Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 23


Bibiyata Akeyi 23
Viral

Page 23

*
Masarauta duka suka nufa” nan da nan kowani sako da lungu, na cikin masarautar ya dauka ” *yareemah* ya isoh, dan ko ba’a fada ba yanda masarautar tadauki kidan algaitu da ko ina hakan ya’isa yasanar da isowar *Yareeema*”.

Cikin fada suka nufa kai tsaye” inda mai martaba da mukarrabansa suke jiran isowarsu”.

Sanda suka gama kwaasan gaisuwa, sannan suka nufi dakin da mai martaba da iyalansa suke cin abinci “.

Aranan idan kaga fuskan MG koda bai kasance mai fara’a ba” amma fuskansa ya nuna yana cikin farinciki”.

Sosai aka tanadar musu kalolin abinci”, duk daman sababban abu ne agidan sarauta, amma nayau daban yake”.

Duk iyalan mai martaba suna tare awajan”.

Abinci sukeci cikin kwanciyar hankali da farinciki, irin wanda suka dade basuji ba.

Dan sundau tsawon lokaci basu hadu haka ba.

Bayan angama cin Abinci ne ” duk suka tare a falon mai martaba, tadi sukeyi Sosai irin na yan uwan da suka dade basu zanta ba”.

Kana kallon wannan zuri’a sai sun burgeka” sun baka sha’awa irin yadda suke tadi kai ahade, dan awajan baza ka taba banbance cewa wannan dan wannan bane.

Affan ne ya kalli MG yace” ya yareemah wai Yaushe wannan antynmu mai sa’ar tadazo ne???? Kallon sa MG yayi” cikin tsolaya ya kashe masa idoh daya, eh ai ya kamata musanta yanzu gaskiya, nan da nan kamar wanda suke jira ayi magana suka hau kansa kowa so yake koda hotonta a nuna masa, dan sun tabbata tacika mai sa’a, samun miji irin yareemah yana wuya”

Gaban intisar sai faduwa yakeyi, Cikin zuciyarta tana addu’a Allah yasa itace wannan mai sa’ar”,

Wacce naji sun kirata da anty surayya ne da karbi zancen, itace first born a yaran mai martaba.

Yareemah yakamata ka duba wannan zancen, tajuya ta kalli duk mutanen falon, sannan tace ” ka kalli irin farincikin da muke ciki yanzu, kuma inada tabbaci da’akwai matarka a ciki, farincikin mu saiya fi haka, bakunan mu sayya fi haka budewa.

Duk danginna bamuda burin da yawuce” muga iyalinka kai kanka kasani duk zuri’ar mu babu mutumin da ya kaika soyuwa cikin rayukanmu.

Kokasan iyayaenmu basuda burin daya wuce ace” yau sunga ‘ya’ yanka, kokasan shiru kawai suka maka dan basasan abinda zai takura ka, amma bawai dan sun hakura da zancen auranka ba” shekarunka fa talatin da biyar 35 ‘yan mata sun kusa su fara cewa kamusu tsufa, sai irinsu affan, tafada cikin sigar tsolaya.

Ganin kansa akasa yasa suka fidda ran samun amsa”.

Mai martaba dama yasan basuda amsar wannan tambayar, yasa bai samusu baki ba, dan sau dayawa yakan zaunar dashi yana masa wannan maganar” amma amsar sa daya na wannan yarinyar, sujira da sauran lokaci, amma da mamakinsa gani yayi ya dago kansa da murmushi.

Wanda duka falon Sanda abun yabasu mamaki, dan irin wannan murmushin yin su awajan sa nada wahala”,

Cikin zumudi wanda kwata kwata basusan shi da hakan ba yafara magana cikin muryarsa mai dadin sauraro baga mata ba har maza” wanda jinta yakanyi tsada”, kodan yasan hakanne yasa yake rowar jinta” ohow”🤷‍♀ idan wannan ne karkudamu matsalarku tazo karshe, nan da 1 to 2 month mai martaba zasuje nemamin aure” gaban kilishi ne ya fadi cikin razana da dubur bur cewa tace ” a’iinah???

” Bauchi” yafada batareda kawo komai aransa ba”.

Wuta ne ta daukewa intisar da kilishi”

Inda duk dakin sai farinciki ya lullubesu gabaki daya sun rasa yadda zasusa kansu don murna.

Affan harda taka rawa, inda mai martaba da ummii kuwa yanda kasan anmusu albishir da gidan al’jannah, Sosai baku nansu yaki rufuwa.

Inda duk Abinci akeyi kilishi da intisar basa fahimtar komai.

Halima ce ta zakud’o cikin zumudi sanda tazo gabasa taruko hannuwansa, *ya* *yareemah* itace wannan wanda kake dakon santa kusan shekara goma,??? d’aga mata kai yayi ” yaya kaima Allah yasa tasoka kamar yadda kake sonta.

Affan ne yayi saurin karbe zancen da’allah malama rufa mana baki, wacece zata kalli yaya tace bataso” ke kanki kinsan duk zur’ar mu bbu mai kyau da kwarjininsa, kallon ummii yayi cikin tsolaya yace” aiko ummii wanda take cikakkiyar balarabiya bbu abinda zata nuna masa, duka ummii takai masa tana girgiza kai irinna shirmen affan.

Kayyyah” affan barta tamun addu’a dan banida wannan tabbbacin akan zata soni, akwai mutanen da kyau da kudi da dukiya bai damesu ba, batasan koni waye ba balle tasoni.

Amma inada tabbbacin arananda nayi asarar ta aranan rayuwata amfaninta kalilan ne, kuma har inde narsata toh bazan iyayin aure ba, yakarasa maganar cikin sigar da duk wanda yake zaune awajan sanda matsanancin tausayinsa yqamasu,

Ummii har idanuwanta ya cicciko dan ita take zaune dashi ita kadai tasan irin son da yake yima wannan yarinya”.

Mai martaba ne cikin sigar kwantar da hankali yace ” *Yareeema* na karfa kamanta kai soja ne, mai juriya da kuma gwarzon taka, eyyah abba ata wannan fannin gaskiya ni rago ne.

Yana fadin yatashi da niyyar futa, wanda bayar iyayensa da yan uwansa da dumbin tausayinsa, affan ne yayi karfin halin cewa yaya baka fada mana sunanta ba”.

================

Nayi tafiya ya plz fans kuyi hakuri dan banida tabbacin kullum zakurunga ganin post dina harsai danawo zai dawo normal bye love uuuuu olll

To be contunieud

_Ur’s_
_Z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply