Bakar Inuwa Hausa Novel Hausa Novels

Bakar Inuwa 49


Bakar Inuwa 49
Viral

Chapter 49
49

………Gaba ɗaya ya gama sabauta mata tunani da lafiyar jiki. Dan kuwa cak ya ɗauketa a karon farko na tarihi, bai direta ko inaba sai saman gado. Bai damu da rawar da jikinta keyiba da roƙon da take masa ya zame towel ɗin da taketa faman riƙo kai kace igiyar neman tsira ce. Batama san ta daka tsalle ta ruƙunƙumesa ba. Atare suka faɗa saman gadon.

“Haba hajjaju ki bini a hankali mana ai zanyi”.

Yay maganar yana danne dariya da ƙyar. Itako kuka ta fashe masa da shi da sake ƙanƙamesa. Burinta bai wuce karya kallar mata jiki ba. Tausayi ta bashi dan yasan wannan wani sabon al’amarine daga gareta. Yajawo bargo da hanu ya lulluɓesu yalwataccen murmushi shimfiɗe a fuskarsa. Jin bil haƙƙi kukan take kuma taƙi barinsa yay ko motsi ya sashi lalubar bakinta ya manne nashi. Cikin salon tsantsar zalama da yanayin da yake ciki ya fara binta da salon da batasan zai iya aikatawa ba.

A wannan lokacin tsabar firgici zamu iya cewa Asthma ɗin Raudha ma motsawa ta nemayi. Dan da gaske numfashin ta a take ya fara fita a rarrabe har tana sarƙewa. Bai barta ba sai da ya fahimci yana neman kama wani layin saɓanin wanda yay niyyar bi kawai.

Shiru yay bayan barinta yana sauraren yanda hawayenta ke sauka a ƙirjinsa har yana huda riga yana ratsasa. Yay tattausan murmushi hanunsa saman kanta da akai ma kitson da baisan anyi ba. Sai da numfashinsu ya gama dai-daita ya kai bakinsa kan kunenta yana magana cikin muryar da batasan ya mallaka ba. “Cutie! Yaufa babu fashi sai anje duniyar samo ƴan huɗun nan bazan iya ɗaga ƙafa ba”.

Sake ƙanƙamesa tai jikinta na rawa dan harga ALLAH tsoro ma yake bata. Kalamansa sake firgita rayuwarta takeyi. Shine na farko daya taɓa mata abinda wani namiji a duniya bai taɓa mata ba. Shine na farko daya taɓa ɗora hanunsa akan abinda wani mahaluki bai taɓa taɓawa ba. Shine na farko daya ganta a yanda wani bai taɓa gani ba sai yau, yau ɗin ma yanzun nan duk da bata da tabbacin ya kalleta ɗin…

Ring ɗin da wayarsa tai a jikinsa ya sashi furzar da numfashi mai ƙarfi. Sosai idanunsa suka canja launi hakama fuskarsa tayi ja abinka da fari. Yasan Maah! ce, ya kuma san abinda take buƙata. Dan ta tabbatar masa tana son ganinsa daya dawo akan zancen aurensa da Aina’u. Da ƙyar ya iya saita kansa yakai wayar kunensa bayan ya ɗaga. Da sauri Raudha dake duƙunƙune a jikinsa tai saurin barin jikjnsa ta dire saman gadon. Bai hanata ba harta sake duƙunƙunewa cikin bargon daya rufa musu. Murmushi yay ganin yanda ta yayesa ita kuma ta nannaɗe a ciki kamar an nannaɗe gawa a likafani. Sosai ya tashi zaune ko zai sake samu muryarsa ta saisaitu.

“Kiyi haƙuri Maah zanzo ALLAH amma sai gobe idan ALLAH ya kaimu. Inaga ma anan zamu yi hutun nan na kwana huɗu yanzu kaina na ciwo”.

Abinda ta faɗa ya sashi sake marairaicewa kamar yana gabanta. “Please maah i promise you bazan saɓa alƙawari ba”.

“Okay thanks you dear Mammah I love you”.

Wannan kalma ta Ramadhan ta bala’in faranta ran Gimbiya Su’adah. Sai taji gaba ɗaya fushin da takeyi da shi ya kwaranye a zuciyarta. Sai dai hakan baisa taji zata janye maganar auren Aina’u ba, tana akan bakanta duk da suna kan rikici da Pa ne akan hakan ma. Dan kuwa su Bappi sunce su babu ruwansu indai Ramadhan ya amince su masu son hakane ai.

Mikewa yay yana kallon Raudha dake ƙudundune fuskarsa da murmushi. “Irin wannan nannaɗa haka Ustazah kamar wata shawarma?. Indai nine nayi nan ina jiran abinci da yunwa na dawo cikina kamar anmun sata”.

Ya ƙare maganar da shafa cikin nasa daya ɗan taso. Shi kansa ya fahimci ya ƙara nauyi, kwana biyun nan baya iya fita training, dole ya dawo kar azo yakai matsayin da ƴar rigimarsa zata kasa ɗaukarsa wata ran. Da wannan tunanin ya fice ya barta bayan ya gwada yayeta ta sake saka masa kuka.

 

Kallon-kallo Aina’u da Muneera kema juna ganin yanda Yayan nasu ya fito a ɗakin Raudha fuska ɗauke da ƙayataccen murmushi da sai dai su hanga yanama wani shi ko su Bappi. Wani irin zafine ya shiga ratsa zuciyar Aina da jin ƙara tsanar Raudha da duk wandama ke tare da ita. jitake zata iya kashe Raudha saboda Ramadhan a yanzu. Dan tun tana shakkar maganar auren nasu a yanzu abin ji take yana ƙara mata tasiri a rai da ɗokin kasancewarta matarsa kodan suma susha romon mulki, dan tasan dai ta auresa yanzu tabbas itace zata zama first lady bawai waccan kazamar yarinyar da ko tsarkin kashi batajin ta gama ƙwarewar yi. Momynta (Adda Asmah) ta gama tabbatar mata indai Ramadhan ne sai ya sota fiye da uwarsa ma a duniya da su Anne, dan zata mallake mata zuciyarsa yanda bazai sake tunawa da kallon wata mace da daraja a duniya ba sai ita. Tabbas tahau ta zauna. Ta kuma yarda. Dan ita shaidace Abbansu a tafin hanun Mom nasu yake. Sai abinda tace yake yi.

 

 

(Hummm🚶🏻🤕. ALLAH yasa sanda za’aima wasu hisabi muna aljannah a fadan MANZON ALLAH (S.A.W).

 

★★★

 

Da ƙyar Raudha ta iya daurewa ranta ta tashi. Sai dai gaba ɗaya a tsorace take da komai ma. Yau gaba ɗaya Ramadhan ya rikita mata lissafi. Tama rasa wane kalar tunani zatai. Shiryawa tai cikin doguwar rigar abaya baƙa. Komai bata shafa ba sai khurah da turare. Sai dai ta wanko fuskarta saboda kukan datai. Cikin ɗar-ɗar da zuciyarta keyi ta fito domin sama masa abincin daya buƙata. Cikin sa’a ALLAH ya taimaketa tai kiciɓus da Bilkisu a kitchen ɗin sama. Dan ƙamshin da taji da motsine ma yaja hankalinta tunda tasan bamai shiga inba itaba sai mama ladi dake gyarawa.

Ido taɗan waro kaɗan na mamaki. “La aunty Bilkisu..”

Bilkisu dake murmushi tai saurin cewa “Kamar kice komai. Kawai naga Yaya a bazatane shiyyasa na rugo kitchen ɗin tunda ba salla zanyi ba. Mun shagala kwata-kwata bamu buɗe television ba balle muga batun dawowarsa.”

Ajiyar zuciya Raudha ta sauke. Cikin danne abinda ke taso mata tace, “Wlhy nima nasha mamaki.”

Ƴar dariya Bilkisu tai. “Uhm ya miki surprise na masoyane kawai”.

Kunya zancen Bilkisu ya bama Raudah, ta kauda kai kawai tana murmushi. Hannu ta saka suka karasa aikin da aready dama Bilkisun tana gab da kammalawa. Sai da suna haɗa abincin a basket Bilkisu ke faɗin. “Niko idonki kamar wadda tai kuka”.

Da sauri Raudha tace, “Abune ya faɗamin a ido daƙyar na samu ya fita bayan nata zuba masa ruwa”.

Sannu Bilkisun ta mata dan har zuciya ta yarda. Raudha ta ɗauka basket ɗin tana mata godiya da addu’ar ALLAH ya kaisu ran aurenta da yanzu haka ana shirin saka rana kusan su biyar.

 

Da ƙyar ta iya kawo kanta ƙofar ɗakin nasa. Ji take kamar bazata iyaba amma ta daure matuƙa. knocking tayi kamar bataso. Tana shirin sake na biyu aka buɗe ƙofar. Bata yarda ta kallesa ba, dan tasan dai shine ɗin. Shiko idonsa a kanta ƙyam yana ƙaremata kallo yanda abayar tai matuƙar mata ƙyau. Matsawa yay ya bata hanya ta shige batare da yace komaiba. Sai da ta gittashi ta shiga ya maida ƙofar ya rufe. Saman kujerar daya tashi ya koma ya zauna tare da ɗaukar Tab.. Da ke a hanunsa kafin shigowarta. Ganin ya basar da ita ya sata daurewa tace, “Ga abincin”.

“Zuba”

Ya faɗa a taƙaice batare da yabar abinda yakeyi ba. So yake yay dauriyar fasa abinda yay niyyar yi a gareta amma zuciyarsa taƙi amsar lallashin sam. Bai kalleta ba harta zuba masa gasashen naman ragon daketa ƙamshi, yaji haɗi na musamman. Sai kunun madara da Bilkisu tayisa a nutse saboda sanin yanda yake ƙaunarsa. Zata zuba abincin yay saurin dakatar da ita. “No bar nan kawai”.

Dakatawa tai ta maida kwanon ta rufe da tura table ɗin gabansa yanda zai samu nutsuwar ci. Sai da ya ɓata wasu sakanni ya ajiye tab.. Ɗin, dai-dai da miƙewar Raudha dake fatan samun hanyar guduwa dan yau bazata juri zama da shi a inuwa ɗaya ba. Caraf ya riƙo hanunta ya zaunar a gefensa.

“Na sallameki ne?”.

Jitai kamar ta fashe masa da kuka kawai, amma ta daure dan kar yaga kamar ta cika rashin wayo. Hankalinsa ya maida ga abincin zuciyarsa na tunanin ta yanda zai ɓullo mata ta saki jikinta. Sai dai ya kai laumar nama baki yake faɗin, “Uhhmm Bestie kinji wani gashi na musamman kamar a birnin sin. K karfa ki zata santi nake naji abunne har cikin kai”.

Murmushi ne ya suɓucema Raudha. A hankali tace. “Uhhmm!”.

“Ai bakiji Humm bama sai kinci”. Ya ɗago gareta da tsoka daya ciro jikin dogon tsinken da Bilkisu ta tsiro guda uku. “Buɗe bakin kiji kar ayi babu ke”.

A kunyace tace, “ALLAH ni na ƙoshi”.

Fuska ya ɓata yana ɗan hararta. “Keni bansan gulma buɗe baki. Ni nasan tun kan ki kawo namannan kike addu’ar ALLAH yasa na sammiki”.

“Ya ALLAHU”. Ta faɗa da dasashshiyar muryarta dariya na suɓuce mata. Shima murmushin yake tare da sake kai mata naman bakinta. Dole ta buɗe saboda cewarsa. “ALLAH sai na miki ɗura. Kuma saina tauna yayi laushi na juye miki a baki dole ki haɗiye”.

Fuska ta yamutse alamar ƙyankyami. Ya dungure mata kai da faɗin, “K yarinyarnanfa ƴar wulaƙancice wani lokacin. Wai ƙyanƙyaminama kikeji? Koda yake hakafa kikaimin kwanaki ina mura. Har shaƙa miki murar nai amma kikaƙi ɗauka saboda ɗan banzan ƙarfin jininki”.

Yanzu kam kasa daurewa tai ta sanya dariya. “Kai Ya Ramadhan ko tausayi babu?”.

“K nifa kibar wani cemin Yaya niba Yayanki bane bamsan kalar dangi. Nasan dai akwai abota tsakaninmu sai kumaaaaa……”

Ya ɗanja ƙarshe yana kashe mata ido batare daya ƙarasa ba. Ba shiri ta miƙe zaram amma yay saurin riƙeta ya maida. “Ustaza bansan fassara irin taku ta Ustazai fa. Kijira na karasa mana kafin ki kaini inda banje ba”.

Dole ta dawo ta zauna kamar ta ɓuya a kujerar dan kunya. Ya dungure mata kai yana kai nama bakinsa da taɓe baki. “Gulmammiyar yarinya nafasan kema kin kamu. A yanzu nan duniya bayan Mommy da Abba babu wanda kike so Kamar Ramadhan…”

“Ni yaushe nace!”.

Ta faɗa cikin suɓutar baki tana taɓe fuska.

“Yo sai kin faɗa? Yanda kika kadandaneni ram ɗazu ke daɗi mijima ai ya isa shaida.”

“Innalillahi….”

Ta faɗa kamar zata fasa kuka dan kunya. Dariya ke cinsa yanda tai wuri-wuri da idanu na kunya. Ya danne da ƙyar. “Oh kice baki son nawa mana kiga in gobe banje an ɗauramin aure da ƴammata uku ba galla-galla”.

Ji Raudha tai kamar ya kwaɗa mata guduma a tsakkiyar zuciya. A take fara’ar fuskarta ta ɓace ɓat. Tai ƙasa da kai zuciyarta na mata zafi da kalamansa…..

Wani daɗi ya baibaye Ramadhan kamar ya tashi ta taka rawa. Cikin shafa sumar dake zagaye da kumatunsa yace, “Oh su Ustazah ba kunya anga sumulmulin yaro ɗan jikan Anne an maƙale. Irin wannan kishi haka Ƙawata? To indai baki so nayo kishiyoyi yau kam dole naje farautar triple koda yake kefa huɗu ma naji kina faɗa saboda tsabar haɗama keda ma ko ɗan kiss ɗin nan na zamani sau ɗaya aka taɓa mik…….”

Ai bata bari ya ƙarasa ba ta daka tsalle ta guntse masa baki da hannayenta. Wayyo dariya kamar ta kashe Ramadhan. Yasan ya riga ya gama da ƴar darunsa yau. Sai dai wani farin ciki ke dawainiya da shi ganin kishinsa ƙuru-ƙuru tattare da ita. Koba komai yaji daɗi bashi kaɗai ke wahalar banzaba akanta ashe. Jikinsa ya jawota ya rungume. Cikin raɗa yace, “Na nayi shiru tashi kici abinci”.

“Kaci kayanka, ko kaje kuci da ƴammatan naka”.

“Wayyo Ramadhana anyi kasuwa. Uhm-uhm fa Bestie ALLAH karki tsaya kallon ruwa ƙwaɗo ya miki ƙafa. BABU SO MIYA KAWO KISHI?”.

Turesa ta shigayi da faɗin, “Wama zaice yana sonka ɗin. Abotarma an fasa”.

Nanma dariya kawai yakeyi yana sake riƙota dan ya fahimci so take tai amfani da damar ta tsere. Ya jima da gane tanada wayo duk da ƙarancin shekarunta. Matseta yay da ƙyau duk yanda taso ya hanata damar dole ta nutsu saboda abinda ya raɗa mata a kunne kamar ta nutse. tanaji tana gani ya tilasta mata cin nama da kunun wanda yay mata matuƙar daɗi. Dama da ƴar sauran yunwarta ta rana. Bayan sun kammala ta tattara kwanika zata fita da su ya hanata. Acewarsa ta tayashi salla ya bata labarin faransa tunda ita bata tambaya ba. Ganin ya zama serious doleta haƙura. Sai dai ta masa complain na rashin hijjab yace abu mai sauƙi yana da shi ai….

 

Raudha dai dauriya kawai take amma tabbas a tsorace take. Bayan sun idar da salla ya dafa kanta yay addu’a kamar yanda musulinci ya tanada ya kuma dace ace tun randa aka kawota gidan hakan ta faru. sai dai lokacin gogan nata na bisa gajimaren hayaƙi hakan bata faru ba. Sosai Raudha tai mamakin yanda taji yana kwararo addu’oi. Sam batai zaton yanada ilimin addini kamar haka ba. Sai taji ya sake birgeta zuciyarta ta ƙara nauyi game da shi.

Bayan sun idar ma ta buƙaci son zillewa ta gudu ya sake hanata. Ƙarshe ma kayan barci da batasan daga ina ya samosu ba ya bata wai ta saka. A matuƙar kunyace ta dubesa cikin marairaicewa amma ya nuna mata babu wani ɗaga ƙafa yau anan zata kwana. Shi ya gaji da raba musu makwanci da takeyi. Daga karshe ya haɗata da kunyar data sakata bin umarninsa dole.

“Ustazah a haka za’a samo ƴan huɗun kina gabas ina yamma. Gara dai kiba marasa ɗa kunya ki haifama Maah jikan da taketa fatan gani. Gashi ma kin ƙudiri surprising ɗinta har ƴan huɗu kika shirya.”

“Kai Ya Ramadhan magana wai bata wucewa a gunka”.

“Oh ikon ALLAH na kulafa kin fara bin hanyar rainani yarinyarnan. Ni miye nawa tunda faɗa kikai naji. Ai har Anne zanma albishir gobe”.

“Na shiga tara dan ALLAH ka taimakeni”.

“Hhhh taimako ɗayane zaki samu sai kin saka kayan nan”.

Wannan kandagarki nasa ya sata shiga toilet ta canja. Sai dai ta jima tana duban kanta a mirror ɗin toilet ɗin ta kasa fitowa. Sai kallon kanta take cike da kunya da ganin ƙyawun da tayi kamar ba itaba. Sai dai gaskiya bazata iya fita da rigarba gabans….

Maƙalewa tunaninta yay jin an buɗe ƙofar toilet ɗin. Tai mugun diriricewa ta ruɗe. Tama rasa mizata jawo ta rufama jikinta. Ramadhan da kamar suman wucin gadi ya riska a bakin ƙofar yana jan numfashi da ƙyar zuciyarsa na wani irin bugu da sauri-sauri. Da ƙyar ya iya ɗaga ƙafa ya ƙaraso gareta. Sai dai a zahiri yanda yake a nutse bazaka taɓa fahimtar halin da yake a ciki ba. A bayanta ya tsaya idanunsa kafe akanta ta cikin mirror da suke fuskanta, sai dai ita ta duƙar da kai ta kuma kuɗindine jikinta da towel ɗin data sami nasarar jawowa.

Ta bayan nata ya zuro hannayensa duka biyu ya zare towel ɗin data rumtse a cikinsu. A wani irin tashin hankali taja numfashi a fisge da rumtse idanunta da ƙarfi tana ayyanawa a ranta. “Shike nan tawa ta ƙare ni Aminatu”.

Lallausan murmushi ya saki yana yaye towel ɗin a hankali saboda furicin zuci datai ya fito fili. idunsa kuma a kan cute face nata da hawaye ke silalowa a hankali. Tabbas matarsa ƙyaƙyƙyawa ce, mai kuma ƙyawun surar jiki abin buƙatar kowane irin namiji mai lafiya. Ya ja nannauyar ajiyar zuciya da kamo kafaɗunta duka ya juyo da ita tana fuskantarsa. Rawa jikinta ya farayi dan ƙafafunta bazasu iya riƙe nauyin gangar jikintaba a yau.

Tausayinta ya sake kamashi, sai kawai ya rungumota cikin jikinsa dan shi kansa ji yake jini na haura masa har saman ƙwaƙwalwar kansa. A tare suka saki kakkaurar ajiyar zuciya, sai kawai ya ɗauketa cak suka fice.

Cikin gadonsa da kullum Raudha ke ƙwaɗayin ganin an saki runmfar net dake jikinta ya nufa da ita. A hankali ya fara kai ƙafarsa ɗaya ya dire gwiwar sa akan lallausan gadon yana rankwafawa ya direta a gadon itama. Cikin wata irin murya mai tsananin sanyi da rauni yace, “To sakeni”.

Sam bazata iyaba. Dan hanun nata ma rawa yakeyi, ta ƙara ƙanƙame wuyan nasa da hannayenta data tallafo ƙeyarsa hawaye na rige-rige sakkowa.

“Ameenatu”.

Ya kira sunanta da murya mai tsananin tsada da tsantsane.

“Uhhmyim!”.

Ta faɗa a shaƙe.

“Kiyi haƙuri na tashi zan canja kaya ne”.

Da sauri ta girgiza masa kai idanunta rumtse. “Ya Ramadhan tsoro nakeji”.

Murmushi ya saki mai sanyi, a hankali ya kai bakinsa kan laɓɓanta da goshinta ya sumbata. Cikin sake raunana harshensa yace, “Nima tsoron nakeji shiyyasa na gayyatoki ki tayani kwana kar ojuju ya kamani”.

Yanda yake mata magana a kunne ya sata sake ƙanƙamesa. Ganinfa ba sakinshi zatai ba sai ya kawai ya kwanto jikinta gaba ɗaya ya sakar mata nauyinsa.

“Mummy zan mutu”. Ta faɗa da ƙyar jin nauyinsa na fitar hankali. Murmushi kawai yayi ya ɗagata, baice komaiba ya fito a cikin gadon. Ita kuma ta samu damar nannaɗe kanta a bargon zuciyarta na gudu kamar zata faso ƙirjinta ta fito kawai kowa ya huta. Harya koma toilet ya kammala kimtso kansa bata buɗe kanta ba. A haka ya kashe fitilar ɗakin yabar lamps kawai ya shiga net ɗin shima. Bargon data ƙudundune a ciki ya ɗaga shima ya shige..

Murmushi yayi jin yanda ta ƙanƙame waje guda lokacin daya kwanto jikinta. A hankali ya kai lips nashi ya sumbaceta ta gefen kunne, ta ƙara curewa waje guda jikinta na rawa. “Haba Ustazah, tsoro fa na ragwayen mata ne, ko kina so masu zuwa Bingon suzo kuma babu cikin ƴan huɗun uhhm?”.

Kasa cewa komai tai, sai hawayen tsoro dake mata gudu, babu abinda ke cin ran Ramadhan sai dariya. Musamman daya shafa fuskarta yaji hawaye.

“Oh ni Ramadhana, ni kuma haka ALLAH yay dani auren raguwa. Yo raguwa mana, tunkan ace kule ke kin tafi cas…”

Tsabar yanda zuciyarta taje maƙura kuka ta fashe masa da shi mai ƙarfi. Ya danne dariyarsa da ƙyar tare da mirginota ta juyo suna fuskantar juna. Sai kawai ya rungumeta yana shafa kanta murmushi ya ƙi barin fuskarsa. Sai da ya tabbatar ta nutsu ya dai-daita fuskarsu waje guda, cikin ɗan hasken dake a ɗakin yake kallonta, itako idonta a rumtse gam.

“Kodai mu haƙura da farautar ƴan huɗun kawai Ustazah?”.

Da sauri ta ɗaga mata kanta.

Ya saki murmushi mai faɗi da ɗora goshinsa kan nata ya riƙo hanunta cikin nashi. “Tom naji, amma idan an haƙura minene tukuycina ni?”.

“Wlhy zan maka nama da yawa da safe”.

Raudha ta faɗa da sauri cikin rawar murya. Mi Ramadhan zai inba dariya ba. Wato yarinyar nan ta maidashi mayen nama. A fili kuwa sai ya cewa yay “Okay ALLAH ya kaimu Ƙawata ta amana”.

Daga haka ɗakin yay shiru, jin kamar ya fara barci Raudha hankalinta ya fara kwanciya, itama sai ta lumshe na idanun. Idanu ya buɗe a hankali yana kallonta da murmushi. “Yaro yarone”. Ya faɗa a hankali da jan bargo ya lulluɓesu baki ɗaya.

Can cikin barci ta tsinkayi abinda yafi ƙarfin saninta, sai dai mai girma shugaban kasa da shirinsa yake, dan cikin ƙanƙanin lokaci yay mata dabaibayin daya sakata shagala da miƙa wuya, sai da labari yay nisa ta raina kanta…….

 

 

*_Bily kama bakinki iya nan🤐🚶🏻_*

Leave a Comment





No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply