Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 46


Bibiyata Akeyi 46
Viral

Page 46

*
Ihuu badaga mutanen wajanba har wanda suke kallo a insta, sanda sukasa Ihuu.”
Hakanne yayi sanadiyar daskarewar najeeb dake zaune ad’akinsa yana riqeda waya ahanunnunsa, ”
Tun farkon fara abun yake kallo awayansa,”
Zafii yakejii sosai na amincewar *hanna* dan hakan yana nufin rabuwa da ita dan dolensa yayi hakuri, ”
Dan yanda yaga MG daga yanayin kyansa da tsarinsama bazai iya ja dashi ba,”
Balle aje ga matsayinsa, ”
Kuka kawai ya fashe dashi na bak’in Cikin rabuwa da *hanna*.” hakane ta faru da yaya jalal dan shima Hameeda ta kira shi duk wani abinda yafaru yana watching, ”
Tun baiso *hanna* ta amince har yadawo yanajin tausqyin MG kuma har Cikin ransa yakeso *hanna* ta amince da auran MG ko bbu komai yasan cewa MG namata sonda shi baya mata kuma zairiketa tsakani da Allah, zaiso duk wani farin Cikin ta, zai faranta mata fiyeda yanda shi zaimata kuma shi arayuwarsa yanason ganin farincikin ta wanda yanada yakinin zata samu hakan, ”
Shiyasa har Cikin ransa yaji dad’in amincewar da tayi duk da cewa yanajin kishi acikin ransa.”
Saleem kuwa yana Cikin kallo shida abokanansa farko dayace musu yarsace k’in yarda sukayi, ”
Shine yace musu su d’aura bet su halarci wajen hakan yasa, suka nufii wajen a motar baban abokinsu daya d’auko musu dan tafiya yawo.”
Ita kuwa anty samha itada Abubakar da suke kallo farinciki kamar zai Kashe su, ”
Anty samha ce tace wannan yarinyar taurin kai kamar ‘yar aljanu,”
Abubakar ne ya d’aga kafad’a sannan yace amma kinsan ni banga laifinta ba, harara anty samha ta galla masa sannan tace tana wahalarda bawan Allah amma a hakan burgeka tayi? ”
Kuma abokinka ma,” riqo hannunta yayi sannan yace honey bazaki fahimci halin matane ba,”
Duk wanda yaga ta aureshi Ahaka zaice kud’insa ko mulkinsa ta ganii, ”
Amma yin hakan zaisa daniya ta fahimci k’anwar taki ta dabance wani kyqlkyalin duniya duk baida metaa ba.”
Kwanciya tayi ajikinsa sannan tace ammadai duk da hakan nidai najii dad’ii ina farinciki, ”
Cikin tsolaya yace anya kinkai ni kuwa nifa abokinane kuma cousine d’ina zaiyi aure na tabbata za’ayi bikinda duk fad’in kasarnan ba’a ta6a irinsa,”
Ahaka suma sukayi ta murnar farinciki. ”
Ita kuwa adda hindu,”
Tsabar murna lokacin nak’uda ta tashi dama yaya auwal nakusa kawai suka wuce asibiti. ”
Ina akabar iyalan gidan sarki kowa na gidan farin ciki idan kacire mutum biyu kilishi da intisar.”
Dan bakin ciki kamar zai kashesu intisar sa kilishi tayi agaba tanata rausa Ihuu, ”
Ita ai dole sai kilishi tasan yanda tayi ta wargaza wannan aure,”
Kinji na fad’a miki abinda malam yace” yace wannan aure saiya yiwu, ”
Amma mubari ayi auren ba za’a rasa abinyi ba kuma kinsan maganar malam daiko har inde yace zaiyyi abu to tabbas zaiyi ki kwatar da hankalinki.”
Cikin kuka intisar tace tayaya kikesoo na kwatar da hankalina umma kinsan irin sonda nake masa kuma kinacewa na kwantar da hankalii nayi shiru ya aurii wata ba niba wannan ma ba mai yiwuwa bane, ”
Kiduba kiga yanda yazuba gwuiwo winsa ak’asa yana roqarta ta aure shi umma wannan wani irin so yake mata?”
Yabarni insonsa kamar zanyi hauka amma ko kallo ban isheshi ba. ”
Kiduba wannan yarinya umma itafa bakyawun arziki ba,”
Kiduba na tabbata da za’a ajiyewa maza dari ita sai 99 sun d’aukeni basu kalleta ba kidubata fa tana fad’in haka takara fashewa da kuka, ”
Ita kuwa kilishi sai rarrshinta takeyi dan tafi sonta fiyeda yaranta data haifa acikinta.”

 

 

Wajen su *hanna* kuwa celebration aka farayi kai har wanda ba’asan da zamansu bama sun zo wayan dan kallon wayannan masoyan kuma ba’a bari ashiga, ”
Sai can su saleem suka iso anan aka k’i barinsu su shiga waya ya d’aga yakira *hanna* a lokacin ya turo wayarta najikinsa dan idan zaifita saiyabi yad’auke wayarta,”
Juyawa yayi yacewa abokan sa lahhhh na manta ashe phn d’inta najikina.”
Kallon mk’aryacii suka fara masa hakanne yasashi kiran hameeda itma bata d’auka dawuri ba sai da yayi 2missed call kafin tadaga, ” Tana d’auka yace sis muna waje fa anki bari mushigo ai babu b’ata lokacii hameeda tazo ta shigo dashi hadda abokansa.”
Tun daga nesa *hanna* wanda suke tsaye da labba tafara galla masa harara yana zuwa kusa tace ban wayana, ”
Sosa kai yafarayi tace idanka k’ara d’aukamin waya Allah nidakai shi kuma sai ido yake mata akan ta bari abokansa amma takii,”
Sanda ta sulleshi tass sannan tabarshi, ”
Amma duk da haka sai wani shan kanshi yake yiwa abokanansa shi ala dole, yarsa zata aurii mai mulki.”
Sai gab da magrib sannan sukabar wajan amma har tym d’in hanna bata bari sun Had’a ido da Yareema ba duk yanda yaso ya kebe yayi magana da ita abun ya faskara dan wata irin kunyarsa da kwarjininsane yarufeta.”
Sai dab magrib sukabar wajan gida suka nufa, ”
Wanda Cikin wajan bbu wanda yasan meyake faruwa jira kawai sukeyi,”
Suna dawowa hameeda tafara zayyana Bayani nan tafara nuna musu, ”
Mamane tace kadai anji jiki ace mutum taurin kai kamar maye,”
Umma ne tace kadai tunda ta amince zancen yawuce mana, ”

 

Aranar su labba suka wuce,” washe gari kuma akatashi da shirye shiryen, kaiwa kayan tambaya. ”

 

_Plz kuyi hakuri da wannan.”_

 

To be continued

 

Ur’s
_z33yyb3rw3r_

[9/24, 8:41 AM] ‪+234 810 367 2210‬: *BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply