Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 78


Bibiyata Akeyi 78
Viral

Page 78

*
Nisawa anty tayi sannan tace, najeeb nima zanso hakan dan karima ta cancanci asota, karima tahad’a duk wani halida za’ayi sha’awa to karima tahad’a shi, sannan xan taimaka maka harsai ka aureta ,wani farinciki ne ya lullube najeeb jin yanada kwarin guiwar wajen anty,
Nisawa anty tayi sannan tak’ara cewa amma yanzu Vanda ikon isarda Kai gunta harsai randa *hanna* tadawo.”
Cikin saurii najeeb yad’ago yadubii anty yace menene had’in *hanna_* aciki? Dahar za’ace saita dawo, girgiza Kai anty tayi sannan tace ba haka bane kada kamun guguwar fahimta, shiru yayi sannan yace toh anty menenen dalili? Kayi hak’urii najeeb bazan bazan iya fad’a maka dalilibq amma inaso kasan cewa tabbas dalilina mai kwarin gaskene, girgiza Kai najeeb yayi sannan yayi biting lips d’insa yace, anty kimin iso wajansu mama nizan Mata bayani, jijjiga kai anty tayi sannan tace, kayi hak’urii najeeb bbu abunda su mama zasuyii akai har indai bawai *hanna* bace tadawo, wani zafaffen numfashi yafutar sannan yace zanjirata ,zanjira dawowar *hanna* amma anty dan Allah kisa yaya yayiwa Abba magana, yak’aramun months akan way’anda yabanii, in sha Allah zanmasa magana sannnan zansan yanda zanyii na had’aku da ita amma kada ka mata maganar soyayya kawai shakuwa tashiga tsakaninku , itama kanta ba samun hankalinta zakayi ba, harsai *hanna* tadawo, runtse ido yayi yanajin zafii wai yaga abunda yakeso amma ace sai *hanna* tadawo.” Maganar anty ne takatseshi dacewa sannan kuma plz kada ka tambayeta ita wacece kokuma wanene iyayenta, kamin alfarmar wannan, jijjiga Kai yayi kawai sannan yace nqgode.” Murmushi kawai anty tayi sannan tace bbu komai, bai dad’eba yatashii ya mata sallama yatafii.”

K’arfe 8:00pm dai-dai, anty takira mama, hassana ce Wanda wayar mama ke hannunta tazo da gudu ta miqawa mama phn tana hakii tanacewa mama Ana kirankii, dasqurii mama takar6a sannan tayi riceiving, gaisheta anty tayi , mama ta amsada lpy ya yaran?”. Lpynsu klau cewar aunty, shiru tayi, nad’an wani lokacii, mama dake tana fahimtar yaranta akowanii hali suke tace, wata matsace, yanayinkii yanuna kinason cewa wani abuu, umhm uhmm dama mama karima nakeso inzo ind’auka takwanamun biyu, mama aiki yanamun yawa, shiru mama tayi sannna tace, fatee kina mace kice aiki yamiki yawa, shiru tayi sannan tace mama wallhy zama ni kad’ai ne yakemun yawa, mama kinsan su amal suna gidan kakansu, shiru mama tayi sannan tace fatee kinsan anama d’ayace bazan hanaki karima ba amma kikula da ita, godiya anty tayi sannan suka gama sallama.”
Ta ajiye wayan baifii da 10 minute ba, kiran *hanna* yashigo dasaurii mama ta amsa danta dad’e bayaji muryar y’artaba, kuma kota kirata baya shiga, gaisawa sukayi nan jikin mama yayi sanyii yanda tajii muryar *Hanna* tace *hanna* wani abunne yasamu abdullahin?” A’a mama bbu abunda yasameshi ,abokin sane yarasu, eyyer Allah yajikansa to DA amin *hanna* ta amsa Sun dad’e suna hira mama tana Mata nasiha sannnan sukayi sallama.”

Kilishine zaune afalo kana kallonta kasan tana cikin tashin hankalii, ” intisar na zaune agefenta, itama ranta abace, kilishine tace, shashashar yarinya tunfarko basanda nace miki kibarnii naje wajanda za’a jawo hankalinsa jikinki ba, kikacemun wai kinsan abunyii, gashi jiyaa yadawo ko sallama baiyiwa mahaifinsaba, balle mu musamu gaisuwa yakoma, idan kikace nabarki da dabararki yanzu me dabararkin yayimana?” Ai amfad’a abunda babba yahango yaro ko yahau rimii bazai hango ba.” Sunkuayrda Kai intisar tayi zuciyarta tana mata suya, itadai tanaso MG sosai kuma duk yanda za’ayi saita aureshi bazata taba barinsa ma wannan munafukar yarinyarba nisawa kilishi tayi sannan tace Yanzu haka tun shekaran jiya anakar6o maganii yayi aikii akansa sosai, sannan yace, harsai sundawo zanzuba musu a abincii, anan zasu fara samun sa6anii, kad’a kai intisar tayi tace, wallhy umma sune sai shagen taurin Kai sekiga anyii abun amma kamar ba’ayiba.”
Yanzudai mubar komai harsai sundawo tukunna.” Amma dai bazan fasa aika musu da abubuwa ba, amma yanzu kikirashi ki gaidashi tukunna a, kada kinuna masa komai, dato kawai intisar ta amsa.”

================

Yana isa yayi duk wani step dazq’abi Dan samun gawar yabii, tukunna, yasamu akabashii, ganin irin halinda yake ciki, yasa duk cikin soldier’s dinanna bbubwanda ya tunkareshi koda maaganane, damuwa awajen MG dolene dan yayi rashin abokin arziki, tunda ya isa wajan bbu Wanda yakula kuma bbu babu, KO magana kasa yinta MG yayi idanuwansa sun rine, barin yanda yashiga yasamu matar da yaran kuka kawai takeyii.” Gabaki d’aya ta zabge, iyayen shahid sunyii waya tun jiya akan akawoshi su binneshi dakansu, alokacin aka fara preparation nazuwa k’asar india dake asalinsa dan canne,”
MG yaso yakoma gida Dan sake kallon *hanna* amma abun bai yiwuba, tako Ina ka kalli sojoji zaka gansu DA farin kyalle d’aure a hannayensu. ”
K’arfe 1:00pm dai-dai jirgin sojoji da dama yatashi Dan Kai way’anda suka mutu k’asarsu.”
MG basu gama yin jana’iza na shahid ba saida dabb magrib, bayan sungama yanemii ganin matar shahid koda wata matsala shi zai wuce, yananan ne amma hankalinsa yana wajen Hanna, baisan wanii halii take ciki ba.”
Tare aka musu iso shida abid dan shima matarshii tana ciki. ” sanda sukayiwa iyayensa Mata naciki ta’aziya sannan suka wuce wajan matan, koda suka shiga sunsami, matarshi yanzu da d’an saukii saidai sharar hawaye datakeyii, kowanii lokacii, bayan yamata ta’aziya ne yake ce Mata ko akwai wani abune zai wucene, girgiza masa Kai kawai tayii.” Bai dad’eba yafitoo yakamo hanya dake jirginsu na sojojine yayi saurii sosai. ” cikin dare suka isa sosai, yana shiga d’akinda take yanufa, yana zuwa yasameta kwance bacci takeyii, sauk’e ajiyar zuciya yayi yakarasa wajanda take, jin yadda take numfashii dakyar yasa yakai Hannunsa jikinta zafii yajii rauu, nan hankalinsa yatashii, zazzabin yadawo kenan,”. Zama yayi kusada ita, jin zaman mutum yasata bud’e idanuwa komardasu tayi ta rufe, amma kuma tagane wayake kusada ita,”. D’agata yayi yace tashi muje kiyi wanka, yana fad’in haka yayi toilet da ita, wanka yamata sannan yafito yahad’a mata ruwan zafii, dakyar *hanna* Tasha sannan yabata maganii,” kwantarda ita yayi shima yashiga yayi wanka, yunwa yakejii sosai Dan tun safe bbu komai acikinsa.” Kitchen yanufa dan yasan yasan, baza’arasa abunda zai Ciba, yaban yad’anci ne yajuya zuwa d’aki kwanciya yayi a kusada *hanna* baidad’eba shima baccii yad’aukeshi.”
Bashi ya farkaba harsaida aka Kira sallan subh, sai bayan yayi yatashi *hanna* itama dakanta tashiga tayi alwala sanna tazo tagabatarda sallah dan yanzu zazza6in yasauka, Sallah tagabatar itama sannan fajitas zuwaga MG tace masa inakwana, murmushii yayi ya amsa da lpy, sanna tace ya hakurii Allah yajikansa da amin kawai ya amsa, sunfii 10minute bbu Wanda yak’ara cewa komai, kallonsa tayi sannna tace, idan garii yayi haske zanje gidan rasuwan, kallonta yakeyi ta kasqn ido yanda take maganar kamar akwai yanda yake Mata ciwo, yace ai suna can k’asqrsu, Dan iyayensa sun bukaacii akaishi can.” Can kaje jiya?” Ta tambayeshi d’aga Mata Kai kawai yayi, Aida baka dawo ba, kaga duk zasu zquna amma banda Kai, sa hannu yayi yajawota daga yanda take zaune yace, tayaya hankalina zai kwanta nabarkii awani hali uhum? Runtse idanuwa taxi sannan tace tom mukoma yau, saikin warke yace atakaice, dasauri tace nawarke muje kawai, zamuje amma sai zuwa yamma, zamu d’auki hanya yafad’a jin haka yasa bata k’aracewa komaiba.”. Yau jikin *hanna* dasaukii hakanne yasa suka shirts Dan zuwa India, k’arfe hud’u na yamma jirginsu yatashi. ”

To be continued

Ur’s z33iiyyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

*Manzon Allah SAW yace,” izha dakhala ramadana futihat abwabal jannat, agulliqat abwabannar, wa sulsulatil shqidhan.”* *(idan Ramadan wata mai albarka mai alfarma yashigo, Ana bud’e k’ofofin ajannah, sannan akan rufe na wuta, kuma akan mille shaidhanuu.)* *Ya Allqh Allah kasa mudace , ameen ya Allah.*

*Manzon Allah SAW yace, izha nasiya waj akhala au shariba ,fal yutimmu sawamahu, adh’amahullah,” (manzon Allah yace har indai kayi mantuwa kacii abincii ko kasha abinsha kana azumii kacii gaba DA azuminka Allah ne yaciyar dakai)”*

.

================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply