Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 41


Bibiyata Akeyi 41
Viral

Page 41

*
Sosai suke zurga-zurga dan ganin sun kammala komai kafin gobe, dan gobe da yamma sukesonyin celebrating na birthday d’in a gidan adda hindu,”
Umma takira wanda zasuyi decorating wajen, with pink and white flawer’s cottons and balloons.”
Sannan sunyi ordering 2 birthday cakes, pink colour mixing with white da kuma golden colour,”
Sai kuma cup cakes da sukayi ordering. ”
Sosai suke tsara yanda komai zai kasance, sunje anwanke mata kai itada hameeda amma batasa relaxer ba,”
Sai sukaje shopping ananne suka sayo kayanda zasu sa. ”
Abubuwa basu kammala ba sai karfe tara na dare 9pm sannan suka samu suka gama wasu abubuwan,
Sai alokacin tasamu dama takira labba ta shaida mata,
Fushi tayi bata kirata sunyi komai tareba ce mata tayi akan tayi hakuri taga ta gajii ne da hidiman biki yasa, sallama sukayi ta shaida mata gobe da safe data isoh. ”
D’akin ummii ta nufa tasameta da murna ummii gobe fa birthday d’in *hanna* ,”
Cikin fara’a ummii tace To gobe saimu shiga kasuwa amata shopping na gift koh, ”
Ummii muje yau mana gobe fa dasafe nakeson zuwa,”
Cikin Murmushin ta tak’ara cewa, yanzufa tara tawuce kibari gobe kinjii, ”
Toh kawai ta amsa tafice Badan taso ba,”
Y’an tsirarun mutane aka fad’awa dan basaso suwuce fifteen 15 awajen, “a sunyi yawa sukai twenty 20.”
Bacci suka kwanta dan sungaji likis, ”
Kusan k’arfe goma taji wayanta na ringing Cikin magagin bacci taduba kawai taga numb d’in najeeb ne kasa picking tayi
Har yakatse,
Can kusan bayan 30 minute akasake kira kawai lokacinma har bacci yak’ara d’aukan, dan kiran farkonma bawai tagama fahimtar mai kiran bane, ”
Tura wayan tayi k’asan pillow ba tareba ta duba ba, ahaka har aka d’auki tsawon awa biyu anayi ba’a kira sai bayan 30 minute batareda ta dubaba duka,”
Alokacin da 12 :00 taduba dai-dai lokacin massage yashigo wayan, ”
Wanda bata damu ta dubaba,”
Kicin jin bacci tazare wayan tayi switching nata off. ”

 

 

Najeeb na kwance ad’akinsa yaji yanason jin muryarta haka kawai wanda baisan dalili ba yayi – yayi ya daure ya kasa, shine dalilin d’aga waya ya kirata Koda ya kirata yaga ba’adauka ba yayi kusan 3 miss call ba’a picking yasashi, hakura yakashe wayan gabaki d’aya.”

 

Gajiya ne yasasu makara har kusan k’arfe shida na asuba bbu wanda yatshi acikinsu,
*Hanna* ce ta d’an bud’e idanuwanta sannan ta mayar ta lumshe, batafi 1 minute da rufe ido ba, sai gata ruff akasa tafado, wanda hakan yasa hameeda mik’ewa zaune bbu shiri tunda taji k’arar faduwa, ”
Waige-Waige hameeda tafarayi yayinda ita kuma *hanna* inahh hankalinta nakan neman wayanta da take yi, tunowa da tayi an turo mata massage bata duba ba yasata wannan fad’uwar tanada tabbacin bbu mai turo mata massage awannna lokacin kuma irin wannan rana inba shiba. ”
Pillow tad’aga aikuwa saiga wayan tana bud’ewa taga massage ai Cikin ihu tace OMG itz dat numb again,” massage tagani Kamar haka,”
*_HBD JAAN ITX TIME.”_*
saurin komawa tayi tab’ude na wancan shekaran, ” shima dai massage ne kamar haka.”
*_HBD JAAN 1YEAR REMAINING. “_*
Tunanin tazaunayi mai hakan yake nufi da itx tym lokacin menene?”
Ita tasan dai shekaran ta biyar da wannan numb tafara mata massage tun ana 5yrs remain har yadawo itx time to lokacin mene ake irga mata. ”
Iya kira tayi kira amma batsamu mai numb d’inba,”
Har campany na layin MTN taje dan tayi bincike anshaida mata cewa layin sai bayan shekara, shekara ake amfanii dashi kuma shi layin ba’a teracging kuma lokacin da aka fad’a mata ana bud’ewa shine lokacin birthday d’inta. ”
Zama tayi abakin gado tayi tagumii kawai can kuwa sai maganar captain bala tafad’o mata,”
“`Karki damu kin kusan sanin dalilin dayasa muke *bibiyarki* lokacin k’alilanne yarage wanda zai amsa miki tamabyoyinki yananan zuwa“`
Tunani ne fall ranta kamar tayi tagumii kamar wanda aka tsikareta ta tashi aguje tayi hanyar waje, ”
Hameeda da take kollonta tun lokacin da take neme neme itama tafita aguje tabita,”
Bata tsaya ba sanda tazo gate sannan ta tsaya alokacin Hameeda ta iso, *hanna* ina zaki futa? ”
Sleeping wears nefa ajikinki.”
Bata saurareta ba tabud’e kofar da yake jikin gate d’in, ”
Tasakai ta fita, gashi lokacin garii bai wayeba, kodaga sallah ba’adawo ba.” To her biggest suprise tana bud’e kofan tacii karo ta qatoton gift a ajiye akofan. ”
D’auka kawai tayi ta tsaya duba gefe da gefe bataga kowaba, hakan yasa tajuya, zuwa ciki Hameeda ma tajuya tabita.”

 

 

 

Suna shiga daki ta ajiye akan gado tayi toilet danyin alwala, tana Fitowa ta samu Hameeda na jiranta, tsareta tayi ta tambayan *hanna* waye ya ajiye wannan k’aton gift d’in awaje? ”
Murmushi tayi Nima bansaniba abinda nasani kawai duk shekaranda zanyi birthday sai an ajiyemun gift da asubahi a kofar gidanda nake.”
Tana fad’in haka tajuya tad’auki sallaya da khimar ta fara sallah. ” MG baibar kofar gidanba sanda yaga tafito ta d’auki gift d’in tukunna yatada mota yawuce,”

Bayan da idarda sallah ne tafara duba massage da suka shigo wayanta, Harda massage nasu amira su yaya jalal mutane barkatai,”
Bubbedewa tayi sannan tab’ude Data nanma massages kamar zasu cinyeta rufewa kawai tayi ta kwanta bacci abinta, ”
Labba ce tatasheta daga bacci kusan 9am.”
Cikin magagin bacci tace labba har kin iso? ”
Eh ke ni ummii nema tatsaidani da tun 7am zan iso,
Babe is ur day wakeup kidena wannan baccin muje musan abinyi, mikewa tayi tashiga bandaki ta yi brush sannan tayi Wanka tafito doguwar riga kawai ta zura ta kalli labba da hameeda sannan tace sai ina?”
Mu ebi drinks mukai gidan anty sai mudawo, ”
Ok suka tashi, drinks d’in suka eba a store suka wuce wanda bbu zasubi su saya.” basu suka gama zirga – zirga ba sai karfe daya, alokacin 4 za’afara, ”
Kuma basu kar6o cake ba.”
2 aka gama decorating komai. ”
Sanda sukayi la’asar suka fara shiri,”
Makeup artist aka kira tamusu simple makeup saikuma aka yi rolling kai da d’an karamin veil. ”
Tayi matukar kyau, gown dinda tasa goldenne sai aka yi rolling da dark pink na veil tayi matuk’ar kyau,”
Sunfara yin abunsu bbu wani hayaniya dan basuyi yawa ba daga saleem dayaki tafiya sai yaya jalal da salman dakuma sauran cousine dinsu anyi birthday party lpy kowa ya gama yatafii 6pm dai-dai suka gama. ”
Alokacin labba tadage saisunje gidansu dayake tana Cikin farinciki bbu musu suka wuce,”
Ummii suka samu afalo tana jiransu tana kallonsu tataso ta rungume *hanna* habibty Allah yak’aro shekaru masu yawa Cikin jin kunya tace amin, dakin labba suka wuce alola sukayi sukayi sallan magrib, nan labba tamatsa ta tatashi tashiga Wanka tashi tayi tashiga bayan tafito ta samu bbu kowa sai wata farar gown mai red flowers mai kyan gaske batada nauyi da mamaki tatsaya kollonta, can sai labba ta bude kofa, au baki saba? ”
Mufa munshirya time yana ja, plz get ready,”
Cikin kallon tuhuma tace mai za’ayi? ”
Itx a suprise kede kisa kawai.”
Bata k’ara magana ba tasa wata yar budurwace tashigo da kit na makeup a hannunta zaunarda ita tayi tafara yi mata makeup, ”
Sosai tayi kyau dayake bawani makeup akamata ba.”
Tamata rolling da jan veil wani farin kyalle hameeda tashigo dashi a hannunta ta rufewa *hanna* fuska taja hannunta zuwa mota, ”
Labba ne taja motar suka tafi, suna isa akabude motar taja hannunta zuwa wani fili da akamasa decorating da farii da jan ballons kawai ga wuta ta ko ina.”
Ta bayanta labba tazaga ta bud’e mata fuska. ”
Batasan lokacinda tace OMG, tana fad’in haka tayi wajen tana waige waige tana dubawa.” ummii ce tak’araso wajen itada wata wanda kana kallo kusan yar tace afeeya ce. ”
Cikin farinciki suka rungume ta suna mata HBD wasu masu aikine suka ringa jerra abubuwa awajen na ciye ciye dana shaye shaye kamarde wanda ake shirinyin proposal awajen.”

 

 

 

Wani d’an karamin kit ummii tqmiqa mata sannan tajuya afeeya ma tqmiqa mata itama tajuya labba ne tazo dai-dai kunnenta tace sai kinzo kallon tuhuma tamata Bata samu ta tambayeta ba tayi saurin jan hannun hameeda sukabar wajen,
Wani irin kamshi ne yaringa ziyartar hancinta juyawa da zatayi ta hangi MG sanyeda bakin jeans da jan t-shird gabantane yahau fad’uwa nan take jikinta ya d’auki bari.”

 

 

 

To be continued

 

 

Ur’s
_Z33yb3rw3r_
[9/23, 10:31 PM] ‪+234 810 367 2210‬: *BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

_Dear Ayusher muh’d ina tayaki murnar kammala buk din ki na zuciya gaskiya buk d’in ya ilimantar Allah yabiyaki kuma Allah yabamu ikon amafana da abinda yake cikinsa. “_
_Ayusher acikin writters dabance basirartama ta dabance zankara fad’a gaskiya zuciya yayi.” Allah yak’ara basira da zak’in hannu_ ILYSM

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply