Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 69


Bibiyata Akeyi 69
Viral

Page 69

*
Likitocii Basu dad’e akanta ba suka fito, suna fitowa wajen MG suka nufa. Babban liktanne yace, Major ka kwantar da hankalinka, she’s out off risk now, but tana buk’atar rest, for about 2hour’s danta razana.”
Haryanzu hankalinshi ba akwance yakeba.”
Tunaninsa jinin dayaganii ajikinta nameye. riqe hannun doctor yayi yace jininda take zubarwafa?” badai harbinta akayi ba?.”
Girgiza kai liktan yayi yace, tsoratan datayii ne yasa, mensturation d’inta yazo, a wannan lokacin, dake date d’in yakusa yasa jinin ya matso kusa, kuma dalilin tsorata datayii yasashi tsinkewa, amma bayan haka bbu komai, sai alokacin MG yafitar d numfashi yana furta Alhmdllhy kawai dan bbu abinda zai iya cewa.”
D’akinda take yawuce, yana bud’e k’ofar da sassafar yak’arasa bakin gadon, yariqe hannunta, itakuma tana baccinta, numfashinta nasauka ahankalii.”
Fuskanta yayi fayau, bakinsa yakai kan goshinta ya sumbata, yak’ureta da ido kawai.”
Wayrshice tayi k’ara, dube – dube yafara danshi baiyi tunanin cewa wayarsa na aljihunsa ba.”
Jin k’arar ajikinsa yasa yakai hannunsa aljihu, yana ta6awa kuwa yajita cirowa yayi, nan ake gayamasa meeting nanda 3hour,”
Kallon *hanna* yayi duk saiyajii bbu dad’ii, kasan cewaar dole yatafii kan lokacin yacika, hakan yana nufiin bazata tashii agabansa ba kenan.”
Wani d’an siririn tsaki yaja wanda saida yafito fili duk saiyajii ransa ya6acii dan baiso ace yarabu da *hanna* kona secound d’aya balle tanacikin wannan halin.”
Yakusan 1hour ahaka Jin kiran sallan magrib ya tuno ko la’asar baiyiba.”
Tashii yayi ya shiga toilet,yad’auro alwala, dake da sabon carfet ashimfid’e sai yayi sallan la’asar akai sannan yagabatar da magrib.”
Dake soldirer’s d’insama asibitin daa akawosu kenan yasashi fita yadubasu kowanne, wasu harsun farfad’o, wasu kuma haryanzu bbu alamun farfad’owa.”yana komawa d’akin da *hanna* take shida wasu sojojin da aka turo masa daga baya, had’uwa sukayi da abid dake zuwa shida matarsa da d’ansu d’aya.”
Ganin matar abid yasa shi, tafiya amma dakyar dan hankalinsa yanakan *hanna* shida abid suka juya suka tafii, Su uku suka had’a motocinsu da sojojin Su zuwa wajan meeting d’in.”
Sun d’auki awowi dayawa wajan meeting d’in, awajanne ake shaida musu cewa yanda aka musu da cewa nan da 1month akeso sukawo
k’arshen wannan terrorism d’in, d’an Sun kashe sojojin dayawa da musu mulki, a wannan karan suka kawowa MG harii wanda k’asahen dayawa bazasu iya taasashiba, gwara, Su fataucesu tun kafin dawowarsu.”
Ahaka Ahaka aka tashii a meeting d’in.” Alokacin *hanna* tayi kusan 2hour’s datashi, ganin tafarfad’o bbu MG awajan wani bak’in ciki yakamata wato bazai iyajiranta tafarka ba kenan?”
Zai tafii damuwarsa.”
Suna barin wajan bbu yanda basuyi da MG ba ko gida yayi ya, gani yakeyi kamar yayi shekara baiga *hanna* ba yasan aduk yanda take yanzu tafarka.” da d’an saurinsa ya shiga cikin asibitin ko soldirer’s d’insama bai jiraba.”
Yana bud’e k’ofa, idanuuwan sune suka had’u waje d’aya wani irin haushinsa ne yakamata.”
Hawaye tajii yana k’okarin zuwa Mata tayi saurin kauda kanta.”
Dasaurii yak’arasa yayi hugging nata tight har wani d’an nishii tayi,ganin matar abid awajen kawai sai kunya takamata, saketa yayi yanaso ya hango kwayar idanuwanta amma firr taqii dantayi k’asa da kanta.”
Hannunta yake murzawa alokacin yana tambauarta tacii abincii tace, d’aga kai kawai tayii, dan idan zatqyi magana to kukane Zai biyo baya.”
Sai Lokacin MG yalura da matar abid dake wajan, cewa yayi au namanta abid yana jiranki yana waje.”
Dariya tayi tace yaushe zaka tuna, aina lura idankana tareda matarka baka ganin kowa.”
Shiryawa tayi, sannan tajuya zata yiwa *hanna* sallama narai-narai tayi da idanuwanta tace dan Allah karki tafii, mukwana anan.”
A’adai gashinan yadawo nasan cewa tun d’azu dakikak’ii magana shii kike jira.”
Tana fad’iin haka tajuya tafice, *hanna* Tana ganin tafita tajuyar dakai hawaye nabinn fuskarta, kwanciya tayi tajuya bayanta, yazo dabb da ita yana Mata magana amma tak’ii kulashii, duk yanda yaso tamasa magana amma tak’ii, ahaka har tayi bacci.”
Sai kusan 2:00.am kafin tatashi, nan ma firr tak’ii ta mishi magana, Koda yamatsa sai tasa masa kuka.”
Zuwa yayi da niyyar yariqeta ya rarrsheta, tace ni karka ta6anii, wallhy nadad’e banga marar imanii irinkaba.”
Har zaka iya kashe raii wallhy saidai, kamaidanii gidanmuu.”
Runtse ido yayi dan yasan haka zata faruu.”
Bayadda za’ace taga mijinta yayi kisa kuma ta aminta dashi awawannan lokacin, gashi yanada tabbacin ko kokuwa mai k’arfii *hanna* bataa ta6a kallo ba.”
Ahaka yak’arasa tana kuka amma ya manna ta ajikinsa.”
Ba yadda batayi takwace ba amma kuma abun ya faskara,”
Kwantarda kanta tayi tacii gaba da kuka, furzarda iska mai tsafii kawai yakeyi, dan baison kukanta, zafii yakejii acikin zuciyarsa, kokad’an baison 6acin ranta.”
MG ayanda yad’auki abun ba haka yayi zato ba.”
Dan har akayi sallah bai runtsa ba *hanna* rikicii kawai takeyii.”
Duk yanda yaso yayi calming d’inta abun yak’ii haka ad’akin yayi sallah, daga ita harshi tun breakfast najiyane a cikinsu.”
Sai a d’akin yatashi yayi sallah Zuwa safiya dole yanemii sallama wajan likita dan bazai iya da rikicin *hanna* a asibiti ba.”
Zuwa 9 aka sallamesu, amota ko kulashii batayiba shikuma duk wani motsin ta yanakan idanuwansa.” Suna isa yace ta shiga tayi wanka, bbu musu tashiga tayi dan itama kanta wani irii takejin jikinta.” tana fitowa awanka taahirya, saiga matan abid da Mata shahid sunshigo, abincii suka kawo Mata tacii sai ita, MG ganin tacii abincin hankalinsa yakwanta.”
Sai alokacin shima yasamu yashiga wanka, yad’ansa wani abu abaknsa.”
Labarin abunda yafaruu harya karad’e duniya, yanzu haka ma, Su ummii sai neman layinsa sukeyi.”
Saida yayi wanka sannan yakunna phn dinsa wayan ummii ne tafara shigowa, d’auka yayi daga yanda ummii Ke magana kasan hankalinta atashe yake.”
Kwantar Mata da hankalii yayi yace Mata bbu abunda yasameshi, dakyar ya lallasheta yad’an Kwantar Mata da hankali.”
Haka ma mai martaba kowa idan yakira saiya tambayi *hanna* dan bbu wanda yayi zaton tana wajan abun yafaruu, kowa yabarii akan tana gida, shikuwa ganin haka yasa baifad’a musu ba dan baiso hanakalinsu yatshii.”
Intisar data kirashi kuka takeyi tsakanii da Allah dakyar yasamu tayi shiru.”
Ajiyar zuciya kawai takeyi, yanzu yarinyar nabawa MG matuk’ar tausayii, dan yasan tana sonsa sosai, shikuwa kosaau d’aya bai ta6ajin sonta bayaga na y’an uwantakaba, duk lokacinda akace wani abuu yasameshi, takanfii kowa nuna tashinn hankalinta.”
Yana tausayin duk wani mai kok’arin shiga yanda *hanna* take, yasan ko takalmin *hanna* saiya fishii soyuwa a’iidanuwansa, Koda kullun *hanna* zata ringa yanka neman jikinsa shidai yanasonta, akullum yanajin zafii idan yaga 6acin ranta.”
Shikansa yasan wannan jarabawace ta ubangijii, ance zuciya nasan mai kyautata Mata, amma shi nashi zuciyar har indai akan *hanna* ne ko munana Mata takeyii yanasonta.”
Nisawa yayi ya lumshe ido, afili yafurta insonki *hanna* har iya k’arshen rayuwata.”
Tashii yayi yanifii falo dan sake ganinta, Koda bata d’ago ta kalleshi ba yakanjii dad’ii aransa, yakanjii sanyii.”
Juyawa yaje zaiyi wayanshi tad’auki k’ara,”
D’agowa *hanna* tayi tadubeshi sannan takawar dakai, tad’anja siririn tsaki, kallonta matar abid tayi tace wani wajanne Ke miki ciwo?”
Girgiza Mata Kai tayi kawai ta kwanta, ganin ta lumshe ido yatsaya daga nesa yana k’are Mata kallo.”
Wani dad”ii ne yaziyarcii xuciyarsa ganin yanda dangin *hanna* suka damu dashi tun d’azu suke kiransa dan sujii lafiyarsa, duk abinda yashafii *hanna* yana mutuntashi yana bashi kimarsa.”

Komawa d’aki yayi yabarsu sunata hira, kiran sallah ne yafito dashi, masallaci yawuce, bayan yadawo baicii komai ba Saida ya tabbatar da cewa *hanna* tacii abincii.”

Kwana biyu MG duk yabii yarame yakuma lalace dan ko kollon yanda yake *hanna* batayi.”
Har zazza6i sanda yayi.”
Gashi saura 5day’s Su tafii war wanda mutuwa ko rayuwa, bbu wanda zaitafii kuma yayi tunanin cewa zaidawo.”
Duk wanda yatafii wannan yanada tabbacin cewa dawowarsa mai wahala, yariga da yasadakar,”
Acikin y’an way’annan kwanakin duk yanda yaso shawo kanta abun yafaskara,”
Ana washegari zasu tafii MG yazo d’aki yasamu *hanna* takoma sama danta dad’e da canja musu d’aki.” Da sallama yashiga, aciki ta amsa, ya nemi kusada ita yazauna kusada ita tashi zatayi yasa hannu yamayarda ita, kawarda kanta gefe tayi.”
Yasa hannu yadawo da kanta yace *hanna* plz kiyafenii, gobe da k’arfe 12:00am zamu tafii *hanna* bbu tabbacin dawwarmu, *hanna* kiyafeni, kitaimakmin kada na mutu baki yafemunba.”
Kitaimaka naga farin cikinki Koda sau d’aya ne.”
*Hanna* zaitafii da kunchii araina kasancewar nabarki cikin bak’in ciki.”
Kukane ya kufcewa *hanna* rugumeta yayi ajikinsa yana rarrashinta Haka kawai *hanna* ta tsincii kanta dajinn zafin tafiyarda MG zaiiyii, jitakeyi kamar tabishi, amma takasa nuna masa hakan.”
Ahaka suka wayii garii bbu wanda yarintsa yanajin sanyii jinta ajikin sa.”
Dasafe dakyar suka karya itadai bata sakee masaba bakuma tanuna tana fushi dashiba tana tsaka tsakiya,
Amma cikin zuciyarta tanajii zafiiin wannan tafiya so sai.”
Dakyar suka iya breakfast bbu mai walwala acikinsu.”
Shi MG damuwarsa yaga tasake amma hakan yagagara.”
Ahaka har lokacin tafiyarsu tazo ta, wasu daga cikin sojojin harsun fara tafiya.”
Ba’adade ba aka bukacii fitowar MG, idon hanna ne yaciko damm, kawarda fuskanta tayi kada yaga hawayen amma abun yafaskara sanda yaganii.”
Jawota jikinsa yayi yace plz kada kiyi kuka kada kisa natafii jikina bbu kwarii.”
Ytasansa yasa yashre Mata hawaye amma abun sai ahankali wasu nabin bayan wasu.”
Had’e bakinsu yayi waje d’aya yafara kissing d’inta, sumd’auki samada 20 minute ahaka, duk yanda MG yayi *hanna* bata hanashi ba, Dakyar yasaketa, yana maida numfashii, kasa had’a ido dashi *hanna* tayi tayarda ita yayi suka nufii hanyar fita, yazo dabb da k’ofa *hanna* tadamke hannunsa yajuyo tafara Girgiza masakai damuwarsa yajii maganarta amma abun yafaskara, rabonda yajii muryarta tun kafin tayi rashin lpy.”
Duk yanda yaso tayi magana tak’ii, kawai sai tasake hannunsa takoma dagudu.”
Ahaka yajuya yatafii.”
Yau *hanna* Kwanan Su MG biyu da tafiya, amma ko waya bbu dakira wayarsa kuma akashe,
Iya tashin hankali *hanna* ta shiga gabaki d’aya tadawo marainiya ta rame, tana kewar MG sosai, yau tatashi dason Jin kashin MG, kayansa ta bud’e tanabii d’aya bayan d’aya tana shanshanawa tana lumshe ido, wani diary ne yafad’o mai kyan gaske, daga alamu Labarin MG ne aciki.”
Tsintar kanta tayi da son karantawa, b’alle botill na jiki tayi sannan ta zuge zip d’in littafin, pics d’intane ya bayyyana acover na buk drin gabantane yafad’ii, tasandai wannan pic d’in yayi kimanin 10yrs bud’e shafin farko tayi. ”

_Kumin afuwa gobe ba lallai kujini ba, amma idannasamu dama zqku jini._

To be continue

Ur’s
Z33iiyyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*

_Bismillahirrahmanirrahim_

Writing by
© _Zaynab Bawa_
( _z33iiyyb3rw3r_ )

_Like my page on Facebook :::Zaynab BAWA novels_

Followed me on instagram ::::mhiz_z33iiyyb3rw3r

*Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace,” kuyawaita yimun salatii ranar juma’at.”*
*Kamar yanda gobe da kasance babban rana juma’at, Allah kabamu ikon yiwa manzonka salatii, ya hayyu ya qayyum ya ziljalalu wal ikram.”*

*Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace, ku ladab tarda y’ay’anku, da abubuwa guda uku.”*
*Yace ku koya musu son Annabinku, sannan ku ladabtar dasu da son mutanen gidan Manzon Allah.” Abu na uku shine ku ladabtar dasu da karatun alqur’anii.”*

================

_Ina kike aminiyar kwarai qawar albarka, kisani ina sonki ina alfahaari dake_ _*murjanatu(gimbiya)* wannan shafin nakine ke kad’ai.”_

================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply