Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 50


Bibiyata Akeyi 50
Viral

Page 50

*
Bayan suna da kwana biyu, Zaune suke ad’aki su shida,suna hira, *hanna* , Hameeda, amira, hafsat, adda hindu, rabi’ah,”
Amira ne tad’an gyara zama, ta kalli *hanna* tace, ke nifa wajenki nazo, biki sai k’aratowa yakeyi, amma ko zancen anko banji kin fara ba. ”
Ta6e baki *hanna* tayi sannan tace ni wasu k’awaye nake dasu da har zan wani fidda anko.”
Harara adda hindu ta galla mata, sannan tace da’allah tafi kibawa mutane waje, ”
Amira ne tace” adda wallhy bakiga yanda ‘yan matan level d’inmu masu shegen girman kai suke kirana akan idan an fidda anko nakawo masu.”
Daa se shegen girman kai ko kallo mutane basu ishesu ba.”
Amma yanzu sai wani kirana sukeyi, wato sunsan cewa nice frnd d’inki insasu acikin frnd. ”
Dariya Hameeda tayi tace ai wollah ko nice zan yi haka, dariya dukkansu sukasa.” ”
Adda hindu ne tace wallhy kuncika yarinta da yawa, ”
Harara *hanna* ta galla mata tace wai dame kika girmenine?”
Wani irin kallo adda hindu ta watsa mata tace” ke nifa inada yaro. ”
Saidai yaronkan injii rabi’ah,”
Dan kinsan nidai baki girme niba. ”
Yakamata dai kufara bani girma danni yanzu na wuce sa’ar ku.” inji adda hindu,
Hafsat ce tace nikam dan Allah kubar wannan abun yanzu musan abinyi,”
Dan gaskiyar amira ne yaci ace yanzu munfara shirye shirye. ”
Ana cikin haka Massages ya shigo wayan tana dubawa taga MG ne.”
Anrubuta zankiraki 8pm plz pick it. ”
D’an siririn tsaki taja wanda yaja hankalin Hameeda ta kai kallonta kan screen na phone d’in,”
Rike baki tayi tahau salati, yanzu ke *hanna* idan zae kiraki Sayya nemi izini? ”
Ina ruwanki bansan munafurcii,” inji *hanna*
Rabi’ah ne tace kyaji dashi anaso ana kaiwa kasuwa.”
Idan ba haka ba waye zai samu mijinda samunsa na wahala kuma kice bakyaso inbanda gulma. ”
nifa kun fara isata inji *hanna* idannace bana sonsa ina ruwanku?” ai ba’aso dole.”
Hameeda ne tace ku rabu da ita duk munafurcii ne.”
Allah adda baku ga ranarda muka fara had’uwa dashiba dan ya tsaya yimun magana shinefa ranta yabacii ta koma Cikin gidanki da b’acin rai. ”
Kuma idan ba haka ba gata ku tambayeta,”
*Hanna* ganin batada na cewa yasata yin shiru da suka isheta ta fice tabar musu d’akin.”

Ummii ce zaune a falonta, itada afeeya da anty hibba da kuma afeeya,”
Shirye shiryen zuwa had’o kayan lefe sukeyi, jibi zasu tafii Yayinda intisar kuma nanan wani irin zazza6i ne yarufeta, har kullum wani irin son MG ne yake rufeta wanda, tarasa yanda zatayi duk wani hanya dazata bi wajan nuna masa tana sonsa abun ya faskara dan baimasan tanayi ba.”
Yana chan yana son maso wani kamar yanda itama intisar takeyi,
Koda affan yaji mai yake damunta hakuri kawai yabata dan ya tabbata cewa yayansa yayi nisa baijin kira, ”
Dan irin sonda MG ke yiwa *hanna* Koda ta aureshi wahala kawai zatasha,”
Da haka yayita bata hakuri sannan yace har in dai mijin kine to bbu makawa sai kin aureshi, komin dad’ewa, dan yayi aure hakan bawai yana nufin bazai k’ara wani ba kenan.”
yayi mata haka ne kawai dan kokad’an baison intisar ta aurii MG dan aganinsa kokad’an basu dace ba.”
Kamar yanda yakejin intisar amatsayin yar uwa haka yakejin *hanna* bazaiso ko d’aya ta cutu acikinsu ba,”
Da haka intisar tasamu ta warware, dan yanzu tasa aranta ko bayan auren saita samu hanyar da tayi ya aureta.”

K’arfe takwas dai-dai, MG yakira *hanna,” yana kwance akan bed da pillow a chest din sa ya matsae pillow d’in sannan yaa k’urawa fan ido, jiran kawai tayi picking yakeyi,”
Sanda takusan katsewa kafin ta d’aga,
Sallama tayi ciki-ciki,”
Jin muryarta haka ya saukar masa da kasala dakyar ya iya amsa sallamr. ”
Itama lumshe idanuwa tayi sakamakon yanda muryar ta daki dodon kumnuwanta,”
Duk yanda takejin rashin sonsa aranta amma fa ba k’arya itama tasan komai nasa yayi saidai kawai tak’i fad’a. ”
Cikin ranta kuwa ji takeyi kamar bata ta6ajin muryar ta takai tasa dad’ii da gard’ii ba.”
Jin shiru yasa shi tunanin kota ajiye wayanne, ”
Are u there? Yayi questioning Cikin whisper voice, umm kawai ta amsa Jin irin muryar da yake magana da ita wanda take hanata aikata komai.”
Kin wunii lpy?”
Ya tambaya, sai sannan taji kunyar gaidashi , ”
Ina wuni tace sannan yayi ‘yar dariya kafin ya amsa,”
Turo bakii tayi sannan tace kai ko?”
Dafe goshinsa yayi yace owwh Allah nime? ”
Sai kayi ta yiwa mutane dariya tafad’a had’eda twisting lips d’inta kamar wanda yake kallonta.”
Inbar dariyan? ”
Yatambaya eh tace kanta tsaye Eh”
Siririn murmushi yayi sannan yace to ai bama kowa nakeyiwa ba.”
Umm kawai taqara cewa,”
Zuciyarta ne keson masa tambaya duk lokacin da yakirata amma saita kasa.”
Daurewa tayi tace masa, in tambayeka mana? ”
Ehem inajii yace,”
Cire wayan tayi ta harareta sannan ta kwaikwayi irin maganarsa, ”
Yana yiwautane magana cikin gadara, mtsew.”
Yaushe ta ta6a kallona lokacin da kace in yarinya kuma a’iina? ”
Yi yayi kamar baiji mai tace ba yace, gobe ina hanya, takaicine yacikata nak’in amsa mata tambayarta tace ni karkazo.”
Baisan lokacin da yatashi zaune ba ya waro eye’s dinsa yayinda eyeballs d’insa masu shape na oval suka k’ara girma, yace karfa inzo kikace? ”
Eh ta amsa atakaice,”
To idan banzo ba yaya zamuyi mu tsara yanda event’s dasu kasance? ”
Ni basai anyi event ba,”
Siririn murmushi yayi wanda sanda both side na dumfull nashi suka lotsa.”
Sannan yace nifa naga alamu har yanzu akwai yarinta mai tarin yawa ajikin ki, ”
Ranta ne ya6aci jin kiranta da yarinya da yayi, kamar zatayi kuka tace nidai wallhy kadena cemun yarinya,”
Rufe bakinsa yayi sannan yace nadaina,”
Fusata tayi jin abin kamar zolaya ma yazama masa tace kaid’in dame ka girmeni? ”
Duk irin dakiyarsa da rashin son yin dariya amma baisan lokacin da ta kwace masa ba yahau yinta kuwa bbu kakkautawa,”
Jin ya maida ita mahaukaciya yasata kashe wayar, sannan ta kifa kanta a fillow tasha kukanta ta koshi. ”
Batabi takan zancen zuwansa ba ta kwanta tayi baccin ta koda safe ma tanayin sallah ta koma bacci, sai 9 tatashi, bayan tatashi ne tatuno da zancen zuwansa, ta6e baki tayi tace ai tun da nace banso yazo halama yafasa, haka tacii gaba da damuwowinta.”
Kusan 10 taji shigowar sako wayarta, ”
Dubawa tayi taga MG ne, an rubuta in sha Allalh zuwa 1 zamu sauka.”
Rasa yanda zatayi tayi, idan taje tafad’awa mama dole zata mata fad’a. ”
Shiga kitchen tayi yanda amma ke zaune ta inna kaltu suna aiki,”
Ra6e-Ra6e tafarayi kaman munafuka, ”
Ammah ne tajuyo tace” *hanna* meyafaru? ”
Sosa kanta um um tafara cewa, kallonta Ammah ta tsaya kawai,”
Ummm dama wai zaizo ne k’arfe d’aya, Ammah ne tace waye zaizo? ”
*Hanna* tace shii man, 6ata rai Ammah tayi tace ke banason shashancii shii wah?”
Ammah yareema ”
Yareema?” Ammah ta maimaita zaizo yau? ”
D’aga kai *hanna* tayi,
Tun yaushe yace miki yana zuwa?”
Ammah tatambaya, kamar wanda take tsoron kar Ammah takai mata duka sai wani kakkare kanta takeyi da hannuwanta tana Sosa kai tace tun jiya, ”
Salati Ammah tayi ta sanar da ubangiji wanda haka yafuto da mama dake d’aki tana tambayar maiya faru?”
Ammah bata tsaya bata amsa ba tace lallai ‘yarnan kin cika marar kunya, wato ke ba’ aisa afad’a miki magana bako? ”
Yanzu da kike fad’amun k’arfe goma da rabi mai kike tunani zanyi kenan?”
Aikuwa ke yanzu zaki Shiga kasuwa kuma kidawo da wuri azo ad’aura musu abincii shashasha kawai, mama ganin basu gayya cetaa ba cikin maganar yasa taja kafafuwanta ta koma. ”
Kud’i Ammah tabata suka Shiga kasuwa itada hameeda da hafsat, duk wani abunda zasu buk’ata sun sayo, suna dawowa suka hau yin aiki batareda su Ammah sunsa musu hannu ba dan sun iya komai nasu.”
Dake aikin ba mutum d’aya bane 1 dai-dai suka gama aiki,, su MG kuwa dake sun d’an samu delay sai lokacin jirginsu ya tashi, dake tsakanin bauchi da kano ba wani nisa bane yasa basu jimaba suka sauka masallaci suka nufa sukayi sallah dashi da wayanda suka rakoshi, yaso tafowa shi kad’ai amma hakan bamai yiwuwa bane, ”
Baisanar da zuwansa ba amma duk da haka sanda yasamu wanda sukazo tar6ansa ciki kuwa harda governor,”
A government house suka yada zango, a lokacin kuma hanna ta Shiga wanka aka gyra falon baba yayi kyau banda kamshi bbu abinda falon yakeyi, wanka tafito ta sanya jan swiss d’in da anty maman amal ta d’inka mata tunda tasa agidanta sau d’aya bata k’ara sawaba,”
Shi tad’auko tasaka yamata kyau sosai, sannan tad’auki bak’in mayafii. ” Light makeup tayi tabi duk jikinta da humra mai dad’ii, ”
Nikuwa nace *hanna* ana ba’aso amma irin wannan kwalliya haka🤔🤷‍♀
Sai pass 2 kafin suka iso gidan, falo saleem yakaisu, sannan ya fita yabasu waje sucii abincii, captain Ahmad ne ya mtso kusada wermer’s d’in yace bari mufara cin abinciin amarya tun daga yanzu, harara MG ya dalla masa, ”
Haka suka zauna sukacii abincinn MG kuwa kokad’an bai ta6a ba.”
Shida yaransa guda tara sukazo shi cikon na goma, ”
Shida captain Ahmad da captain bala da wani wanda bansan ko waye bane sukasa jamfa yayinda sauran kuma duka kakii ne ajikinsu,”
Captain bala da wasu sauran uku ne kawai fatansu yad’anyi duhu suma ahakan sunada haske agaban sauranne fatarsu tayi duhu dan su d’in sauran ba blacks bane. ”
Danna wayarsa yayi yak’ira *hanna* a lokacin amira ta iso tare suka tashi suka nufii d’akin da su hud’u da amira hafsat hameeda da *hanna* da sallama suka Shiga lokacin sun gama har sun gyara wajan, gaisawa sukayi sannan su amira suka mike da niyyar futa, ”
Wannan d’aya wanda yasa jamfa d’innan wanda tare sukayita bibiyar *hanna* da captain bala ne yak’urawa hafsat ido har suka fice ainihin kama suka masa da *hanna* sai bayan sun fita ne sauran sojojin suka fara gaisheta, amsawa tayi amma da captain bala da kuma wannan d’ayan suka gaidata kin amsawa tayi tabisu da harara, “.
Wanda su kansu basai anfad’a ba sunsan ma’anar hararar yayinda MG ya riqe dariyarsa,”
D’ayanne wanda bansan sunansa ba yace yalla6ai anema mana afuwa tuba mukeyi. ”
Kollonta MG yayi bqice komai ba.”
Sosa kai captain bala yayi yace ayi hakuri madam, ”
Kawarda kanta tayi batace komai ba,”
MG ne aransa yace yar rigima, ”
Gyara zama yayi sannan yayi gyaran murya, lokacii d’aya dukansu suka tashi suka fice yazamana daga ita saishi,”
Turo baki tayi tace ina wuni, lpy ya amsa atqkaice nan suka gaisa, yace yau zamu koma nazone naji shirye shiryen da zamuyi ta6e baki tayi tace nifa bzanyi wani shirye shirye ba. ”
Karkace kansa yayi yace waii dama da gaske kikeyi?”
D’aga masa kai kawai, baisake cewa komai ba yace ban phone d’inki bbu musu ta mika masa,”
Numb d’in amira da hameeda yayi dialing yace suzo ba 6ata lokacii suka zo su uku, sannan ya kira captain Ahmad yace yazo shida c bala da kuma c bilal, ba 6ata lokacii suka Shigo nan suka fara shiri kamar wasu sune amaren sosai suke shiri saikace auran y’ar shugaban k’asa, sake baki kawai *hanna* tayi tana kallonsu sanda, suka gama sannan MG yace yanaso ya gaisa dasu mama, saleem ne yamasa iso har ciki yashiga ya gaidasu,
Suna gamawa ya damqawa amira atm sannan suka wuce. ”

_Idan kunga mistake afuwan bansamu lokacii gyara ba.”_

 

Comment

 

To be countinued

 

Ur’s
Z33yyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

_*Y’ar uwa, Y’ar uwa Y’ar uwa, kalmar nan tamkar zinare take, agaskiya ina alfaharii dake Y’ar uwata my other half, antyna ba na wata ba,”*_
*Anty rashida wannan shafin nakine durungum ke d’aya ina sonki ina alfaharii dake.*

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply