Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 16


Bibiyata Akeyi 16
Viral

Page 16

*

Sai wajan karfe uku 3:00 sannan suka bar gidan anty,,,,,,
Amira ta wuce gida suma suka wuce gida,,,,,,,,
Bayan isansu gida sunyi sallar la’asar wani sabon hira suka dasa
Kai sis wallahi najeeb ya hadu wani farr tayi da idoh duk farin ciki ya cikata anyabi abin sonta
Allah koh tace,,,, eh mana kunyi bala’in da cewa
Saleem ne yashigo kanin *hanna* anty hameedah wai kizo inji Ammah yafada yana kallon wayarta,,,,,,,,,,
Kai meye kawani zubawa wayarta ido da’alllah fice kabawa mutane waje,,,,,,
Kai sis kinfiya takura Ina ruwanki kokuma wayarki ya kallah zonan Saleem karba,,,,,,
Zuwa yayi ya tsaya medakayi da phone din sosa keyarsa yayI game yafada atakaice karba katafi,,,,, itakuwa *hanna* murmushin dakisan waye Saleem tabita dashi,,,,,,,,

Ke wai ba Ammah ne kekiran kiba kikatsaya yatsine fuska tayi kyaleta kawai bawani akyaleta tashi muje,,,,,,,,
Nasan wani abin take nema Sai kiji dadin bata amsa,,,,,,,,,,,,,
Mikewa tayi suka nufi dakin Ammah
Suna shiga suka sameta itada yaranta rabi’ah da hafsat suna zaune
Afalo Sallama sukayi basusami amsawa hakan baida mesu ba suka zauna,,,,,,,,,,,,
Juyowa tayi ta kallesu gidan ubanki ne nan dazaki isoh tun safe bakizo kin gaishe niba,,,,,,
Maciya amana ko yanzu kuma dawani cin amana uwartaki ta aikoki,,,,,,

Ko uwarki bata isa tazonan gidan,,,,, tanuna batasan inanan ba,,,,,
Balle ke karamar marar kunya,,,,,,,
Iya bacin rai ransu yakai kololuwa wajan baci,,,,,
Hameedah ce cikin bacin rai tabude baki zatai magana s damke hannun ta *_hanna_* tayi da karfi kallon ta tayi ta girgiza Mata kayi kawar da kanta tayi cikin takaici na hanata ramawa da *hanna* tayi

Juyawa tayi ta fuskanci Amma kingama akwai Abu me mahimmanci da mukeyi tafada hadeda wani murmushi wanda Ammah takasa tantance namiye shi,,,,,,,,
Sake baki tayi Dan uwarki aibake nakira ba,,,,,
Rashin kunyan ki haryakai ki Har yakai agaban idanuwamu kiyiwa mahaifiyar mu raini,,,
Hafsat ce tatashi da niyyar dukanta,,,
Ammah tahanata kull karki tabata kibarni da uwarta zanyi ni,
Jan hannun hameedah tayi wadda ga baki daya ji take kaman ta fashe tsabar bakin ciki,,,,,,,,,
Janta tayi Har sunzo bakin kofa Ammah tace shegiya mai bakin jini,,,,,,
Saurin tura hameedah waje tayi tadawo cikin dakin wani kallon kaskanci tabi hafsa dashi,,
Wato kece Har zaki dakeni ko tabani wallahi saina miki shegen duka,,,
Sannan tajuya gun Ammah da gabaki daya al’ajabi yahanata cewa komai,,,,,,
Idan Har zaki iya duban idona kice mun mai bakin jini kamata yayi ki fara aurar da nagabanki wanda duk cikinsu bbu wacce bata bani sama da shekara ba tukunna kisamo bakin gori,,,,,,,,,

Tana fadin Haka tajuya tafice tabarsu cikin jimami
Samin hameedah tayi tsaye tana jiranta a bakin kofa,,, dayake taso biyota Amma takulle kofan,,

Murmushi tabita dashi saurin kawar da kanta tayi tafice fuuuuuuu
Binta *hanna* tayi abaya Har suka shiga dakin mama ganinsu Ahaka yasa anty takirasu tana tambayarsu,,,,,,,

*Hanna* taso boye Mata amma hameedah takwashe komai yafada mata ran anty yabaci Amma Sai ta danne kawai Dan yanada kyau tun yanzu afara koya musu yin hakuri kafin auransu

Ahaka yaya jalal yashigo yasamesu,
Kallon *hanna* yayi wai Ina kuka shiga ne kam tun safe,,,, gidan anty fa mukaje,,, shine ba gayyata yafada tareda zama kan kujera,,,,, yaya daga makaranta fa muka wuce,,,,, Haka suka zauna sukayi ta tadi Dan Har sunmanta da bakin cikin da Ammah ta durka musu

Sallar magrib ne ta tashe su sukayi sallar suka dawo akasake sabon hira,,,,,,,,,,,,,,
Saikusan 9:00 najeeb yakirata suka sha soyayyarsu sanda tafara jin bacci kafin sukayi Sallama takwanta Dan hameedah ta dade da bacci,,,,,,,,,,,,,
Irin mafarkin jiya data karayi ne yatashe ta,,,,
Tarasa me wannan mutumi yake nema da take kallonsa gurfane agabanta,,,,,,,,

Datarasa mafita kawae ta dauro alwala tagiba dayin nafila Har bacci yadauketa,,,,,,,,,,
Har ta makara a sallar asubahi Sai wajen 6:30 ta tashi tayi sallah
Tunda ta farka ta tsinci kanta cikin wata irin matsanan ciyar faduwar gaba
Gabaki daya Tanaji kamar akwai wani abunda ke damunta amma tayi duk iya tunanin ta tarasa dalilin damuwar tata

================

Taro yayi iya Taro Dan duk wani manyan duniyar nan sun halacci wannan Taro
Amfara gudanar da taro komai na tafiya daidai Ina tawajan MG haryanzu faduwar gabansa tsananta takeyi

Duk wani tsaro daya kamata awajan antanadar
Inda layin da MG yake zaune layin manyan mutane ne wayar sace tadauki ruri ganin yanda wajan yake a cike yasa yatashi dan amsa wayar, mahaifinsa ne yake kira yasa bazai iya kindauka ba

Kokarin fita daga wajan dayake yake niyyar yi soldiers suka taso Dan bin bayansa daga musu hannu yayi alamun su koma,,,
Bamusu suka tsaya inda captain Ahmed yabi bayansa,,,,,,,

To be continued

Ur’s
Z33yyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*

_Bismillahirahmanirrahim_

Writting by
© _zaynab bawa_
_( z33yyb3rw3r)_

*_Edited_* *_by_* _KSA_ _precious_ _Hajjah_ ce

*Dedicated to*
_*Ummi Aysha* (haske Writter) novel d’in ki na mijina sirrina yayi sosai Allah ya kara basira da zakin hannu_

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply