Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 47


Bibiyata Akeyi 47
Viral

Page 47

*
Tun sassafe aka fara shirin zuwa nemo aure, ”
Alokacin aka kira baba aka sanar dashi zuwan,
Aikuwa yaje yasamu Abba ya fad’a masa.”
Abba ne yace amma yaya gani nayi kamar yayi wuri dasun bari nan da zuwa koda satii ne sai, ”
Suzosu kaga yanzu bawani shiri mukayi ba.”
Babane yace nima abinda nagani kenan, amma idan mukace wani abu zasuga kamar basan abun mukayi ba. ”
Kuma ni maganganunda yarinyar nan ta fad’a ranar auren samha sai ina kallo kamar akwai wani abuu ak’asa,”
Kaga kuwa yakamata mu amince musu ayi wannan zancen da wuri kamar yanda suka bukata.”
D’an gwauron numfashi Abba yaja sannan yace nima nayi tunanin hakan dan inaga akwai masu yiwa yarinyar nan ba dai-dai ba tunda dakanta tace aidama tasan bazasu barta ba, ”
Acika mata burinta kamar yanda ta bukata abarta tazauna haka,”
Ai yaya kanajin wannan magana zakasan da wani abuu ak’asa, ”
Kuma ta iya yiwuwa yanzu haka ita yarinyar tajii da kunnenta ne yasa ta fad’ar haka.”
Dan ni gaskiya yaya bazan 6oyeba gidankanna bakowa nayarda dashi ba kawai abun yafi yanzu mudage da addu’a sannan kuma musa ayita mana saukar qur’ani, ”
Kasan mutum kai baka damu dashi ba amma kai yadamu da rayuwarka.”
Baba ne ya nisa sannan yace toh Allah yataimaka sai musan abinyi dan nasan zuwa jimawa zasu iso. ”
Shiga Cikin gida sukayi,”
Suka samu mama da umma kud’in aikin da za’ayi na Cikin gida aka basu sannan su Abba suka wuce dan tanadarwa bak’i snacks da kuma drinks, ”
Saleem ne ke fitowa daga dakiin su, Alokacin abokinsa yakirashi dan tun jiya sai samun kira yakeyi,”
Wa’yanda da ba frndz nasa bane, wanda then suna kallo mahaifinsa baida kud’in da zasuyi abota dashi yanzu haka sai kiransa sukeyi,”
Sunaso su jonehh. ”
D’aukan wayan yayi cikin gadara.”
Daga can Cikin wayan nayi ance palz yadai naji wani labari wai dagaske ne? ”
D’an gyarawa yayi yafara koro Bayani yanayi yana wani gadara,”
Aikuwa duk abinda yake fad’a a kunnen Ammah datake zaune abakin kofa,”
Rikicewa tayi wai metake jine waishin dagaske *hanna* aure zatayi?” kuma dan gidan sarkin kano zata aura?”
kamar yanda tajii Saleem yadad’a, ”
Afili tace kai ina haka bamai yiwuwa bane.”
Shikuwa Saleem baimasan tanayi ba.”
Can garin kano kuwa MG harya gajii da amsa call, dan governor’s minister’s ambasador’s da president, ”
Na k’asa she daban daban sai kiransa sukayi suna mai murna dan abu kamar wasa yabaza duniya sosai,”
Dayawa mutane ke sharing wannan video d’in. ”
Aranar kuwa followe’r kamar zasu cinye, amira da hameeda.”
Kai har takaiga radio’s station, ”
Tv chennel’s,”
Bana k’asarnan zallah ba har na k’asa she da yawa.”
Zance gabki d’aya ya karad’e duniya. ”
Kowani tasha kika bud’e labaran kenan.” MG daya gajine da recieving call, kawai sai ya yanke call saidai massag gashi har yanzu yan wshing basu barshi ya d’an samu tym yakira *hanna* ba. ”
K’anin mai martaba ne zaune a falon mai martaba,”
Magana yake yi, yana cewa, ”
Yaya aduba wannan lamari gaskiya baida ce ace ya auri yar gidan talaka ba.”
Mahaifin yarinyar fa malamin makaranta ne,”
Kaduba matsayi da dukiya irinna yareema ga mulki, arasa wacce za’a aura masa sai yar gidan malamin makaranta yanzu yaya maiyaci yabawa iyalinsa har za’a gani ayi sha’awar aure? ”
Ran mai martaba in yayi dubu yab’aci, dan irin maganganun da k’aninsa yake fad’i ya6ata masa rai,”
Amma dayake dattijo ne mai hakuri yasashi sharewa yabarshi yaci yacigaba da cewa ai wannan yakamata yayi tunda munada ‘ya’ya mata sai qhad’ashi da d’aya aciki, ”
Mai martaba ne ya nisa sannan yace,”
Mai dukiya dakuma talaka duk Allah ne yayisu, ”
Kuma inaso kasani koda yar bukka yareema yakawo yace yanaso toh ita zan aura masa.”
Balle mahaifin yarinyar yanada rufiin asirinsa duk abinda ake nema wajen aure to wannan yarinya da mahaifanta suna dashi addu’a yakamata muyi Allah yasanya alkhairii acikinsa. ”
Duk da bahaka yasoba amma jikinsa yayi sanyi.” Ammah bata tsaya ko inaba sai gidan kawar ta aminiyarta,”
Hajiya lamii tana zuwa tafara mata birgima tana cewa wallhy malam yacuceni duk kud’in da nake she ace baimin aiki mai kyauba, ”
Shege dan iska halama boka ne,” 😳nikuwa nace kajimin amman nan dama ke atunaniki wajan malami kike zuwa toka kin yaudarii kankii. ”
Dan wannan ba malamii bane.”
Hajiya lamii ne tayita rarrshinta sannan tace tayi hakuri su k’ara jarrava wani suganii,”
Cikin kuka Ammah tace mai nake dashi dazanje wajan wani kefa kina kallo na tattare duk kada rori na nasayar naba wannan macucin,”
Menake dashi dazan je wani waje,”
Cikin lallashi tace mata kiyi hakurii mutafii wani kauye abincika kinsan irinsu basusan zqfin kud’ii ba sai mu bincika.”
Cikin d’an gamsuwa da maganar ta Ammah tayi shiru sannan tace to yanzu yaya zanyi tace kodaiyaya kisan yanda kikayi kika nemo kud’ii koda bbu yawa, ”
Gaki da yara ai Had’a musu wuta zakiyi sai sun nemo miki.”
Ahaka sukayi sallama Ammah tatafi bayan tagama kitsa mata makircii.”

Can wajen su umma kuwa sunanan suna shiri iya dai-dai gwargwado sunyi k’okari sosai wajan tanadarwa da baki abun buk’ata. ”
Alokacinne anty maman amal tace ashirya *hanna* dan tasan dangin sarauta yanzu haka da mata za’azo kuma zasu bukqcii ganinta,”

Governor na garin bauchi kuwa yasha mamakin ganin cewa MG yasauka agarinsa batare da yasani ba, ”
Amma yanzu ankirashi akan cewa jirgin mai martaba yakusa sauka,”
Hakama yakira abokinsa sarkin bauchi yasanar dashi. ”
Aikuwa nan ma aka fara shirin tar6an sa.”
Duk ilahiran masu tarban sarkii sun hallara a airpot na Abubakar tafawa balewa.”
Kafin su taso daga kano kuwa sanda zance yakai kunnen fulani kakar MG bakaramin farin ciki tayiba, ”
Tunda tajii zancen zuwa tace ai atafar sai anje da ita zataje taga jikanta.”
Dake tana samun kulawa sosai kuma ga kud’ii yasa tsufanta baiyi yawa sosai ba. ”
Aikuwa hakanne tafaru aka shirya hadda gwaggonsu khadija k’anwarsu mai martaba da sauran ‘yan uwah zuwa garin bauchin yakubu.”
K’arfe 12 :00 dai-dai jirginsu yasauka a airpot, ”
Kai tsaye fada suka wuce,”
Basu d’auki lokacii ba akayi gidan su *hanna*, ”
Alokacin angama shirye komai dan, har Abokan baba samada biyar sun zo tar6an baki da kuma wasu dattijai,”
Yan anguwarsu duk aka had’u, ”
Isowarsu ba jama’ar anguwar ba kad’ai har makwabtan anguwar fitowa sukayi dan ganin wa’yannan mutane ak’ofar gidan da suka sauka ne yasa mutane shan mamaki basu k’ara sarewa ba sanda sukaga har Governor awannna tafiyar.”
Da fara’a su Abba da sauran dajjijan nan suka fito suka tar6e su Cikin amince, ”
Suka wuce falon Abba dasu,”
Su kuma matan Cikin gida suka wuce aka wuce shashin mama dasu,”
Ammah ta window take leqe yayinda wani irin bakin ciki yacika ta har wani dushu dushu take kallo. ”
Data sani takeyi marar adadi dabata rabata da najeeb ba da tabarta dashi akan ace ta auri wannan dan banzan mai kud’in.” abin bakin ciki ma yanda algaitu ya ciki anguwar tako ina algaita ansan dangin sarauta sun shigo, “gaba ki d’aya anguwar sai ta d’auki kamshii dan duk yanda suka wuce akwai masu bin wajan da turaren wuta na gaushi. haka al’adinsu yake har indai za’aje neman aure a gidan sarauta to anguwar sai tasan da zuwansu.”
Jiri ne yafara ebanta Aikuwa awajan ta sulale ak’asa Batasan yanda takeba. ”
Gashi hafsat tatafii makarnat rabi’ah kuma tana gidan anty maryam jiya da tazo tare suka tafii.”
D’aki aka shiga nan akafara gaigaisawa Cikin mutumta juna.”
Nan da nan bada 6ata lokacii ba suka fara abinda yakawosu lokacin an kawo musu kayan motsa baki, ”
Alokacin Momy kadija kanwar Abba tatashi tafita sai gata tashigo da dogarawa har guda goma sha biyu kowa da akwatii ahannunsa yashigo dashi ajiyewa sukayi sunayi suna kirari a matar yareema ahaka suka gama suka fice da baya-baya,”
Kallon kayan suka tsyayi nan aka musu bayanin kan cewa kayan naganii inaso ne. ”
Nan mama tace ai atafar kayan sunyi yawa saidai arage,”
Fulanii ce tace ai matar yareema ta cancanchi fiyeda haka dan haka k’arna k’ara jin wannan abun ai muma yar muce. ”
Ahaka sukayi ta hira kamar da ansaba da juna.”
Fulani ce tace aishin zaku kawomin kishyata naganta ne kosai nabi duk dakunan ina bincikawa, ”
Dariya dukansu sukasa Momy khadija ne tace wa Fulanii,”
Umma wannan kishiyarde ta tsorataki tun daga jinta kika rikice gabaki d’aya saikin ganta. ”
Dariya duka d’akin ak’asa sannan Fulanii tace to ba dolena naji kishi ba,”
Tanason kwacemun wannan had’adden miji wanda ni kad’ai keda irinsa. ”
Nanma dariya akayi sosai, sannan anty mmn amal tatashi tashiga d’aya daga Cikin d’akunan,”
Can jimawa tafito hannunta riqeda *hanna* kanta rufe da qyale amma fuskanta abud’e yake kanta yana k’asa, ”
Tundaga nesa suke kallonta suna masha Allah,”
Dan *hanna* tayi kyau sosai.”
Zuwa tayi ta zauna acan d’an nesa dasu tafara gidansu ahankali Cikin fara’a suka amshe yayinda Momy khadija taja hannunta zuwa gabanta, ”
Tsugunawa tayi ta rungumeta sannan tace welcome to our family dear,”
Hakan kuwa ba karamin dad’ii yayiwa su mama da umma ba sunsan sunakai ‘yarsu yanda ake sonta Ahaka kowacce mata tayita rungumeta Cikin farin ciki. ”
Daga k’ arshe fulani tariqeta gam kamar za’a kwaceta tana cewa aikwa bari mu gaisa ko,”
Aikuwa *hanna* taji dad’ii janta datayi yisukeyi kamar zasu cinyeta dan kowanne acikinsu murna sukeyi sunga matar yareema pics kam alokacin tasha bbu adadii. ”
Fulani kam riqeta tayi gam tana cewa Allah yamiki albarka,”
Allah yamiki albarka, abunda take nana tawa kenan hannunta na riqe dana *hanna* duka biyun wanda hakan sanda yayi sanadiyar da yasa *hanna* zubda hawaye. ”
Data tuna lokacin da ko mashinshini bata da shi har abin gorii yazama sai gashi waiyau itane Cikin dangin mujinda zata aura suna sonta kamar su halaka.”
Fulani ne talura da hawayen ahankali tasa gefen gyalenta ta share mata bata bari kowa yaganii ba ta Girgiza mata kai ko ba’a fad’a ba tasan kukan farin ciki takeyi. ”
Dan duk wani labarinta moddibbo yasanr da fulani shi yasa takejin son yarinyarda tausayinta.” Maza kuwa suma awajensu sungama yanke shawarar za’ayi aure nan da wata d’aya da satii biyu. ”
Ahaka Cikin farin ciki aka gama komai kowa sai yaba halin kowa yakeyi dan daga wajen kowa anga halin karamcii,” Daga mata aka futo da huhun goro da caton na mint da dabino, kowane gida abinda ake kaimusu kenan, ”
Duk anguwar bbu gidanda baisamu huhun goro da caton d’in mint dana dabino ba kuma,”
Kuma ko ina idan aka shiga sai an shaida musu cewa na neman auren *hanna* ne, ”
Duk gidanda aka shiga sai anyi mamaki dan tunda suke sunsan ba’at6a sallama ta cewa anzo wajen *hanna* ba sai gashi yau dogarawa ne ke raba goronta kuma wai hakanma goronda za’akai na neman auren wata shine ake rabashi kowane gida,”
Bayan angama komai suka fito sukasa akira musu matan su tafii. ”
Nan wani bafade yashiga yasanar dasu da suka taso tafiyane fulani ta bud’e gyalen *hanna*ta cusa mata wani d’an karamin akwai sannan aka fita rakasu.”

Bqyan sun tafii ne ya auwal yayi waya ya shaida musu tun jiya adda hindu ta haihu, ta haifa d’anta namiji wanda tun jiya yaki fada ne dan bayaso yaraba musu hankali. ”

 

To be continued

Ur’s
*Z33yyb3rw3r*
[9/24, 8:45 AM] ‪+234 810 367 2210‬: *BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

*Alhamdulillahi am feelling much better,”*
*Thank u all for d du’a, care.* *Massages, luv.”*
*Luv u all* ❤. “

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply