Bibiyata Akeyi Hausa Novel Hausa Novels

Bibiyata Akeyi 84


Bibiyata Akeyi 84
Viral

Page 84

*
K’arasawa kusada ita yayi yazauna, yace cutie kiyi hak’uri kinjii?” am srry, jijjiga kai tayi sannan tace bbu komai tak’ara komawa ta lafe akan kujeran.”
Haka yakasa futa dan tunaninsa d’aya, wani hali zata shiga idanya barta.”

kilishii ce zaune a bedroom dinta, waya takeyi tana cewa, wallhy nagajii da wannan yarinyar, duk abubwan da nakeyi amma abuu yacii tura, shawararki ta farkon kawai zanbii.” yanzu ki kirashi basai safiya ba, ahaukatarda ita, shiru tayi na y’an wasu dakikai sannan tace, to ai yanzu nagane, yanzu abunda nakeso kawai zuwa safiya, nafarka najii, ance tahaukace,” zuwa safiya zanturo miki da kud’in.”
Kashe wayar tayi tana hucii.”

Da daddare kuwa marshall ganin yanda jikin *hanna* yayi zafii zazza6i yarufeta, baisamu daman yin sallah ba.” kwana tayi ajikinsa tana kyarma, shikuma yana riqeda ita haka bai iya runtsawa ba.”
Da asuba dakyar yasamu ya kwaci jikinsa yayi sallah itakuma *hanna* ko sallah bata iya tashi tayiba.”
Kusan 7 yasauk’a kitchen yahad’a mata tea mai kaurii, yahau sama, duk yanda yaso *hanna* ta sha tak’ii, dan bakintama rawa yakeyi.” har 9:00.am *hanna* bata bud’e idanuwanta ba, zuwa wannan lokaci iya tashin hankali marshall ya shigeshi.”
Idanuwansa sunyiii jazirr, kamar qauta, hawayene kawai bai zuba a idanuwansa ba.” hakanma dan yakasance mai taurin zuciya ne shine yahanashi zubda hawaye.”
Sai 10:00.am kafin *hanna* tatashi, sai yazamana kamar ancire mata ciwon.”
Riqo hannunta yayi yace, yawwa cutie tunda kintashi, muje kisa wani abuu bakinki.” yatsine fuska tayi tace banfa yi sallah ba.” ok tom sha tea d’in da ke gabanki tukunna, ai lapiyanki klau baki fashin sallah, lalurine ko dear, gyada masa kai tayi, yad’auko cup d’in yana shirin kaiwa bakinta, wani irin juyawa kanta yafarayii, dafe kanta tayi saikuma tasake, tatsaya tana kallon sa.” kaiwa cup d’in bakinta yayi ta saka hannu ta bige cup d’in ya watse ajikinsa.” kallo yabita dashi yace dear why?” tsaki taja tatashi tayi hanyar waje, runtse idanuwa yayi.” kafin lokacin harta fita palour, dasaurii yatashi yabita, har yak’araso wajan ta, fincikota yayi yana cewa ina zaki je?”
D’agowa tayi ta sharara masa marii sannan tace gidan ubanka zanje, dasaurii tak’ara cewa nace gidan ubanka zanje, ta fad’a tana juyawa zata k’ara tafiya, mutuwar tsaye marshall yayi a’iiya saninsa *hanna* bazata iya aikata hakanba.” afili ya furta something strange is happening.” k’arasowa yayi kusada ita yajawaota yariqeta gamm, ihuu tafara tana kwararo masa ashar tana dukansa harda cizo, ganin abunna ta yawuce tunaninsa yasashi kalleta tabaya, yanufii shashin ummii hankali tashe.”

Kilishii zaune ad’aki sai zurga-zurga takeyi, ganin bazata iyayin hak’uri bane yasata d’aukan wayarta takira ta, tana d’auka ko gaisuwa babu tace nifa najii shiru.” haryanzu bbu wani labarii wannan matsiyaciyar bata haukace ba.” daga cikin wayar najii ance, kekuwa mai kikecii nabaka yana zuba?.” ya tabbatarmun zata haukace amma gaskiya bazatayi hauka tu6urum ba, dan suna yawan yin addu’a, eh kmadai menene tayi, inyaso saimu 6atarda ita.”
Ahaka takatse wayar.”

Yana shiga baisamu ummii apalour ba ad’aki yasameta da gudu yak’araso kusada ita cikin tashin hankali yafara cewa ummii *hanna* ummii *hanna* batada lpy, dasaurii ummii tamiqe ganin halinda d’annata yake ciki, dukda bbu hawaye afuskarsa, amma kuma cikin kwayar idanuwansa ta fahimci irin tashin hankalin yake ciki.”
Itama da saurin ta surii himarinta ta bishi abaya, danshi yarigada ya futa.”
Tsakanin shashin ummii danasu *hanna* danisa amma few minute ne suka kaisu.”
Bud’e k’ofan yayi suna shiga, aikuwa sukayi turuss ganin yanda jinii yake zuba jikin *hanna* ga baki d’aya tayi caka-caka da falon.”
Duk ta yayyanka jikinta da gilasai, jin bud’e k’ofa yasata juyawa, aikuwa tana ganin su, ta jefo glass na humra dake hannunta, tarewa marshall yayi da hannunsa, nan da nan, hannun yatsage jinii yafara zuba, dagashi har ummiin kanta sukayi yana zuwa kuwa yariqeta kamar wanda take jira ariqeta, tayii luuu tafad’ii hannunsa, sumammiya.” kuka ummii tafashe sosai tanayi tana magana.” futada ita mota mukaita asibitii.” cikin tsawa tace nace maka mufice asibitii.”
Waje yayi da ita ummii nabinshi abaya tsabar tashin hankali tunkafin yazo har an bud’e masa mota tsabar irin kirin da yakeyiwa sajen.”
Ganin marar lafiya yasa sajen yanufii asibitii direct.”
Suna isa aka karbeta ciwukan jikinta akafara, mata dressing, sannan aka ce tana buk’atan jini dan yazuba ajikinta sosai.”
Ajikin marshall aka eba aka fara k’ara mata.”
Dakyar yayarda shima aka masa dressing ciwonsa, dan yafii jin zafin ciwon jikin *hanna*, ummii Dakyar tasashi yakoma gida yaje yagayawa mai martaba, dan ita bazata iya tafiyaba, alokacinma jimawa kad’an tashare hawaye jimawa kad’an tashare hawaye.” Doctor yasanarwa da momy cewa *hanna* tana d’aukeda juna biyu na wata d’aya kacal, kuma sunyiii iya bincikensu basu samiii wata matsala akwakwalwarta ba.”
Kuka ummii tarushe dashi na tausayin *hanna* da kuma abunda yake cikinta.”
Roqon Doctor tayi da karya fad’awa marshall, dan batasan irin tashin hankainda zai shiga cikinba.”
Kwanan *hanna* biyu a asibitii amma abuu gaba yake dad’awa, ganin haka yasa ummii tayanke shawarar sanarda umma, aikuwa ranar sunshiga tashin hankali barinma hameeda da yaya jalal.” umma ne tahana fad’awa mama dan tana gudu mata tashin hankali.” lokacii d’aya ummii da marshall suka zabge dan kowannensu cikin damuwa yake.”
Idan kagansu zaka d’auka sune majin yatan.”
Ganin ciwon yak’ii warkewa yasa mai martaba yacewa affan yaje yad’auko modibbo, sukuma likitoci sun bada shawarar fita da ita wajan likitan kwakwalwa.”
Dasaurii affan yafito daga shashinsa, wuce kilishii yayi afalo tana zaune, kwala masa kira tayi, kai inazakaje?” umma wallhy abbane, yace ind’auko modibbo inkaishi asibitii, koda abunda zaiyii akan ciwon, matar yaya yareema,”
Gaban ummane yafad’ii, had’erai tayi tace maza jeka kad’aukomin intisar tana gidan hajiya salamatu, waro ido yayi yace umma, abban,,,, tsawa tadaka masa, kai da’allah rufamin baki, kaje kad’aukota tunda bawai guduwa modibbo d’in zaiyii ba.”
Fita yayi ransa yana suya, yana fita takira wayan kawarta, tace ke abu ynason kwabewa, yanzu kiyi saurii kafin yaronnan yaje yadawo, a6atarda ita kawai tabar k’asar ga baki d’aya sannan, sannan arufe bakinta kada hankalinta yadawo bazata iya bud’an baki tafad’ii daga ina takeba.”
Daga cikin wayan aka ce mata kinsan shifa baya aikii saida sharad’ii, kilishii tace koma menene nad’auka, yanzu fa ko 30 minute kada ak’ara takashe wayan.”

To be continued

Ur’s
Z33iiyyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL’S_

*Manzon Allah sallalahu alaihii wasallam yace, ku karanta suratul kahfii ranar juma’a, Allah zaicika maka haskenta har wata juma’ar, zaka kasance cikin haske da farinciki.”*

================

*Godiya masu kirana danjin mai jiki, Alhmdllhy jiki dasauki, siyama na amsa gaisuwarku tana godiya, nagode sosai queen najii dad’in, kulawarki sosai, Nagode all, Allah yabar k’auna.”*

.

================

Leave a Comment

No one has commented yet. Be the first!
Leave a Reply