Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 28


Bibiyata Akeyi 28
Viral

Page 28

*

Futa tayii ahankali kamar wata marar gaskiya.”

Hange ” hange” tafara can ” sai ta hango motarsu awajen can dan nesa Da gidan.”

Nufarsu tayi Da gwarin guiwa, amma duk da haka gabanta yanata faduwa dar-dar.

Tana isah” bakin motar ta bubbuga glass din, ahankali suka zuge, kara hade rai tayi sannan tadauko ledar Da mika musu, ba musu dayan ya karba wanda yawanci shi yakeyin _driving_ din _car_ din. ”

Kara turnuke fuska tayi, sannan tace kudaina zama Da yunwa, ta dalilina gwanna idan zaku ringa futa kuna neman abinci ku futa.”

Tana fadin haka tajuya. ”

Binta sukayi Da kallon mamaki,

Juyawa yayi ya kalli dayan sannan yace, captain bala yarinyar nan nada abin mamaki.”

Yadda kasan oga data murtuke fuskar ta shima haka yake, an hadu an dace sukace hadeda kyalkyalewa da dariya, bude ledan sukayi, gaskiya yarinyar nada kirki, wato hartaji tausayinmu. ”

Dama yunwa sukeji, take suka fara cin abinci.”

Karfe biyu suka fito dan wucewa kano, sosai sukayi kewar maman nana mace mai kirki. ”

Sun dau hanya, sun kai wudil najeeb yakirata, tayi mamaki nasanin cewa yasan dasudau hanya amma ko saudaya bai kirata ba.”

Sauke ajiyan zuciya, tayi sannan tayi picking call din, hira sukayi sosai, har ta manta Da yaya jalal a motar. ”

Haka kawai yaya jalal ya tsinci kansa Da bakin cikin wayar da takeyi, shi yasan ya dade yanason *hanna* amma kuma yarasa dalilin dayasa har yanzu yakasa furtawa.”

Saida suka shiga garin kano sannan sukayi sallama da najeeb, alokacin ran yaya jalal yakai kololuwa wajen baci, yayi kucin kicin ya hade rai,

================

Wannan mutuminne wanda haryanzu bawai nasan waye bane, yadaga waya yana kira da alamun wani yake nema.”

Can aka dauki wayar, cikin firgici yafara magana, chief sanda nace ma a airport mutada bomb yamutu ahuta kukaki, gashi abinda nakeji yafara, faruwa. ”

Yanzu Haka dan gidan minister yananan a asibiti yafara daukar fansa.”

D’azu yakirani yake shaidamin, cikin wayanne naji ankatseshi, ya’akayi har yasan mune muka aikata??” shima ya fada cikin tsoro, Yanzu abinyi shine, duk kai musu waya muhadu musan abinyi, tun kafin kwabar mu tayi ruwa, nan Da zuwa _week_ duk muhadu a abuja. ”

Cikin kid’ima ya amsa Da _yes_ kawai, yana gama wayar ya cire hula duk ac dake falon amma gumi na tsatsafo masa.”

Haka kira yayita shigowa wayarsa kowa cikin tashin hankali yake tambaya danjin, cikekken labari. ”

Ahaka dai suka tsaida magana akan zuwa _next week_ zasu samu yin meeting dan samun _solution_.”

Akarshe ne yakira wani awaya, bayan ya dauka ne yafara ce masa, ”

Inason ka samomin tak’aitaccen _history_ MG Abudullahi abdulaziz lamido ne.”

Duk wani wanda yasha feshi, Inason sani koda jaririyar da aka haifa a family din akawo min sunanta Da kuma pic din su, zuwa nan da _3days_ banji mai akace ba yasauke wayar akunnensa. ”

===============

Sai yamma likis suka shiga garin kano, kowannensu agajiye yake, gashi kokadan yaya jalal baya gudu amota.”

Kuma k’arin abinma, bacin ran dayake ciki yasashi k’ara saibi. ”

Suna isa cikin gidan ko gaisawa da umma basuyi ba suka wuce part din ‘yan mata yanda dakin anty samha da hameeda yake.”

Suna shiga agajiye suka zube kan gado, sis wai meya batawa ya jalal raine a mota?? ”

Ki kalla fa ko magana yakiyi.”

Damuka iso ma ko kallon mu baiyiba yafice yabar motan. ”
Ohonsa nikam, tana fadin Haka tashige ta dauro alwala, bayan tafito *hanna* ma tashiga tayi wanka, bata damu Da yamma Da tayiba, ta d’ane gado sai baccin gajiya, dama rabonta da irin Wannan tafiyar tun tana yarinya.”

Bayan hameeda ta idarda sallah ne itama tabita gadon, nan danan bacci mai nauyi yayi awon gaba dasu. ”

To be continued

_Ur’s_
_Z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

 

*this Page is humbly dedicated To u maman manal yhur such a nice an wonderful person luv u so much* “`nima inasonki kamar yadda kike sona“` “`muna mugun tare“`👍

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply