Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 55


Bibiyata Akeyi 55
Viral

Page 55

*
Dasafe haka tatashi duk jikinta bbu k’arfii dan kukan datasha jiya da daddadre, ”
Tun sassafe bak’i suka k’ara cika gidan tamm bbu masaka tsinke danma Allah yataimaka gidan yanada d’an girmansa.”
Auren za’a d’aura shine a masallacin a babban masallacin fahda dake bauchin yakubu.”
Can kano kuwa su MG sai shirin tafowa d’aurin aure akeyi, ”
MG kuwa yana shashinsa tareda abokanan sa wanda sukazo daga k’asashe daban daban.”
Shahid mahmud abbas, dakuma hamood bn abid ne kusa dashi suna zaune, ” banda tsokanarsa bbu abunda sukeyi gabaki d’aya tare sukayi passing out,”
Idan baku manta ba ashekarar dasu MG sukayi passing out a rusia nafad’a muku su uku ne.”
Kuma dukansu musulmai ne, so sun zo bikinne, dan sukam sunyi aure. ”
Yayinda Shahid yaransa biyu shi kuma hamood d’ansa d’aya,
Alokacinda sukayi aure bbu irin takurawa wanda basuyiwa MG ba Amma yak’ii,”
Shi yasa yanzu suka sashi agaba suna tsokana, ”
Shiru yamusu kawai yana murmushi dan wani irin nishad’i da farinciki yake ciki.”
Ko bbu komai yasan ayau zai mallaki *hanna* yauce ranarda yayi shekara goma ciff yana jira, ”
To dan maiyasa bazaiyi farinciki ba.”
Murmushi kawai yakeyi yana shafa gashin kansa, ”
Baice musu komai kawai da ido yake binsu.”
Hamood ne yatashi ya kalli MG yace” soldier nifa tun jiya bansa matata a ido naba dan haka katashi kaje ka kainii wajanta na ganta.”
Murmushin rainin hankali MG yayi sannan yace ai Idan kaga nafita anan to katabbata cewa nafita ne da nufiin tafiya aje a d’aureni da sweery ne,”
Idan bahaka ba kam ina nan yanzu ma barina tashii plzz katashi ku shirya karkumuyi latti dan, ”
Sake baki sukeyi suna kallonsa tunda suke basu ta6a tunanin cewa MG zaiyiwa wani abu zumud’i hakaba,”
Ganin haka yasa kowa fara shiri kafin k’arfe tara 9:00.am duka abokanan ango sungama shiri,”.
MG kuwa farar shadda yasa karrr babbar riga gara.” tasha bak’in aikii, ”
Da bak’in hula gashinsa yakwanta yayi luff luff,”
Da bak’in takalmii sau ciki sai shek’ii yakeyi. ”
Sai link dayasa a hannun rigarsa ta ciki, links d’in black diamon ne,”
Kai alikacin kaga MG sai numfashinka yad’auke bak’aramun kyau yayiba Idan ana fad’in kyau to ina nufin kyau Kai ni aganina kalmar kyau tayi ka d’an ta fasaltashi. ”
Koda yafito abokanansa tsayawa sukayi suna kallonsa,”
Dan sunsan yanada kyau Amma kuma nayau dabanne dakuma yahad’u da fara’a da kuma yanayin farinciki dayake ciki, ”
Sai kyawunsa yak’ara bayyana,”
Futa yayi ya nufii shashin Unmii yayinda abokanan sa suka take masa baya har zuwa sashin Unmii Koda yashiga yasameta itama tayi shiga ta alfarma tayi wani masifar kyau. ”
Sai annashuwa yakeyi tako ina hakwaranta awaje yake ga y’an uwanta sunsata agaba sai hira mai dad’ii suke yi,”
Alokacin MG yayi sallama yashigo tundaga nesa Unmii ke kollon d’an nata wani irin kyau dayamata da wani k’ayataccen murmushi afuskarsa, ”
Kana kallonsa kasan yana cikin farinciki marar misaltuwa.”
Koda yak’araso zuwa yayi ya zube guiwowinsa agabanta, ”
Saurin sa hannuwanta tayi ta rige k’qfafunsa Tana magana tanacewa mai son katashi kada ka 6ata wannna kwalliyar dan banso ko kwayar zarra ta kura ta sauka ajikinka harsai wanda akayi kwalliyar dominta taganii.”
Mai son ina matuk’ar farinciki yau in sha Allah burinka zai cika yau in sha Allah zan kalli ranarda nadad’e ina jiranta. ”
Allah yamaka albarka yabaka zaman lpy arayuwar aurenka,”
Allah yarabaka da duk wani sharrii da fitintunuu da zasu taso cikin aurenku. ”
Ahaka tayita masa addu’a masu matuk’ar mahimmancii har sanda yaji hawaye na k’ok’arin zubowa a idanuwansa,”
Ganin yanda idanuwansa suka cika da hawaye najin dad’iin addu’arda mahaifiyarsa take masa. ”
Girgiza masa Kai Unmii tayi tace a’a mai son ko ka manta yau ranar meyece?”
Dakake shirin yin kuka.”
A’a karka fara katashi kaje ku tafii kar Kuyi latti. ”
Had’a hannuwanta biyu yayi ya sumbata sannan yace ba kuka zanyiba ummiina,”
Ummiina kokin manta waye d’ankii. ne.”
Ummiina na d’ankii fa jarimii ne,”
Kawai dai najii dad’iin addu’ooiinkii ne. ”
Inasonkii ummiina,” Inasonkii fiyeda kowa aduniyar nan,”
Kinfii min kowa da komai mahimmancii. ”
Allah yabanii ikon yimiki biyayya,”
Sa hannu tayi alips d’inta tamasa alamun yayi shiru shhhh tashi katafii Allah yamaka albarka amsawa yayi da amin, ”
Mutanen d’akin duk sun zuba musu ido gabakii d’aya sai d’a da uwar suka burgeshi sai rayuwarsu tabasu sha’awa.”
Yatashi haka sanda ya sunbacii umminsa agoshi kafinnan ya gaida mutanen wajen yajuya zai fita, ”
Yak’ara juyowa yakalli amminsa yace Inasonkii ummiina,”
Murmushin ta mayar masa tace nima inasonka d’ana sosai Ahaka yafice yanufii shashin kilishi, ”
Koda ya isa yayi sallama ya jira akamasa isoo ya shiga, ta na kallonsa afili tanuna tana farinciki a zuciyarta kuwa ba haka bane.” bak’in cikin Auren bare dazaiyiibe makill. ”
Koda intisar tajii muryarsa saita futo ganinsa haka da wani irin kyau dayayi ga annashuwa da farinciki afuskarsa,”
Ba k’aramin kishi bane ya turnuk’eta,”
Tasan wannnan farinciki da annashuwa duk dan zai aurii watane take idanuwanta suka cike da kwalla. ”
Dkayr ta iya gaidashi ya amsa da fara’a sosai haryana tambayarta yatakwana hakan kuwa bak’aramun dad’ii yamata ba ko bbu komai yau tasamu dariya da kuma kulawarsa.”
Daganan yafice kilishi namasa addu’ooiin zaman lafiyanda ko zuciyarta bata kaiba. ” Daganan wajan mai marataba yanufa yaje yasamu harya gama shiri su ake jira. ”
K’arfe goma dai-dai suka tashi damai martaba da iyalansa dakuma y’an uwa da abokanai zuwa wajan d’aurin aure.”
Dake ajirgi ne basu dad’ee ba suka isa, ”
Agidan mai martaba sarkin bauchi suka yada zango k’arfe shad’aya masallacii da wajan sun cikin bbu masaka tsinke.”
Jama’akam fad’ansu 6ata baki ne sojoji birjikk ta ko inaa, ”
Fararen fata sunfii kowa yawa awajen bikin,”
Dan idan kaga taron wajen zakace taron k’asa da k’asa akeyi k’arfe shad’aya da rabii 11:30 dai-dai aranar asabar ranar rana mai dum6in tarihi aka d’ aura auren *Abudullahi abdul’aziz lameed’o da hannatu muhammad dambam* akan sadakii naira dubu hamsin ka call.”
A dai-dai wannnan lokacii gaban *hanna* yayi wata irin mummunan fad’uwa. ”
Jitakryi kamar tasa hannunta akayi ta kwala ihuu.”
Yayinda shikuma MG alokacin wani abuu daya tokare masa makoshi tsawon shekara goma sai alokacin ya fad’a. ”

To be countinued

 

Ur’s
*z33yyb3rw3r*

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply