Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 15


Bibiyata Akeyi 15
Viral

Page 15

*

Ni na tabbata akwae wanda yarigashi kuma haka kawai zaizo yayiwa wani wucel aiba haka akeyiba
Cikin bacin rai *hanna* tace toh saiki mutu Amma aure kam na auri najeeb angama saikuje kuyita haukanku keda su
Tajuya gun waynnan mutanen ta maka musu harara,,,,,
Jan jakarta tayi tana shirin barin wajen
Saurin riketa hameedah tayi sannan takalli amira ku fahimtar dani mana har yanzu bawai nagane yanda kuka dosa bane

Juyar da kanta *hanna* tayi tarike kugu tana karkada karkada jikinta ida adole ranta ya baci
Dakyar suka shawo kanta ta zauna Dan Sanda amira tabada hakuri tukunna,,,,,,,,,,,,,,,,,
Labari suka fara bawa hameedah ba abinda suka boye Mata tass suka kwashe komai suka fada Mata,,,,,
Ai nan da nan idanuwan ta sukayi jawur,,,,, Kai Amma wannan Ammah nan anyi tsinanniya na tabbata da umma(mamar hameeda) tasani Sai ta Mata tass tass ai tasanta
Ke matar wan mahaifinki kike tsinewa,,,, ai wallahi Sai na Mata tsiya tunda ba yanxu zan tafi ba ai zata gane kuranta,,,,,,, adai Mata sassauci sukace tareda tuntsirewa da dariya,,,,,,
Amma kinsan me ni Allah banga laifin amira ba Nima inaji kaman akwae wani alkairi a tattare da waynnan mutanen tafada tareda kallonsu ta kasan idoh,,,,,
Harara *hanna* ta galla Mata da’allah malama rufa mana bakii!!!!!
Amma kinsan me kemafa banga laifinki na zurfafa ason najeeb ba danna tabbata gayan yayi danke ko akaya baki zaben jebbu!!!!!!

Kallan wayanta tayi subhanallah ke time din test yawuce,,,,
Wani test kum“““saurin rufe bakinta tayi da tafukan hannunta tunowa da tayi karyar data shirga mata dazu

Kallo mai cike da tuhuma *hanna* tayi mata,,,,,,,
Sorry Beb Allah narasa yadda zanyi kizo Skull ne nadau zancen jiyannane yahanaki zuwa shiyasa,,,
Dakiyi ma yafi haka,,,, ita kuwa hameedah banda dariya ba abinda take musu

Fita sukayi ta niyyar wucewa gidan anty ai kuwa acan suka sami najeeb Dan zumudin ganinta bayan sungaisa da najeeb dinne,,,,,,
Suka shige suka barsu su kadai itakuwa anty murnar ganin yar uwarta hameedah yasa ta manta dasu,,,,,

Soyayya sukasha kaman bbu gobe kamar karsu rabu saidai duk wani Soyayyar su sukanyi ta cikin sanin yaka mata Dan basu taba goce hanya duk wani abinda addini yahana basa yinshi
Domin albarka Soyayyar suke nema,,,,,,,,

================

Dubai

Kasar dubai aranar yau tatashi cikin wani irin cikowar mutane sakamokon taron kasa da za’ayi gobe MG kokadan baysamu lokacin kansa ba danko lokacin cin abinci bai samu ba sakamokon yadda garin yake makill da jama’a yanata kokarin yadda zaikare lafiyan al’umma
Garin acike yake Dan manya manya sunfara suka duk wani waje da kuka sani nacikin Kasar Dubai acike yake Dan bakinmu na Nigeria a wani katon estate yasauke a _emarr_ _sidra_ _hills_ _eatate_
Inda sarakunan larabawa kuwa sunsha karrama ansauesu a _arabella_ _town_ _houses_
Wanda wasu da yawancin su sunje ne Dan yawan bude idoh Dan dubai kasaace Wanda taci gaba sosai afadin duniya
Shirya sojojinsa kawai yakeyi inda bayaso asamu wata matsala awannan taron
Bakin Nigeria sun isoh Wanda suka hada da manya manyan yan shiyasa aciki kuwa hadda wanda suke neman rayuwarsa,,,,, shikuwa yananan yana shirin kare tasu rayuwar

Sanda yaje airport yataresu yasada su da masaukin su sannan yawuce zuwa wani wajan
Dan taran wasu shuwa gabannin
Dan kowani shugaba burinsa daya yakaaance MG yana daya daga cikin masu taryan sa awannan lokaci

Har kusan tsakiyan dare MG baisamu hutu ba dakyar su captain Ahmad sika yakiceshi Dan yasa mu hutu,,,,,

Futa sukayi suka shirya masa motoci 9 hadu na bayansa hadu na gaban sa Sai kuma tashi atsakiya,,,,,,,
Captain Ahmed ne yake tuki gefensa kuma daniel ne Wanda Shima MG ya yarda dashi sosai Dan yanada rikon gaskiya shiyasa Har yabarshi yashiga jikinsa sosai

Koda suka isa gida daniel ne yayi saurin fitiowa ya bude masa kofa fita yayi cikin takun sa nakasaita Wanda ko ba’afada ba kasan jinin sarauta ne

Kai tsaye cikin gidan yanufa,,,
Kowani soldier yazauna awajan tsayuwar sa captain Ahmed da daniel ne suka rufa masa baya hannu yadaga musu alamun su tsaya sannan yacewa captain Ahmed yabiyoshi akwae sakon dayakeson bashi bbu musu daniel yatsaya shikuwa captain ahmad yabishi abaya Dan karban sakon

Bayan shigansu ne daniel ya cije libs yarasa me captain Ahmed yafishi da MG yake nuna bamban ci atsakaninsu
Kuma hakan Yana matukar yimasa zafi aransa
Amma ya alakanta hakan da bambam cin addini dasuke

Abinda be saniba shine duk cikin sojojin MG yafiji da Ahmed duk da yafishi agirme dakuma matsayi hakan bai hanashi zama yayi shawara da, Captain Ahmed ba

Tunda yashiga yariga da yasan ummii tayi bacci to baibi takanta ba,,,,,,,,,,, abinda baisaniba shine ko karfe nawa zekai nadare ummii,,,, saitaga dawowanshi dake iya runtsawa sake labulen dake hannun ta tayi sannan taje ta kwanta,,,, koba komai ranta yayi dadi naganinsa cikin kwanciyar hankali,,,,, bandaki yawuce ya watsa ruwa baifi mintuna kadan da kwaciya ba bacci yadaukeshi,,,,,,,,,,

Asuban fari ya farka wani irin mummunan faduwan gaba yatashi da ita Wanda yarasa dalili wanka yayi ya shirya cikin kakinsaa mai fitar da ainihin kyawunsa da cikar zatinsa

Dakin ummii yawuce yasameta tana bacci baiso tada ita ba hakan yasa yajuya yatafi Amma irin wannan taron yaso ace yafita da addu’ar mahaifiya akansa,,,,
Sanda suka tsaya amasallaci musulmen cikin suka gabatar da sallah kafin suka nufi burj al’arab hotel din da za’a gabatar da taron

To be continued

Ur’s
Z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

_
_This_ _page_ _is_ _Dedicated_ to _u_ :: *hajja* *_ceh_* * _kece * * _mutum_ * *ta* farko _datafara_ _bani_ _kwarin_ _guiwan_ _rubutun_ _littafi_ _tanks_ _alot_ _I_ _luv_ u _so_ _much__

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply