Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 60


Bibiyata Akeyi 60
Viral

Page 60

*
Zagaya d’aki yakeyi yaje yadawo.”
Yak’ara zuwa yadawo, sanyin ac ne yake ratsa ko ina ad’akin, amma kuma gumii yakeyi. ”
Haajiya suwaiba dake kwance, ganin mijinta na zirga-zirga duk yanda yanda taso tq jure abun yafaskara,” bata ta6a kallonsa cikin tashin hankali ba irinna wannan karan, ”
Dan dai duk damuwa bata hanashi bacci.”
Tashi tayi tadafashi tace, ”
Baban mufeedat lapiya naganka cikin wannan yanayi?”
Yanzu k’arfe 12:35pm darene amma kakasa bacci,”
Idan da wata matsala kafad’in mana aisai muyi tamaka add’u’a kokuma muyi sallah cikin darennann, mu roki gafara awajen ubangiji, ”
Kai da kanka kake tunasar damu iyalenka, cewa bbu wani abunda yafii k’arfinn Allah.”
Ganin yayi shiru baice komai bane yasa tacigaba da cewa ni idanma aikin minister d’in nanne kawai Kayi resining, wallhy tunda kahau mulkinnan samun nutsuwa ya k’auracex maka. ”
Da mamakinta
Gani tayi yajuyao ya riqe hannunta yazaunar da ita bakin gado,”
Shafo fuskarta yayi ya ce je kikiramun karimah ad’qkinta akwai zancenda zamuyi daku, ”
Tashi tayi tanufii d’akinta,” tasan ayanzu kotaje shashin karima ta kulle amma tasan batayi bacci ba, wayarta abud’e zata samu. ”
Wyarta tad’auka tayi dialing numb d’in da aka rubuta habibty, ”
Ana d’auka najii tace ziko d’akin babanku yanson magana dake.”
Gaban karimah ne yafad’ii tunda take da mahaifinsu bai ta6a kiranta a irin wannan lokacin ba. ”
Ahaka jiki bbu kwarii tatshi tanufii shashin babnsu.”
Da sallama tashiga d’akin dukansu suka amsa mata, kusada mahaifiyarta tazauna tayi musu sannu duka suka amsa. ”
Sanda tazauna nak’are mata kallo sosai sai alokacin na hangii tsananin kama dasukeyi da mahaifiyarta,”
Farace doguwa tanadakyau sosai. ”

Gyara zama minister yayi ya fuskancii iyalansa sannan yace,”
Kugafarcenii tabbas nasan abun da zan fad’a bazai muku dad’ii ba, amma kuma yakamata infad’a muku. ”
Shekara d’aya da watanni d suka shud’e,”
Ina office, ”
Sectery yakirani kam cewa inada visitor’s ban d’auki lokacii ba kasancewa yasanar danii way’anda keson ganina band’auki lokacii ba nace su shigo duk da cewa abun yabani mamaki.”
Senator ne shida shugaban y’an kasuwa sukazo nemana, ”
Cikin mutumcii da karramawa muka gaisa tareda y’an barkwancii da baza’a rasaba,”
Nan suka zauna Senator ke sanar danii munada muhimminyar maganane, ”
Tom alokacin ban fahimcii komai ba,”
Kawai dai nad’auka kan wani siyasa ne. ”
Munyanke shawara akan zqmu had’u da su a guest house na Senator.”
Anan muka had’u alokacin naga ashe munada yawa wanda za’ayi meeting d’in. ”
Ganinsu ahaka ya tabbatar mun cewa ba abin alkhairy bane,”
Koda nazauna suka fad’amun buktar su, da farko nak’ii amincewa,”
Kan cewa zan aikata abunda suka bik’ata, ”
Amma Daga baya idanuwana suka rufe kiriff da ganin kud’ii na aikata sa6on Allah.”
Tun kafin yafad’ii lqifinda ya aikata, karima tafara hawaye dan ta tabbata ba abuu ma dad’inn jii bane mahaifinta ya aikata. ”
Hajiya suwaiba da duk itama zuciyarta ta karye tace,”
Abban mufeedat wani irin abubuwane haka ka aikata? ”
Nisawa yayi yace munshigo da gur6ataccen maganii wanda ak’allah mutane samada d’arii biyu suka mutu ta dalilin shan wannan maganii.”
Dagowa yayi ya kalli iyalansa wanda duk hankalinsu atashe yake dan kukama sukeyi yace.” Wallhy da hannuna danni da kaina nasa hannu atakardar muka shigo da maganganuwan. ”
Idan baku manta ba shekara d’aya data wuce anyi ta mutuwa wanda aka alaqanta hakan da annoba,”
Mutane darii biyu sun rasa rqyukansu, samada darii biyu sun nakashe. ”
Kuka Hajiya suwaiba takeyi tana dukan k’irjinsa tana cewa Abban mufeedat meyasa?”
Meyasa bakayi tunanin bayin Allah ba awannan lokacii?”
Adah nad’auka cewa mujina adalin shugabane ashe bansan cewa ina zaune da wanda baya tausayin talakawansa bane. ”
Rungumeta yayi yana rarrshinta Kuka kawai takeyi banda karima da itama har shid’ewa takeyi dan Kuka.”
Share hawaye yayi yace suwaiba san zuciya ne yasa, ”
Wata k’asace suka karyar mana da farshin maganin Kan sunyishi ba ka’iida ba,”
Amma kuma abun mamakin Anan shine sukuma y’an kasar da suka sayar mana, suma sun sayar ak’asarsu amma kuma hakan bata faruu ba. ”
Maganii baya musu amfanii amma bai kashee wani kokuma naksar da wani ba.”

Alokacinne nashiga buncike, ”
Abinciken da nayi ya nunamin cewa amfanii sukayi da jinin al’ummar suakcii za6e.”
Sannan Abinciken nagano cewa mu biyu aka rufe bamusanda wannan al’amarii ba. ”
Ganin mutuwar tayi yawa yasa shugaban sojjoji na k’asa da k’asa wannan yaron wanda akeyin bikinsa,”
Yashiga buncike ton duk yagano cewa dasa hannu aciki kuma yasamu evidence, ”
Wanda alokacii d’aya zaigamo masu hanuu,”.
Hakan yazao kunnemu ne daga wajen shugaban sojjoji na k’asar Nan.”
Dan duk wani abunda zqmu yin da hannunsa aciki. ”
Sannan kuma yashaida mana cewa yagano da hannun shugaban kasuwa da custome aciki,”
Kuma yatabbata zai iya gano wa cewa da hannunmu aciki. ”
Bamusan maiya faruba yayi tafiya na y’an month,”
Acan dubai muka shurya kasheshi Allah baiyiba. ”
And yaban yadawo na wasu month muke tunanin sake Kai masa harii.”
Amma nafuto na fad’a musu cewa bazan iyaba, ”
Dan yanzu nikaina nafii buk’atar hukuncii fiyeda komai.”
Nafii buk’atar ayiwa way’anda na zalumta sakayya, ”
Ina tsoron gamuwata da Allah.” tashi yayi yabud’e wasu jakka Sannan yad’auko duk takardunda yake ciki ya miqa musu, ”
Da kunnena najii suna cewa wai zasu kasheni gwamma sikasheni Tun yansu,”
Su d’auke duk wani zunubinda nake dashi akansu. ”
Fargabata d’aya kada suce zasu ta6amun iyalina kuma nasan zasuyi k’akarin aikata hakan,”
Ki dauki y’ay’ankii kuje kada ku zauna.”
Inada wani gida acan gandun albasa, bansaya da sunana ba ku je can bbu mai sanin cewa kuna raye, ”
Kungq mufeedat bata k’asa idanna ce,” Kuje wajanta za’agane cewa kunfita daga k’asar dan kunsan ba kananun mutane bane. ”
Nabiyu gashi duk wata dukiyar dana mallaka tana cikin nan da takarduna da information na bankuna,”
Kada wani acikinku yasake amfanii da atm d’insa ga tsaban kudii acikin wancan jakar kuyita amfanii dashi, harsai randa kukajii cewa ankamasu Sannan kufito Kuyi rayuwarku Kamar kowa. ”
Kuka hajiya suwaiba takeyi sosai tace wallhy abban mufeedat bazan iya tafiya nabarka ba,”
Bazan iyaba idanma mutuwane nafii buk’atar namutu kusada mijina. ”
Girgiza matakai yakeyi yana a’a hajiya kitafii da yara kinga kinada k’ananun yara,”
D’gowa tayi ta kalli karima tace karima Ki riqe k’annanki da kyau dan Allah Ki musu tarbiya mai kyau, ”
Idan Allah yasa kwanan mu yak’are nida mahaifinki kuyita manq addu’a.” bayadda mahaifin karima baiyiba akan hajiya sawaiba tabisu ba amma takii, ”
Jakar kud’in yad’auka kirar dana ta kardiun ya nafii bayan gidansa yasa abayan wata mota vibe.”
Hajiya suwaiba kuma ta shiryawa d’iyanta kayansu a trolyn dukansu.”
Itama takai musu motan, ”
Ahaka tatashi abida dake bacci wanda bazata wuce 17 ba sai dan sa’ad dan 14. Da kuma y’an biyu hassana da usaina,”
Sai autansu kabir 7yr’s, ”
Karima tana Kuka Kamar ranta zaifita iyayenta suka turata amota,”
Duk sauran basusan maiyake faruwa ba, amma suma Kuka kawai sukeyii iyayen sukabii d’aya bayan d’aya suna rungumewa suna yiwa y’ay’ansu addu’ar nasara. ”
Sauran yaranma duk Kuka sukeyii banda kabir dayake bacci.”
Minister ne ya leqa ta window yabata wani photo yace, ba lallai abinda nashirya yatafii dai-dai ba, ”
Amma duk lokacin da Kuka shiga matsala kinemi tajikin pic d’innan inada tabbacin zata taimakeku.”
Kada Ki tada motar harsai kinga kirana yashiga wayarki. ”

Ahaka suna kallo babanta yawuce yatafii ta baban gate nan y’an sandan da suke tsaronsa suka takemasa baya.”
yana futa kuwa yaga abinda yake zato mutane ne acikin mota har uku agaban gidan. ”
D’aya ya dagwa yawa yakira sauran akan suzo ko za’asamu matsala ga Minister nan tanan k’ofar.”
Aikuwa duka suka tattaro zuwa nan alokacin Minister yadanna wayarsa dake aljihu yakira diyarsa, ”
Tana kallon kiran mahaifinsa ta tada motar ahankali tafice tabar anguwar.”

Shikuma sanda yatabbatr tabar anguwar ya juya yakoma, ”
Gabaki d’aya kansu yad’aure ganin yakoma.”
Yana shiga gida yakira senator, ”
Senator na d’auka yace dama nasan zaga sauko ma.”
Dariya Minister yayi yace kakarancenii abaibai, ”
Kasa tsaro ak’ofar gidana kana tinani zan gudu ko,
To Allah yafiaka, yana fad’in haka ya katse kiran.”

=============== wannan rana takasance ranar da mutane dayawa bazasu manceta ba, wasu takasance musu ranar farinciki wasu kuma takasance na bak’in ciki.”
Ranar intisar kwana tayi bata runtsa ba tsabar bak’in ciki da kishi. ”
MG kuwa shima hakane takasance anasa wajan amma shi saba’anin haka,”
Tsantsar farinciki da nishad’ii yake ciki kokad’an baisamu bacci ba sai 3:30 yana nafil fili na yiwa Allah godiya, nacika masa burinsa.”
Sai 3:30 yasamu ya kwanta bacci yayi wanda rabonsa da bacci mai da d’in haka shekara goma tunda yad’aura idonsa akan *hanna* ko kuma ince bai taba bacci mai nishad’in haka ba. ”
Sanda yamakara asallah, sai 6:00am kafinnan yafarka yayi sallah duk da haka bawqi baccin ya isheshi bane yana idarda sallah ya kwanta bacci.”
Dan jinsa yakeyi fayau Kamar wanda aka d’auke masa nauyii. ”
Itakuwa *hanna* anata wajen bazaka iya bambamce farinciki take cikiba ko saba’anin haka, amma dai tana cikin kewar mahaifanta na gaske,”
Dakyar bacci yad’auketa.”
Wajan minister kuwa da hajiya sadiya kwana sukayi nafil fili, sunata zuba ido suga abinda zai biyo baya amma shiru har garii ya waye bbu wanda ya runtsa.”
Sai karima da sun isa gidan tasa, yan kannenta dasuke bacci agaba kuka kawai takeyi, ”
Ahaka takwana bata ko runtsa ba,”
Ahaka abida ma ta kwana tana kallon yayarta, batasan mai yakeyi damunta ba, ”
Tatambayeta iya tambaya amma bbu amsa haka tazauna tazuba mata ido.”
Kawai suka kwana bbu bacci. ”

Iya sauka anyiwa Su *hanna* sauka, da safe abincii kala kala aka kawo musu na karyawa.”
Sai 9 MG yatshi
Haka kawai yaji yanson kallon *hanna* kiran labba yayi ta dauka, gaidashi tayi ya amsa kawai sayya fara kame kame, ”
Can kuma yadake yace,”
Inason ganinta ne Inason zan mata magana, ”
Dariya labba ta kumshe tace yaya yareema waye ita kuma,” tsaki yaja yace *hanna* adak’ile, ”
Yaya kakira wayanta mana.”
Bazan kiraba yace atakaice, Ki kawota ina garden ta baya kufito ta k’ofar baya.”
Yana fad’in haka ya katse wayar, ”
Ad’aki tasamu *hanna* . Nazaune abakin gado sungama waya da mama kenan,”
Kamo hannunta tayi tace zo kiji, ”
Injii mene?” *hanna* tatambaya bata jira amsar taba tacigaba da janta, ”
Wata k’ofa ta bud’e acewar *hanna* wannan k’ofar d’aki ne amma kawai taga, shuke shuke awajan,”
Abinda *hanna* ke matuk’ar so yasq bata kara tambayar ina zasu ba tabita. ”
Ganinsa yana nufosu yasa labba juyawa,”
Ita *hanna* batasanna tajuya ba, ”
Ya iso ya dad’e abayanta batasanma yazo ba,”
Kawai jitayi ankamo waist d’inta harta dakar kare zata kwala ihu yajuyo da ita suka kalli juna,”
Armless shirt ne ajikinza sai 3quater na army,”
Runtse idanuwanta tayi Ganinsa da singlet abin ba k’aramun dariya yabashi ba yanda ta tamke idanuwanta Kamar taga dodo.”
K’akarin kwacewa tafarayi, ”
Amma takasa saima k’ara matseta dayayi Kamar zatayi kuma tace,”
Dan Allah kasakenii bbu musu yasaketa,”
Taja da baya Sannan tace ina kwana, ”
Bai amsaba sai da ya zauna awata kujera dake wajen yace zoki zauna bbu musu tazo ta zauna,”
Kwanciya yayi akan cinyoyinta ya lumshe idanuwansa Kamar mai yin bacci. ”
Ad’arare take amma ganin ya rufe idanuwansa hakan bai hanata kare masa kallo ba.”
Kallonsa takeyi sosai wanda ita kanta batasan ta shagala akallonsa hakaba. ”
Aranta tana jinjina kyau irinna MG, tasan duk da cewa ita d’iya macece amma kyawunta ko k’ofar nasa bai kamaba.”
Ayadda take kallon labba tafito suffar larabawa sakk amma MG yafita kyau. ”
Ta shagala akallonsa muryarsa yadwo da ita Daga tunajinta jin yanacewa,”
Sweery kinsan mene? ”
Dubanta takai gun fuskar sa haryanzu still arufe,”
Girgiza Kai tayi tace A’a,”
Gyara zaman kansa yayi akan cinyarta yace, ”
Cinyanki na da dad’in kwanciya jinakeyi Kamar nakoma bacci akai.”
Gabaki d’aya maganarsa kunya tabata sai ta kasa amsa masa tace umm kawai, ”
Nayi bacci?” ya tambaya, ”
Umm Ta k’ara cewa,”
Kusan 10 minute kowa yayi shiru, ganin Kamar yayi bacci yasa tafara wasa da gashin kansa wanda gashin yadade yana burgeta, ”
Idonsa biyu jin yanda take wasa da gashin kansa Kamar susa yakejii,”
D’aga hannunta tayi ta kalli face d’insa still arufe tace bacci, ”
Tukunna yace,”
Nan kunya takamata duk atunanin ta yayi bacci ne. ”
Tashi yayi yazauna.”
Ta kalleshi tace kaga za’ayita nemana bari na tafii,”
Yi yayi kamar baiji ba Sanda tasake maiamaitawa, Sannan yace Dan wa aka kawoki gudannan? ”
Shiru tayi Kamar batajii ba, yace ashe bakison tafiya tunda bazaki amsa tambayata ba.”
Cikin jin kunya tace Kai, yace toh idan suka tambayeki yanda kike saikice musu ankawoki wajan wanda kike gidan dashi ne.”
Sake baki tayi tana kallonsa, ”
Rufe bakin yace mata ta juya ta rufeeshi kiriff, had’eda turo bakinta juyo da ita yayi yace mani kike turawa baki?”
Tuno ranar daya balle mata baki tayi yasa tayi saurin Girgiza Kai. ”
Ahaka suka zauna kusan 1hour bawani tad’in kirki sukeyi ba amma kuma kowannensu najin dad”in zamansu ahaka.”
Tashi yayi yace Tashi in rakaki y’ar dad’ii miji anzo wajen miji anmanta da mutane najira, ”
Shiru tayi bata bashi amsaba Dan tasan magana yake nema.”
Har sunzo bakin k’ofar tasakai tana niyar shiga yace baki jiba, ”
Juyowa tayi da niyyar jin mai zai fad’a mata kawai saijin bakinta tayi acikin nasa.”
Kissing d’inta yafarayi, duk yanda taso kokuwar kwacewa abun ya faskara. ” Dan kanta takahura tabarshi, Sanda yakusan 10 minute kafin yasaketa.”
Yana saketa da gudu tashige kofan,”
Yafii 5 minute kafin ya Iya jan jikinsa yabar wajan. ”
Itakuwa kasa shiga mutane tayi dan ganii takeyi kowa yaganta yasan maiyafaruu.”

K’arfe 4 kowa yagama shirin bud’ar Kai. ”
Nan aka fara gudanar da biki,”
Banda algaitu da kalangu bbu abinda yake tashi a fadahh,” *hanna* tasha alkyabba mai tsadar gaske sai MG shima Tashi shigar tasarauta ne, ”
Ahaka akayi budar Kai aka goma ango yabud’e kan maryar sa.”

To be continued

Ur’s

*Z33yyb3rw3r*

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

*Ka/kiyi aikin kirki domin duniya ba matabbata bane*

*Ka/ki guji hassada domin hassada kan Iya kawo gaba tsakanin al umma, Sannan hassada na cinye ayyuka.*

*Ka/Ki guji shiga hakkin mutane, domin hakan zai Kai ki/Ka ga halaka.*

*Yiwa dan uwanka kyakkyawan zato, ” domin hakan na Iya sawa kaima wataran amaka kyakkyawan zato*

*Nasiha ce*

================

_*Sawwama kawwama* ina tayaki farincikin kammala buk d’inki na *bani nayi kaina ba* Allah yabamu damar amfanu da abin alkhairyy dake cikinsa.”_
_Muna jiran sabon buk Allah yataimaka_

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply