimm Jay yayi, sai kuma ya kaɗa kansa alamar karɓawar alfarmar baba malam ɗin.
Badan Umar yaso ba ya amince zai cire. Dan haka aka ɗakko Adda daga lungun zuwa sashen Malam. Gaba ɗaya yaran sa’an su Muhammad zuwa kansu Adawiya ba’a barsu sun shigaba. Duk da kuka da Adawiya keyi iyakar ƙarfinta wanda babu wanda yasan dalilinsa. Su Hajarah da sauran yayunta na ma’auri duk suna gidajensu basusan abinda akeyiba. Sai malam ƙarami kawai da sauran ƙannensu. Shiko gaba ɗaya da alama ma jinsa da ganinsa sun gushe dan bai iya motsawa a lungunba har kowa ya fice. Hakama Abba Mustapha saida Hajjo ta kama hannunsa da kanta saboda tsabar firgici.

★★★

Bayan azabar cire bullet da Addah ta gama sha Omar yay mata allurar rage raɗaɗi. Umm dake kuka har yanzu ta sake duban Addah. “Fauza dan ALLAH ina roƙonki a karo na ƙarshe ki ƙaryata tuhumar da ake miki. Ki tabbatar musu da kawai yau ƙaddara ta kawoki amma ba ke bace. Har abada bana fatan kunnuwana da zuciyata suji saɓanin tunaninsu a kanki Fauza…….”
Shiru Addah batai ko motsiba, kanta a ƙasa kuma taƙi kallon kowa. Gyaran murya Jawaad yayi da gyara zama. “Hajiya karki wahal damu anan, dan alfarma ki ke ci, badan darajar malam ba da zamu wuce dake station ne ki mana bayani ta duk hanyar da mukaso bi da ke. Kar kiyi tunanin ɓoye mana komai dan a tafin hanunmu kike, duk wanda ke cikin labarinki sai da na gurfanar da shi a gabana kafin ki ganni anan, na zaɓi bin komai mataki-mataki ne saboda sauƙaƙa firgici a zuciyar waɗanda kikema cin dunduniya. Nasan kinsan Hamisu ai gashi a gabanki tsaye”.
Da sauri Addah ta ɗago ta kalli inda Jay ke nuna mata. Kallon ido cikin ido sukaima juna kuwa ita da Hamisu. ya ko zuba mata mummunan kallo. Da sauri maida kallonta ga Jay. Kai shima ya jinjina mata fuska a ɗaure. “Bayan Hamisu akwai ƴarki Kubrah ko, sannan akwai……”
Da sauri ta ɗaga masa hannu, sai kuma ta fara tari, gefen ɗan kwalinta tasa ta tare bakinta sai ga jini na zuba. Babu wanda bai mata kallon tsoro da firgici ba a falon. Ta goge mabinta saboda tsagaitawar tarin sannan ta kalli kowa dake falon tana Murmushi mai ciwo a karon farko. Ta kalli ƙafarta dake naɗe da bandage hawaye na ziraro mata. Dan har yanzu tanajin raɗaɗin azabar shigar bullet a karon farko na rayuwarta. Kallon baba malam tayi ta sake sakin murmushi sannan ta maida akan Umm dake a gabanta zaune.
“Ko babu ƙarfin iko hukuma dama lokaci yayi da Firdausi! Zata san wacece Fauza a gareta. Dan tun bayan auren Nu’aymah wannan ranar dama nakewa zaman jiran tazo a gareni, dan nasan tana cikin ranakun da ko naso koban soba sai sun riskeni a duniya ko a lahira, musamman daya kasance gajerun kwanaki suka ragemin a duniya. Wannan Fauzar dake gabanku ba Fauza bace ta shekarun baya mai lafiya, hatsabibiya, mai aiki da zuciya kawai bada tunaniba, mai son kanta, mai aiki da huɗubar shaiɗan. Wannan Fauzar maƙasƙanciyace a gabanku yanzu, mai rauni, mai ɗauke da ciwon zuciya da ciwon kansar jini (blood cancer), wadda likita ya tabbatarma watanni kaɗanne suka rage mata a duniya. Wannan Fauzar mai dana sani ce da nadama da yin kaico akan ayyukan data tafka batare daku kun saniba saboda iya SARAN ƁOYE”.
Tarine ya kuma sarƙeta da kuka. Nanma tanayi jini na fita, saida ta tsagaita sannan ta sake dubansu. “Da wahala shara’ar alƙalin duniya ta iya dacewa da laifukan Fauza, shara’ar UBANGIJI datafi cancanta dani ta fara bayyana a gareni tun daga randa likitanci suka sanarmin sakamakon abinda nakeji a jikina. Amma lallai halina dolene yaje kunnunwan mai saurare ko zai zama izina ga masu irin halin suji tsoron ALLAH su canja kafin lokaci ya ƙure musu”.
“Firdausi! Da gaske ni Addah na soki so na gaskiya a zamanin ƙuruciyarmu. Duk da ko a wancan lokacin duk randa kika samu abinda ni nafi cancanta da samunsa inajin zafinki a raina. Musamman idan nai la’akari dana fiki komai a rayuwa. Ni ƴar gatace ko a gidanmu, duk wani jin daɗi da yaro kan tashi ya samu daga iyaye na samesa. Mahaifina yafi naki komai a rayuwa. Hakama mahaifiyata tafi taki. Hasalima da yawan lokuta ƴan gidanku kunaci ne daga alfarmar iyayena. Sai dai kash duk da wannan gatan namu da tarin alfarma kin fini basirar karatu, bama ke kaɗaiba duk ƴan gidanku ALLAH ya basu wannan baiwar, gashi duk kun fimu ƙyau, sannan da wahala ku zauna da mutane basu soku ba. Dan yayyenki ma sunsha ciwo nasarorin dake sa yayuna jin zafinsu, sai dai mahaifiyarmu kan ƙwaɓemu akan hakan. Nasararki a kaina bata taɓa kaini ga ƙololuwar jin zafinkiba sai a randa Sheikh Soorajidden yazo har gidanmu akan neman aurenki”.
Ta share hawaye masu zafi dake gangaro mata har yanzu sannan ta cigaba da faɗin,
“Hakan ta faru dalilin soyayyarsa da taimin shigar sauri cikin zuciya tun a ranar kammala karatunmu. Idan baki mantaba tun a wajen bakina bai hutaba da zance a kansa har kika nuna ƙosawarki akan hakan. Mun dawo gida zuciyata na ɗunbin begensa, sai dai a randa na buɗi ido na gansa a gidanmu sai labari ya canja salo. Ke! ke! ke!! Firdausi! kin sake yanke igiyar nasarata kamar yanda kika saba a koda yaushe”.
Tai maganar da matsanancin kukan da har ya hanata kasa cigaba da magana sai da tai tari mai tsaho. Falon kansa yayi tsit ko motsi kowa ya kasa saboda shock. Da ƙyar ta tsagaita kukanta da tarin sannan ta cigaba.
“Naji zafinki a wannan ranar zafin da idan aka bani makami zan iya halakaki. Nayi kuka harna rasa hawayen zubarwa. Amma daga ƙarshe sai nayi haƙuri bisa ga shawara da nasihar da babbar yayarmu ta min, a lokacin sai naji na haƙura na barmiki, duk da dai son nasa na nan maƙale a raina. A haka aka kammala komai na maganar aurenku ni bani da wani tsayayyen saryima. Har lokacin biki yayi mukasha bikinku. ALLAH ya sani ban taɓa cin karo da rana mai ciwo da raɗaɗi ba irin ranar aurenku. Dan aranar na gama yanke hukuncin dolene na shigo gidanki matsayin kishiyarki. Amma sai kash. Ƙaddara ta riga fata, dan kuwa haɗuwata da Mustapha sai ta kasance almakashin daya datse wannan zaren a karo na biyu. Ya nuna yana sona, amma ban amsa masaba a ranar, shi kuma ya zata kunyace ta sani ƙin amsawar, dan haka yay amfani da wannan damar yayma rayuwata kutse ta bayan gidan adalilin neman aurena da Sooraj yaje yayima ƙaninsa a gidanmu tamkar yanda yayima kainsa. Babana kuma babu wani tsayawa ja’in-ja ya bashi. Na sake shiga ruɗani a karo na biyu, amma sai yayata dai ta sake ɗorani akan mizanin hankali da nasiha kamar wancan karon. Ta kuma tabbatarmin Mustapha shine mijina dama ba Sooraj ba, tanada yaƙinin kuma shine zai zama mafi alkairi a gareni insha ALLAHU. A wannan karonma taci nasara. Dan duk da babu son Mustapha a raina na aminta zan auresa kodan darajar jini da suka haɗa da Sooraj, sannan a fuska ma suna kammani da juna”.
Ta share hawayenta tana murmushi da kallon Umm.
“Firdausi! Shigowata gidan nan shine ya sake canzama zuciyata salo a kanki. Dan tun a yanayin taron aurena da Mustapha na fahimci a wannan gaɓarma kin sake min tsere. Ban sake tabbatarwa ba sai da na tabbata ɗaya daga cin wannan ahalin. Zamantakewar ki da Sooraj tana ɗaya daga abinda ya dagula min tunani. A zahiri mutane ɗauka suke tsoron Sooraj kikeyi, amma wanda zai ganku a sashenku kaɗaine zai goge wannan tunanin a ransa saboda soyayya da tattalin da kike samu daga garesa. Sannan kasancewarsa babban ɗa a gidannan duk wata daraja ta matar gida kin kwashe a sama da tamu. Wannan yasa ita kanta Momyn Abdallah kejin zafinki ganin anan kikazo kika sameta. Abinda ya ɗan sakamin sassauci a kanki lokacin haihuwa dana rigaki yi kuma namiji, har takai sai da na jera huɗu sannan kika samu ciki. Maganar gaskiya bazan ɓoye mikiba naji matuƙar jin kishi akan samun cikinki duk da kuwa inada ƴaƴa har huɗu a lokacin. Dan idan ina ƙaunar mutuwata to ina ƙaunar buɗar ido naganki da wani cigaba daya ɗara nawa a rayuwa, dan na tsani cikin nan naki tun yana ɗan tayinsa. Duk da ban taɓa tunanin cutar dake ba adalilin cikin nan zuciyata ta fara rayamin hakan, dan kullum huɗuba takemin na ɓarar da cikin kawai kowa ya huta. Sai dai ina shirin aikata hakan a gareki Sooraj ya ɗaukeki kuka wuce saudia, nayi baƙin ciki nayi takaici irin wanda bazai misaltuba. Gashi baku dawoba sai gab da zaki haihu. Koda kuka dawo ban fasa aiwatar da ƙudirina akan cikinki ba, sai dai babu wata makamar yin hakan dana samu har ALLAH ya saukeki lafiya a wani dare. Hankalina ya tashi ganin kema da namiji kika fara, zuciyata ta sake bushewa da kangarewa akan na kashesa kawai tun yana jaririn………”
Cikin ɗacin murya Baba malam ya katse Addah da cewar, “Fauza kenan kece kika kashe mana yaro?”.
Kuka Addah ta sake fashewa da shi kanta a ƙasa ta kasa kallonsu. Ga tari ya kuma sarƙeta har jini na fita guda-guda yanzun.
Ko batace komaiba sun fahimci shirunta na nufin haka ɗinne. A take gaba ɗaya falon suka ɗauki salati. Umm kam ido kawai ta tsurama Addah hawayenma sun tsaya cak. Hakama baba malam kallon ƙasa kawai yake ya gaza koda motsi. Abba Mustapha zai miƙe Hajjo ta hanashi, dan har yanzu ai ba’azo inda take buƙatar ba.
Jay ne ya katse shirun nata da faɗin, “Ke muke saurare”. Yay maganar yana kallon agogon hannunsa.
Da ƙyar Addah ta tsagaita kukanta ta cigaba da faɗin, “Na shaƙa masa maganine, irin wanda naso shaƙama Nu’aymah aka samu akasi Rabi mai aikinki ta kusa rutsani, dan a lokacin kin tafi wanka Nu’aymah kin barta ta dinga leƙata a ɗaki, ni kuma saina aiketa domin aiwatar da ƙudirina, sai akai rashin sa’a kafin na shaƙama yarinyar maganin Rabi ta shigo, motsin nufowarta bedroom. Wannan shine dalilin tsoratata na saketa a ƙasa kanta ya bugu. A take ta suma, ni kuma nai saurin ɓoyewa dan kar rabi ta ganni gakuma kema naji yanda kika rikice a toilet kina ƙoƙarin fitowa. Sai da ta fita da gudu tana ihun kiranki saboda rikicewar da tayi ni kuma na samu na fita a sashen, daga baya na shigo cikin matan gidan muka shiga jajen yaya akai a tare. Kowa yama zata Nu’aymah ta rasu, sai dai hajjo ta matsa a kira likita. Zuwansane ya tabbatar mana da suma tayi, ba haka nasoba, amma lokacin da aka dawo da ita daga asibiti da tabbacin sanadin faɗuwar tata ta samu ciwo a ƙwaƙwalwa sai naji daɗi a raina saboda bushewar zuciya da huɗubar sheɗan”.
“Likita ya fara ɓusa zargin yaddota akai daga gado, kema kuma Firdausi kin tabbatarma kowa kina toilet kinji motsin shigowar mutum bedroom ɗinki, sai dai kin zata Rabi ce, sannan kuma kinji sanda yarinyar ta faɗi ƙasa ta bugu. hakan yasa aka tuhumi Rabi, amma kuma saita rantse da iya gaskiyarta ba ita bace dan nama aiketane ta dawo,, tana shigowa taji ƙarar Nu’aymah datai sau ɗaya kafin ta suma. Maigadi ne ya sake wanke Rabi a wajen kowa. Haka kawai na tsargi kaina akan karfa asirina ya tonu, dalilin da yasani saurin ɗaukar mataki kenan na saka malamin da ya bani abinda zan shaƙama yarinyar rufemin bakin kowa a gidan nan akama bar wani hasashe-hasashen son sanin yaya akai Nu’aymah ta faɗo a gadon?. Ban sake yunƙurin cutar da yarinyarba, dan a ganina ciwon data kamu da shi ya isa kai rayuwarta ƙarshe. Sai dai na saka an daɗe bakin mahaifarki yanda bazaki sake haihuwa ba. ALLAH kuwa ya amincemin baki sake samun ciki ba sai bayan haihuwar Nu’aymah da kusan shekaru biyar, hankalina ya sake tashi na nufi malamina. Saina iske ALLAH ya masa rasuwa. Lallai nayi gamo da tashin hankali na haƙiƙa a wannan lokacin, dan zan iya cemuku daga wannan lokacin ban sake samun malamin da yaymin aikin da yaci a kanku ba…….”
“Mtsoww!! Malami ko boka dai”. Abban Abdallah ya faɗa a fusasce.
Wani irin kallo Addah tai masa, sai kuma ta kwashe da dariya ta ɗauke kanta kawai. Hakan da tayi kuwa yaba kowa mamaki. Amma sai babu wanda yayi magana. Har shima Abban Abdallah ɗin bai sake cewa komaiba.
Addah ta cigaba da faɗin, “Tunda na fahimci aikin malami ya daina tasiri sai na koma laɓe da son zubar da cikinki, to ALLAH ya tabbatar Muhammad sai ya shaƙi iskar duniya sai gashi kin haihu lafiya duk da ba haka nasoba. ta wannan hanyar laɓe ne nakejin duk wani abinda ya shafeku, dan duk da amintarmu firdausi ke mutumce mai zurfin ciki. Nakan faɗa miki sirrikana kai tsaye ko kema zaki warwaremin naki babu shamaki. Amma sai da na fara muku laɓe na fahimci kina bala’i-bala’in rainan hankali. Dan babu wani sirrinki mai muhimmanci da kike sanarmin sai ƙananu kawai. Hakan yasa nima na ɗauki ɗammarar bi dake ta yanda kikazo min”.
Ta kai dubanta ga Abban Abdallah. Wanda a take mood ɗinsa ya canja ya wani zazzaro mata idanu kamar zai haɗiyeta da su. Murmushi tayi da ɗauke kanta ta cigaba da faɗin, “A dalilin son halaka Muhammad na haɗu da babban makirin daya ƙara faɗaɗa ƙwaƙwalwata akan ƙiyayyarki da zuri’arki. Dan ta sanadinsa ne wasan ya canja salo daga soyayyar Sooraj zuwa wani abun daban. Ba kowa nake nufiba sai Lurwan ga shinan”. Tai maganar tana nuna Abban Abdallah da tun fara maganar tata ya zabura zai miƙe a fusace amma Hajjo ta riƙoshi cikin fushi.
Babu wanda bai zaro ido ba a jama’ar falon. Abban Abdallah ya sake zabura yana ƙoƙarin ƙwace hanunsa daga hajjo. “K baƙar annamimiya, makira, azzaluma. dan ubanki sharrin naki da makirci yazo kainane kenan komai?”.
Dariya sosai Addah tayi tana kallonsa, tace, “Lurwanu ai ka fini iya makirci, dan kaine malamina a wannan fanin kuwa. Da farko ta hanyar malami kawai nake samun nasara akan Firdausi, amma haɗuwata da kai ya sani hutawa daga zuwa wajen kowanne irin malami, dan kai kafi malamin hatsabibanci ma. Yau ranace mai kama da ranar hissabi, yanda nasan cewar ayyukanmu bazasu ɓoyu ba a wannan rana dake jiranmu to ina tabbatar maka yau ɗin nanma tun a duniya zan fara fallasasu dan kowa ya yaji. Dan wlhy yanda duniya tasan waceceni a yau, ƴaƴana sukaji shukar danayi, mijina yaji, dolene kaima uwarka da yayanka da matarka da ƴaƴanka da sauran ƴan uwanka susan kai wanene a cikinsu”.
Sake zabura yay kanta kuwa da ƙarfin tuwo ya fisge hannunsa a cikin na hajjo, amma sai Dawood yay azamar shan gabansa da bindiga. “Ka kama girmanka, inba hakaba zan maka irin tabon dake a ƙafarta kaima. Ka nutsu ka riƙe sauran mutuncinka”.
Jikin Abban Abdallah rawa yakeyi sosai, dan bai taɓa kawowa a ransa tone-tonen Addah zai iso kansaba musamman da yasan irin gargaɗin da yay mata kafin ya yarda su fara aiki tare, da kuma kalaman datai amfani dasu a yau wajen shimfiɗa labarinta. Yayi zaton zata rufa asirinsa ne.
A hankali baba malam ya yunƙura ya miƙe hawaye na sakko masa akan fuska. Yasa babbar rigarsa ya share sannan ya dubi jama’ar falon. “Inaga dan ALLAH mubar maganarnan gaba ɗaya, wannan tone-tonen a ganina sam bashi da amfani. Sun aikata abinsu a ɓoye sai mu barsu kawai da nauyinsu suje can su ƙarta. Bana buƙatar jin abinda Rudwan ya aikata ku barni haka, n…….”
“Dolene kuwa kaji ɗan malam, dan haka koma ka zauna”. Hajjo tai maganar cike da bada umarni. Baya iya ƙetare maganar mahaifiyarsa. dan haka ya koma jagwab ya zauna yana mai dafe kansa da hannaye biyu saboda jirin dake kwasarsa.
Addah tai murmushi mai ciwo da cigaba da faɗin, “Lurwanu shiya canja tunanina daga fushin rasa masoyi zuwa na mallakar dukiya, dan huɗubarsace ta fahimtar dani cewa ina dukan taiki ne kawai ina barin jaki, haukana kawai nake akan nafi Firdausi ƴaƴa nafita nasara yanzun. sai dai ashe dukiyar da mijinta ya mallaka a cikin ƴan uwansa ta ninka wadda nawa mijin ke da shi sau fiye da bakwai. Kaso biyu na dukiyar gidan nan mallakarsace, kaso ɗaya ne na mazajenmu da Hajjo. Gaba ɗaya komai ya susuce min a lokacin nama nema rasa makamar tunani da hankalina. Amma sai ya dinga kwantarmin da hankali ta hanyar nunamin inhar zan taimakesa muyi aiki tare to lallai dukiyar baba malam zata koma ƙarƙashin ikonmu ne. Nace masa ta yaya kenan?. Ya bani tabbacin ta hanyar Abdallah. Tunda akwai shaƙuwa sosai tsakanin Nu’aymah da Abdallah hakan na nufin nangaba kaɗan soyayya zata iya bayyana a tsakani duk da ƙuruciyarsu.  Dan bazaiyi wasaba wajen ɗora Abdallah akan matakin daya kamata game da Nu’aymah. Ɗari bisa ɗari na yarda da hakan a wancan lokacin. Saboda a yanda ya faɗaɗa min bayanansa na fahimci inba ta wannan hanyarba babu ta inda zamu mallaki wannan dukiyar. Wannan shine sanadin dunƙulewarmu waje guda ni da Lurwan muka fara aiki tare. Amma wlhy kullum hankalinmu cikin ƙara tashi yake gameda haɓaka da dukiyar Sooraj keyi abun tamkar roƙo. Shima kuma sake ɗaukaka yakeyi fiye da sauran ƴan uwansa akan ilimi da soyayyar mutane. Wanda ɗaukakar tasa itama tana ɗaya daga cikin abinda ke ƙara ɗora Lurwan ga son cutar da shi. Haka muka cigaba da tafiya munama Sooraj *SARAN ƁOYE* da iyalinsa harma da duk wanda tsautsayi ya sakko a tarkonmu. Dan kuwa dai Rabi na ɗaya daga cikinsu. Mun sakata tana mana wasu ayyukan akan dole wasu ko bama tasan muna amfani da ita munayiba musamman ta wayarta. Akwana a tashi mun cigaba da tafiya wataran muyi nasara akan aikinmu wataran su tsallake tarkonmu. A haka maganar soyayyar Abdallah da Nu’aymah ta fito, har takai Nasir yayi zuciya yabar gidan nan dan shima yana sonta. Da gaske Abdallah tsananin son Nu’aymah yakeyi, kamar yanda itama sonsa takeyi saboda tsananin shaƙuwar dake a tsakaninsu, amma a hankali muka fara canja tunanin Abdallah muna kwaɗaita masa dukiyar Sooraj. Tun yaron nan baya fahimtar mi muke nufi yana bijire mana harya hau kan hanya saboda ɗaukesa da iyayensa sukayi zuwa wajensu. Dan mun fahimci zamansa da Firdausi ne ke mana illa komin masa huɗuba itake wargaza mana komai ta hanyar ƙaunar da take nuna masa ta gaskiya. Gaba ɗaya mun tattara shirinmu ne akan auren Nu’aymah da Abdallah, shiyyasa duk likitan da aka samo da tabbacin zai mata aiki akan matsalarta sai munbi duk hanyar da zamubi wajan daƙile hakan saboda wani likita ya tabbatar mana da wahala ai mata aikin nan ta tashi, mukuma burinmu muyi amfani da wannan damar sai bayan aurenta da Abdallah aimata aikin ta sheƙa mu samu abinda muke buƙata, dan inhar muka gama da yarinyar kauda ƙaninta abune mai sauƙi a garemu. Har ALLAH yasa burinmu ya cika aka tsaida ranar auren Abdallah da Nu’aymah. Sai dai Abdallah baisan da shirinmu akan bayan aurensa da Nu’aymah so muke ta mutu ba. Wannan daga ni sai mahaifinsa ne muke shirinmu. Amma kash tarihi sai ya nema maimaita kansa tsakanin Adawiya da Nu’aymah tamkar ni da Firdausi. Dan kuwa dai Adawiya soyayyar Abdallah ce tai mata shigar sauri, tanata ɓoyewa har takai ta gagara hakan lokacin data tabbatar zai kubuce mata. Na jima da fahimtar tana sonsa amma sai na ɗauka kawai ƙuruciyace, sai da aka tsaida rana na fahimci yarinyata da gaske takeyi. Shine fa na samu Abban Abdallah da zancen kozamu samu mafita. Kai tsaye ya nunamin hakan bamai yuwuwa bane. Na harzuƙa matuƙa, dan ina buƙatar farin cikin ƴaƴana, dan haka nace to kuwa sai dai kowa ya rasa. Da dai ya fahimci zan lalata komai bayan nasara dake tunkaromu sai ya lallasheni akan to na fahimcesa mana, mu bari ayi auren Nu’aymah da Abdallah. bayan komai ya faru Aymah ta mutu wajen aiki duk yanda zaiyi zaiyi a aurama Abdallah Adawiya. Na zauna nayi nazari sosai kafin na yarda da tsarinsa, dan nima a nawa hangen dukiyar da zamu mallaka ɗin idan Abdallah ya auri Adawiya zata sake dawowa wajenane tunda jikokina sune zasu zama magadan Abdallah, daga haka muka cigaba da shirye-shiryen biki, sai dai kash ana gobe matakin cikar burinmu zai tabbata aka sace Nu’aymah. Ina mai tabbatar muku munfi iyayenta shiga tashin hankali a wannan lokacin, duk da ni ɗaura auren Adawiya da Abdallah ya ɗan min daɗin da har tashin hankalina ya sassautu. Amma bayyana muku kalar ruɗanin da Lurwan ya shiga a wannan ranar ba’a magana. Dan har sai da muka samu matsala kanmu ya rabu, ni haushina ƙiyayyar da Abdaallah ya nuna akan yarinyata, shi kuma Lurwan takaicinsa suɓucewar damarmu. Daga baya dai muka dai-daita muka tafi shirya filan b. Iya bincike kuma munyi mun rasa gano yaya akai? ta wace hanya hakan ta faru? Sannan wanene ya aikata mana hakan? Da gaske mun fara zargin asirinmu ne ya tonu, sai dai har ƙura ta lafa bamuga wani alamar hakanba sai hankalinmu yaɗan kwanta”.
Karan farko Hajjo tai murmushi mai ciwo. Amma batace komaiba.
Addah ta cigaba da faɗin. “Mun sake son ƙulla auren Abdallah da Nu’aymah a karo na biyu. Sai kuma ga Naser ya dawo wai shima da soyayyar ta. Da alama kuma tayi shirin amsarsa. Sannan hajjo da Ananah sun goya masa baya a wannan karon. Shi kansa Sooraj mun fahimci so yake ya bama Naser ɗin. Dan yanda suke takun saƙa da Abdallah baisa wani ya taɓa nuna goyon bayan Abdallah ba. Muna tsaka da neman mafita Abdallah ya saki Adawiya da Yusrah. Wannan saki shine ya kawo saɓani mai girma a tsakaninmu. Dan nikam dai na tabbatar musu sai Abdallah ya maida Adawiya zan cigaba da basu goyon bayan cigaba da aiki tare. Amma sai Abdallah ya tubure, ƙarshema ya gudu ya bar gidan saboda takurawar da mukai masa ni da Abbansa. Sai dai ya tabbatar mana shifa da gaske yanason Nu’aymah ya kuma gaji da biye mana. Hankalinmu duk ya tashi, dan tabbas da gaske munga soyayyar yarinyar a cikin idanunsa. Mun kuma tabbatar da ya daina mana biyayya kenan”.
“Ana tsaka da wannan rikicine ciwon da nake yawan ji ya takura mani, batare da sanin kowaba Mustapha ya kaini asibiti, a gwaje-gwajensu aka tabbatar mana da ina ɗauke da ciwon kansar jini, ga kuma ciwon zuciya daya ci jikina sosai shima, wanda na tabbatar yanada alaƙa da hana kaina zaman lafiya danai akan ƙadarar da ban isa canjataba tunda rubutacciyace daga littafin Firdausi da Sooraj. Lallai jikina yayi sanyi, duk wani kaushina ya sulale, adadin watanni da likitanci sukai ƙiyasin bazan zartaba ya ruguza dukkan burikana da zalamata. A karan farko zuciyata ta kwaɗaitu da son yin ƙyautatawa ga Firdausi koda sau ɗaya ne a rayuwata”. Kuka yaci ƙarfinta da tari. Yanzu kam gaba ɗaya ta cire ɗan-kwalin ta tare jinin dake fita da tarin, sai da ta tsagaita da ƙyar sannan ta cigaba da faɗin,
“Na roƙi Mustapha ya rufe zancen ciwona harga ƴaƴana saboda banason ɗagama kowa hankali, da farko bai aminceba, amma da naita lallaɓasa da hujjoji sai ya fahimta. Son kuɓutar Nu’aymah daga tarkon Lurwan ya sakani sakebin hanyar wani malami aka sakar mata jini. Ni da kaina na zuba garin magani a zoɓo na kai sashensu saboda a gabana Firdausi tasa Rabi ta dafama Sooraj zoɓi shima. sai nayi amfani da wannan damar kawai, ni na kwaɗaitama Rabi kaima Nu’aymah zoɓon ɗaki lokacin dana shigo sashen da nufin neman cucumber. Sai na aiketa ta faɗoma Firdausi zan ɗauki cucumber ɗin. Tana fita na zuba maganin. Ina laɓe ta bayan kitchen lokacin da Rabi ta tafi kaima Nu’aymah zoɓo sai ma suka gamu a falo. Inajin Nu’aymah tace bazatasha zoɓon ba na shiga damuwa. Inata ƙulla yaya zanyi kuma sai ga Rabi ta dawo kitchen ɗin ta ɗaura shayi. Dabarar bugar glass ɗin Windown nayi, Rabi ta kalla wajen ta ɗauke kai. Na sakeyi har sau biyu, shine ta leƙo, bataga komaiba da alama, shine na sake bugarsa. Shine fa tai tsaki ta fito domin dubawa. Nikuma nai amfani da wannan damar na shigo na zuba maganin na fita ta falo. Inda na wuce Aymah na kallo, sai  hankalinta bai kau kainaba harna fice da sauri. Na bada awa guda sannan na sake dawowa na laɓe jikin window ɗinta, banbar wajenba harta fara ciwon ciki wanda na tabbatar magani ya fara aiki. Nabar wajen cike da farin ciki. Kafinma na isa sashena ihunta ya karaɗe gidan. Malam ya tabbatar min dama kowanne irin bincike likitoci zasuyi ciki kawai zasuyita gani ya zube a jikinta, hakanne kuma ya faru. Da wannan damar zancen ciki na sakeyin amfani na tursasa Hamisu bisa tsoratarwar zan kashe mahaifiyarsa ya kawo hotunan da ni na ɗauki Yoohan da Nu’aymah su ba shiba, ba kuma Kubrah ba kamar yanda nasan Nu’aymah zatai zargi. Nayi amfani da Hamisu ne saboda kusancinsa dana sani da Sooraj sosai, na kuma san Sooraj ya yarda dashi. Duk da Sooraj da Firdausi sun bani tausayi sosai a wannan halin na danne zuciyata na cigaba da aikata shirina dan nasan shine kawai zai kuɓutar da Nu’aymah daga sharrin Lurwan akan kwaɗayin dukiyar mahaifinta……………✍

Turƙashi😭🚶🏻

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!😋🤗

Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[7/6, 9:39 AM] +234 913 412 2711: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

 

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply