Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 29


Bibiyata Akeyi 29
Viral

Page 29

*
Basu suka tashi daga bacci ba, sai kusan bayan magrib. ”

Umma batsan da dawowarsu ba dan tajira har tagaji kuma takira waynsu *hanna* ba’a _picking_ yaya jalal dama ransa abace yake shiyasa yana isa yakashe wayansa, saleem kuma bayansa yabi suka shige daki.”

Kusan _eight_ 8:00 wata irin yunwa tatashi *hanna*. ” gani tayi hameeda tawani baje sai baccin take sharar bacci.”

Dak’ar k’arewa tayi ta sake mata marii, a _back_ dinta sanda ta tashi zaune bbu shiri. ”

Ke da’allah yunwa nakeji.” shine dan rashin mutunci sai ki dake ni banza kawai, tafada hadeda komawa baccin ta. ”

_Please sis wake up am terribly hungry_ , bakisan kofa ba kenan, tafada atakaice.”

_But i said am srry_ *_hanna_* tace had’eda langa6ar Da kanta, banza marar mutunci tafad’a had’eda mikewa tayi hanyan futa, ai *hanna* dataga ba sarki sai Allah kuma tafiya zatayi ta barta. ” a arba’in taduro akan gadon tabi bayanta.”

Afalo suka sami Umma tayi tagumi, ai Da gudu *hanna* tawuce hameeda tafad’a jikinta. ”

A razane Umma ta juya jin mutun ajikinta, ai tana ganin *hanna* cikin murna ta kankameta ajikinta, sai can ta sake ta.”

Ba kunya *hanna* ta gyara zamanta dere-dere akan cinyan Umma, kod’od’uwa Da ita sai wani zuba mata shagwaba take zubawa kamar ‘yar goye. ”

Tsakin da hameeda taja ne yasa hankalinsu yakai kanta datake tsaye.”

Ware mata hannu ummah tayi, sannan tasaki murmushi ta shige jikin Umma. ”
Umma Haka Allah yayita dasan yaranta da kuma jansu ajiki.”

Ture ture suka fara kamar wasu yan biyu,, dariya kawai Umma keyi musu, dan yanda takejin hameeda Haka takejin *hanna* kokadan bata tabajin banbanci akansu ba, hasalima dukansu da ita suke kama. ”

Yaran ummah biyar ne Allah ya azirtasu dasu, babban danta ya auwal shike auran anty hindatu yar mama, sai me bi masa yaya jalal, daga nan sai anty samha wanda za’ayi aure tagana degree dinta a buk.” sai salman wanda hameeda ke bi masa, yagama degree dinshi agana yana service, kunsan yanayin karatun mu bad’aya dana muba dan anty samha tarigashi shiga da shekara daya amma tare suka gama, sai hameeda itace auta.”

*Hanna* ce tarik’e cikinta cikin muryar shagwaba tace Umma yunwa, tashi tayi taja hannun su zuwa dining, sanda sukaci suka koshi sannan suka fara tamvayar wajen anty samha. ” shaida musu tayi tana d’akinta aguje sukatashi sukayi dakinta, tana waya da mijin da zata aura saiji tayi kawai anzube akanta had’eda saka ihu.”

Itama cikin razana ta saki nata ihun wanda sanda yasa abubakar dake zaune a kusa da MG yana waya saurin kawarda wayar a kunnensa, afili kuma ya furta su hameeda an isoh kenan. ”

Gaban MG ne yafadi, yanason masa tambaya amma bayaso ad’ago shi, kawai saiya share.”

Amma ransa fall yake da farinciki, ya tabbata *hannan* sa ta isoh lafiya. ”

Juyowa tayi aikuwa tana kallonsu wani sabon ihun ta dad’a sakewa sanna ta rungumesu, Umma tana daga falo amma tanajin ihunsu.”

Yan iska yaushe kuka isoh?? ”

Tun da yamma” shine kuka shige daki? ” kunsan tun yaushe nake jira kuzo kufutar da ashoben kanne yan iska kukaki zuwa.”

*Hanna* Da hameeda ne suka kalli juna harsuna hada baki wajen cewa k’anne?? ” *Hanna* ce ta tabe baki yanzu ke anty samha ku kunya bakijiba wajan cewa wai mu muyi ankon k’anne, hameeda ce ta amshe zancen haba anty yanzu dame kika fimu?” har mun daraki atsayi fa gaskiya aduba wannan zancen.”

Daura kafa daya kan daya sukayi sai wani jujjuyata sukeyi, irinna mararsa mutuncinnan. ”

Ita kuma anty samha tunda suka fara magana tasake baki kawai tana kallonsu, Ita kanta tasan gaskiya ne inba fuska aka duba ba ba’ace ta girmesu ba.”

Idan ta jiki ne ma sai ace sun girmeta. ”
Cikin rasa abin cewa tace ku6ude, _wadrope_ dina zaku kalli kalli kala biyar biyu na k’anne, uku na kawaye, green da yellow dinne na kannen saiku ebi na kawayan.”

*Hanna* ce tatashi ta bude sif din, na kawaye tafara cirowa sanda taciro set uku, sannan tajuyo, taga yanda anty tazuba mata idoh, meye🤷‍♀?? ” *Hanna* hameeda amira tafad’a atakaice.”

Hameeda ne tataso, Itama, ” na kannen ta eba set biyu.”
Kwasan kayan sukayi dasu fice, anty tatsaresu, me kuma dakuyi dana k’annen, owh anty dan munce baza musa abiki ba _doesn’t mean_ ba maso, ” A’a kawai abikinne baza musaba.” suna fadin haka suka fice suka barta _totally speechless_

Abubakar kuwa dariya yakeyi kamar dan itah aka aikoshi yi duniya.” tun lokacin bawai yakashe wayan bane, saima samusu Ita da yayi a _handsfree_ koh MG dako murmushi bawai yacika yi bane amma yau sanda yayi har hak’waransa yafito. ”

Jin muryar ta da yayi yasashi awani irin nishadi, soyayyarta ne ke ratsa duk wani gabbai najikinsa,” wanda har wani kasala yasaukar masa dashi, ” sai wani shimfid’aden murmushi wanda ke kwance a fuskarsa dayasa, kuma tunshi suka zauna a lobe wato dimfull, wanda wasu ke kira da _beauty point_.”

Damashi ko motsa bakin sa yayi, toh _side da side_ na _cheeks_ dinsa sai sun lotsa, ”

Su *Hanna* nashiga daki duk suka zube kayan ak’asa, *Hanna* ce tacire doguwar rigar dake jikinta, da niyyar shiga wanka, yarage daga itah sai _bra_ da short din wando wanda yawuce guiwa amma baikarasa kasaba.”

Hameeda ce tashigo, daga falo taje dauko ruwan sanyi,, saurin daukan rigarata tayi da niyyar kare jiknta. ”

Wata muguwar harara da hameeda ta watsa mata da’allah banza, with dis yhur platty tommy mai mutum zai kalla?” eh din najidai futa da’allah. ”

K’arasa shigowa tayi saikiyi kuma.”

Tsaki taja ta shige _toilet_. ”

================

Tashi yayi ya shige shaashinsa.” idanda sabo abubakar yasaba, shi bayayun sallama saidai kawai kanemeshi karasa. “girgiza kai abubakar yayi sannan shima yatashi yatafi.”

Yana shiga dakinsa wani godon alfarmane aciki, wanda daka kalla ansan gadone wanda jinin sarauta ne kawai masu irinsa wanda ake kira da _royal bed_ . ”

Farin _bed shit_ ne kall a kan gadon a shifideh, kamar yanda _paint_ nadakin yake fari,
Dakin yakai akarsa gado uku aciki kawai dan girma da kyau.”

Dakin a gyare yake tsaf-tsaf bazakace akwai mai rayuwa adakin ba tsabar yanda dakin yake so _cleanness_. ” wani sanyi mai dadda dan kamshi ne ketashi wanda yahadu da kamshin _room_ _freshner_ dana turarukan dayake amfanida su yabada kamshin sanyi.”

Wata kofar _glass_ yanufa ammata _design_ mai dan karan kyau, wasu numbers yadanna kofar tabude. ”

Ashe wani dakinne aciki, shima komai nadakin farii fat _pics_ din *Hanna* ne akowani lungu da sako nadakin.” tun tana karama har lokacin da tadan tasa har izuwa girmanta nayanzu. ”

Kurawa pics din idanuwa, sannan yakarasa ya6ude wata _drawer_ yadauko wani diary mai kyau harda bironsa a manne Ajiki.”

Wasu yan rubuce rubuce sannan yamayar ya aji’yeh, ya tashi zai tafi yabige _drawern_ wani file ne yafado, takardun ciki suka watse, kurawa takardun idoh yayi.”

To be continued

_Ur’s_
_z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply