Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 58


Bibiyata Akeyi 58
Viral

Page 58

* Zaune suke acikin wajen sunkai kimanin shida,”
Cikin muryar k’aguwa da damuwa d’ayan yace duk rintsi musan yanda za’ayi yau mu kashe Shi. ”
Idan ba haka bafa muna kallo kamar ya sake ne amma tabbas zai dawo kanmu.”
D’ayanne ya nisa yace senator inaso ka fahimceni duk yanda kake tunani tsaron wajannan yawuce haka. ”
Duk iya dabar barunmu da k’ok’arinmu hakan bazaisa musamu Wani k’ofa ba,”
Tun jiya ake tsaron hotel d’in bbu mai shigarsa balle kuma yau dazai shiga kuyi tunani mana. ”
Bafa k’aramin mutumi bane da zamu samu damar kasheshi dasauki.”
Ko wancan karanma dan daniel ya kasance d’aya daga Cikin sojojin chief ne yasa muka samu damar kai masa harii. ”
Karfa ku manta awancan lokaciin munyi amfani da tsanar dake Cikin zuciyar daniel ne muka tursaasa Shi ya yarda harya rasa rayuwarsa,”
To yanzu kuma mushkila ke d’an za’asamu asirinmu ya tonuu.”
Mujura lokacii amma ba wannan ba. ”
Amma acikinku duk wanda yace ba hakaba toh tabbas saidai yayi Shi kad’ai idan kuma dukanku zakuyi toni bbu hanuna.”
Kai barima nafito fili nagaya muku nikam nagajii da wannan shurmen,”
Laipy ne mun aikatashi mezai hana mu kar6i hukun cinmu?. ”
Musan cewa munyi ba dai-dai ba.”
Nigabaki d’aya ma wallhy ina danasanin biye muku danayi muka cucii al’umma,”
Wallhy Allah bazai ta6a barinmu ba.”
Allah sayya sakawa way’anda muka zalunta,”
gwara mu kar6i hukuncin mu tun agidan duniya,”
Bansan lokacindaa na’aikata wannan abuu mai yashiga kaina ba, ”
Gabaki d’aya namanta cewa bayin Allah muke zalunta namanta cewa komai daren dad’ewa Allah zaimusu sakayya.”
Hawaye nagani afuskar sa,”
Yace zanje zancii gaba da rok’on gafarar ubangiji kafin gaskiya ta fito.”
Danni yanzu nafii buk’atar hukuncii dai-dai da abinda na aikata. ”
Tashi yayi yace nidai kunga tafiyata,”.
Amma yakamata kuyi shawara ya fad’a sannan ya sa Kai zai fice. ”
D’ayanne wanda najii ankira da senator yace minister minister yaya zakqmaanq haka kafasan irin hukuncin dake kanmu.”
Fucewa yayi bai saurare Su ba. ”
Cheif ne yace haba senator Ahmadu yaya zakq d’aga hanklinka mubashi nanda kwana biyu idan yak’i Sai atura akawar dashi, shine zaifii mana sauk’ii kawai,”
Nisawa wanda aka kira da alhaji sulaiman yayi sannan yace tun farkon sanda nacewa, senator kada asa minister acikin har kallan nan gashi Yana shirin kawo mana matsala. ”
Kokad’an banso yashiga ba dan yanada saurin karaya.”
Senator ne yace yanzudai kawai shawarar chief zamubii, ”
Kawrda shid’in shine rufin asirinmu.”
Ahaka suka tashi kan gobe zasu kirashi sujii mai ya yanke, ”
Dandai bazassu lamunci yatona musu asiri ba.”
Ahaka suka tashi daga meeting d’in,
Kowa ransa a6ace.”

*Royal tropicana suit hotel*

A Dai-dai nan motociin suka tsaya,”
Kai tundaga wajen hotel d’in zakasan ana bikin manya,”
Captain Ahmad ne ya Bud’e masa k’ofa sannan shikuma MG ya zagaya ya Bud’e wa *hanna* k’ofa, ”
Hannuwansa yasa mata ta kama ta futo,”
Sai tayi kamar bata ganii ba da dafa kof’ar motan da front seat,
ta zuro k’afafunta ta fito. ”
Dakyar tasamu ta tsaya dai-dai dan tsinin takalmin yayi tsini dayawa.”
Fita k’awayen amarya da abokan ango suka matso suka.”
Jerawa sukayi abin gwanin ba sha’awa. ”
Afeeya ne tafito daga Cikin wajen tsaya tayi turuss ganin Su seprated.”
Kamo hannun MG tayi sannan takamo ba *hanna* tahad’a Su waje d’aya, ”
Wani irin shock sukayi dan wannan ne first tym na *hanna* data ta ta6a riqe hannun MG fatanshi is soft n silk *hanna* sanda ta lumshe idanuwanta tsabar irin yanda taji hannunsa kamar tissue.”
Shima MG hakanne yake anasa wajen dauriya kawai yayi ya riqe hannunta. ”
Ahaka suka fara tafiya Cikin takun angwaye da amare komai na k’asaita.”
Ahaka suna tafiya masu pics vedio harda y’an jarida, ”
Flash ne kawai ke haske Su tako ina.”
Hasken dayayi yawa ne yasa *hanna* kafafunta suka fara rawa danko kallon hanya sosai batayi. ”
Ganin haka yasa MG yasa hannu yaza gaya awaist d’inta,”
Batasan lokacin da ta kalleshi dasaurii, ba amma shi ko ajikin sa, hanya kawai yake kallo yacii gaba da tafiyarsa, ita kuma takasa d’auke idanuwanta daaga kansa. ”
Yasan tana kallonsa amma yak’ii juyawa,”
Sai can tadacii gaba da kallonsa can sunzo shiga event hall d’in yajuyo ya hure mata idanuwa, ”
Lumshesu tayi ta k’ara bud’esu akansa sannan takawar da idanuwanta kunya duk ta isheta.”
Ahaka suka shiga wajan gaskiya ba k’aramin decorating akayiwa wajen ba. ”
Farine soll Sai pink bolb,”
A haka har suka isa wajan zamansu suka Zauna, ”
Event yayi event Alokacin ummii suka iso,
Alokacin aka kirasu tsakiyan fili, suka sauko hannunsa mak’ale da nata ba k’aramin dad’ii ummii tajiba ganinsu haka,”
Alokacin su kilishi umma da sauran iyaye Suna tsaye afilin. ”
Sanda sukazo dabb Su sannan *hanna* tatsuguna k’asa tana gaidasu yayinda MG shima yabita ya tsugunna.”
Shima Yana gaishesu abin yamatuk’ar k’ayatar da duk mutanen dake wajan.” Hakan yanuna musu alamomi dayawa.”
Nafarko tanuna mutane yarbiyanta gashi na biyu yanda ta nuna wa mutane cewa samun mace tagari Yana daga Cikin abin da yakesa namiji gyara halayensa. ”
Yanzu kuduba yanda MG baiyi niyar tsugunawa ba amma ganin tayi hakan yasa yayi.”
Allah yasa muzama mata nagarii. ”
Ameen
Kasancewar tsugunawa wajan gaida nagaba ak’asar hausa abune maikyau wanda hakan ana samunsa ga yaro mai tarbiya yasa mahaifansu jin dad’ii da alfaharii da yaransu,”
Dad’ii ne yacika ummii na irin girmamawa da diyansu suka basu. ”
Sa hannu tayi ta dago Su duka Su biyun sannan ta rungume *hanna* tsam kamar mai shirin maidata ciki,”
Ganin haka kawai MG yafarqyi musu liqi da 1000 dubu dubu sabii, ”
Sannan labba ma tshigo itada afeeya suka jona,”
A sauran dangima sukabi bayansu, ”
Kowa liqi yake musu,”
Dakyar ummii tasaketa, Itama tahau yimata liqi,”
Waje yayi waje biki yayi biki. ”
Manyan mutane sun hallarq,”
Can na hango y’an BIBIYATA AKEYI FANS, hardasu ameen, aishatu g sabo, aisha ayuba, mmn hassan, maman waleed, Su asm’aul husna,
Su bintu abacha kam ba kantq tasa plate agaba Sai taga k’arshensa, ”
Sai kiyi saurii dan ummu sudais na jirankine ita takawa takesonyi,”
Su momy bayo kam andad’e afilin rawa Itada saudat.”
Kunsan bikin na manya ne Can na hango murjanatu gimbiya liqi kawai takeyi, ”
Maimunat da hajara ya’u aliyu haka kuka iya rawa😳
Maman twinx madai ba’abarta abaya ba dan tura twinx gefe tayi tashiga hidima.”
*Hanna* na godiya kuma tajii dad’inn halartar bikinta da kukayi😃.”

Intisar idan ka ganta Sai kace aljana dan Wani irin kyau tayi. ”
Batafin 10 minute bata wuce gaban MG ba tanayi tana karai raya,”
Amira kuwa anmak’ale itada ya jalal Sai soyewa sukeyi. ”
Balle hafsat da abuu yayi nisa.”
Tare da yaya jalal suka shigo fili suka yi barnar dukiya, yaya jalal yafice ya tafii ita kuma dasu labba hameeda da sauran kawaye rawarsu sukasha *hanna* tataso har fili tamusu liqi Sai dariya take tana annashuwa amma koda wasa bata yi rawa ba bbu yanda basuyi da itaba dariya kawai take musu tana liqi. ”
Sanda suka gajii kafin suka fita daga filin.”
Nan aka bukacii ganin ango da amarya kawai afilii Nan suka fito. ”
Bbu yanda MG baiyi sutaka ba amma bbu wanda yayi rawa acikinsu.”
Yau anga dunkum d’in amarya da ango banda murmushi bbu abunda sukeyi, ”
Amma bbu mai alamun fara rawa.”
MG ne ya bukacii abashi loud speaker, ba Tare da bata lokaciba aka miko masa,
Yajuya yakalli *hanna* yace. ”

_Kuyi hakurin jina shiru da kukayi jiya amma kubini bashi zuwa dare zan biyaku._

To be continued

Ur’s

*Z33yyb3rw3r*

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

 

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply